Showing 39001 words to 42000 words out of 73884 words
matuk'ar gigita tashi da d'aga mishi hankali shine sunan nauwara sa'eed haruna da saleem
sa'eed haruna sune suka shigar dashi k'ara wayyo xan so kuga yanda fuskar Alhj salisu ta
koma saboda tsanani tashin hankali, d'aya daga cikin mai kula da office d'in shi ya shigo bayan
yayi mishi ixinin shigowa wasu files ne a hannun shi ya ajiye akan table d'in sannan ya d'an saci
kallon Alhj salisu ya ga baya kallon shi da sauri ya d'auko wata er K'aramar wani abu ya d'ora
kan table d'in Inda baxai gani ba ya bar office d'in da sauri yana fita daga office d'in ya d'auki
waya ya Kira wata number cikin k'asa k'asa da murya don kada aji shi yace "yalla6ai na ajiye
abin da ka bani " d'an shiru yayi alamar sauraren mai maganar can yace "ba matsala duk xa'a yi
abin da kace Allah ya baku nasara" yana gama fad'in hka ya mayar da wayar aljihu sannan ya
d'an wai waiga bai ga kowa sai ya juya ya tafi
wayar shi ne tayi k'ara da sauri ya dauka ya duba sunan d'aya daga cikin yaran shi ne da sauri
yayi picking
"what!!!!? "
Abin da ya fad'i da k'arfi sannan yace
"ta gudu kuka ce toh ina neman ku da gaggawa kuxo kaduna yau d'in nan akwai aikin da xaku
yi min mu had'u a guest house d'ina "
Yana gama fad'in hka yayi hanging up d'in wayar yana furxar da wani xaxxafan gumi nan take
ya kirawo Alhj lawan shana da yanxu sam basa shiri sunyi fad'a kaca kaca akan kud'in da bai
bashi yanda yake so ba suka yi baram baram sai yanxu ya nemo shi don shi kad'ai ne xai bashi
shawarar don hka sun gama magana kan karfe 8 na dare su had'u a guest house d'in shi don
su tattauna yanda xasu 6ullo wa wannan Shari'ar tunani sosai ya xurfafa sai faman had'a uban
gumi yake Duk da sanyin ac dake cikin office d'in daman ance komai nisan jifa k'asa xai dawo
********
Yana xaune a office d'in shi gaban shi wata er K'aramar computer ce yana jujjuya wa akan
kujerar duk abin da Alhj salisu ya ke fad'a da wayar da yayi da yaran shi xuwa kiran da yayi wa
Alhj lawan shana duk ya gansu kuma ya jisu wani murmishin mugunta ya saki MG abduljabbar
kenan
Tun da yaxo abuja ya fara bincike akan Alhj salisu har kaduna sai da yaje sau biyu company nin
su nauwara da ya koma nashi ta k'arfi da yaji yaje toh da yake kusan duk ma'aikatan ba k'aunar
Alhj salisu suke ba saboda rashin mutuncin shi da mugunta yasa shi abduljabbar bai sha
wahalar samun had'in kan su ba amman mutum d'aya hankalin shi ya fi kwanta wa dashi ya
fada mishi abin da yake so aikuwa nan take ya amince shine ya bashi er na'urar nan yasa ta a
Office d'in Alhj salisu da guest house d'in shi don yasan duk motsin shi da abin da suke shirin
aikatawa don yafi son ya samu kwararan hujjoji a hannun shi Kafin a shiga kotu
Wayar shi ya d'auka yayi Kira ba'a dad'e ba wasu yaran shi joseph driven shi da wani suka
shigo office d'in kallon su yayi tare da yi musu magana da abin da yake so suyi mishi sannan
yace
"yanxu xamu shige kaduna bana son wasa da shirme duk abin da na tsara haka xaku bi"
Lokaci d'aya suka had'a baki wajen cewa
"okay boss "
daga hka suka juya suka fita shima abduljabbar mik'e wa yayi ya fita daga office d'in , mota ya
shiga su joseph suma suka shiga Joseph yayi wa motar key suka d'auki hanyar kaduna
Yana fitowa daga masallacin da yayi sallahr isha'e shi da wannan d'aya daga cikin ma'aikatan
Alhj salisu mota suka shiga inda su joseph suke ciki shi ya nuna musu hanya har guest house
d'in Alhj salisu a farkon layin suka yi parking Abduljabbar ya sallami wannan mutumin mai suna
yusuf da kud'i masu yawa tare da yi mishi Godiya sosai sannan kuma yana buk'atar yaje kano
ko akwai wani abin da xa'a buk'ata yayi mishi alkawarin Insha Allah xai xo Sannan suka rabu
Duk wannan binciken da abduljabbar yake su abba basu da labari
en maganganu suka yi da su joseph sannan ya fito daga motar shi kad'ai ya nufi guest house
d'in ya tunkare shi ba shakkar komai a tattare dashi abin da ya d'aure min kai ganin mai gadin
ya bud'e mishi get har da gaida shi cikin girmamawa nace Lallai abduljabbar ya siyi shi kenan
kai tsaye inda nauwara ta ta6a xuwa har ta la6e ta saurari hirar su shi ma nan ya tsaya yaji duk
shirye shiryen da suke don ganin asirin su bai tonu ba bayan sun gama maganar tasu Alhj
salisu da Alhj lawan shana sai hajia binta suka fita daga falon suka bar yaran nasu su 3 a gidan
Wayar shi ya d'auko yayi wa su joseph waya ba 6ata lokaci suka shigo gidan bayan sunyi
parking d'in motar su a wajen gidan kai tsaye falon suka shiga xumbur wad'annan yaran Alhj
salisu suka mik'e tare da janyo makamin da yake jikin su babu alamar tsoro a tare da
abduljabbar da su joseph suka nufi inda suke wani naushi suka yi musu a ciki nan take suka
xube a k'asa cikin matuk'ar gala6aita sannan suka janyo su har gurin motar su ka shigar dasu
kai tsaye a cikin Wannan daren abuja suka nufa
Washe gari da mummunan labarin 6atan yaran shi suka tashi don hka duk sun bi sun firgice
saboda sune suka san sirrin gaba d'aya kuma Idan suka sha wahala xasu iya tona musu asiri
Lallai Wannan karan shegiyar yarinyar nan (wato nauwara) da babban shiri ta xo Cewar Alhj
salisu kenan nan suka fara binciken inda yaran shi suke da kuma Inda nauwara da saleem suke
6angaren su abba sun gama shirin su sai jiran ranar shiga kotu duk sun Duk'ufa da addu'a Allah
ya basu nasara akan Alhj salisu sun samu barrister wanda yasan aikin shi sosai shima yana
nashi binciken cikin K'warewa irin ta aikin shi
******
Ranar monday xa'a fara xaman kotu duk wani wanda ya kamata ya hallara a kotun an hallara
waje ya cika yayi makil da jama'a don sauraran wannan k'ara mai cike da cin amana tsantsa da
xalinci
A wannan rana Alhj salisu yayi nadamar abin da ya aikata sau ba adadi musamman lokacin da
ya tsaya a gaban kotu gashi suka had'a ido da ammi nauwara saleem da kuma inna da baffah
mahaifin shi duk jikin shi yayi matuk'ar yin sanyi bai ga alamar samun nasara ba sam
Toh dai a Wannan xaman da aka yi ba'a samu wasu kwararan hujjoji ba saboda su nauwara
basu da wata karfaffiyar hujjar su akan Alhj salisu don hka kotu ta d'aga k'arar xuwa 2 weeks
masu xuwa
Haka aka tashi daga kotun abin da ya ban mamaki shine me ya hana abduljabbar xuwa bayan
shi yake da kwararan hujjojin a hannun shi ......
Aishat A muh'd
[25/07, 09:56] Aishat A. Muhd: í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*K'ARSHEN WAHALA*
í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*written by*
Aishat A muh'd
*~Pg 81~*
Acikin satin nan biyu da aka basu xasu koma kotu sun Duk'ufa da addu'a sosai tare da cigaba
da bincike toh duk wasu binciken da suke basu samu wasu hujjoji ba don gaba d'aya
Abduljabbar ya bi ya tattara su a wajen shi kuma bai sanar da kowa ba kuma yak'i xuwa har
yanxu
Har aka sake shiga kotu xama na biyu babu wasu kwararan hujjoji kan dukiyar su ce tunda ga
takardun duk dukiyar su nauwara but sunan Alhj salisu ne akai balle axo batun shi yasa aka
k'ona gidan su har safah ta mutu da mai gadi don hka barrister di'n su nauwara shi ya nemi
alfarmar a sake d'aga k'arar en jarida sosai sun taru a wajen suna d'aukan rahoton wannan
Shari'ar mai matuk'ar d'aure kai da ban mamaki
Wani murmishin mugunta Alhj salisu yayi lokacin da suka had'a ido da nauwara wajen da take
ya nufa duk da ta tsorata da ganin hakan amman hka ta dake ta tsaya wani d'an iskan kallo
yake yi mata yace
"Wato ke ga shegiyar mara kunya koh, da ni xaki ja uban ki ma na cikin kabari yayi Kad'an balle
ke "
Sauke numfashi yayi sannan ya cigaba da cewa
"nasan xanyi nasara kuma ki shirya mutuwar ki ke da saleem kuma sai na auri uwar ki Kina
kallo Kafin ki mutu shegiya ke ga mai taurin kai xanga uban da ya tsaya miki "
"Hahahaha loser "
Yatsine fuska tayi sannan ta dalla mishi harara tare da cewa
"wlh kayi Kad'an sai naga bayan ka mugu axxalimi kuma da kake cewa sai ka kashe ni *a
rayuwa da mutuwa a hannun Allah take* sau nawa kake yunkurin kashe mu Allah bai yi ba
daman ance *d'an hakin da ka raina shike tsone maka ido* kuma Insha Allah sai na tsone maka
idanun ka gaba d'aya da ikon ubangiji ai xalinci baya dore wa maci amana butulu" Sam bai yi mamakin abin da nauwara tayi mishi yasan xata fad'i abin da yafi hka ma ba
K'aramar mara kunya ce ba maganganin ta sun 6ata mishi rai amman da yake d'an duniya ne
sai ya maxe Ya nuna ta da hannu yace
"xaki gani? "
Murgud'a mishi baki tayi ita ma tace
"xa dai ka gani wlh "
Tana gama fad'in hka taja tsaki tare da juyawa ta tafi abin ta shima tsakin yaja tare da cewa
"yanda na kashe uban ki har lahira kema Hka xaki bishi "
Yana gama fad'in hka ya juya ya shiga mota suka tafi, kash! rashin sani yafi duhu inji malam
bahaushe da yasani bai kula nauwara ba har sunyi magana haka ba saboda d'an leken asirin
abduljabbar yana gefe yana d'aukan su video a waya ya tura wa abduljabbar ta what's app
sannan ya tafi
Hka su nauwara suka koma gida cikin rashin k'warin gwiwa amman sun sake damarar sake
bincike na sosai
Bari na waiwayi 6angaren abduljabbar naga ko me yasa yak'i xuwa
*******
Yana xaune kan kujera yana sanye da white d'in three quarter da maroon di'n riga mara hannu
irin ta shan iska fuskar nan tashi d'auke da Murmishi laptop d'in shi tana kan kafar shi yana
sarrafa ta cikin kwanciyar hankali yana kur6an xaxxafan coffee yana kallon duk yanda ta
kasance a kotu yana d'an murmishi wani lokacin har d'an darawa yake Idan yaga yanda Alhj
salisu yake hararar nauwara yana jifan ta da kallon tsana k'arara
Shigowar message yaji a cikin d'aya daga cikin wayoyin shi dake xube a gefen shi hannu yasa
ya d'auka ya bud'e password d'in wayar sannan ya duba cikin what's app nashi yaga videon aka
turo mishi bud'e wa yayi ya nutsu yana kallo murmishin mugunta ya saki tare da furxar da wani
xaxxafan huci a hankali yace "d'an iska xaka san baka da wayo wlh dole wannan Karon na uku na bayyana don na nuna
maka kai k'aramin k'waro ne "
D'an turo ya saki tare da rufe laptop d'in shi ya d'an kwanta kan kujerar yana kallon wani film a
mbc 2 wanda suke yanxu mai suna death race
Lokacin da suka xo da yaran Alhj salisu abuja da farko k'in fad'in komai suka yi sai da suka ji
wahala kamar xasu mutu sannan suka fad'i komai sosai abduljabbar ya gigita da jin wannan
rashin imanin irin na Alhj salisu kuma suka yi alk'awarin fad'in gaskia a kotu amman duk da hka
sai da abduljabbar ya gwara musu kawunan su saboda tsabar 6acin rai tuni suka suma saboda
tsabar axaba maimakon a k'wara musu ruwan sanyi su farfad'o amman ina ruwan xafi
abduljabbar yasa aka xuba musu sai da yaga sun farfad'o sannan ya fita daga d'akin duk sunyi
bak'i sun rame tsabar axabar da suka sha
Kuma yana sani yak'i halartar kotun don ya fison su d'an sha wahala sannan ya bayyana don a
ganin shi yanke hukunci lokaci d'aya basu sha d'an wahala ba baxai yi mishi kyan gani ba
kuma ya fison sai Alhj salisu ya sawa ranshi samun nasara daga K'arshe ayi mishi kwaf d'aya
Tun ana gobe xa'a yi xaman kotu na K'arshe abduljabbar ya shigo kano dashi da amintattun
yaran shi joseph da mubaraq tare da yaran Alhj salisu a d'akin da yake punishment di'n yaran
shi a d'akin aka xube yaran Alhj salisu sannan ya nufi part d'in su ya bar Joseph da mubaraq
suna gadin su duk da wajen a rufe yake
Yana shiga jiddah ta taso da d'an gudu ta rungume shi tana murnar ganin shi don ya dad'e bai
xo ba don hka yana wanka aka shiga biyan bashin k'wanakin da ba'a tare, ranar yini yayi a gida
yana huta wa tare da xuba soyayya da jiddah yinin farin ciki yayi ba wanda yasan yaxo Kano
saboda ya fison su had'u a kotu gobe..... Washe gari misalin wajen karfe 10 na safe kotu ta cika da mutane ga en jaridu suma kallo d'aya
xaka yiwa su Alhj salisu kasan suna cikin tsantsar farin ciki wannan Karon har da hajia binta
matar Alhj salisu da baban ta Alhj salisu har da ladi (wadda Alhj salisu ya kai ta gidan su
nauwara don ta dunga yi musu aiki a xahiri)
Su nauwara kuwa duk jikin su a sanyaye Har da barrister di'n don basu da wata shaida mai
k'arfi sai kame kame amman duk da hka basu karaya ba sun dogara ga Allah sai addu'a suke a
cikin xuciyar su
Karfe 10 dai dai aka fara Shari'ar su nauwara nan aka shiga tafka tambayoyi tsakanin barrister
di'n su nauwara da nasu Alhj salisu har xuwa lokacin da aka tattara wa alkali bayanai aka bashi
duk anyi tsit ana jiran hukuncin da xai yanke
Har alkalin ya bud'e baki xai yi magana kenan aka bud'e kofar aka shigo gaba d'aya kallo ya
koma kan kofar don ganin wanda ya shigo, nauwara ma da kanta yake kallon k'asa ta d'ago
kanta tare da kallon kofar ganin yanda gaba d'aya mutanen cikin kotun hankalin su yayi kan
kofar shigo wa.....
Aishat A muh'd
[25/07, 09:57] Aishat A. Muhd: í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*K'ARSHEN WAHALA*
í ¼í½€í ¼í½€â˜˜â˜˜í ¼í½€í ¼í½€
*written by*
Aishat A muh'd
*~Pg 82~*
Gaban ta ne yayi mugun fad'uwa ganin bayyanar Abduljabbar sanye yake cikin kakin shi yayi
kyau kwarjinin shi ya cika wa mutane kai tafiya yake cikin kasaita har ya k'araso cikin kotun
gaba d'aya mutanen cikin kotun binshi suke da kallo suna mamakin mai ya kawo wannan
babban sojan mai muk'amin MG kotu xama yayi tare da had'a ido da barrister di'n su nauwara
ya kashe mishi ido d'aya Jijjiga kai barrister yayi tare da sakin wani murmishin mugunta (na ce
toh shi wannan abduljabbar d'in sai kace wani aljani yana abuja har yasan barrister di'n da xai
tsaya wa su nauwara)
A karo na biyu alkali ya gyara xaman glass d'in shi a ido ya bud'e baki xai yi magana kenan
barrister kabeer Ya nemi alfarmar xai gabatar da hujjar shi ta K'arshe nan barrister di'n su Alhj
salisu yak'i yarda da hakan amman ina har alkalin ya bashi wannan favour di'n xama yayi cike
da takaice ya kallo abduljabbar ai kuwa ya kashe shi da killer samiling sai da yaji d'an tsoron
abduljabbar kuma yana kula da kashe idon da yayi wa barrister kabeer
Nan fah ya shiga gabatar da hujjojin shi har da bawa nuna jakar da nauwara ta yarda da ita
wanda Kaf takardun dukiyar su yana ciki nan alkali ya kar6a ya ajiye a gefen shi lokacin da
nauwara ta ga jakar nan sai da gaban ta ya fad'i saboda tsabar farinciki don ta tabbatar xa'a
samu hujjoji akanta
Ta 6angaren Alhj salisu sun d'an fara tsorata musamman yanda suka ga lawyer di'n su ya kasa
ta6uka komai basu k'ara tsinken wa ba da al'amarin sai da suka ga Shigowar yaran su a
matuk'ar gala6aice saboda tsabar firgita sai da Alhj salisu da hajia binta suka saki fitsari a
tsayen sai jin Fitowar shi suka yi yana bin kafafun su tuni jikin su ya fara rawar shoki
Wani murmishin mugunta abduljabbar ya saki da ya Kalli su Alhj salisu yanda suka kid'ime tare
da gigicewa rashin gaskiya ya bayyana k'arara a fuskar su, babu gardama yaran Alhj salisu
suka bayyana komai tun daga lokacin da suke bibiyar Alhj sa'eed don su kashe shi basu yi
nasara ba sai lokacin da xai je kano wurin aminin shi suka markad'e su a mota sannan suka
sace ammin su nauwara suka sawa gidan wuta don su nauwara su mutu sai kuma d'aya ce ta
mutu ya umarce mu da mu binciko sauran mu kashe su da muka gansu sai muka bi ta kansu da
mota muka gudu............. Duk suka sanar da komai
Gaba d'aya kotun tayi shiru sai shashshak'ar kukan mutane saboda tsabar tausayin su nauwara
bayan sun gama fad'in komai su Alhj salisu Alhj lawan shana da hajia binta ladi suka fara ihun
cewa k'arya suke musu sharri ne
Wani kallo da abduljabbar ya watsa musu sai da sukayi shiru ba shiri don ba k'aramin kwarjini
yayi musu ba K'arshe kuma da kanshi abduljabbar ya nuna wa alkalin videon da Alhj salisu
yake fad'a wa nauwara xai kashe ta ita da saleem kamar yanda ya kashe