Showing 18001 words to 21000 words out of 73884 words
son shi a cikin xuciya ta don baxan
ta6a bayyana kowa halin da nake ciki ba ko da xan mutu wannan tsakanina ne da
*DANGARTAKAR ZUCIya* na.
Nan fah husna ta dunga xuba mata hirar yanda ita ma take k'aunar Yah Abdullah Ilham duk ta
danne abin da take ji a cikin xuciyar ta ta dunga xuga husna kan ta saki jiki su sha soyayya
yanda ta dunga fad'in tayi dace da miji mai nutsuwa hankali, kyau uwa uba ilimi da yake dashi
da addini dana boko tana ta yabon Yah Abdullah har ta fara sakin layi anan husna ta xuba mata
ido tare da son karato wani abu a tattare da Ilham nan ta fara kok'arin d'iga aya akan Ilham
dawowar mamee ne daga wajen aiki ya katse mush hirar tasu.
A cikin Wannan lokacin wata soyayya mai xafi ake gudanar wa tsakanin Yah Abdullah da husna
bashi kaduna bashi abuja kullum yana faman xirga xirga duk week end, ana cikin hka ne result
d'in su Ilham, husna, raudah da Fadila ya fito ba 6ata lokaci aka sama musu admission a
university di'n kaduna tuni sun goge sun dad'a waye wa sosai barin ma husna daman duk a
cikin su ta fisu rawar kai iyayi ga Yah Abdullah ya tsaya mata komai yi mata yake.
Fadila kuwa har yanxu son Yah ibraheem yana nan acikin xuciyar ta jira kawai take ya dawo
don tana yawan yi mishi waya sosai ganin yana dan kulata yasa ta dunga kok'arin cusa kanta
tsab ya karance ta sai dai murmishi kawai yake don Akwai wadda xuciyar shi take so, yayin da
Ilham ma ta Duk'ufa da addu'a Allah ya cire mata son Yah Abdullah amman kamar sake cusa
mishi son shi ake a cikin xuciyar ta tayi kukan tayi cutar duk tabi ta rame sosai ta sake xama
silent daman can Ilham tana da sanyi kamar Yah Abdullah shima akwai hak'uri ................
_k'wana 2 kun ji mu shiru Kuyi hak'uri uxiri ne,ku cigaba da bibiyar mu don jin yanda xata
kaya_ν ½νΈ
Aishat A muh'd
*&*
Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:30] Aishat A. Muhd: ν Όν½ *DANGARTAKAR ZUCI*ν Όν½
*written by*
Aishat A muh'd
*&*
Sumayya salees sadeeq
_wannan page d'in sadaukarwa gare ku masoyan littafin *DANGARTAKAR ZUCI* kuna hak'uri
akan rashin jinmu da bakwa yi kullum_
*Page 25-26*
Haka lokaci ya cigaba da tafiya su husna sun yi nisa a karatun su sosai ana cikin hka hajia
maamaa ta had'a taron gaggawa wanda sun saba yin family meeting so wannan taron na
gaggawa da ta fad'a shi ya d'an d'aure musu kai don ko 2 weeks ba'a yi da yin family meeting
ba.
Gaba d'ayan su sun taru a babban palon hajia maamaa ban da Yah Abdullah da Yah ibraheem
amman duk sun had'u har su aunty marwa bayan an bud'e taro da addu'a hajia maamaa ta fara
magana kamar hka
"nasan xaku yi mamakin tara ku da nayi anan to ba wani abun ba ne sai abin alkhairi da xai faru
"
Sai lokacin hankalin su ya kwanta don duk gaba d'aya ba'a cikin nutsuwar su suke ba, d'an
gyaran murya hajia maamaa tayi kafin ta fara cewa
"gani nayi kun xuba wa Abdullah ido kun k'i mishi maganar aure bayan ya gama karatun shi ya
samu aikin yi gashi shine babba duk a 'ya'yan gidan "
Duk sunyi tsit suna jiran hajia maamaa ta K'arasa maganar ta cigaba da cewa tayi
"Don hka nayi tunani na yanke hukuncin xan aura mishi Ilham "
Gaba d'aya suka xaro ido cike da mamaki yayin da husna da Ilham sukayi suman xaune mumy
ce tayi k'arfin halin cewa
"husna kike nufi hajia maamaa koh? "
Girgixa kai hajia maamaa tayi tare da cewa "Ilham nake nufi ba husna ba "
Caraf raudah tace "wlh hajia maamaa Yah Abdullah da husna suke soyayya ba Ilham ba kowa
na gidan nan ya sani "
Harara hajia maamaa ta wurga mata tare da cewa "yo ai ni bansani ba na riga da kuma na
yanke hukunci ko iyayen ku basu isa ba su canja min balle ku "
Gaba d'aya jikin husna Idan ban da rawa babu abin da yake yi tsabar tashin hankali wasu
xafafan hawaye ne masu xafin gaske suke fito wa Daga idanun ta ta ma rasa tunanin da xata yi
sai en palon da take bi da kallo kamar yau ta fara ganin su kafe idanun ta tayi akan hajia
maamaa tana watsa mata wani kallo mai tattare da fassarori daban daban wanda bansan da
me xan fassara muku shi ba.
Abban Ilham ne cikin muryar lalla6a yace "Don girman Allah hajia maamaa kiyi duba xuwa ga
yaran nan kin ga suna son junan su ki duba ki ga shakuwar dake tsakanin su ma kad'ai ta isa a
aura musu juna balle sun amince xasu auri junam su ki kyale su ita Ilham Allah xai kawo mata
wani "
D'an shiru hajia maamaa tayi alamar tunani take sai suka fara addu'ar Allah yasa ta amince da
shawarar abban Ilham d'an gyaran murya tayi tare da cewa
"a gaskia ban yarda da shawarar ka ba mustapha yanda Abdullah yake da sanyi da hak'uri
xaman su baxai xo d'aya da husna ba dad'in da d'awa komai take so koda baya so to sai yayi
idan akayi auren juya shi xata dunga yi ni kuwa baxan lamunta ba Ilham ce dai dai dashi ita ma
akwai hak'uri ba ruwan ta, ita ma husnar xan sama mata dai dai da ita "
Wayyo tashin hankali bashi da dad'i husna batasan lokacin da ta K'arasa wajen hajia maamaa
ba ta rik'e mata kafafuwan ta kuka take har da majina cikin shesshak'ar kuka husna tace "Don
girman Allah hajia maamaa ki taimaka min kada ki raba ni da Yah Abdullah ina son shi please "
Duk da ta bawa hajia maamaa tausayi amman hka ta dake tace "aure babu fashi nan da sati
uku nake so ayi a gama na gama yanke hukunci kada wanda ya k'ara xuwa ya sake min
magana "
Tana gama fad'in hka ta shige bedroom d'in ta don kada husna ta rinjaye ta don ba k'aramin
tausayi ta bata.
Kuka sosai husna take duk sun tausaya wa husna masu saurin hawaye ma kukan suka fara su
Abba 1, Abba 2 da daddy suka bar falon kowanne xuciyar shi ba dad'i da hukuncin da hajia
maamaa ta xartar, nan suka dunga rarrashin husna amman kamar sake xuga ta suke Ilham ce
taxo ta rungume ta itama tana nata kukan wanda tak'amai mai bata gane kukan me take ba
kukan farinciki ne na jin dad'in Allah ya kar6i addu'ar ta ya bata Yah Abdullah a lokacin da ta
fidda rai akan shi ko kuma kukan tausayin husna da Yah Abdullah da suke masifar k'aunar
junan su ko kuma auren maso wani da xata yi don tasan Yah Abdullah sam baya sonta sai dai
na en uwanta ka.
A fusace husna ta hankade ta daga jikin ta tare da fice wa daga palon gaba d'aya duk da kallo
suka bi husna da tsantsar mamaki don husna da Ilham sun fi shakuwa da junan su suna shiri
sosai da wuya aji kansu sai gashi hajia maamaa tana kok'arin raba kanna su akan wani dalilin
nata na daban.
Kowa jikin shi a sanyaye suka tashi suna mai fargabar idan Yah Abdullah yaji wannan hukunci
me xai faru don kowa yasan yanda ya xuciyar shi ta ginu da k'aunar husna.
Tun daga lokacin husna bata k'ara shiga part d'in hajia maamaa ba tun da ta tsane ta bata
k'aunar ta daman tun farko a Cewar husna kenan daga skul sai islamia idan kaga husna ta fita
kenan gaba d'aya ta fita a hayyacin ta karatun ma bata fahimta sosai duk tabi ta rame tayi wani
iri ko yaushe idanun ta a kumbure gashi sunyi ja saboda tsabar kuka.
Ilham kullum sai taxo part d'in su husna tana nata kukan ita ma sam bata ji dad'in hukuncin da
hajia maamaa ta yanke ba, ko kallon ta husna bata yi don ita ma haushin ta take ji sai da
mamee ta yiwa husna fad'a sosai sannan take kula Ilham amman ba kamar da ba da kuma tayi
tunanin ita ma Ilham din ba laifin ta bane tun da had'a su aka yi dole ta hak'ura ko tak'i ko taso
kuwa don hka tun daga ranar da tayi wannan tunanin sai kuma suka cigaba da sha'anin su
kamar da sai dai fah son Yah Abdullah yana nan mak'ale a cikin xuciyar husna baxata iya cire
son Yah Abdullah ba sai dai ta mutu dashi, hajia maamaa kuwa husna ta dai na kula ta Ko part
d'in ta ta dai na shiga idan suka had'u sai dai kawai ta gaida ita baxa ta jira amsar ta ba xata
wuce gaba d'aya jikin hajia maamaa yayi sanyi tana jin tausayin husna.
Tun daga ranar da hajia maamaa ta yanke hukuncin auren Yah Abdullah da Ilham, husna bata
k'ara d'aukan kiran yah Abdullah ba to me xata fad'a mishi gwara ta fara sabawa da rashin shi
text mssg kira Hka yake yini yana kiran husna amman baxata d'auka ba sai dai ma ta koma
gefe tana xabga kuka mai ban tausayi tasan tayi rashin masoyin ta.
Hankalin Yah Abdullah ba k'aramin tashi yayi ba na k'in d'aga wayar shi da husna batayi gashi
ba wanda ya fad'a mishi don hajia maamaa ta gargad'i kowa kada wanda ya fad'a mishi Idan
yaxo yaji a bakin ta, ko yace a had'a shi da husna sai a fara yi mishi hanya hanya don daga
K'arshe husna kashe wayar nata tayi gaba d'aya ma, don hka a matuk'ar tashin hankali ya taho
kaduna.................
_Kuyi hak'uri da wannan battery low_ν ½νΈ₯
Aishat A muh'd
*&*
Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:31] Aishat A. Muhd: ν Όν½ *DANGARTAKAR ZUCI*ν Όν½
*written by*
Aishat A muh'd
*&*
Sumayya salees sadeeq
*Page 27-28*
Yana shiga gidan kai tsaye part d'in mamee ya nufa don shi husna kawai yake son yayi
toxali da ita yaji dalilin k'in d'aga wayar shi da bata yi, da sallama ya shiga palon mamee ce ta
amsa mishi sallamar tana xaune kan kujera da news papers a hand nata tana duba wa d'ago
kai tayi ta kalle shi har ya rame da ganin shi kasan yana cikin tarin damuwa tsantsa, xube wa
yayi kan carpet tare da gaida mamee sannan yace
"mamee ina husna ne? "
"tana skul don suna da lectures d'in yamma ne "
Mik'e wa tsaye yayi tare da cewa "mamee don Allah ko Kinsan laifin da nayi wa husna bata
picking d'in waya na? "
Dan girgixa kai mamee tayi gaba d'aya tausayin Yah Abdullah ya kamata dakyar ta iya bud'e
baki tace
"bansani ba Abdullah gaskia "
"okay mamee ki taya ni da addu'a Allah yasa ta huce duk da bansan laifin da nayi mata ya fad'i
yana rik'o hannun mamee gaba d'aya muryar shi rawa take alamun yana gaf da fashe wa da
kuka, kallon shi mamee tayi a cikin xuciyar ta tace lallai hajia maamaa tayi hangen nesa da an
had'a yah Abdullah da husna da bakaramin juya shi xata yi ba, sam baya son laifin ta yana
mata wani irin so da ko tayi mishi laifi baxai iya d'aukan mataki ba.
"kada ka damu Abdullah kaje ka huta tukunna "
Gid'a kai kawai ya iya yi sannan jikin sanyin jiki ya fice daga falon mamee ta bishi da kallon
tausayi tana jinjina halin da Yah Abdullah xai shiga da xarar ya ji labarin hukuncin da hajia
maamaa ta yanke.
Shi kuwa Yah Abdullah yana fita daga part d'in mamee kai tsaye shashen hajia maamaa ya
shige bankad'a labulen palon yayi ya shiga tana xaune a kan kujera ta k'wama glass a fuskar ta
tana kallon sunnah tv tana sauraron wa'azin sheik Isah Ali pantami cikin tsokana Yah Abdullah
yace
"kai wannan tsohuwar da nacin kallo take kullum a k'wama glass a fuska sannan a xuba wa tv
ido me kika sani? "
Hararar shi hajia maamaa tayi tare da dunkule hannun ta wara mishi su tare da cewa
"uban ka nake gani kaji yaro da rashin kunya ni xaka kalla kace me nasani "
xauna wa yayi a kusa da ita tare da cewa "tuba nake "
Tare da sa hannun shi cikin d'an k'aramin bowl di'n dake gabanta wanda cike yake da danyen
dabino nunannu masu kyau da xak'i ya d'ebo yana ci ya bud'e baki xai yi magana kenan wayar
hajia maamaa ta fara ringing don hka ta d'auka tare da mak'ala wa a kunnen ta tuni fuskar ta ta
fad'ad'a da fara'a tana cewa
"Waalaikumussalam ibraheem khaleel yanxu nake tunanin ka yinin yau gaba d'aya baka kirawo
ni ba, ince dai lafia? "
Ibraheem da yake xaune gefen swimming pool cikin wata kujera ya dad'a lafewa tare da lumshe
idon shi yace
"lafia qlau maamaa "
Washe hak'ora ta dad'a yi tare da cewa"masha Allah haka nake son ji"
Yah Abdullah sakin baki yayi yana kallon yanda hajia maamaa take 6angala fara'a kawai don
Yah ibraheem ya kirawo ta nan ya dad'a tabbatar wa ba k'aramin so take ma ibraheem ba.
Daga can 6angaren Yah ibraheem yace "ina ajiya ta dafatan tana nan lafia "
"ahh lafia qlau xaka xo ka same ta yanda kaban ajiya Insha Allah "
Wani shegen murmishi ya saki tare da shafa lallausar sumar kanshi ya cigaba da cewa
"alright, dafatan kin yi yanda na tsara miki "
"ae nayi yanda ka fad'i kasan bana son tashin hankalin ka ibraheem ka kwantar da hankali ka "
"okay granny xan dan kwanta na huta sai gobe bye "
"toh a huta lafia "
Tana gama fad'in hka ta sauke wayar a kunnen ta tare da ajiye wa muryar Yah Abdullah taji
yana cewa "akan me kuke magana da ibraheem? "
Harara ta dalla mishi tare da cewa "ina ruwan ka wannan sirrin mu ne bana son sa ido"
D'aga kafad'a yayi alamar can ta matse muku mik'e tsaye yayi tare da cewa"bari naje na d'auko
my husna daga skul don na matsu nayi toxali da kyakkyawar fuskar ta "
Tuni hajia maamaa ta K'ware da ruwan da take sha nan ta fara tari, Yah Abdullah yana mata
sannu har sai da tarin ya lafa sannan tace "Yawwa kama tuna min yanxu xauna xamu yi
magana da kai "
"ni kuma, gaskia ki bari sai na dawo "
Cikin er tsawa tace "idan da ubanka nake ya isa yayi min gaddama "
Ganin ta had'e fuska alamar ba wasa yasa ya xauna haka kawai yaji gaban shi yana mugun
fad'uwa dan kallon shi tayi tare da cewa
"so nake ka fitar da husna daga cikin xuciyar ka? "
Da sauri ya d'ago kanshi ya Kalli ta tare da furta "what!!! "
"ehh ae kaji abin da nace sarai na xa6a maka ilham a matsayin wadda xaka aura nan da 3
weeks "
A matuk'ar kad'uwa da firgita yah Abdullah ya mik'e tsaye tare da cewa "Haba maamaa idan ma
wasa kike ki daina bana son irin wasan nan ni ae husna nake so ba ilham ba "
"da gaske nake maka Abdullah ni kuma ilham ce xa6ina ita na xa6a maka ka aura "
"kuttt abin da baxai ta6a yiwu ba kenan "
"ka xuba ido xaka gani da idanun ka idan kaga an fasa Wannan auren sai dai idan na mutu
amman idan har ina raye wlh kaji na rantse sai anyi "
Gaba d'aya Yah Abdullah ya rikice hankalin shi yayi masifar tashi jin abin da hajia maamaa ta
fad'i wani gumi ne yake xiraro musu ta ko'ina saboda tsabar tashin hankali duk da sanyin AC
dake aiki a palon, cikin hargo wa ya fara cewa
"baki isa ba ki rabani da husna don xuciya ta ta ginu a k'aunar ta tun ina jin sonta dagani sai
*DANGARTAKAR ZUCIya* ta har takai na furta mata munyi alk'awarin aure a tsakanin mu xaki
xo da wani banxan hargitsin ki na tsufa kixo ki wargaxa mana farincikin mu "
Cikin tsananin mamaki hajia maamaa take kallon Yah Abdullah sai kuma ta fashe da kuka tana
tafa hannayen ta tare da cewa
"ni ka xaga Abdullah nice banxar? "
"ni fah ba xagin ki nayi ba kawai nace abin da baxai ta6a yiwu ba ne na auri ilham"
"yo xagi na nawa kuma ka xage ni kaci min mutunci don ina maka gata Indai ka auri husna mijin
tace xaka koma juya ka xata dunga yi yanda take so"
Wani irin kallo yake mata Kafin ya had'iyi yawu dakyar yace "so what don na xama mijin tace ae
ni kan tace ma zan xama don hka kiyi gaggawar kunce abin da kika kulluwa "
Wayyo Allah hajia maamaa d'ora hannu tayi akai tana gurzar kuka haik'an wai Yah