Showing 12001 words to 15000 words out of 73884 words

Chapter 5 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

505

daga makaranta yana cike da son ganin husna tare da jin muryar ta kwatsam
abban shi ya nemi da xai aike shi abuja wajen wani aminin abban kan harkar business di'n su
abban tuni murna ta koma cikin Yah Abdullah kamar xai yi kuka haka yake ji ya kwallafa ran
xuwa gobe tayi amman haka ya hak'ura tun da aiken na Abba ne haka ya kwanta duk xuciyar
shi ba dad'i.

Washe gari da sassafe Yah Abdullah ya nufi abuja don yana son yaje da wuri don ya dawo da
wuri, bayan tafiyar shi ne Abba ya nemi Yah ibraheem da yaje ya d'auko su husna daga skul,
wani shegen murmishin mugunta ya saki duk da yana da lectures ranar haka ya yarda xai je ba
tare da ya musa ba ko ya nemi driver ya d'auko su ba Duk sunyi mamakin yanda ya yarda farat
d'aya batare da nuna k'in amince war ba (Hmmm Allah ne kad'ai yasan muguntar da Yah
ibraheem ya shirya wa husna har na fara tausaya mata), xuciyar fal farin ciki ya yiwa motar shi
key bayan yasha gargad'i wajen mumyn sa akan kada ya yi wa husna wani abun kai tsaye skul
d'in su ya shige.


Bayan an watse daga assembly ne an fad'a musu iya adadin k'wanakin hutun sannan aka yi
musu en nasihohi tukunna aka sallame su nan fah kowa ya fara fito da jakar kayan shi Idan an
xo d'aukan mutum sai yayi sallama da friends d'in shi ya tafi da haka aka dunga raguwa d'aliban
cike da tsananin kewa don an d'an saba da juna.

Suna xaune a k'ark'ashin wata bishiya akan chairs irin wanda ake gina su sai er hira suke Ilham
da raudah, Fadila bata wajen yanxu ta tashi don ta gaji da xama waje d'aya yayin da husna take
Jan tsaki akai akai tare da cewa

"Gaskia Yah Abdullah ya ji ma komai mai ya tsayar dashi ni fah na matsu na ganni a gida wollah
"

Har raudah ta bud'e baki xatayi magana kenan sai ga fadila da gudu ta K'arasa wajen tana d'an

haki Kafin ta bud'e bakin ta tace

"ku taso mu tafi an xo d'aukan mu"
Da sauri husna ta mik'e tsaye tare da d'aukan kayan ta tana cewa "da gaske kike Fadila? "
Cikin d'oki husna ta fad'a da dariya fadila tace "wallahi da gaske nake kalli can ki ga Yah
ibraheem ne ya xo d'aukan mu "
Dummm gaban husna yayi mugun fad'uwa nan take ta d'aure fuska su kuwa su Fadila basu
k'ara bi ta kanta ba balle su san halin da ta shiga nan suka fara d'iban kayan su suna kai wa
cikin boot d'in motar har sai da suka gama Kafin Ilham taja hannun husna su k'arasa wajen
motar ganin yanda ta ga husna ta kafe a tsaye.
Suna k'araso wa fadila cikin rawar kai ta shige gaban motar yayin da raudah ta shiga baya
Ilham ma shiga tayi suna jiran husna ta shigo don Ilham tana sakin hannun ta bata k'ara
yunkurin takawa ba ji tayi kafar tayi mata nauyi take dakyar ta iya ciran hannun ta takai xata
bud'e motar kenan kamar kiftawar ido sai ta ga Yah ibraheem yaja motar da mugun gudu ya fice
daga skul d'in da yake kuma gate a bud'e yake, d'ora hannu akai su Fadila suka yi tare da sakin
ihu suna cewa
"wayyo Allah Yah ibraheem don Allah ka koma mun bar husna acan ba"
Wata irin tsawa ya daka musu tare da cewa "ko Kuyi min shiru da baki ko na ci uban ku ina
ruwa na da ita "
tsit suka yi suna goge hawayen fuskar su na tausayin husna lallai sun k'ara tabbatar wa da ba
k'aramin k'iyayya Yah ibraheem yake nuna wa husna ba sai kace ba *dangin juna* ba (littafin
Asmy b aliyu), shi kuwa Yah ibraheem hankalin shi kwance yake driving cikin K'ware wa ya
kunna wak'ar cikin film d'in Aashiqui don ba k'aramin son wak'ar yake ba don kusan ta shafi irin
yanda yake ji wanda tsakanin shi da *DANGARTAKAR ZUCIn* shi ne kawai har wani lumshe
idon shi yake alamar yana cikin tsananin farinciki bai damu da yanda su Ilham suke kuka ba.

Turk'ashi! tsananin bak'in ciki takaice ko kuma k'iyayyar Yah ibraheem ne take sake ruruwa a
cikin xuciyar husna wadda ke tsaye bayan kurar da Yah ibraheem ya gama bula mata kuka ta
rushe dashi tare xube wa a wajen................






Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃

*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 17-18*









Kuka ta xube tana rusawa hannu akan ta Yah ibraheem mugu ne bashi da kirki shine ya tafi
ya barta a cikin kungurimin dajin uban wa ta sani wayyo Allah ni husna haka tayi ta kuka sauran
d'aliban suna kallon ta wad'anda abin ya faru a gaban su ta basu tausayi sosai.

Har kusan gaba d'aya students di'n sun tafi sai en Kad'an wad'anda garin su yake da nisa ba'a
xo d'aukan su ba har wurin la'asar husna tana xaune tana kuka ga wata axababbiyar yunwa da
take yamutsa mata en hanji ko sallahr axahar bata yi ba, wata d'aya daga cikin d'aliban ne da
basu tafi ba ta janyo hannun husna tana rarrashin ta da tayi hak'uri dole xa'a xo d'aukan ta
kuwa dakyar ta hak'ura da kukan suka yi sallahr axahar da la'asar.

Suna xaune sun yi jugum jugum duk surutun husna a wannan lokacin baxa ta iya ba idanu duk
sunyi jawur dasu gashi sun kumbura ga wata shegiyar yunwa duk tayi wani wujiga wujiga ta
xabga uban tagumi lokaci xuwa lokaci tana goge hawayen fuskar ta.



Da murnar shi yayi parking a farfajiyar gidan ya fito da sauri ko part d'in su bai yi ba, duk kuwa
da tsananin gajiya da yunwar da yake ji kuwa amman sai yayi toxali da husnar shi cikin farinciki

ya tunkari part d'in hajia maamaa don yasan a wannan lokacin suna nan suna hira da d'okin shi
yayi sallama amman kuma sai yayi turus ganin su Ilham sun xuba tagumi ga hajia maamaa ita
ma fuskar ta d'auke da tarin damuwa da sauri ya K'arasa tare da kama hannun hajia maamaa
yace
"lafia hajia maamaa?"
Cikin sanyin murya tace " wai ja'irar yarinyar nan ce aka neme ta a makaranta a kasa rasa har
ibraheem ya gaji da xaman rik'e ta ya xuciya ya taho ba ita ga iyayen ku gaba d'aya basa nan "

Tun da hajia maamaa ta fara magana ya xuba mata ido yana kallon ta cike da tashin hankali sai
huci yake cikin tsawa yace

"what!, wannnan xancen ban yarda da shi ba, husna baxa ta yi haka taya Abba xai aiki
ibraheem why? "
Hajia maamaa sakin baki tayi da ido tana kallon Yah Abdullah wanda bata ta6a ganin shi a haka
ba, amman don ta k'are d'an gaban goshin nata yasa tace

"ae ibraheem bashi da laifi ita husnar da ta tafi yawon ta ita ke da laifi "
Wata harara Yah Abdullah ya aikawa hajia maamaa don ya rasa me ma xaice juya wa yayi kan
su Ilham ya kwantsama musu tsawa tare da fad'in
"ku fad'a min gaskia barin ta yayi ko??? "

Cikin sauri su Ilham suka ce "Gaskia ne Yah Abdullah mun neme ta mun rasa ne "
(Yah ibraheem ne yaja musu kunne akan Idan suka fad'i gaskia sai yasa su hawan bango ba
ma jump frog ba kuma sai yaci uban su tare da rufe su a toilet na tsayin yini guda ba ci ba sha
ba k'aramin tsoratar dasu yayi ba shine suna ji suna gani suka bashi gaskia don basu da yanda
xasu yi).
Wani kallon dukka k'arya kuke yayi musu tare da fice wa da sauri kamar xai tashi sama da
masifar gudu ya fice daga gidan a cikin mota megadi Ya bishi da addu'ar sauka lafia, ya kure
speed di'n motar gudu yake sosai xuciyar shi na tafarfasa sai faman huci yake.

Bai K'arasa makarantar ba sai daf da mangariba yana parking ana kiran sallahr mangariba duhu
ya fara yi, dube dube ya fara yi yana kiran sunan ta amman shiru gaba d'aya hankalin shi ya
dad'a tashi matuk'a fiye da da, sai da ya d'auki wajen 25mint yana neman husna har masu
gadin makarantar suna taya shi nema don sun tabbatar tana nan cikin bata fita ba.
Dakyar suka gano ta k'ark'ashin wata bishiya tana kwance kan kujera ta dukunkune jikin ta waje
d'aya sai faman ajiyar xuciya take saki alamar taci kuka ta koshi, tsugunna wa Yah Abdullah
yayi ya kura mata ido hannun shi yasa ya shafi gefen face d'in ta yana ayyana wasu abubuwa a
cikin xuciyar shi, kafin ya fara tashin ta a hankali a tsorace ta bud'e idanun ta suna had'a ido da
Yah Abdullah ta fad'a jikin shi tare da sakin wani kuka bubbuga bayanta yake yana cewa
"shiiiii baby nah ya isa hka tashi mu tafi "

Hannun ta ya kama yaja har xuwa inda yayi parking ya bud'e motar ya kwantar da ita a seat di'n
baya sannan ya shiga yayi wa motar key sai da yaxo dai dai gate ya sallami masu gadin da
kud'i sannan ya fice daga skul d'in yana driving yana d'an waiwayen husna.

Yah Abdullah da husna suna barin wajen naga wani ya fito daga bayan bishiyar da husna ta
kwanta a k'ark'ashin ta ya nufi inda yayi parking ya shiga tare da fita daga skul d'in gaba d'aya.

Sai wurin 8 suka isa gida Yah Abdullah yana parking da motar shi Yah ibraheem shi ma yayi
parking ya fito tare da cewa "Yah Abdullah a ina ka tsinto ta kuma? "
Wata harara ya samu a wajen Yah Abdullah da husna basu kula shi ba suka shige cikin gidan
yayin da Yah ibraheem ya saki wani shi'umin murmishi wanda na kasa banbance wane kalar
murmishi ne hankalin shi kwance yayi part d'in hajia maamaa don a matuk'ar gajiye yake jin shi
yinin yau through out bai samu zama yana tafiya yana cilla key di'n shi yana cafewa da haka har
ya K'arasa part d'in.

Yana shiga ya had'a ido dasu Ilham ya 6alla musu harara sunkuyar da kansu suka yi da sauri
d'an siririn tsaki yasaki tareda shigewa bedroom d'in shi don ya watsa ruwa ko yaji dad'i.

Lokacin da labarin yaje kunnen su Abba 1, wato Alhj muktar da daddy Alhj Omar sai Abba 2
Alhj mustapha nan fah aka kirawo su gaba d'ayan su don tabbatar da wanda yake da Gaskia a
tsakanin Yah ibraheem da husna, yana xaune a gefe sai faman murmishin mugunta yake
hankalin shi kwance anan dai duk su Ilham suka goyi bayan Yah ibraheem haushi da takaice ya
turnik'e husna kamar xata rushe da kuka ganin yanda duk ita aka bawa laifin sai fad'a ake mata
Yah Abdullah da su Yah mus'ab sun san husna baxa tayi haka ba sharrin Yah ibraheem ne
kawai.

Danne kukan ta tayi tak'i bar hawayen ya fito duk da yanda xuciyar ta take cikin bak'in ciki kuwa
don a ganin ta Idan har ta xubar da hawaye a gaban mak'iyan ta (Yah ibraheem) har ya gansu
alamar ya samu sa'a a kanta don hka tak'i barin su Su fito sai huci take fuskar nan a had'e
fuuuu ta fice daga palon yayin da Yah Abdullah ya tashi ya bita da sauri don ya rarrashe ta Hka
sauran duk suka mik'e aka bar hajia maamaa, Abba 1,abba 2 da daddy sai mumy, mamee da
umma sai ibraheem kanshi yana cinyar mameen husna yana mata shagwa6a ita kuma ta biye
mishi sai wani lalla6a shi take.

Tana shiga bedroom d'in su ta xube kan bed tana rusa kukan bak'in ciki da takaici wata sabuwar
tsanar Yah ibraheem tana sake ruruwa a cikin xuciyar ta nan Yah Abdullah dasu Yah mus'ab
suka xo suna rarrashin ta har da su Ilham, Fadila da raudah dakyar tayi shiru ta share hawayen
ta sai da dare ya d'an yi sannan suka fito daga d'akin aka bar Ilham, raudah da Fadila sai husna
anan suke sake bata hak'uri tare da sanar da ita abin da Yah ibraheem yayi niyyar yi musu idan
suka fad'i gaskia, wani murmishin takaici husna ta saki tare da cewa
"ba komai kada ku samu damuwa k'iyayya ni da Yah ibraheem yanxu muka fara ta "
Kallon ta suke amman sun kasa cewa komai toh me xasu ce mata shiru suka yi kowanne
xuciyar shi cike da sak'e sak'e.

Tun da ga lokacin husna ta d'auki wani hali ta yafa wa kanta fad'a, masifa idan aka ta6o ta ta
dunga yi kenan, tsakanin ta da Yah ibraheem ko kallon mutunci Bata yi mishi balle aje batun
magana ta fatar baki shi kanshi yana mamakin yanda husna ta koma ko irin tsoran nan da yake
gani a fuskar ta idan ta ganshi yanxu sam babu shi.
Da hka har suka cinye hutun su suka koma makaranta wannan Karon ba'a yi kuka sosai ba hka
Yah Abdullah ya kai su makarantar sannan ya jiyo xuciyar shi cike da tunanin husnar shi sam
baya son tayi nesa dashi...............



_kuyi hak'uri da wannan wlh har yanxu sister Sumy bata samu cikakken lafiar yin typing ba ku
dunga yi mana uxiri don komai sai da lafia, i luv yhu oll my fans_�

Aishat A muh'd


*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃





*written by*
Aishat A muh'd


*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 19-20*

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su su husna sun mayar da hankalin su kan karatu, yayin da
har yanxu husna take nuna wa Yah ibraheem irin k'iyayyar da take mishi kullum gaba take bata
kula shi ko shiga harkar shi ko kallon Inda yake bata yi Idan sun xo hutu gida, a yanxu sun saba
da makarantar sosai.
Suna Js 3 ne Yah ibraheem abban shi ya sama mishi wata university a k'asar Malaysia ya tafi
cigaba da karatun shi dakyar aka shawo kan Yah ibraheem ya yarda saboda shi ya fison ya
xauna a kusa da hajia maamaa da iyayen shi sai da abba yayi mishi tatas sannan ya amince ba
don yaso ba haka ya tarkata ya tafi malaysia.
An fara girma su husna yanxu ko jikin Yah Abdullah ta dai na xama idan yaxo musu visiting Ko
sun je gida hutu sai dai su xauna suna hira cikin kwanciyar hankali ba dai su had'a jiki da juna
ba sai dai idan ya kasance da uxiri babba, duk da yana dan uwan ta kuwa don ba abu ne mai
kyau shi kanshi Yah Abdullah yaja baya da janta a jikin shi tun da yanxu girma yaxo musu sai
dai har yanxu wannan shakuwar nan da suka yi juna tana nan sai ma cigaba take wajen
kok'arin rikid'a ta koma so da kauna amman har yanxu Yah Abdullah ya kasa fad'a wa husna
abin da yake ji a cikin xuciyar shi don yana ganin har yanxu akwai sauran time.

Yayin da kulawar da yake bawa husna ta fita daban da yanda yake kula da su Ilham, raudah da
Fadila a gaban ko wane yana nuna wannan banbancin, lokacin da husna taji labarin Yah
ibraheem abba ya tura shi k'asar Malaysia karatu ba k'aramin jin dad'i tayi ba a xuciyar ta don
ita har cikin xuciyar ta tak'i jinin ganin Yah ibraheem ta tsane shi ba Kad'an ba.
Suna ss one ne Yah Abdullah ya kammala karatun shi na accounting cikin nasara tare da
samun aiki a abuja nan ya tarkata ya tafi sai week end yake samun shigo wa kaduna yanxu
suna d'an dad'e wa basu had'u da husna ba saboda yanayin aikin shi amman duk da hka yana
kok'arin lek'a wa skul d'in don ya ganta, ana cikin hka ne aka sanya ranar bikin su aunty
khadijah, aunty Amina, aunty marwa, aunty aimana da aunty rufaida don sun kammala had'a
diploma hajia maamaa ta dage akan baza su cigaba da karatu ba aure xa'a yi musu sun girma
idan yaso sa cigaba a d'akunan maxajen su kuma gashi kusan duk tsiran su ba yawa don hka
kowacce ta fito da wanda xata aura kusan duk en uwan hajia maamaa ne don ita ta fison auren
xumunci kusan duk ita ta had'a kowanne da wanda xasu aura.

Su husna sun sha takaicin basu aka yi bikin don lokacin suna skul gashi daf da xana exam suke
haka hak'ura amman ranar kowacce rai a 6ace yake ana can ana shan shagalin biki babu su
kuma wannan auren Kusan shine na farko wanda xa'a yi a gidan nasu.


Ilham ce take xaune tana kallon wani photo a hannun ta ta kura mishi ido sosai tana murmishi
ita dai tana masifar son Yah Abdullah tun lokacin da bata san mene so ba har xuwa yanxu da ta

fahimci ta fad'a son Yah Abdullah yayi mata kamu a xuciyar ta bana wasa hannu tasa ta shafa
kyakkyawar fuskar shi tare da furta "Yah Allah ka mallaka min wannan bawan naka Ina son shi
da yawa "

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0