Showing 9001 words to 12000 words out of 73884 words

Chapter 4 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

536

shi dakyar bacci ya dauke shi.

Husna kuwa tana fita part d'in su ta shige tana kuka sosai kan kujera ta fad'a tana kukan a haka
Yah Abdullah ya shigo ya rarrashe ta wani mugun xaxxa6i ne ya rufe ta nan da nan sai da
mamee tayi mata allura tare da bata magani sannan ta gasa mata jikin ta, sai da husna tayi
k'wanaki uku sannan ta warware ta cigaba da sabgogin gabanta.
Tun da ga ranar bata k'ara kula Inda Yah ibraheem yake ba balle har ta tsokane shi ya jibgi
banxa, ta fita harkar shi k'wata k'wata.

Ana cikin hka ne su husna, Ilham, raudah da fadila suka kammala primary school, lokacin da
result ya fito Yah Abdullah ya xa6a musu wata privet school mai kyau da tsada amman don
mugunta irin ta Yah ibraheem haka ya shiga ya fita sai dai akai su bording school kuma dukka
iyayen maxa suka amince da hakan don hka dad'i ya ishi ibraheem don yanxu baya samun cin

xalin husna don ta fita harkar shi, yayin da 6angaren su husna, Ilham, raudah da Fadila, Yah
Abdullah bai yi musu dad'i kuma basu da yanda xasu yi don hajia maamaa ce ta tilas ta su
Abba don idan abu ya faru toh Indai ya fad'a wa hajia maamaa Shikenan ya xaunu.

Ranar da xa'a kai su school d'in da sassafe suka shirya angama had'a musu komai husna ta fito
da gudu daga part d'in su xata je d'akin Yah Abdullah su yi sallama suka hadu a hanya cikin
dariya ta ce
"Wow Yah Abdullah kayi kyau wlh "
Kallon jikin shi yayi yana murmishi yana sanye da yadin kufta bak'i abin ka da farar fata ba
k'aramin haska shi yayi ba cikin murmishi yace
"ngde my cwt sister "
Ya cigaba da cewa "yanxu sai ina? "
Tana yamutsa fuska tace "xuwa xanyi mu yi sallama da kai don har an xuba kayan mu a mota "
Har yanxu da murmishi kan fuskar shi yace "ae ni xan kai ku"
Tsallen murna ta fara yi yana kallon ta yana mata dariya, a lokacin Ilham da raudah da fadila
suka fito tare da sauran en gida an rako su Yah Abdullah yana xaune a seat d'in driver yayin da
husna take xaune a front seat sai Fadila Ilham da raudah suke xaune a bayan motar bayan
angama yi musu nasihohi sosae kan suyi abin da kai su ban da shiririta sannan kuma suka yi
musu addu'ar sauka lafia, Yah Abdullah yayi wa mota key suka fara tafiya a dai dai bakin gate
husna ta had'a ido da ibraheem yana xaune kan bike d'in shi rik'e da key di'n mashin a hannun
shi daman sometimes yafi amfani da mashin akan mota wani shegen murmishin mugunta ya
bita dashi hararar shi tayi tare da kau dakan ta da sauri daga barin kallon shi a xuciyar ta tana
cewa ba dole kayi mana murmishin mugunta ba tun da ka tura mu bording mugu axxalimi kawai
ta fad'i tana Murgud'a baki kallon ta yah Abdullah yayi yana cewa
"ke dawa kike Murgud'a baki? "
Dan murmishi kawai tayi tare da cewa "ni da Yah ibraheem ne da yake min murmishin mugunta
"
Dariya kawai su Yah Abdullah suka yi mata, cikin nutsuwa yake driving ya dau hanyar da xata
kai su school d'in.........





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:29] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGANTAKAR XUCI* 🍃

Written by

Sumayya salees sadeeq



*&*



Aishat A mu'hd







*Page 13-14*







"Suna shiga skul direct ya Abdullah ya nufi office d'in principal dasu, gaba daya jikinsu yyi sanyi,
ba kamar husna da dakyar take d'aga kafarta dan jitayi ta mata nauyi. Ya Abdullah bai sha wuya
ba dan dama principal din kawar momy ce tasan da xuwansu a wannan lokacin.

"Farar mace mai dan jiki bata da fara'a sosai, fuskarta sanye da farin glass wanda xamu kirashi
da medical,xaune take a babban office d'in ta wanda yaji kayan alatu, principal hajia kande
kenan. Kallon kallon suke a tsakaninsu da alama akwai magana a bakinsu, durkusawa sukayi a
kasa yah Abdullah ya xauna a kujerar da aka tanada dan bak'i

"Taunar jingum take irin na yan dunia, kas-kas ta kalli su husna da suma d'in ita suke kallo,
murmushi tayi ta maida kallon ta ga ya Abdullah,fuskarta dauk'e da murmushi ta kira sunan sa
dan tasan sa. Abdullah ko? Murmushi ya Abdullah yyi "eh nine hajia" gaskia ka girma sosai,
lokacin dana sanka ai baka fi waccen ba ta nuna husna da hannu" daria yyi mara sauti dan jiyay
kunya ta kamashi, xata masa tijara a gaban kannensa,"eh hajia lokacin da dadewa kam".

"Shiru tayi ta fara rubuce - rubuce a wasu files sannan ta fara magana, tana kallon su rauda da
sunyi wiki wiki da ido kamar shege a rabon gado,"xa'a kaiku kaiku hostel daya amma class ba
daya ba, ke husna da ilham kuna js1A fadila da rauda a js1C"a hankali ta daura xancen ta, "nan
boarding skul ce duk da private ce Amma akwai dealing, dole kuyi respect ga wadanda suka
fiko aji, and sai kunyi hakuri dan rayuwar ba irin wanda kuka saba bace". Gaba daya jikinsu ya
fara bari dan fargaba husna uwar tsoro har an fara kuka,yah Abdullah jiyay kamar ya koma da
kannensa dan yaji abinda hajia kande tace, shi kam baya bukatar husna tasha wuya a rayuwar
sa, ko menene dalili ku cigaba da bin mu xakuji yarda xata kasance.



"Hajia kande ta kwalawa Messenger d'in ta kira, da sauri ya shigo ya baje a kasa, gani hajia.
"yawwa ka kwashi kayan yaran nan ka kaisu rahmat hostel corner ta karshe" , to hajia an gama
ya mike ya fice.




"Hajia kande ta kalli ya Abdullah da jikinsa yyi sanyi gaba daya tayi murmushi, "ok Abdullah
xaka iya wucewa gida nasa a kai kayan su hostel sai su wuce cikin skul" ok hajia mun gode" ya
fada ya mike suma su fadila suka rufa masa baya.




"Suna fita ya Abdullah ya nufi motarsa ganin messenger na jiransa, boot d'in motar ya bude
suka fara dibar kayan suna saukewa kasa, ya Abdullah komawa yyi wajen su husna da suka
durkusa kasa suna kuka. Jiki bbu kwari ya durkusa shima yana kallon su kamar yyi hawaye,
"kuyi hakuri kannena, menene abin kuka,? Boarding akwai dadi sai kun xauna a ciki xaku gane
hakan, ni dai fatana daku banda wasa, ku dage a karatun ku kunji?" gaba daya suka daga kai
alamar eh," yawwa my sisters, xamu dinga xiyaryar ku akai akai basai lokacin visiting ba"a
hankali ya Abdullah ya gama kwantar musu da hankali har suka saki ransu, an gama shiga da
kayan su dan haka suma suka tashi xasu tafi, a nan kam suka kara tsinewa ya Ibrahim a xuciar
su dan shi ne silar rabasu da gida.




"Juyawa sukayi suka fara tafia suna waiwayon ya Abdullah,husna ce ta juyo da gudu ta
rungumeshi ta kara fashewa da kuka, wayyo ya Abdullah jiyay wani abu ya tsarga masa tunda

ga kafarsa har kai, wani kasala yaji ya saukar masa a lokacin, ilham na kallon su har irin shock
d'in da ya Abdullah yyi a hankali ta dauke ido tana tunanin dangantakar xucin dake ranta.




"Da kyar ya raba husna da jikinsa ta nufi wajen su rauda suka shige cikin makaranta.




"Wani irin tuki ya Abdullah keyi yana tafe yana share hawayen dake xuba a fuskarsa, lallai bai
taba tunanin haka ya shaku da husna ba sai yau, gaba daya tunanin ta ya addabi brain d'in sa
ya kuma tuna a halin daya barta, sosai ya Abdullah ke kuka kamar karamin yaro, dan dama ba
karamar dauria yyi ba a gaban su bai xubar da hawaye ba, speed ya kara dan gani yake gidan
ya masa nisa, Allah ne ya kai Abdullah gida lpy. Tunda ga horn gate man ya tsorata dan haka
ya leko, ganin Abdullah yasa shi wangale gate d'in, bai gama budewa Abdullah ya cusa kan
motarsa ciki ya ajiye ta a fusace ya bude kofar ko arxikin rufewa bata samu ba ya nufi part d'in
shi dan bayasan haduwa da kowa a yarda xuciar sa ke xafi kadaici yake bukata.





"Gate man baki ya saki yana kallon ikon Allah,ganin Abdullah a wannan yanayin dan bai taba
ganin sa a haka ba, Bayan ya rufe gate d'in ya nufi motar Abdullah ya rufe.




"Abdullah na shiga room dinsa ya shige toilet dan wani xafi yake ji yana ratsashi, bayan ya fito
ya baje a bed dinsa yana kallon ceiling, rungumar da husna ta masa ya tuna, murmushi yyi ya
shafa sumar kansa yana tunanin dangantakar xuciarsa. A hankali yaji nutsuwarsa ta dawo dan
haka ya nufi part d'in momy dan shaida mata ya dawo. A xaune ya tarar da ita ta buga tagumi
tana tunani, murmushin takaici Abdullah yyi dan yasan dalilin tagumin momy, shi kansa ji yay
gidan ya masa shiru bbu dad'i dan sun saba da hayaniyar yaran. Sallama yyi ya k'arasa jikin
momy ya d'aura kansa a kafad'ar ta, juyowa tayi da Jan ido da alama itama tayi kukan,
Murmushi Abdullah yyi ya kalli momy yana mata daria kasa kasa, "momy kuka kokari?" hararar
sa momy tayi" eh shi nayi kamar yarda kaima kayi "kallon momy yyi da mamakin yarda akai ta
gane yyi kuka, ta lura da hakan dan haka ita ta fara bashi labari," ina jikin barrander naga
shigowarka a fusace har kana neman buge gate man, ga fuskarka da idon ka sunyi ja suma,
ban dauki tafiar yaran nan da wani mahimmanci ba amma sai daxu da kuka tafi na kuma
tabbatar nida ganinsu sai dai naje wallahi Abdullah a nan hankali na ya tashi, gaba daya na

kasa sukuni"share hawayen fuskarta Abdullah yyi yana mai jin tausayin momy a ransa.



"Ibrahim kwance a dakinsa wanda ya kasa sukuni tunda su husna suka bar gidan, bbu irin
tambayar da maamaa bata masa ba akan ko bashi da lpy ne amma yace bbu komai, tunani ya
tafi na dangantakar xuciar sa dashi kadai ya barwa kansa sani. Hajia maamaa bata hakura ba
dan haka ta kuma takowa dakin Ibrahim dan rarrashinsa ya fita yaci abinci gashi chan xai
daskare. Da sallama ta shiga dakin ta xauna a gefen bed din sa wanda ya tafi duniar tunani
baisan da xuwan maamaa ba. A hankali takai hannu ta taba fuskarsa, dago kai yyi ya kalleta
fuskarta dauke da damuwa, sai yaji shima gaba daya bbu dadi. Tashi yyi xaune ya jin gina da
gefen bed bed din yana kallon maamaa, "haba Ibrahim mai kake so ne haka, mai ya dameka?
Yau fa kamata ka hada mana party a gidan nan sbd ja'irar yarinyar nan bata nan ka huta da bari
bari, wani kallo ibrahim ya watsa mata dan gaba daya maganar maamaa ba dadi take masa ba.
A kufule ya tashi ya nufi wardrobe ya chanja kayan jikinsa, riga da wando yasa na shadda ash
colour a gurguje ya shirya duk maamaa na xaune tana kallon sa, key d'in motarsa ya dauka ta
kalli maamaa," sai na dawo "baijira tacewarta ba ya fice daga dakin. Tunda Ibrahim ya fita ya
rasa ina xai nufa, skul ya shiga dan ya hadu da friends ko ranshi xaiyi dadi.






Kuyi hakuri da wannan fans har Allah ya bawa sumy lpy mu daura a inda muka tsaya.




Sumayya salees sadeeq



&




Aishat A mu'hd
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃

*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 15-16*






Yinin ranar gaba d'aya su husna basu da kuxari sun yi jugum jugum gaba d'aya kewar gida ta
dame su, husna a xuciyar ta Allah ya isa kawai take yiwa Yah ibraheem mugu kawai kuma
yatasan duk saboda tsanar ta yasa ya nema musu bording, ji tayi wani bak'in ciki ya sake kama
husna a cikin xuciyar ta tsanar Yah ibraheem ta sake ninkuwa acikin xuciyar ta hannu tasa ta
goge hawayen fuskar ta tare da gyara kwanciyar saman bed d'in da suke, Allah sarki Yah
Abdullah bawan Allah xanyi kewar ka, ta furta hakan a Hankali tare da k'ara kudundune jikin ta
dakyar bacci ya d'auki husna.

Haka a gida Yah Abdullah shi ma kasa baccin yayi yana rungume da picture d'in husna yinin
yau yayi kewar ta sosai idanun shi ba suyi toxali da kyakkyawar fuskar ta ba bai ji dadd'ar
murya ta ba ta ratsa kunnuwan shi, akwai wani abun wanda tsakanin shi ne da
*DANGARTAKAR ZUCIyar* shi ne baxai iya furta hakan ba har sai xuwa wani lokaci mai tsayi
bai iya bacci sosai a cikin Wannan daren ba.


Toh haka su husna suka cigaba da rayuwar su a bording duk da kewar gidan da suke hakan bai
hana su dage wa wajen karatu ba basa yin wani shirme ko shashanci karatu kawai suke, har
ranar visiting taxo Yah Abdullah, mumy, umma da aunty fatyma babar fadila wato kanwar baban
su husna su suka xo musu visiting dad'i ya ishi su husna sai tsallen murna suke iyayen nasu ma
sai faman fara'a suke da alamar sun ji dad'in ganin su husna Sun kwantar da hankalin su.


Yah Abdullah kuwa baki yak'i rufuwa shima ba k'aramin jin dad'in ganin husna yayi ba, sai

surutu take xuba mishi tana bashi labarin skul d'in wani abin yayi dariya wani lokacin sai yayi
Murmishi Hmmm husna anan da halin bai canja ba.

Sai yaga ta k'ara yi mishi girma a idanun shi gaba d'aya ta canja mishi har sai da ya furta yace

"my cwt sister me kike ci haka kin wani k'ara girma? "

Baki ta turo gaba cikin shagwa6a tace "ni Allah ban k'ara girma ba, Fadila ce katuwa don duk ta
fimu girma (da yake Fadila tana da dan jiki) "

Gaba d'aya aka tuntsire da dariya ban da fadila da tayi kicin kicin da fuska a fusace tace "wlh
husna ki kiyaye ni idan ba hka ba xanyi miki duka Kinsan nafi k'arfin ki "

Hararar ta husna tayi kafin tace "tabbb ae kuwa sai dai mu doki juna ni ga sakarai sai na xauna
ki doke ni "

A fusace Fadila ta kawo wa husna duka da sauri Yah Abdullah yasa hannun shi ya kare husnar
sannan ya 6ata rai ya kalli Fadila yace "Kinsan ban san wasan duka koh, daman abin da kuke yi
a skul d'in kenan? "

Da sauri suka girgixa kai tare da fad'in "nooo Yah Abdullah ba ma yin haka just don muna tare
da ku ne "
Dan murmishi yayi tare da cewa "Yayi kyau hakan"

Ilham ce ta xuba mishi ido tana kallon shi cikin wani irin yanayi a tattare da ita dama itace
husna tana bala'in son taga ya sake dasu kamar yanda yake yi da husna ita dai Yah Abdullah
yana birge ta duk surutun nan da ake yi baka jin bakin ta don bata fiye magana ba sosai ba ga
ta da sanyi sosai kuma cikin sanyi take yin shi, shi yasa Yah ibraheem baya son sata aiki idan
ya sata bata saurin gama wa yayi tayi mata masifa alhalin halittar tace haka.

Lura da kallon shi da take yawan yi ne yasa shi cewa "lafia Ilham wannan kallon fah ko Kina
buk'atar wani abun ne ?"

Cikin sanyin ta ta girgixa kai tare da fad'in "ba komai yayah "
"okay "

Anyi hira sosai kamar baxa su tafi ba haka su Mumy suke ji balle Yah Abdullah ji yake kamar ya
d'auko husna su koma tare dakyar suka tafi bayan sun xube musu uban shopping d'in da suka
yi musu bayan wannan kuma ga wanda Yah Abdullah yayi husnar shi ita kad'ai nan suka jidi
kayan su har xuwa hostel, kowanne jikin shi a sanyaye.

Haka suka cigaba da rayuwar su don har sun d'an saba da makarantar Yah ibraheem da yake

kiran husna dakikiya su Ilham sun fita kok'ari wannan Karon ta xage damtse sosai wajen karatu
don tana son ta nuna mishi ita ma da brain d'in ta just wasa ne yake d'auke mata hankali, gashi
Yah Abdullah ya bata k'warin gwiwa kan ta dage da karatu don ta bawa Yah ibraheem kunya ae
kuwa ta dagen sosai don duk abin da xai sanya Yah ibraheem bak'in ciki shi take so.

A cikin Wannan week d'in su husna suka fara exam sun mayar da hankalin su kan karatun
exam har xuwa lokacin da suka kammala lafia suna ta d'okin xuwa gida duk sun harhad'a kayan
su hutu kawai suke jira ayi musu su taho gida duk a cikin su ba wanda ya kai husna d'okin xuwa
gida kamar ta xama tsintsuwa ta ganta a gaban Yah Abdullah haka take ji.

Ana gobe xa'a bawa su husna hutu, Yah Abdullah farin ciki sosai yake yana d'okin gobe tayi don
yaje ya d'auko su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0