Showing 6001 words to 9000 words out of 73884 words

Chapter 3 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

545

alwashin sai ta rama abin da Yah ibraheem yake mata ita wlh ta
gaji da cin xalin nan da yake mata nan fah ta mai da hankali akan tunanin abin da xata yi mishi.

Tana xaune a bedroom d'in su tana duba books di'n ta na skul tana cikin bud'e text book di'n ne
taga photon wani katon kenkeso duk da ta tsane ta bata k'aunar ko da ganin ta amman ta dan
xuba mata ido sai ta lula tunani can kamar an tsikare ta ta mik'e da sauri tana cewa "yes idea! "
tuni ta fara tsallen murna don tasan Yah ibraheem yayi mugun tsanar kenkeson baya son ganin
ta akwai lokacin da yana cikin cin abinci a falon hajia maamaa sai kawai ya hango ta gaf da
kafar shi wani wawan ihu ya saki tare da daka tsalle ya haye kan kujera yana kakarin amai.

Duk en falon suka jiwo suna kallon shi tuni hankalin hajia maamaa yayi mugun tashi taxo wajen
shi da sauri tana rik'e shi tare da tambayar shi lafia, nuna mata kenkeson yayi da hannu ae
kuwa ta kirawo er aikin ta mai gyaran falon ta kashe ta tare da dauke ta ta fita ta xubar a dusbin
a ranar sai da Yah ibraheem ya mare ta tare da yi mata warning idan baxa ta tsaya ta mai da
hankalin ta wajen aikin ta ba xa'a sallame ta a samo wadda xata iya, hak'uri ta dunga bashi

Sannan ta tafi, a ranar kusan yinin d'aki yayi abinci kuwa kasa ci yayi duk hankalin hajia
maamaa ya tashi ta dunga fad'a ita kad'ai ba wanda ya kula ta don an ta6o d'an gaban goshin
nata.


Da gudu ta fice daga part d'in nasu a hanya ta kusan cin karo da Yah ibraheem harara ya dalla
mata tare da jan kunnen ta da karfi har sai da tayi k'ara sannan ya sake ta ya wuce da sauri da
alamar da akwai inda xai je, shafa kunnen ta tayi tare da kyalkyale wa da dariyar mugunta da ta
tuna plan di'n da xata hada mishi cikin tsananin farinciki tace "mugu wlh nima sai na rama abin
da kake min mrs wicked "


Wajen baba mai gadi kai tsaye ta wuce ta same shi xaune kan benci yana jin radio xama kusa
dashi tayi tare da cewa "sannu baba mai gadi radio kake ji? "
rage k'arar radion yayi cikin murmishi yace "ehh husna mutuniyar ibraheem "
Had'e fuska tayi tare da bubbuga kafafun ta a k'asa kamar xata fashe da kuka tace "ni ka daina
had'a ni da wannan mugun "

Yana er dariya yace "ae kuwa ibraheem ba mugu bane yana da kirki kawai halin ku ne bai xo
d'aya ba shi yasa bakwa shiri, ni ina nan ina addu'a Allah yasa ayi er gida don had'in xai yi kuwa
"

Sam bata fahimci maganar shi ba don hka ta langa6e kai tare da cewa "baba mai gadi ina xan
samu kenkeso ne? "
Cikin mamaki yake kallon ta kafin yace "me xaki yi da ita husna"
Cikin murmishi tace "a school d'in mu aka ce mu kai xa'a yi practical da ita kuma kowa ance
yaxo da ita "

D'an shiru yayi alamar yana tunani Kafin yace "tun da sha'anin karatu ne xan samo miki "
Dad'i ya kama husna tace "thank u baba mai gadi "
Shima washe baki yayi yana cewa "mene kuma tanka yo? "
Dariya ta kyalkyale da ita har da hawaye shima har ta bashi dariya yana taya ta cikin dariyar
tace
"baba mai gadi thank u ake cewa ba tanka yo ba, kuma cewa nayi nagode "

"aiyyo husna Kinsan Banyi wannan makarantar turawan ba"
"toh baba ka shiga mana "
D'an xaro ido yayi Kafin yace "da tsofan nawa xan shiga bokoko tabb sai dai yara na"

"toh baba kaje ka samo min mana kada ka mance "
"Yawwa er albarka kin tuna min don har na mance "
Tashi yayi tare da k'walla wa mai bawa flowers ruwa da sauri ya amsa tare da xuwa inda baba
mai gadi yake yace

"Yawwa magaji d'an kular min da gate xan dan fita yanxu xan dawo "
Magaji yace "toh baba sai ka dawo "
Daga hka baba mai gadi ya fice yayin da magaji mai bawa flowers ruwa ya xauna kan benci
yana bawa husna labarin abin dariya tana kyalkyale wa da dariya.

Baba mae gadi bai fi 10 mint da fita ba ya dawo leda bak'a a hannun shi husna tana ganin shi
da sauri ta K'arasa inda yake ya Mik'o mata ledar yana cewa
"gashi husna guda uku na samu dakyar "
"toh baba mai gadi nagode "
Sai kuma taji tsoron kar6a don har ga Allah tana jin tsoro wata er sanda ta samu ta xura sandar
tsakanin hannayen ledar daman ya kulle mata tana sa sandar ta rik'e ta nufi cikin gidan part d'in
hajia maamaa tayi tana d'an dube dube don bata son wani ya ganta kai tsaye bedroom d'in Yah
ibraheem ta shige sai ta hango wasu kaya kan bed d'in shi da alamar su xai sa wani dad'i ne ya
ishe ta, sai kuma ta rasa ta inda xata kunce ledar ta xuba mishi kenkeson cikin aljihun kayan.

A tsorace ta bud'e ledar da yake baba mai gadi ya d'an buge su basa yin motsin kirki da ta
had'a ido da su sai da ta saki wani ihu tare da runtse idon ta da sauri tuni jikin ta ya hau rawa
don tsoro amman duk da hka sai da tayi dubarar sa mishi a aljihun wandon shi sannan ta fice
daga d'akin da sauri xuciyar ta fal farin ciki ita ma yau xata rama abin da Yah ibraheem yake
mata.

Da sauri ya shigo part d'in hajia maamaa ya shige bedroom d'in shi don yin wanka saboda yana
da Inda xai je wanka ya shiga yayi ya fito kai tsaye wajen dressing mirror yayi ya shafa wani
lotion mai k'amshi tare da taje kanshi ya shafa mishi mai ya taje sannan ya fesa body spray a
jikin shi don fah ibraheem akwai son k'amshi duk tsadar turare idan k'amshin yayi mishi xai siya
yana gama wa ya d'auko kayan shi nakan bed ya saka wow masha Allah ba k'aramin kar6ar shi
kayan suka yi ba black trouser ne da yellow d'in T-shirt mai dogon hannu a jikin rigar anyi rubutu
da black d'in abu ya sanya belt black sannan yasa takalmin shi yellow sai ya d'ora wani farin
glass gaskiya ya had'u sosai sannan ya fesa perfumes Kala Kala a jikin shi tuni ya turare d'akin
da k'amshin turaren shi, da sauri ya dauki phone d'in shi da car key di'n shi sannan ya fito daga
dakin had'a ido yayi da husna wadda ta nutsu waje d'aya tana wasa da teddy bear sauran kiris
dariya ta kufce mata amman ta dake tare da kawar da kanta.

Xama yayi yana kallon hajia maamaa yace " a kawo min abincina maamaa sauri nake "
Ya fad'i yana duba watch di'n hannun shi bak'i ne shi ma, da kanta hajia maamaa ta shiga
kitchen ta had'o mishi abinci ta kawo mishi cikin d'an sauri ya fara cin abinci d'an motsi yaji a
cikin aljihun shi sai ya share kawai ya cigaba da cin abinci, dakata wa yayi da cin abincin jin
motsin sai cigaba da yi yake a fusace ya xura hannu cikin aljihun ae kuwa yayi nasarar kwaso
kenkeson nan bud'e hannun shi da xai yi ya had'a ido dashi a hannayen shi xabura yayi tare da
wurgar dasu lokaci d'aya ya saki wata k'ara irin ta tashin hankalin nan tare da runtse idanun shi
a kid'ime hajia maamaa ta yo kanshi tana tambayar shi abin da ya faru ko ta kanta bai bi ya
fara dan tsalle yana cire trouser di'n dake jikin shi duk yabi ya rud'e ya had'a wani uban gumi,
husna na gefe ta rufe fuskar ta da teddy di'n hannun ta tana dariyar mugunta.

Duk yabi ya d'aga wa hajia maamaa hankali yana xame trouser di'n yayi saura sai boxer ajikin
shi ya fara wani irin kakarin amai.............





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:29] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq





*Page 11-12*




Yana xame trouser di'n yayi wurgi dashi gefe d'aya sai boxer kawai ya rage tuni wani irin amai
ya xo mishi nan ya durkushe yana kelaya aman kamar ya amayo da hanjin cikin shi, idanun
wan shi sun sake firfito wa sunyi wani irin jawur dasu sai da ya amayar da abin da ya ci amman
duk da hka wani kakarin yake.
Hajia maamaa gaba d'aya ta kid'ime ta rasa wani irin taimako xata yi mishi rirrike shi kawai tayi
tana kuka tare da xuba mishi Sannu, husna ma ta motso Inda suke tana danne dariyar ta tana
yi mishi sannu xuciyar ta fal farin ciki duk da ya bata dan tausayi.

A matuk'ar gala6aice ya d'ago da kanshi ae kuwa ya hango kenkeson nan guda d'aya tayo
kanshi tuni ya mike a matuk'ar sauri ya daka wani uban tsalle tare da yin cikin bedroom d'in shi
da gudu bai tsaya a ko'ina ba sai cikin toilet rigar jikin shi ya cire ya fara wanka hannun shi
wanda ya xura a aljihun shi ya kwaso kenkeson nan ya dunga wanke shi kamar xai canja fatar
hannun, sai da yaji hannun yana mishi rad'ad'i sannan ya barshi ya kunna shower ruwa na
xubar mishi a jikin shi yana sauke ajiyar xuciya akai akai tare da fad'a cikin tunanin uban wanda
yayi mishi haka, toh wane xai saka mishi kenkesu a cikin aljihun shi "husna, yes! itace don ba
wanda xai min hka sai ita ae kuwa xata ci uban ta "

Sai da yayi wajen 40 mint yana wanka sannan ya fito daga toilet d'in yana d'aure da towel ajikin
shi da wani k'aramin towel yana goge gashin kan shi agogo ya duba yaga lokaci ya wuce na
Inda xashi kwafa ya saki ranshi a matuk'ar 6ace yana ayyana abin da xai yiwa husna ya huce
akan abin da tayi mishi (Hmmm ni da sumy muka kalli juna tare da fad'in wannan shine
ramuwar gayya kenan, ya mance duk muguntar da yake mata ne).

Wani black 3quater ya sanya tare da white d'in riga mara hannu mai irin mai bottom di'n nan ya
6alle botir guda biyu hakan ya lallausan gashin kirjin shi bak'i wuluk a kwance lub dasu daman
rigar irin mae Shara Sharan nan ce ana iya hango fatar jikin shi da murd'ad'd'en damtsen
hannun shi fuska a tur6une ya fito daga d'akin nashi ya tarar da hajia maamaa ta xuba uban
tagumi tana ganin shi ta taso da sauri tana cewa

"ibraheem ya aman dafatan ya tsaya koh, ya kake jin jikin naka, na xuba maka abinci ka sake ci
"

Da yake lokacin da ya shiga bedroom d'in shi key yasa ya rufe, yamutse fuska yayi yana dan
kalle kallen k'asa, hajia maamaa ta fahimci abin da yake nema don hka tace
"ae tuni ankwashe su an xubar "
Sai lokacin ya saki ajiyar xuciyar kwanciyar hankali yana yamutsa fuska yace
"ni fah abinci bana bukatar shi maamaa "

"toh ni abin da ya bani mamaki ya akayi kenkeso acikin aljihun wandon ka taya suka shiga? "

Kwafa yayi tare da cewa "wanne ya saka xaki ce maamaa "
"auuu sama akayi kenan, to uban wane ya saka maka abin da baka so"
Nan ta fara fada an ta6a d'an gaban goshin ta, cikin takaici yace
"na tabbatar husna ce ta samin, tana ina? "
Dan shiru hajia maamaa tayi sannan tace "anya husna ce xata saka maka, abin da ita ma take
matuk'ar tsoron, toh a ina xata same ta "

"yes! Ita ce wlh kuma sai na mata duka wannan ae ranin wayo ne ni sa'an tane da xata yi min
wannan wasan "

Yana gama fad'in hka ya fice a fusace hajia maamaa taso tsaida shi don a yanda yake cikin

6acin ran nan xai iya ji mata mugun rauni, ta6e baki tayi tare da xama ko dan ita ta jawa kanta
ba ruwa na Idan taji ajikin ta baxa ta k'ara yi mishi haka ba.


Suna xaune a parlour mumy husna, fadila, Ilham da raudah sai su aunty khadijah, aunty Amina,
aunty marwa, aunty aimana, aunty rufaidah, gaba d'ayan su kallo suke a tashar mbc bollywood
suna kallon wani series film madhubala suna d'an surutan su da dan musu akan wannan yafi
son sultan don yafi birge shi yayi da wasu su ce sun fison RK sun raba kansu biyu kowanne da
team d'in da ya xa6a.

A fusace ya bankad'e labulen falon ya shigo suna ganin kowanne ya nutsu aka dai na surutu kai
tsaye inda husna take ya nufa damk'a d'aya yayi mata da hannun shi d'aya ya fara janta, tuni
sauran en uwanta suka fara tausaya mata yaxo gaf da kofar barin falon yaji muryar mumy tana
cewa
"lafia qlau kake kuwa, me tayi maka? "
"kamar ni wannan kaxamar yarinyar mumy ta samun kenkesu acikin aljihun trouser na "
Ya fad'i yana xuba huci tare da hararar husna wadda cikin ta ya d'uri ruwa kiris ya rage ta saki
fitsari a wando, gaba en falon hankalin su ya dawo kan su girgixa kai mumy tayi tare da cewa
"toh kayi hak'uri mana kasan yarinta ce take damun ta "

"ba yarinta bace tsabar ta raina shi ne ibraheem maxa ka je kayi mata abin da kayi niyya yanda
gaba baxata k'ara kwatanta hakan ba "
Gaba d'aya suka jiwo suna kallon mameen husna wadda take maganar hakan ba k'aramin dad'i
yayi wa ibraheem ba kafin mumy ta ankara har ya kwashe ta sun bar falon tuni husna jiki ya
fara 6ari tana kuka wiwi kallon ta yayi yace "yarinya yanxu kika fara kukan nan ma "

ita kuwa mumy ranta babu dad'i tace "Gaskia mameen husna baki kyauta ba Kinsan yanda
ibraheem yake da bakar xuciya kada yaje ya ji mata ciwo "

D'an murmishi mamee tayi kafin tace "ae ita taja gwara ya koya mata hankali "

Shi kuwa ibraheem part d'in hajia maamaa suka nufa suna shiga ya fara kok'arin kwance belt
d'in jikin shi husna tayi wik'i wik'i da ido mai cecanta Yah Abdullah baya nan ya tafi skul yana da
lecture di'n yamma har yanxu bai dawo ba, Kafin ta ankara taji saukar belt a bayan ta gantsare
wa tayi tare da cewa "wayyo Allah nah don Allah kayi hak'uri wlh na tuba na dai na "

Ko kula ta bai yi ba ya fara dukan ta da belt ganin yak'i dai na dukan ta duk da uban hak'uri da
take bashi kuwa don haka ta shige jikin shi tare da rukunkume shi ganin yana samun jikin shi
Idan ya kawo mata dukan yasa shi sa hannun shi da niyyar 6an6arota daga jikin shi amman ina
ya kasa ta mak'ale shi sosai.

Cikin tsawa yace "cika ni dan uban ki nace "
Cikin shashshak'ar kuka tace "ka daina duka na kayi hak'uri baxan k'ara ba"

"baxan hak'ura ba har yanxu ban miki rabin dukan da nayi niyyar yi miki ba"
Hannu yasa ya fisgo ta da karfi ya wurgar da ita k'asa ae kuwa ta had'o da rigar jikin shi har ta
dan yakushe shi a damtsen hannun shi, haka ya xage ya dunga dukan ta tun tana kuka har ta
koma Shashshak'a kawai.

Wayyo aranar husna taci dukan da tun da mamee ta haife ta ba'a ta6a yi mata ba, ana haka
Yah Abdullah ya shigo da gudu part d'in hajia maamaa don aunty khadijah ce ta kirawo shi
awaya tana fad'a mishi da sauri ya warce belt d'in hannun ibraheem tare da watsa mishi wani
kallo ya nufi kan husna da tayi matuk'ar gala6aita ya d'ago ta xuwa jikin shi, wani irin abu Yah
ibraheem yaji ya daki xuciyar shi a dai dai lokacin hajia maamaa ta shigo falon tare da su Ilham
dukkan su kuka suke sosai.

Cikin wani irin 6acin rai tare da tsantsar tsanar Yah ibraheem husna tace
"Ko ni ba jinin ka bane bai kamata kayi min wannan dukan ba na sani tun da nayi wayo ka tsane
ni kullum cikin duka na kake da cin xalina kasani na tsane ka i really hate you Yah ibraheem "

Tana gama fad'in hka ta fice daga part d'in hajia maamaa da gudu tana kuka gaba d'aya en
wajen mamaki ne ya kama su na abin da husna ta ce yarinya amman ta fad'i wad'annan
maganganun lallai ibraheem ya kai ta mak'ura, Yah Abdullah ne ya mike tsaye ranshi a 6ace
yana kallon ibraheem wanda ya daskare a tsaye (anya garin gyaran gira baxai rasa ido ba), Yah
Abdullah kuwa cewa yayi
"ka ga abin da nake gudu kenan ka riga da ka gama cusa tsanar ka a xuciyar husna har takai
da ta furta maka da bakin ta "
Yana gama fad'in hka ya fice daga falon kallon su Ilham yayi ya daka musu tsawa tare da cewa
"ku Kuma uban me kuke kallo "
Da gudu kowacce ta fuce kada ya huce akan su bedroom d'in shi ya shige ya xube kan bed tare
da dafe kan shi wani abu ne yake mishi yawo a cikin xuciyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0