Showing 30001 words to 33000 words out of 86820 words

Chapter 11 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

769

manya me zafi na dubu
daya ta saka a ledar ta shiga Napep sai gidan Aslam,shi Kuma yayi wanka sosai ya Sha kana
Nan kaya ya zuba kyau abinka ga me kyau da aji ya bude kofa da Niyyar zuwa gidan su Siyama
sai ya ganta tana Shirin biyan me Napep kudi,Me Napep ta tsayar tace to gashi ma na ganshi
karka tafi tsaya ka maidani gida,Aslam ne yace me Napep jeka Zan maidata,Siyama tace bafa

shiga gidanka zanyi ba yanzu baka da Mata bazan shiga gidan Gwauro ba,Murmushi Aslam
yayi yace me Napep jeka Kawai don't mind her, Me Napep yayi gaba abinsa,Siyama ta tsaya a
gaban Aslam ya kalleta yace kina Jin dadi Siyama irin wannan wanka haka,dariya tayi ba shiri
tare da Mika Masa ledar abincin tace tafiya zanyi ni,yace Kinga nan wajen duk student ne ki
saki jikinki ga waje can mu zauna to a waje,Kan wani tudun siminti me Fadi Suka zauna ya
bude ledar ya dakko abincinsa a wajen ya fara ci ya saka kifinsa soyayye Yana ci yace kamar
kin San yunwa nake ji,Siyama ta kalle shi tace karka yabi yanda na iya girki ni bana so ma
yanzu, Wai dan ya yabeta taji bai yaba ba shi yasa ta Fara Masa hannunka me Sanda,Dariya
Aslam ya fara sosai,tace ae Kar dai ka yabeni nace, fuskarta yake kallo yasa hannu a hancinta
ya cire Mata wani dan zare baki da ya makale mata,sai da ya cinye abincin tas tana kallo
sannan ya Shiga gidansa ya Sha ruwa ya fito ya sameta yace tashi muje yawo,Siyama ta mike
Suka jera suna tafiya suna Shan iskar gari suna tafiya Kamar saurayi da budurwa,Siyama tace
kawata dai ta matsa an saketa, Aslam yace tayiwa kanta ta rasa saurayi me tashe,Siyama ta
kyalkyale da dariya har da durkusawa tana dukawa kasa tana dariya,Aslam yace get up sarkin
dariya ya riko hannunta tare da janta sama ta mike tana kwace hannunta,sai Yamma likis
Siyama tace zata tafi Napep ya tare Mata ta shiga shima ya Shiga tace ya naga ka shigo
Kuma?

Yace gida Zan kaiki da kaina Suka tafi tare again Suna sauka a Napep Suka yi arba da
Nusaiba da Mama sun dawo daga unguwa,Mama ta nuna Siyama da hannu tace ke butulu
ashe kadan kike jira dama kaga maciya amana,Nusaiba Kuwa dariya ta hau shekawa tace
Siyama kice da gaske kina ciki yanzu wannan gidan Zaki shiga hhhhhhh ta sake kecewa da
dariya tace asha talauci lafiya karki ji kunya Ni Kam na bar miki wlh bana Yi,Siyama ce ta kalle
su tace mahaukata Jahilai an fada Miki tsoronki zanji ko bai sakeki ba kina jin Zan kasa aurensa
idan nayi niyya,Kuma wallahi da Sannu sai kunyi kuka Watarana,Aslam Yana jinsu yace Kinga
let's go Siyama kina saurarar Wanda basu San me suke ba a duniya magana da su ai bata
lokaci ne,Mama tace iyye wato Aslam yanzu na zama waccen ban San me nake ba ka manta
Sanda kake zuwa kana roko a aura maka Nusaiba,Aslam hannun Siyama ya rike tare da janta
Suka tafi,Mama tace yau Naga dan iskan karshen zamani Kinga harda rike hannunta wato mu
gani Yana sonta,Nusaiba tace Mama ke Kika damu dashi ga sabon me kudi nan new Money
Sufyan muje Kawai Suka tafi gida tare da Mama ko a jikinsu.
Aslam kuwa Kuwa a kofar gidan su Siyama ya tsaya Suka ci gaba da hirar su cike da nishadi
da farin ciki.





Waye Aslam

AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢�AUREN MU🛢�

41-45


Official


By
AsmaBaffa






Page naki ne

Fateemah Farouk
Ameerah Abdussalam
Hanana Smart









Aslam Shareef Alhassan cikakken Fulanin Mambila ne gaf da Cameron fulanine
usil,babansa Shareef Alhassan me tarin arziki ne na shanu da kadarori sannan Kuma Yana da
ilimin addini Dana zamani Alhaji ne sosai a Mambila,auren zumunci aka Masa da Yar uwarsa
Zuwaira wato Maman Aslam Mum,sai da Aslam ya girma bayan an haife shi yana secondary
Suka dawo Kano da Zama lokacin kasuwancin Shareef ya shahara ga siyasa Yana yi Katsam
Allah ya Masa rasuwa sanadin hatsarin jirgin sama zuwa India,Bayan komai ya lafa Juwairiyya
mum wacce suke cewa Zuwaira itace taci gaba da kasuwancin Kamar Namiji tana daukan
nauyin danta Aslam yayi ilimi har ta kaishi kasar waje America karatu lokacin Mum arziki yaci
gaba sosai ta bunkasa komai Dake Allah yayita da kwazo da fasaha Kuma itama tayi ilimi har

matakin Diploma a hannun mijinta tayi Diploma sannan komai nasa Yana shawara da ita da
taimakonta ake komai sabo da Haka Yana rasuwa ta Haye karagarsa taci gaba da juya Dukiyar
Aslam Allah Kuma yasa shi kadai Suka Haifa dama dangin su Mum kusan basa haihuwa da
yawa daga me haihuwa Daya sai me haihuwa biyu haka suke,tunda iyayensu Suka rasu gashi
Basu da yawan dangi sosai tunda basa haihuwa da yawa wannan yasa zumuncin ma Sai lokaci
lokaci suke zuwa can,Sai Kuma Yan Uwa Wanda suke aure a Kano ko Kaduna.

Aslam a haka ya Zama saurayi kyakyawan Matashin hadadden gaske ga iya daukan wanka
ga saka sutura duk inda ya wuce kamshi yake zubawa Kamar me,gashi da addini ga hakuri ga
hankali gaba Daya iyayensa ya gado a kyakyawan hali ya samu tarbiya da ilimin boko Dana
addini,Yana yin masters sannan Mum ta kyaleshi ta damka Masa dukiyarsa a hannunsa ya
koma juya abinsa,Aslam sai da ya Zama hamshakin Mai mudi Kai da gani ba karya bai fuskanci
wani Jarabta ba ba ko daya kullum a huce yake,Mum gaba daya sabo da Yana damunta da aiki
ya Masa yawa sai ta gudu Qatar inda kanwar Babarta ke aure a can suke zaune abinsu ,duk
haka Aslam sai Sanda yaga dama yake zuwa Office Sai wasu kamfanunuwan nasa da yake
lekawa Yana kula da ma'aikata tsabar son hutunsa idan yaga dama Sai yayi sati biyu a iya
samansa ba tare da ya sakko ko kasa ba,har Allah ya hada shi da su Nusaiba ya sota Kuma ya
aure ta a Nan jarabtarsa take shi kam.

Aslam fari tas kyakyawa ne ajin farko,dogo ne amma ba can ba haka ba ramamme ba baza
Kuma ace me kiba ba,sumarsa baka wuluk ce me yawan gaske taji gyara style style yake Mata
Kamar dan turai,hancinsa dogo ne ba can ba bakinsa karami me dauke da jajayen
lips,idanuwansa matsagaita masu kyau,sannan fuskarsa ba me Fadi ba Kuma ba sirirya ba
komai nasa chas dai dai kowacce mace ta ganshi sai ta kyasa.

Siyama
Siyama Ahmad Sani Yan Niger ne asalinsu buzaye ne amma tun iyaye da kakanni a Kano Suka
taso a Kano Suka gansu daga zuwa Neman kudi Suka dinga hayayyafa har Suka tara dangi a
Nan Kano Kuma sun watsu gari daban daban wasu a kauyen Kano wasu a birni,Baban Siyama
Ahmad Wanda suke cewa Amadou kanin Dauda ne kawun Siyama bayan Dauda yayi aure
Allah bai bashi haihuwa ba gashi su biyu ne rak a wajen iyayensu,Dauda Yana ta aure aure
amma ko wacce mace rashin haihuwa yasa take ficewa har ya gaji da aure ya hakura,shi kuwa
Ahmad Yana aure shekara daya Matarsa Maryam ta Haifi yarta kyakyawar gaske fara,ai
Maryam tana haihuwa abinka da zumunci irin na da Amadou ya kira yayansa yace yayi 'ya
matata ta Haifi mace amma na bar maka ita halak malak sabo da haka Suna ma Kai zaka zaba
Mata,Dauda harda kukan farin ciki yace na zabi Siyama a saka mata,ai Kuwa yarinya taci suna
Siyama,Dauda dalilin kyautar yarsa Siyama ya nemi Hajara wato Aunty wacce bazawara ce
itama bata haihuwa Kawai ya aureta tunda lalurarsu iri daya ce.

Ranar da aka yaye Siyama Amadou ya dakko Siyama da kayanta kaf ya kawowa Dauda har
gidansa Dake rijiyar lemo Kano yace Yaya ga yarka na kawo maka ta damemu da fitina,Dauda
yace a bani a bata dama duk kewarta ta dameni ya karbe Siyama,Amadou akan hanyarsa ta
komawa gida mota ta bige shi Nan take ya rasu,Dauda Kamar zaiyi hauka har gobe idan ya

tuna Amadou sai ya zubar da hawaye,Siyama ta taso cikin gata so da kulawa sai abinda take
so duk duniya ba Wanda Dauda yake so sama da Siyama,itama Aunty ta dauki son duniya ta
dorawa Siyama sakamakon bata taba haihuwa ba,macece me iya Zama da mutane ga iya raino
da kula haka ta tsaya akan Siyama har ta Isa zuwa makaranta Suka sata a makarantar boko da
Islamiyya,data Kara girma har makarantar dare take zuwa shi yasa Siyama take da kokari
primary ma private aka saka ta shi yasa take Jin turanci sosai,..

Sun taso a unguwar tare da Nusaiba dake layinsu daya ita Nusaiba ma har primary ta
gomnati tayi sabo da talauci,Sanda Shehu yayi Dan kudin nasa basu taso ba,Kuma ba kudi
bane rufin asiri ne Kawai, ana Kai Siyama Secondary school Suka hadu da Nusaiba a can,ko a
class Nusaiba dama bata da mutunci idan ta Raina kurar mutum zaiga wulakanci,Bata kawa da
mutum sai tasan kun fita arziki shine zata Shige maka abinda ya hadata kawance da Siyama
kenan idan taje gidan su Siyama zata ci shinkafa da Miya su kuwa gidansu sai a kwashe wata
guda ba ayi shinkafa da Miya ba,suna Ss2 Nusaiba ta daina zuwa makaranta sai tallan kosai
kannenta ke zuwa sabo da talauci gwara ta Nemo musu ko zasu samu abincin ci,Siyama Kuwa
ita da sauran sun Gama secondary school suna da shekaru 19 tana zaune sai dai tallan su har
ta Kara shekara hudu Wanda da akwai kudi da tuni sun Gama degree,yanzu sun Kai 23yrs, Yan
Mata ne sosai .
Siyama doguwa ce Fara me round face me dauke da dogon hancinta zarkadede,idanuwanta
manya dasu masu kyau kamar tana Jin bacci haka take sai ka rantse bacci take ji kullum a
Haka take,gashi ne da ita sosai gata da dan jikinta mul mul ba Kashi sai dai ba me kiba za a ce
ba,komai mashaallah.
Nusaiba Kuwa Yan asalin Rogo ne wajen jahar Kano Shehu dan dangi ne Yana da Yan
Uwa da yawa sai dai Basu da Hali duk talakawa ne a kauyen Rogo,itama Mama tana da nata
Dangin da yawa a Rogo amma guda Daya ce wacce suke uwa Daya uba daya sauran duk
dangi ne, Amma duk cikinsu babu me iyaye duk sun mutu tunda Suma sun tsufa bare iyayensu
sai dangi,Mama me Suna Bara'atu Yar asalin kauyen kayau ce a Rogo ma a wani mugun Kauye
take Wanda basu karatu Babu ilimin Addink bare boko,a haka Shehu ya nace sai ita shi yaga
fetsarariya dama sai da aka fada kaf gidan su Mama basu da mutunci a kauyen basu da Kara
Basu da kunya su kamar a jininsu yake Imaninsu kudi Kawai,Shehu yace ba komai zai sata a
makaranta,Bayan ya aureta tun Yana zuwa cikin birni cirani har ya mallaki filinsa ya Gina ya
dakko Mama daga Kauye ya dawo da ita birni,ya sata a makarantar yaki da jahilci ta matan
aure inda ake koya musu ilimin addini da karatun hausa

Mama ita ko a makarantar ma dakikiya ce sam bata ganewa sai ta dade a aya Daya,aya daya
sai ta kwashe satikai bata iya ba,a Haka ma dan Shehu Yana koya Mata a gida,idan Suka Zo
karatu ta dinga kunkuni da masifa kenan Shehu har rankwashinta yasha Yi sabo da jahilci da
kin karatu,Fatiha ma Sai da ya tsaya a kanta sosai ta iya,ya koya Mata wankan haila da
komai,Sallah ma Shehu ya koya Mata,a hankali Mama ta Fara Zama tsagera a unguwar,duk
Sanda Shehu ya siyo kayan abinci kwana kadan sai yaji tace ya kare, sai da masu shagunan
unguwar Suka fada Masa cewar matarsa fa tana kawo musu su shinkafa,taliya etc suna siya ya
sa ido Ashe siyarwa takeyi ta soke kudin,Shehu ya Kai kararta gidansu yafi a irga karshe ma

Dangin Mama suci ubansa ya dawo bashi da bakin fadawa Yan Uwansa tunda dama tun farko
sun hanashi yaki ji,ana Haka Mama ta haifo yarta mace,Shehu yace zai maida sunan uwarsa
Mama tace bai Isa ba ita tun tana yarinya take mafarkin yarta ana fada Mata a mafarki sunan
yarki Nusaiba,Shehu yace sai kace wata manzo ko waliyiya to baki Isa ba,Suka dinga fada
karshe dole ya hakura ya saka suna Nusaiba ta Haifi Danta na biyu Nan ma ta kafa ta tsare
tace Ameer ake yayi shi za a sawa danta,Shehu ya saka,ta haifo Ihsan

Tace yanzu an waye sunayen larabawa ake yayi Ihsan kawai,Shehu ya kyaleta ya saka sai
da kyar da ta sake haihuwa ta yarda aka sa sunan Babar Shehu Asmau ai Kuwa tace Husna
Kawai ita fa ta waye Kuma baza ta boye ba ai ba uwarta bace haka ta Haifi yaranta karshe ma
Shehu Yana son haihuwa tace ta gama tayi planing shike nan ta tsaya da haihuwa abinta, gaba
Daya tafi karfin Shehu ya rasa inda zaiyi da ita,wulakanci iri iri,da kudinsa Shehu zai siyi abinci
amma idan ta dafa ta hanashi sannan yaranta kadai zata bawa Kuma Suma kadan sai ta siyar
da sauran taci tsire da kudin, idan taga dama zagin Shehu ma takeyi shi Kuma Shehu hakuri
yake da ita Kawai Sabo da yaranta,duk sabo da yaran data tara yake kyaleta sabo da idan ya
koreta ma ya zaiyi da yaransa sannan rashin uwa a zamanin nan ba karamin matsala bane ga
Yara shi yasa Kawai yake hakuri,akwai Sanda ma idan Suka Yi fada to da wuri zata rufe gidan
idan Shehu ya fita masallaci Sallar Isha ya Sha kwana a masallaci
Ita Kuma bata ganin hakurinsa haka tunaninta Kawai Dan ta Isa ne ko masifarta ce tasa,ya
rasa ya zaiyi da ita Kawai ya daina bata ficika Kuma ya daina bata abinci Wai ko zata Yi
hankali,wannan talaucin yasa Mama tayi laushi ita da Nusaiba Kawai ta ya zasu ci su koshi
suke yi amma gashi Aslam Yana zuwa Suka samu kudi sai wulakanci Kuma Wanda yafi na
baya ma,gidanta Kuma da Shehu yace ya siyar ba siyarwa yayi ba gani yayi akan Addua yarta
ta bace zata siyar da gidanta yaji tsoro ne Kar ta koma bin bokaye abin bazai Yi da kyau ba shi
yasa yayi Mata wayo ya nuna ya siyar da shi,duk wani zalunci sau tari ba zakuntarta yake Yi ba
Yana yi ne sabo da nemawa Kansa sauki sai gashi dai karshe sai da ta kaishi ga zaluntar
yaransa da matar ma tunda ya hanasu abinci Wanda hakkinsa ne,ita Kuma
Nusaiba tun tana karama zuwa tasha talla da yawan rike kudi shi ya jawo idonta ya bude da
kudi da shegen son kudi Idan kaci kayan me talla ka hanata kudi zaka ga rashin mutunci shi
yasa takewa Aslam haka ta Saba fada da maza a wajen talla dama mafadaciya ce Kawai dai ita
ba Yar iska bace bata bari a kawo Mata iskanci amma talla Yana daya daga cikin abinda ya
jawo Nusaiba tafi karfin kowa bata tsoron kowa komai girman mutum ga Kuma gadon su na
uwa wajen rashin mutunci da rashin sanin ya kamata,Mama sabo da rashin karatunta shi yasa
Bata damu da ilimin yaranta ba.

Nusaiba wankan tarwada ce Kuma ba laifi tana da kyanta dai dai gwargwado baza ace Mata
mummuna ba,itama doguwa ce sai dai siririya ce amma ba can ba sannan tana da shape dinta
dai dai ita Kuma dama Indai ta samu Kayan kwalliya to Yar kwalliya ce sabanin Siyama da tun
tana karama bata kwalliya ita sai dai ta sa Riga da wando Bata taba saka skert ko zani kullum
da Riga da wando har ta girma take zuwa wajen gwanjo ta zabo kala kala masu Fadi manya
manya hakan yasa aka sa Mata suna Charity tace Begins at home taji ta karba shike Nan
sunan ya bita Indai baka ce Siyama Charity ba Babu me ganeta ko kace Siyama sai ance
wacce? Sai kace Charity sannan za a gane.

Charity saka Riga da wandonta ya jawo Mata bata samari da yawa sai dai dai kadan amma
Nusaiba Kuwa Allah ya bata kowa sonta yake sabo da Yar kwalliyarta,Kuma Charity gata
kyakyawa Fara amma Riga da wando yasa ba a zuwa ma wasu ma zaton su Yar Igbo ce in ka
ganta haka,Nusaiba Kuwa iyayinta kadai da gwalli Yana jawo Mata samari amma bata taba
samun me kudi ba sai Aslam shi yasa Kawai ta aure shi Dan kudin ita Indai Namiji me kyau ne
baya birgeta tafi son kudi duk kyansa bata bukata
Siyama Kuwa Samarinta Basu da yawa amma duk na kirki ne masu sonta tsakani da Allah
Kuma masu rufin asiri ne kowanne ba na banza lokacin bata son zancen ma aure harkarta
takeyi tunda Dangin Hunaif Suka Mata sharrin Yar lesbian ce ta daina kula kowanne Namiji
harkarta Kawai takeyi,kowa kallon wata Yar duniya yakewa Siyama ana yiwa Nusaiba kallon
mutuniyar kirki,Haka Kawai ma Siyama bata Yi komai ba za a dinga Mata kazafi a layin ana
gulmarta musamman samarin layin sun sata a gaba. wannan kenan

Yau Affan yayi Niyyar zuwa gidan su Siyama,Liman ya bashi number Dauda kawun Siyama
yace idan yaje ya Kira shine kawun Yarinyar, Affan wata sabuwar Shadda ya bare gal dinki me
kyau na manyan samari masu tashe da ji da kansu, Yana furta Siyama...Wai Siyama yo ai naga
Sima ma karewa, shiri ya Fara ya sa wani short tight ya matse shi sosai ya kalli Kansa yace
yawwa Yana kallon Sandar girma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0