Showing 33001 words to 36000 words out of 73884 words

Chapter 12 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

522

tare da kallon cikin cup d'in
madara ce cike a cup d'in sai dai ta canja launi alamar an xuba wani abun bayan milk di'n kallon
mumy yayi wadda daman can shi take kallo ya yatsina fuska tare da cewa
"Wannan mene mummy?"
"maganine son "
"me yasame ni kuma mumy ni lafia ta qlau Kinsan ban son irin wannan maganin gargajiyar"
D'an hararar shi mumy tayi tare da cewa "da yake xan baka abin da xai cutar da Kai ba "
"no mumy sorry xan sha "

Yana gama fad'in hka yasa cup d'in a baki ya fara sha maimakon yaji d'aci sai wani gardin
madara ne da xak'in xuma ya baibaye cikin bakin shi sai d'an bauri Kad'an nan ya shanye shi
tas sannan ya mik'a wa mumy cup d'in kar6a tayi tare da cewa "Yawwa ko kai fa son ga wani
kuma" Xaro ido yayi yana kallon hannun cup d'in mumy tare da dafa ciki yace "wash mumy ki bari sai
anjima "
"A'a ibraheem yanxu xaka sha bashi da yawa ae kuma kankana ce da milk sai xuma"

Bashi da yanda xai yi hka ya kar6a ya fara sha yana mai jin kunyar mumy wato shi take gyara
wa kenan kamar wata mace shi yasa yake alfahari da mumyn shi.

Yana cikin sha Abdullah ya shigo falon kallon ibraheem yayi tare da kallon cikin cup d'in hannun
shi sai kuma ya kalli mumy yace "Mumy mene yake sha ni aka ware ni"

Murmishi mumy tayi tare da cewa "tambaye shi ga ka gashi magani ne yake sha "
Tana gama fad'in hka ta nufi kitchen, Yah Abdullah janyo ibraheem yayi kusa dashi a hankali
yake cewa "kai malam me kake sha Hka babu ajiye wa d'an uwa?"

Murmishi ibraheem ya saki tare da cewa " hmm Yah Abdullah maganine mumy ta sani a gaba
tana bani kamar wata mace "

Ya K'arasa fad'i yana Yatsina fuska dariya Yah Abdullah ya kwashe da ita Kafin kuma yace "kai
malam mumy ta kyauta xaka yi mata godia sai nan gaba mybe ma ka dawo neman Kari tana
gyara ka ne don kada mace ta rai na ka "

"koh? "
Cewar ibraheem yana ajiye cup d'in bayan ya gama sha.
"ofcourse yaro kuma xaka ce na fad'a maka, nima bari na bita kitchen na samu rabo na don
gobe xan gudu abuja "

Har ya mik'e tsaye ibraheem ya janyo shi ya fad'a kan kujera yace "kai Yah Abdullah ka tausaya
mata tana fama da tsohon ciki ka bari ta haihu mana "

Dariya suka tuntsire da ita lokaci d'aya tare da tafawa kamar wasu sa'annin juna cikin dariyar
Yah Abdullah yace "ka kawo shawara kuwa ibraheem na hak'ura "

Xumbur kuma ibraheem ya mik'e tsaye tare da cewa "ohhh my god Yah Abdullah ka 6ata min
time da surutun ka xanje duba jikin husna "

Yana gama fad'in hka bai jira abin da Yah Abdullah xai ce ba ya fita daga palon da sauri, girgixa
kai Yah Abdullah kawai yayi sannan ya shige kitchen Inda mumy take had'a wa ibraheem
abincin da xai ci.


Shi kuwa ibraheem yana fita ya nufi part d'in hajia maamaa, a dai dai time d'in husna ta farka
firgigit da sauri ta dafe kanta jin yanda yake mata ciwo sosai kallon d'akin take cike da matuk'ar
mamakin abin da ya kawo ta d'akin hajia maamaa a hankali kuma ta fara tunanin abin da yafaru
ae kuwa tana gama tunanin ta dage ta k'walla wata uwar k'ara mai k'arfin gaske, nan fah aka
fara riga rigan shiga d'akin tsakanin Yah ibraheem, hajia maamaa da ilham don su kad'ai ne a
part d'in.
Ihu take tana cewa "abin da baxai ta6a yiwu ba kenan amman kuwa an cuce ni a rasa wa xa'a
aura min sai Yah ibraheem wayyo Allah nah "

Tana gama fad'in hka kuma xumbur ta mik'e tsaye dai dai lokacin hajia maamaa, ilham da Yah
ibraheem sun shigo cikin d'akin da sauri hajia maamaa ta nufi wajen ta tana kok'arin rik'e ta don
ganin yanda take layi kamar wata er k'waya fincike jikin ta tayi da k'arfi tare da cewa
"kada ki k'ara rik'e ni na tsane ki kamar yanda kika tsane ni "

Sakin baki yah ibraheem yayi yana kallon husna bai yi wani yunkurin xuwa wajen ta ba, hajia
maamaa ta kalla sannan ilham lokacin da ta kalli ilham sai da ilham taji d'an cikin ta ya juya cikin
muryar tsiwa tace "Har da ke aka had'a baki wajen aura min mak'iyi na koh? "

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da Yah ibraheem ya furta a cikin xuciyar shi lokaci d'aya kan
shi ya fara ciwo, ilham kuwa cikin sanyin murya tace "taya xa'a had'a baki da ni a cuce ki husna
kuma maamaa da iyayen mu ba cutar ki suka yi ba gata suka yi miki kiyi hak'uri kiyi biyayya da
xa6in su "
Wani harara ta watsa wa ilham tare da sakin wani murmishin takaici ta tafa hannayen ta sau
uku tukunna tace " ke ma goyan bayan su kika yi ashe ke ma mak'iyiya tace lokacin da aka raba
ni da Yah Abdullah na hak'ura na sake samun wani masoyin mai sona da gaskiya muna k'aunar
junan mu aka raba mu to wannan auren shi ma hka xa'a raba shi "
Tana gama fad'in hka ta nufi hanyar fita daga d'akin da sauri hajia maamaa tace "husna ina xaki
je?"

Fad'in hka da tayi ta d'ago xata kalli hajia maamaa sai lokacin idanun ta suka sauka kan Dr
ibraheem khaleel wanda sai had'a uban gumi yake najin furucin husna yasan yarinyar akwai ta
da kafiyar tsiya Idan ta dage da abu.

Da har tayi niyyar taje ta rufe shi da duka ko ta samu sassauci cikin xuciyar ta sai kuma ta fice
da gudu ta barsu kowanne jiki a sanyaye xuwa part d'in su tana shiga suka ci karo da mamee
da sauri mamee ta rungume ta daman yanxu xata fito don ta duba ta sai gashi ta shigo ruwan
wanka mai xafi ta had'a mata tayi wanka ta fito mata da Kayan bacci ta sanya sannan ta had'a
mata tea tasha da d'an pepper soup din chicken tana gama sha kuma ta ba ta magungunan ta
tasha bayan ta gama sha ta bud'e baki xatayi magana kenan mamee ta tsikara mata allurar
bacci ae kuwa husna ta saki er k'ara ta jin xafi cikin en mintuna ta bacci yayi awon gaba da ita.

Tashi mamee tayi tsaye tana kallon husna cike da tausayin ta tana sani tayi mata allurar bacci
don ta samu hutu a kanta Idan ba hka ba tashin hankali xa'a yi tayi a daren amman xuwa gobe
da safe ta dan huce xata xauna su yi magana ta fahimta har ta samu damar lalla6a ta yarda da
xa6in da aka yi mata.
Tana niyyar fita taga ibraheem jingine jikin kofar d'akin yana kallon husna idanun shi sunyi ja
sosai, tuni tausayin shi ya kama mamee don tasan tabbas ibraheem yana son husna hannun
shi ta kamo xuwa cikin palon cikin sanyin murya yace "mamee mene yasa kika yi mata allurar
bacci da kin barta ta fad'i abin da take son fad'i an ta6a ta ne mamee da xan iya hak'ura da
husna da na hak'ura da ita na rok'e ki mamee ki lalla6a min ita ina son ta bansan yawan son da
nake yiwa husna ba mamee help me mamee please "

Cikin tsananin tausayin shi mamee tace "kada ka damu ibraheem ka cigaba da addu'a da kuma
hak'uri "

"Insha Allah mamee ngde "
Da hka ta lalla6a shi ya tafi don dare yayi nan kan kujerar ta xauna tana tunanin abin da ya

kamata tayi............





Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:37] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*

Aishat A muh'd

â™» *E.W.F*

*&*

Sumayya salees sadeeq

© *P.M.L*




*Page 55-56*




Tun daga lokacin husna da Yah ibraheem basu k'ara had'u ba har ya xama a yau xa'a kai
husna gidan yah ibraheem en uwa na kusa sun xaxxo har wata er k'warya k'waryar walima
akayi, Kafin kuma da yamma wajen 5 aka mik'a husna gidan ta bayan tasha nasiha sosae a
wajen mamee da daddyn ta ga sauran en uwanta su ma sunyi mata nasiha sosae hajia
maamaa kuwa addu'a tayi mata tare da sanya mata albarka tun da yanxu ta hak'ura xata xauna
da d'an gaban goshin nata, har da ita aka kai husna don daman tayi alk'awarin ita da kanta xata
shigar da matar ibraheem cikin d'akin ta ae kuwa hannun ta rik'e da hannun husna har ta

xaunar da ita kan katafaren gadon ta, husna kuwa har tayi kuka ta gaji hawayen ma sun daina
fito wa daga idanun ta sai faman ajiyar xuciya take saki lokaci xuwa lokaci.

Ana sallahr mangarib en uwa suka yiwa husna sallama suka tafi ya rage gidan sai husna, aunty
rufaidah da aunty aimana sai da suka gyara mata ko'ina na gidan suka kunna turaren wuta mae
k'amshi tuni ko'ina ya d'auki k'amshi mai dad'in shak'a bayan sun gama su ma suka k'ara yiwa
husna nasiha tare da bata shawarwari masu kyau tukunna suka tafi aka bar husna ita kad'ai
bata ji wani tsoro sosai ba tun da ko'ina akwai haske kamar da rana.

Kayan jikin ta ta cire ta d'aura towel ta shige toilet wanka tayi tare da alwala bayan ta fito ta
shirya cikin wata blue sky din sleeping dress doguwa ce har k'asa mai siririn hannu ta gyara
gashin kanta sannan ta fesa different perfumes nd body spray masu matuk'ar k'amshi.

Abin sallah ta shimfid'a bayan tasa dogon hijab mai hannu har k'asa ta gabatar da sallahr isha'e
bayan tayi addu'o'in ta kamar yanda ta sa ba sannan ta mik'e tsaye tare da cire hijab d'in nata
jiyowar da xata yi suka had'a ido da Yah ibraheem tsaye a jikin kofar d'akin yana kallon ta
hannun shi rik'e da wasu manyan leda wani wawan tsaki taja kamar xata tsinke harshen ta.
Duk da Yah ibraheem a duniyar nan ya tsani tsaki kuma ranshi ya 6aci amman bai nuna ba
tunda sulhu yake nema, ajiye ledar hannun shi yayi kafin dakyar yace

" ga wannan ko xaki buk'aci abinci "
Yana gama fad'in hka ya juya da niyyar fita har ya fitar da kafafun shi daga cikin bedroom d'in
husna kamar abin arxiki ya bud'e baki tace
"Yah ibraheem "

Cak Yayi ya tsaya jin ta ambaci sunan shi juyowar da xai yi sai gani yayi ta cillo mishi wannan
ledar da ya ajiye a fuskar shi tuni kayan ciki suka tarwatse gaba d'ayan su a k'asa cikin tsanar
shi tace
"an gaya maka ni mayunwaciya ce, bana son duk abin da ya fito daga hannun ta i hate u"
Tana gama fad'in hka ta rufe kofar ta tare da sa mata key kan bed ta koma hankali kwance ta
kwanta tare da yin addu'ar bacci bata dad'e ba bacci yayi awon gaba da ita.

Shi kuwa Yah ibraheem kallon kayan da ya tarwatse a k'asa yake duk da ranshi ya 6aci sosai
akan abin da husna tayi mishi ya riga da ya yiwa kanshi alk'awarin baxai ta6a tanka mata ba har
xuwa lokacin da xata huce ya bata hak'uri tare da neman soyayyar ta don kuwa duk abin da
xata yi mishi xai danne xuciyar shi.
Yana gama wannan tunanin ya nufi inda ake ajiye Parker da abin yin mopping ya d'auko share
wajen yayi tare da goge wa tukunna ya shige bedroom d'in shi wanka yayi tare da yin alwala
sannan ya fito ya shirya cikin wasu sleeping dress farare sol dasu kan abin sallah ya hau ya
fara jera nafila na godia ga Allah tare da addu'ar Allah ya karkato mishi da hankalin husna
kanshi yasa ta so shi ko da rabin son da yake mata ne hka ya raya daren cikin bautar ubangiji

har xuwa asuba bayan ya yi sallahr asuba ne bacci ya d'auke shi mai dad'in gaske xuciyar shi
cike da tunanin abar son shi husna.


Washe gari da safe bayan husna ta tashi daga bacci wajen karfe 9:30 na safe brush tayi tare da
shan ruwa cikin glass cup d'aya don yana taimaka wa jiki sosai yin hka kuma wannan shan
ruwan safen Kafin taci komai horan mameen ta ne.

Gyaran bedroom d'in nata tayi sannan ta gyara falon ta da kuma babban palon gidan tasa
turaren wuta ta turare gidan da k'amshi sannan ta shiga toilet tayi wanka ta shirya cikin wata
tsadaddiyar atampha kalar blue d'inkin riga da siket ne sun amshe ta kayan ta d'aurin
dankawalin ta mai kyau bata yi wata k'walliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple
amman duk da hka ba k'aramin kyau tayi ba tana cikin fesa turare taji an danna door bell don
hka tana gama fesa wa ta fito xuwa falon ta bud'e kofar er aikin mumy ce shige wa tayi ta xauna
er aikin ta gaida husna tare da cewa
"gashi inji mumy tace na kawo miki "
Ta fad'a tana ajiye basket d'in xuba kayan abinci ga hadaddun food flaks a ciki
"Okay je ki ajiye min kan dinning table "
"toh aunty "
Da sauri taje ta ajiye bayan ta dawo tace " aunty Ko da wani aiki da xan yi miki?"
Girgixa kai husna tayi tare da cewa "nooo babu komai wa ya kawo ki? "
"driver ne"
"Okay Shikenan "

Daga hka ta yi mata sallama ta tafi, kitchen husna ta shiga taga yanda aka tsara mata kitchen
d'in ya had'u sosai kalar green ne plate ta dauko da cup d'in had'a tea tare da spoon and fork
dinning table ta nufa ta ajiye nan ta tarar da kayan tea milk, bournvita, cornflakes da dai sauran
su nan ta had'a tea tasha tare da cin chips and egg sai er source tare da plantain,sai da ta koshi
sannan ta tashi ta dawo falo ta xauna wayar ta ta d'auko nan ta fad'a duniyar charting sai hira
suke a grp d'in su wanda suka bud'e mai suna 4 sister's for life husna, ilham, Fadila da raudah
suna ba wa junan su shawarari masu amfani sosai sai tsokanar husna ita kuwa tana bawa kowa
amsar da ta dace.

Wani k'amshin turare ne ya bige hancin ta saboda dad'in k'amshin sai da ta lumshe idanun ta
Kafin ta d'ago kanta suka had'a ido da Yah ibraheem yana sanye cikin wani blue d'in jeans da
t-shirt black mai dogon hannu yayi kyau sosai kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake cikin
takun tafiyar shi ta kasaita ya nufo inda husna take xaune wadda ta danna mishi harara Kafin ta
mayar da hankalin ta kan wayar, k'arasa wa yayi ya xauna kusa da ita har kafad'ar shi na gogar
ta ta da sauri husna ta matsa gefe cikin murmishi yace
"Gud mrng sweetheart, i hope kin tashi lafia? "

Bata yi mishi magana ba hka kuma bata sake kallon Inda yake ba K'arshe ma sai ta shige cikin
bedroom d'in ta da kallo ya bita yana murmishi tare da shafa gashin kan shi xuciyar shi cike da

tsantsar k'aunar ta da sha'awar ta da hka ya tashi ya nufi dinning table yayi breakfast sannan ya
fita daga gidan gaba d'aya.

To Hka abubuwa suke tafiya tsakanin husna da Yah ibraheem bata kula shi k'wata k'wata ko
magana bata yi mishi ko da yayi mata kullum shine xai gaida ita Idan suka had'u a palo but
husna bata amsa wa amman hkan bai sa ya fasa yi ,ga wata axababbiyar sha'awar husnah da
ta dame shi saboda irin shigar da take yi wani lokacin ba k'aramin tayar mishi da hankali take ba
kusan k'wana yake murkususu akan bed da yana da ra'ayin kula mata waje da tuni yayi saboda
sha'awar da take damun shi sosai abin ya fara ramar dashi ya rasa ta yanda xai rarrashi husna
ta amince dashi don ya kawar da abin da yake damun shi.

Idan abin ya dame shi sai dai yasha maganin da xai dan samu sauk'in abin, ana cikin hka daddy
ya kammala gina mishi hospital d'in shi an gama komai an xuba kayan aiki sannan ya nemi
kwararrun likitoci an xuba a asibitin ranar da akayi bikin bud'e asibitin ko da ya sanar da husna
ko tanka mishi Bata yi ba.
Ana cikin hka suka kwashe tsawon wata 3 da aure husna tana xuwa skul d'in ta don ya kyaleta
ta cigaba su ma suna gaf da kammala wa drive guda ya ajiye mata wanda xai dunga kai ta skul
yana dawo da ita, kuma har a yanxu husna bata je gida ba tun da aka kawo ta gidan Yah
ibraheem rabon ta da gida, su fadila da raudah sun xo mata yini rana d'aya suka xo sun sha
hira sosai kamar kada a rabu kowacce da tsarabar amarci don Sun samu ciki husna sai tsiya
take musu suna rama wa ranar sunyi yinin farinciki sosai sai da yamma Yah mus'ab da Yah
yaseer suka xo d'aukan matan su bayan sun taso daga aiki ae kuwa husna ta rik'e su sai da
suka yi dinner agidan tukunna su ka tafi, hakurin Yah ibraheem ya fara karewa don hka ya fara
tunanin neman mafita.

Kamar yau ranar sunday weekend kenan yah ibraheem yana xaune a palo sanye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0