Showing 24001 words to 27000 words out of 73884 words

Chapter 9 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

520






Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃







*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq

*Page 33-34*








ita kuwa husna tana fita a fusace kai tsaye cikin motar ta ta shige ta rufe sannan ta
kwantar da kujerar ta kishingid'a tare lumshe idon ta ranta ba k'aramin 6aci yayi ba akan abin da
d'an rainin wayon malamin nan yayi mata, wani wawan tsaki ta sake ja a karo na biyu Sannan
ta d'auko wayar ta tare da kunna data nan message suka fara shigo wa ta what's app tuni ta
tsunduma a duniyar charting.



Sai da su raudah da Fadila suka shiga fito tare da bud'e motar suka shiga ciki sannan husna ta
ankare dasu nan fah suka bud'e shafin hirar wannan malamin wato safwan Ahmad tsaki husna
ta ja tare da fad'in

"ku har d'an air Indai nice xan koya mishi hankali ne "

Raudah wadda duk tafi so tsoro idan ka d'auke ilham tace "kin ga husna ki kyale shi ki fita
harkar shi kada ya baki matsala fah Kinsan halin lectures d'in nan "


Mtswww husna taja tsaki tare da cewa "banxa matsoraciya kawai wlh kin fiye tsoro raudah "

"Ehhh naji di'n " Cewar raudah tana Murgud'a baki kwashe da dariya suka yi husna da fadila har
ita ma raudah ta d'an dara, Kafin husna tayi wa mota key suka nufi hanyar fita daga skul d'in.


Tana kok'arin fita daga get d'in skul kenan shi kuwa safwan Ahmad na kok'arin shigo wa had'a
idon da suka yi da husna yasa ta fasa kok'arin kauce wa sai ma ta janyo wani black glass ta
d'ora a idanun ta yayin da shima safwan Ahmad shima yaja mota ya tsaya yak'i kaucewa, don
kowanne yana ji da miskilan ci da kasaita.

Sosai husna ta bawa safwan Ahmad mamaki don bai yi tsammani yarinyar hka ba sai kawai ya
xuba mata ido yana kallon ta cikin mamaki yana matsayin malamin ta yaci ace ta bashi girman
shi.


Cikin matuk'ar tsoro raudah tace "na rok'e ki husna ki janye motar ki a bashi hanya wlh wannan
safwan Ahmad d'in bai da kirki "

Cikin halin ko inkula husna tace "wlh baxan janye ba sai dai shi ya janye kuma yayi min uban da
ya ga dama"

"Haba husna yaci darajar malamin ki mana ki bashi hanya ya wuce kin ga mutane a bayan mu "
Cewar Fadila


"Mtsww kan ku ake ji enmata"

Tana gama fad'in hka ta sanya headphone a kunnen ta tana jin wak'ar Jojo cikin wak'ar ta ta
baby it's you tana wani kid'a kai raudah da fadila duk suka bita da kallo duk a tsorace suke suna
mamakin k'arfin halin husna.


Sun d'auki tsawon mintuna 20 a hka mutane sai uban horn suke musu amman ba wanda yayi
wani yunkuri ,ana cikin hka wayar safwan tayi ringing da sauri ya d'auka ganin sunan umman
shine bayan ya d'auka take sanar dashi yayi sauri yaje ya d'auko mahaifin shi Alhj Ahmad a filin
airport nan ya amsa mata tare da katse wayar cikin hanxari ya juya motar tare da d'aukan
hanyar da xata kai shi airport xuciyar shi cike da tunanin husna yana son sanin ita wace.


Ganin haka yasa husna jan motar suka fice daga skul d'in sannan mutane suka samu hanyar
tafia, dariya husna ta kyalkyale da ita har da buga steering tare da fad'in

"Yeeeee yaji tsoro ya juya daman ae irin nasu cika bakin nan duk yawan cin su matsorata ne "

Fadila da raudah suka taya ta dariyar tare da tafawa suka ce "wlh husna ke er air ce kada kisa
d'alibai su daina ganin girman shi "

Kafad'a ta d'aga alamar ko ajikin ta da hka suka K'arasa gida husna tayi part d'in su yayi da
raudah da fadila suka wuce part d'in hajia maamaa.


Hka rayuwa ta cigaba da tafiya tun daga ranar nan husna bata k'ara sa safwan Ahmad a cikin
idanun ta ba, suna ta shirye shiryen bikin Yah Abdullah da Ilham a fili tana nuna tana farinciki da

Wannan auren amman idan ta ke6e waje d'aya sai kuka sosai abin gwanin ban tausayi gaskia
husna ba k'aramin son Yah Abdullah take ba duk da xuciyar ta ta sawa hakurin rabu wa dashi
xata d'auke shi yanda kowacce kanwa take son yayan ta.


Yah Abdullah kuwa ya kasa xuwa kaduna duk kuwa da neman shi da ake ya dad'e rabon shi da
xuwa, k'in xuwan nashi ba k'aramin damun husna yayi, haka a 6angaren ilham itama ta damu
sosai da rashin xuwan Yah Abdullah duk ta damu sosai ta d'an rame saboda tsabar tunanin
shi....................







Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃


*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq



*Page 35-36*




Tafiya take cikin takun ta na kasaita tasha wata irin gown green colour tayi rolling d'in kanta
da black d'in veil sai ta sanya flat shoes bak'i sai er purse a hannun ta da waya tasha bak'in
glass tayi kyau sosae husna Omar kenan, tana tsaye a gefen titi kallo d'aya xaka yi mata kasan

ranta a matuk'ar 6ace yake, saboda motar da ta fito da itace ta lalace mata gashi yamma tayi
gaf ake da a kira sallahr mangarib daga gidan aunty rufaida ta dawo mamee ta aike ta daman
bason xuwan take ba gashi kuma mota ta bata matsala.


Mtswww taja wani uban tsaki kamar harshen ta xai tsinke tana duba agogon hannun ta ganin
6:35 tayi cikin 6acin rai tace

"wlh da nasan motar Yah yaseer hka take da ban d'auka ba" mtswww ta sake jan tsaki a karo
na biyu tana kok'arin kiran number d'in mamee ta turo driver ya d'auke ta sai ga wata
hadaddiyar mota nan k'irar Range Rover kalar dark ash da gani sabuwa ce sai shek'i da
d'aukan ido take da gudu motar taxo ta shige husna .

"wad'annan sune masu jawo wa ana accident ji wani irin gudu kamar xai tashi sama " Cewar
husna kenan tana bin motar da harara kamar itace ta yi mata laifin.

A hankali mai tuk'in motar yayi rebos tare da dawowa baya ya samu kusa da motar husna yayi
parking sannan ya fito ya nufi inda husna ta tsaya jikin motar, ko d'aga kanta bata yi jin anyi
parking kusa da ita ta cigaba da try d'in number d'in mamee don tak'i shiga.


Ja yayi ya tsaya yana kare mata kallo tare da girgixa kai lallai wannan yarinyar er jin kai ce
ganin tak'i d'ago wa yasa shi bud'e baki cikin muryar shi mai dad'in gaske yace

"Assalamu Alaiki "

Da sauri ta d'ago kanta don kamar ta gane mai muryar ae kuwa suka yi ido hud'u da safwan
Ahmad yana sanye cikin wani yadi ash colour anyi mishi aiki da bak'in xare haka takalmin shi
bak'i ne sai dai kan shi ba hula sumar kanshi ta sha gyara irin ta matasan xamani masu ji da
gayu, saukar da idon ta tayi daga barin kallon shi.
Cikin murmishi yace "wa na kama "

dummm gaban husna ya fad'i lokaci guda ga wani tsoro da ya lullu6e ta lokaci d'aya ta shiga
uku yanxu ya xata yi ga hanyar ba mutane sosae yanda xata yi ihu a ji ta don a kawo mata a
gaji don tasan ramuwa yaxo yi akan abin da tayi mishi tasan ba kyale ta xai yi ba don ba kirki ne
dashi tuni gumi ya fara yanko mata har jikin ta ya fara rawa.
Murmishi ya sake yi a karo na biyu a cikin xuciyar shi yace ashe duk cika bakin banxa ne
shegen tsoro ne da ita, ganin yana murmishi ta dauka murmishin mugunta ne haba tuni husna
ta sake tsinke wa, cikin muryar shi mai dad'in sauraro yace

"Haba husna bai kamata ki ji tsoro ba na d'auka ke jaruma ce "

Cikin tsananin mamaki ta d'ago kai tana kallon shi don jin ya kirawo sunan ta d'aga mata gira
yayi yana cewa

"Kina mamakin yanda nasan sunan ki koh abin da kika yi min ranannan ne ya d'aure min kai har
ya kai da na binciki ko ke wace, kuma nayi mamakin yanda aka ce wannan ba halin ki bane
asali ma kin samu tarbiyya mai kyau daga iyayen ki "

Shiru husna tayi kawai bata ce komai ba ganin tana duban agogo yasa ya gane abin da take
nufi sai yace

"me ya samu motar taki?"

Ganin sauri take gashi mangarib ta kusa yasa tace

"nima ban sani ba just ina cikin tafiya ne naji ta tsaya "

Cikin sigar tsokana yace "Ko ba mai ne? "
Batasan lokacin da ta d'ago kanta ta d'an harare shi ba don maganar ta bata haushi, er dariya
ya saki mai birgewa tare da kama kunnen shi duk biyun cikin shagwa6a yace

"sorry "

Kallon shi tayi cikin mamaki kamar ba safwan Ahmad ba, wajen motar ya shige ya d'an
dudduba ta amman tak'i tashi dawowa yayi Inda take ya fito da wayar shi magana yayi na tsayin
mintuna uku tukunna ya kashe wayar ya d'ago kanshi ya Kalli husna yace

"ranki ya dad'e nayi en dabaruna tak'i tashi amman na kirawo mai gyara wa don hka kixo na kai
ki gida idan ya gyara xan kawo miki har gida "

Shiru tayi bata ce komae ba ganin hka yasa yace "Ko kina tunanin xan sace miki "

Hararar shi tayi ta gefen ido sannan ta mik'a mishi key di'n motar yasa hannu ya kar6a ana cikin
hka sai ga mai gyaran nan ya bashi key di'n motar sannan ya bud'e wa husna gaban motar ta
shiga a d'an tsorace sannan ya rufe ya xagayo shima ya shiga a nutse ya ya yiwa motar key
suka fara tafiya ba me magana a cikin su sai wak'ar Justin Bieber da take tashi ta love me
kowannen su xuciyar shi cike da tunani musamman husna.

Mamakin ta ne ya k'aru ganin ko ya tambaye ta Inda gidan su yake ita kuma miskilan ci ya hana
ta bud'e baki tayi mishi magana, gashi kuma sai bin hanyar da xata kaisu gidan su yake.

Lallai ma mutumin nan ba k'aramin bincike yayi a kanta ba ganin yana horn a kofar get d'in

gidan da sauri me gadi ya bud'e kofar ganin husna a cikin motar sai da ya samu waje yayi
parking yana tsayar da motar husna ta yunkura ta bud'e motar sai da ta fito tukunna tace mishi

"Na gode sai anjima "

Tana gama fad'in hka ta yi gaba abin ta kallon ta kawai yake yana murmishi sosai yarinyar take
birge shi tun ganin ta na farko da yayi, murmishin shi ya k'aru ganin ta mance wayar ta garin
sauri d'aukan wayar yayi tare da yi mata kissing bayan ya shak'i k'amshin daddad'an turaren
husna har sai da ya lumshe idon shi don dad'in k'amshin,a hankali ya furta cewa "ina son ki
husna! I really luv u tun lokacin da na fara sanya ki a idanu na"
Kafin tukunna ya ja motar shi ya nufi gida.


*WANE NE SAFWAN AHMAD*

Safwan Ahmad d'a ne ga Alhj Ahmad mai gwanjo da hajia karimatu suna da yara guda 3
safwan shine babba sai habib da ruqayya su kad'ai ne yaran da Allah ya basu.
Alhj Ahmad mai gwanjo asalin sunan mai gwanjo Inda ya samu sana'ar ta ya fara yi Kafin Allah
ya axurta shi da samun arxiki ya bunkasa sana'ar tashi d'an kasuwa ne sosai yana fita su dubai,
china da sauran kasashen wajen kasuwan cin shi ba k'aramin nasara yake samu ba akan
harkar kasuwanci nashi yana da arxiki sosai, d'an asalin garin kaduna nane haifaffen can.
Iyayen shi managarta ne akwai so da taimako sun bawa yaran su tarbiyya mai kyau tare da
ilimin addini dana boko.

Safwan Ahmad mai gwanjo yaro ne matashi wanda shekarun shi baxa su gaxa 35 kyakkyawan
saurayi ne sosai fari tas dashi gashi dogo ne yana da K'ira mai kyau yana da hancin sai dai
idanun shi basu cika girma ba ga sajen nan nashi da matasa yanxu suke Bari ta ko'ina dai
safwan ya had'u sosai enmata suke rububi akan shi.
Yayi ilimin shi na addini dai dai gwargwado na boko kuwa kusan a k'asar England yayi su,
lokacin da yake university tashen samartaka yana kan shi an d'an ta6a neman mata da d'an
shan giya amman daga lokacin da ya dawo nigeria duk ya watsar da wannan dabi'ar ya nutsu
daman can da xubar abokai toh yanxu ya rabu dashi Allah ya shirye shi har haushin kanshi
yake ji Idan ya tuna da rayuwar da yayi a baya, bayan ya dawo ya samu aiki a university a
matsayin lecture.


_Mun dawo labari_


Da sallama ya shiga parlourn gidan nasu xuciyar shi cike da tsantsar farin ciki hajia karimatu ta
amsa mishi sallamar tashi da fara'a akan fuskar ta tace
"sai yanxu ka dawo my son ina ka mak'ale ko wajen surukar tawa ka tsaya don wannan gayun

da magana"

Dariya yayi tare da cewa "Kaiii umma ni ba inda naje daga gidan hajia kaka nake "
Cikin murmishi tace "Okay yayi kyau hkan ya ka baro ta? "
"tana nan lafia "

Idanun ta ne suka sauka kan wayar hannun shi ta husna tace "yaushe ka siyi waya kuma don
bansan ka da irin ta ba? "
D'an sosa k'eya yayi tare da cewa "uhm uhm umma ta... "

"ban san ka da k'arya ba fah safwan"cewar umma
"umma ta husna ce ta mance ta a mota ta "
Wani dad'i ne ya ishe umma ganin d'an nata yau yayi magana akan mace "Wace husna kuma?
"umma ta tambaye shi
"wata d'aliba tace na rage mata xuwa gida motar tace ta lalace mata a hanya "
"ka kyauta kuwa amman Naga alama d'an nawa kamar....."
Sai tayi shiru tana dariya shima dariyar yake yana cewa "Allah umma ba wani abun "
"idan tayi tsami ma ji "
Daga hka hirar tasu ta yanke ya fita xuwa masallaci umma kuwa ta shige d'akin ta.........




Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃



*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




_Godiya ga dukkanin makarantar DANGARTAKAR ZUCI mun gode da yanda kuke son littafin

da yanda kuke bibiyar shi Allah ya bamu ikon kammala muku shi lafia_❀😍




*Page 37-38*



Husna tana shiga gida ta tuna ta bar wayar ta a motar safwan da sauri ta jiyo don ganin ko
bai riga ya fita ba har tana d'an had'a da d'an gudu sai dai kash tana xuwa mai gadi yana rufe
get alamar fitar shi kenan, haushi ya rufe husna don me yasa baxai bawa baba mai gadi ya
kawo mata ba sai tafar mata da waya Mtsww taja tsaki cike da jin haushin safwan don tana son
amfani da wayar ta ta, ganin tsayuwar baxa ta amfane ta ba yasa ta juya xuwa part d'in su,gashi
abin takaicin nata bai wuce ta cire security d'in jikin wayar ta ta, tasan bincike xai mata a wayar
Amman mutumin nan ya rai na min hankali.


Kwance yake saman bed tunanin husna yake yi shi kanshi yana mamakin yanda son yarinyar
ya shiga xuciyar shi farat d'aya wayar ta ya d'auka nan ya shiga sarrafa ta da yake ba security a
wayar cikin memory card nata ya shiga ya fara kallon picture's d'in ta anan ya sake tabbatar wa
da kanshi Indan ya samu husna matsayin matar shi ya gama more wa.
Contact di'n ta ya d'auka yayi serving a phone d'in shi sannan ya cigaba da kallon pictures d'in
husna xuciyar shi tana k'ara k'aunar ta, safwan kenan jarumin namiji mai ji da kyau da nera
gashi yau ya fad'a son husna, daman Hka enmatan da suke son shi suke daman hka so yake,
yake tambayar kanshi bayan ya gama kallon photo nan husna, daman shi bai ta6a yin soyayya
ba wannan karon shine na farko a cikin rayuwar shi.


_Abuja_

Yah Abdullah na hango xaune acikin garden di'n gidan shi kallo d'aya nayi mishi na firgita
ganin yanda ya rame yayi bak'i kamar ba Yah Abdullah dana sani ba duk ya tara wani uban
kasumba saboda tsananin tarin damuwa da tunani da yake ciki.

Anya hajia maamaa tana son shi kuwa taya xata raba shi da abar son shi akan wani banxan
shirme wai xata juya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0