Showing 9001 words to 12000 words out of 86820 words
barshi,Mama cikin jarinta ta dauki dari biyar ta
bawa Ameer danta tace ungo kaje masallacin juma'a kaga yau Juma'a ka siyi ruwa na du kudin
ka rabawa Alummar annabi Allah ya bayyana Mana su Nusaiba,Ameer ya karba da sauri ya tafi
zai siyi ruwa ya rabawa Alummar annabi Sadaqa,Mama tana da filinta na gado ta ajiye
abinta,sabo da tayi Sadaka Allah ya bayyana Mata yarta tace zata siyar da filin,Shehu Sadakar
dari biyu ya kasa Amma tana daga filinta zata siyar yace zai siya ya lallaba Mama zai siyi fili,filin
a Kauye yake Bai wuce dubu dari biyu ba amma Shehu yace filin Bai wuce dubu dari da talatin
ba Mama bata San Kan komai ba yace ya siya zai bada kudi ya lallaba ya karbe takardu tayi
signing da komai shima haka ba shedu bata fadawa kowa ba Shehu ya hana kudi tana ta binsa
karshe ma Sai labari taji ya siyar da filin dubu dari uku Kuma ko ficika bai bata ba,idan tayi yaji
ta tafi ta barwa wa yaranta ga yarta har sati guda shuru,Mama ta kwana takeyi tana kuka tana
kaiwa Allah kukanta.
Charity idonsu duk ya kumbura sabo da kuka basu ga kowa ba Kuma an hanasu fita,Oga zai
iya sati biyu a gida ba tare da ya leko ko compound ba Haka yake shi,Sun wanke kayansu ya
bushe sun maida shi jikiksu bayan sunyi wanka,Palo Suka dawo Suka zauna babu Wacce
tayiwa Yar uwarta magana sunyi jugum jugum a Palo,Tv tana yi Amma ko kallonta basu
Yi,kamshi suka ji ya mamaye palon,wani me uban kyau Suka gani yana sakkowa daga steps
sanye yake cikin wani silk doguwar Riga Kuma armless gefe da gefe an tsagata Silver color
takalminsa ma haka sumarsa ta Sha gyara na musamman fadar kyawunsa bata baki ne komai
nasa na daban ne,sheki Kawai yake da walwali,kwarjininsa ya kamasu Suka kasa magana har
ya samu kujera ya zauna irin Zama na isassu na masu Hannu da shuni kana gani kasan Hutu
ya ratsa shi.
Gyaran murya yayi kadan lokacin Charity tace Ina yini cike da Ladabi Nusaiba Kuwa ta kafe
shi da Ido tana kallonsa sai da Charity ta dan bigi hannunta sannan tace Ina kwana au na
manta Ina yini? A takaice ya amsa ya kalli Nusaiba yace ke kina kama da Baban Mum da gani
jikarsa ce ko?,da sauri Nusaiba tace ae,ya kalli Charity yace ke da alama Yar Hajjo ce ta
gangare ko? Charity tace ae,yace sorry Allah yaji kanta,Charity tace Ameen harda kuka dan a
barsu su tafi tace ka tuna min da babana Yana can shi daya gwara na koma, Oga yace har Kun
gaji baza ku tafi yanzu ba ya Dace ku huta sosai ya furta tare da mikewa ya fice suna ji ya shiga
mota, Nusaiba suka sake fashewa da kuka,tunda ya fita bai dawo ba sai tsakar dare sunyi bacci
lokacin harda siyo musu kayan makulashe da safe suna tashi suka gani a bakin kofar su Leda
guda, Charity tace wlh da wannan kayan dadin gwara muna gidan Iyayenmu,Nusaiba ta kalleta
tace hmm ai ni abin ya isheni gashi Muna fadar gaskiya za a kamamu sai gidan kaso masu kudi
zasu Yi tunanin ma da abinda ya kawo mu,ai Kar mu sake mu fada Kuma Kinga Yana kamamu
sai Iyayenmu sunji abinda muke yi,Nusaiba tace badluck, har suka gaji suka fito suna zaga
gidan ko Ina sai da suka gani sun Sha kallo amma Sam abin baya birge su burunsu su koma
gida,Palo suka koma sai gashi a zaune Yana kallon film sannan Yana latsa wayarsa.
Zama suka Yi can nesa da shi yace hope Kuna Jin dadin birni ya furta Yana kallon Nusaiba,
Charity tace sosai ma Alhmdllh amma gida muke so mu tafi yau Iyayenmu zasu Mana
fada,Ogan yace ai Indai kunce a nan kuke ba matsala kadaici ya min yawa kuyi zamanku kwa
dan ebe min kewa ko ba komai na dinga Jin motsin mutane, Nusaiba ce ta kalli Charity suka
hada Ido idanuwansu ya ciko da kwalla zasu Yi kuka ya tashi ya haura sama shi dama ya gaji
da Shuru shi kadai a gida ga Yan uwa sunzo yaji motsin mutane ko da na yan satikai ne, Yana
fita Charity tace kamar fa wannan mutumin kwakwalwarsa a takashinsa take ta kowa a kansa
aka Masa brain amma Banda shi tasa a takashi aka Masa ita baya tunanin Iyayen nu chab
Aisha ce ta shiga motarta tana tukawa a layin har makwafta suka tsiri zuwa suna gaida su
Sabo da aga ta siyi mota ko Ina da key a hannunta tana karkadawa,Sunday Yana gida Aisha
anci gayu ta fito tace Maggi fa ya Kare sannan ba kayan miya ko yaji Banda shi bare nayi Mana
shinkafa da wake,Farooq yace Wai ku Mata me yasa baku da hankali ne sau Nawa Ina fada
miki idan Abu ya kusa karewa ki sanar min amma kinki ji sai komai ya Kare kat Zaki zo ki fada
min to yanzu kin San wata yayi nisa ba kudi sai mu yini haka ya furta Yana Jan tsaki,Aisha tace
Farooq kafa isheni tsakani da Allah na gaji Kai ba haihuwa kake ba how many years? 5yrs da
auren mu maimakon ka lallaba ni sabo da nice ke hakuri Ina taimaka maka wajen Zama da Kai
ba haihuwa Alfarma fa nake maka,for how long Zan dinga jira ba haihuwa ta juya ta saka Hijab
ta fice ba ko neman izini haka tasa kudinta tayi cefane ta dafa abincinta ita kadai taci na Rana
ta boye na dare Yana kallonta,tashi yayi ya fice zuwa gidan Abokinsa a can yaci ya
koshi,tsakanin Aisha da Farooq an rasa waye me gaskiya tsakaninsu idan wannan yayi rashin
mutunci gobe wannan ne zaiyi kullum basa shiri abinda ya damu Farooq irin gorin haihuwar da
Aisha take Masa kullum,kwana biyu Babar Aisha tazo gidan suna dakin Aisha Babarta tace ke
dai anyi shashasha mene amfanin aurenki da Farooq mutumin da baya haihuwa kunje asibiti
yafi a irga ance a shine ai ya kamata kisa ya sakeki,ribar aure ai haihuwa ce tun wuri kisan me
kike ciki,Babar Aisha haka ta gama zuga yarta daga ranar Aisha ta daina girki Farooq Yana
Mata magana sai masifa tace juya Wanda baya haihuwa ka sakeni tun baya damuwa har abin
ya dameshi ya sanar da Babarsa tace yayi hakuri Kawai kowa haka yake hakuri,da a baya suna
yin Dan fadansu su shirya haka Yar karyar su dai sukeyi yanzu duk Aisha ta canja ba mutunci
Kawai a sake ta taje ta samu me haihuwa.
Affan ne ya fito yasha wata shadda fara yayi mugun kyau Yana kamshi Raudat itama ta fito
cikin farin lace zata tafi wajen aiki Kawai taga Affan da fararen kaya Ido suka hada tace Allah ya
kiyaye na saka Kaya kala daya da Kai God for bid ta juya cikin fushi ta canja wata blue atamfa
ta fito Yana tsaye da mamaki Tsaki yaja ya juya zai fita tace masu appointment kullum Ina da
appointment kullum meeting ba uwar komai a kasa ba Sisi,kallon baki Isa ba ya Mata yace
Banda lokacinki ya Bude karamar kofar gate ya fice,ita Kuma ta bude gate ta fita da motarta
yace arga akwarabas da na Shiga wannan motar gwara na tafi a kafa,Tsaki ta ja tare da Shiga
motarta tazo ta gabansa Malam bani hanya gurgu kawai masu mota suke da kafa ta daga glass
din motarta sama tayi gaba.
Yau kwanan su Charity goma Sha biyu da bacewa Mama ta rame ta lalace ga bakin cikin
Shehu ga bacin rai yarta ta bace Addua kullum suke ba dare ba rana,Bangaren Charity Kuwa
Matar kanin Babanta wacce take Kira da Anty cewa tayi ban yarda ba Dauda yarka karuwanci
ta tafi Siyama duniya Kawai ta shiga,nima Ina zargin haka cewar Dauda, Su Nusaiba kuwa sunfi
sati daya basu ga ko alamar Oga ba sunci kukan har sun gaji,me aikin ma da suke gani yau ta
tafi ganin gida sai nan da kwana biyu zata dawo sai ranar Suka ga Oga ya fito daga dakinsa ya
musu murmushinsa me kayatarwa yace Hey,suka kalle shi Kawai yace me aiki yau ta tafi kuyi
hakuri sai jibi sai ku tafi idan Kun tafi babu me gyara min gida ni Kuma bana son kazanta Dan
Allah ku gyara gidan nan ya juya tare da komawa sama,ba yanda Suka iya Haka suka hau
gyara ko Ina na gidan
Bayansu ciwo suna gyara garden Nusaiba ta rike bayanta tana Nishi tace gwara tallan kosai
na sau dubu da irin wannan aikin, Charity tace hmm ai nayi missing tallan Alala ashe haka talla
yake da sauki kana zaune za a Zo a siya,tun ba ma an soya ba kafin ka tafi tallan sai kaci ka
koshi cewar Nusaiba itama Ai sai ma Ina zubawa mutane Ina daga zaune abina da yajina a gefe,daina tuna min cewar
Charity suka ci gaba da uban aikin gidan
Ku dinga sharhi please novel zai Fara wuta nan gaba
AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: í ½í»¢ï¸�AUREN MUí ½í»¢ï¸�
21-25
Official
By
AsmaBaffa
Page naki ne
MRS CHIEF
Biki Saura kwana uku Charity taga ba a sata a harkar itama bata Shiga ba uzurinta take
yi,ana gobe daurin aure Nusaiba tazo gidan su Charity tace kinki zuwa ana ta shagali ba
ke,Charity tace kice ana ta soya kwankwason rago,wa yake ta wani rago ana fada Miki
kwankwason bijimin sa,dariya tayi ta shirya tare da yiwa Aunty sallama suka tafi,leshin da
Nusaiba ta sa aka dinkama Charity ta Bata tace gashi shi Zaki sa da safe ni na Kai Miki dinki
me tsada aka Miki, Charity ta ajiye Kaya a gefe Nusaiba tace an fa goge su ki Adana Kaya
masu tsada ne fa sai ana kula,Charity tace hmm kawai,Nusaiba tace Ni tsoro ma nake ji Kar ki
fini kyau ranar bikin yanda kike farar nan kyakyawa Ni Kuwa wankan tarwada da ma nice ke
Charity,Siyama tayi dariya Nusaiba ta sake cewa ji dimple dinki sis gaskiya ki godewa Allah ya
Miki baiwa,Siyama tace kema ai kyakyawa ce Nusaiba hancinki ai yafi nawa tsayi,Ni ba Fara ba
Yaushe ma na Kama kafarki,sai gashi a hakan me kudin ke yace Yana so ba farar ba ko ta nan
ai Kya godewa Allah ni da kin sani ma dinkin Riga da wando Kika min ban iya sa Riga da skert
ko da zani ba kin sani,Baki Isa ba bikina guda ki sa Riga da wando bazai yuwu ba shegen
duwawunki su ja hankalin mijina,Siyama tace da Zan ja hankalinsa ai da tuni ya gani ki daina
kishi dani wlh sister bazan taba cutarki ba,Nan ta kalli Lefe akwati kusan ashirin aka kawowa
Nusaiba.
A gidan charity ta kwana duk wani aiki da ita akeyi tana gaba gaba ranar daurin aure 11am za
a daura su Charity an Sha kyau tafi amaryar kyau duk da cewa Amarya me makeup tazo ta
Mata nan take Nusaiba ta bata rai ganin Charity tayi kyau cikin Riga da skert din less
kawayensu duk sunci kwalliya sun Zo Basu sa anko ba Basu da kudin siya,Ango da best friend
dinsa Sabeer sun gayyaci abokai Nan da nan masallacin kusa da gidan ya cika da mutane ko
Ina Yan gayu ne da manyan masu kudi lokaci na Yi aka daura auren Aslam Mu'az da Amarya
Nusaiba Usman,kowa yayi mamakin Wai Aslam ne zai auro mace Yar talakawa haka Basu
shigo gidan ba Suka wuce reception kowa a can yaci ya sha daga nan abokai suka wuce gidan
da suke angwanci.
Nusaiba haka aka yini ana hada hada sai 5pm duk Suka yi wanka aka Fara Shirin Kai
Amarya,Shehu yasa yarsa a daki ya dinga Mata Nasiha yace ki zauna lafiya da mijinki Nusaiba
Allah ya Miki zabi,ki rike mijinki da Yan Uwansa babu batun Maganar son kudi a cikin aure idan
ka auri mace ko mace tayi aureka baka fata ku rabu sannan zaka tsaya ka jure samunsa da
rashinsa ki Zama mace me tunani ke ba yarinya bace kin girma kin wuce shekara ashirin ki San
me kike, Mahaifiyarki Aminatu kin San mu Yan asalin Rogo ne dake nan Kano,sanda na ganta
Ina sonta Ina da kudi lokacin kasuwanci Yana gara min na aureta Bayan na aureta na hadu da
karayar arziki daga lokacin Mamanku ta dinga wulakantani tana ci min mutunci sabo da bani da
kwandala,bayan wasu shekaru Allah yasa kudina ya dawo daga nan Kuma kauna ta dawo ta
dinga nuna min so Sabo da kudina shi yasa Kika ga na fita safgarta gaba Daya ba karamin
wulakantani tayi ba lokacin da Banda shi to karki haka Nusaiba ki zauna lafiya a nan dai yayi ta
Mata fada ita Kuwa Mama ance ga Amarya ko Zaki Mata fada,Mama tace mu yaranmu ai tun
suna gabanmu mun Gama musu fada da can basu ji nasiha ba sai yanzu da ake Shirin kaita
dakinta, menene basu sani ba na zaman duniya ku tafi Kawai a kaita zata Yi zamanta
daram,Yan Uwan Shehu da Yan Uwan Mama Suka fita da Amarya sai kawaye motoci ne
lafiyayyu sunfi talatin aka dauki Amarya zuwa gidan mijinta.
Duk Wanda yaga gidan sai ya kasa rufe baki,Amarya Kuwa tun a mota ta Fara cewa kunga
tun gidan da Muka sani ne tun Ina budurwa bai canja komai na gidan ba Amarya guda ai ya
kamata ace an canja komai na gidan tana magana kasa kasa an zaci kuka ma take Yi,ko Ina
kamshi ke tashi na gidan ga Amarya ta Sha gyara bayan Yan Kai Amarya sun gama ganin gida
suna ta Santi Suka fito Suka tafi gaba Daya har Charity bata zauna ba,Ango ne ya shigo bayan
Sallar Isha ya Sha wanka cikin shadda Yar gaske sky Yana tafiya cikin takamarsa da ya Saba
Kyau Kam ba a magana Kamar shi yayi kansa,bedroom dinsa ya wuce direct ya iske Amarya
abar kaunarsa a zaune saman makeken gadonsa,a gefen gadon ya zauna ya Kare Mata kallo
cike da Murmushi,Hannu yasa tare da Bude mayafin data rufe fuska da shi fuskarsa ya Dora a
saitin wuyanta Yana shakar kamshinta a hankali ya furta a I love you Nusaiba tace me
too,wuyanta ya fara kissing Kamar Wasa Yana binta da sumbata Yana shafata jikinta sai rawa
yake yana yi har ya fara cire Mata sutura a hankali Yana tsotsar bakinta Yana so suyi Sallah
suci kayan makulashe amma ya kasa a cikin gaggawa yake bai iya hakura,Nusaiba tana ganin
kamar Wasa taga da gaske yake,a hankali tace ji nake sai munje kasar waje zamu Fara
amarcin,wacce irin kasar waje ya tambaya Yana shafata,tace ban gane wacce ba kasar waje
dai ai ji nake acan zamu Yi Honeymoon?, A'a gidan zuma zamuyi ba Honeymoon ba cewar
Aslam ya furta da Wasa Yana ci gaba da abinda yake,Boobs dinta ya cafka basu da wani girma
ma Yan kuyas a hannunsa haka ya dinga murzasu,Nusaiba kasa komai tayi kamar gunki haka
yayi kidansa da rawarsa har ya samu ya shigeta yau ta yabawa aya zakinta Harijine sosai bai
kawowa da wuri tayi kukanta ta hakura sai da ya samu gamsuwa sannan ya lallabata suka ci
abin dadin bayan sunyi wanka tare da tsarkake jikinsu Yana ta yabonta tana Jin Dadi.
Bayan kwana biyu Nusaiba taga Shuru bai da Niyyar kaita kasar waje tana zaune a Palo ta
Sha gayu ya fito yace wow you look good tayi Murmushi ya zauna a gefenta tace har yanzu
banji ka Fara cewa mu Fara Shirin Visa ba,Aslam yace ta me fa? Honeymoon Mana ya kamata
ace Muna kasar waje yanzu,Ganin ta dameshi da zancen kasar waje baiyi niyya ba Amma sabo
da a zauna lafiya yace ba komai zamuje Saudiya ya Kika gani? Kallonsa tayi tace Saudiya?
Makkah kake nufi? Ibada zamu je Yi kenan? Ni ban shirya zuwa Makkah ba turai zaka kaini irin
su Paris,Germerny etc kana wani Maganar Saudiya shike Nan kullum Muna masallaci bazan je
ba ta mike tsaye tace ka rike kudinka bazan je ba Indai Makkah ce ni na taba ganin me kudi
Dan tsumulmula ma irinka,Baki Aslam ya Bude cike da mamaki duk kudin da ya kashe Mata da
danginsa dan tsumulmula ne shi gaba Daya sai abin ya daure Masa kai sabo da ya samu Yar
tarbiyya me nutsuwa ya nemi Yar talakawa irin Nusaiba Ashe gwara Yan masu arzikin ma.
Tsayawa yayi Kawai Yana Shan mamaki just 3days da aure har an Fara fada,sharewa yayi ya
hakura ya rabu da ita suna soyayyarsu har Suka cika sati biyu da aure Nusaiba ta shirya cikin
tsadadaddjen material blue and purple ta Sha kyau ta fito sanye da takalmi me tsini da jaka ta
yafa Dan siririn mayafi,Aslam bai fiye fita ba Yana gida ta same shi a bedroom dinsa Yana
Shirin fita tace Baby kudin gyaran jiki zaka bani daga nan Zan biya a min make up,okay ya furta
ya irga dubu ashirin ya bata,galala ta karbi kudin tace dubu ashirin kacal gyaran jiki fa nace da
kwalliya,dubu biyar ya Kara Mata tace Bari dai nayi manage duk da Haka basu Isa ba,Kawai
kallonta yake da mamaki,tace yawwa na manta yau Mama zata Zo da kannena anjima da
Yamma,yace Allah ya kawosu lafiya Ina gida ai lokacin Zan Dan je Office na dawo Alright,ta
zabi key cikin motocinsa ta Kira driver Suka fita ba inda taje wani gyaran jiki bank taje ta saka
kudin a accnt dinta ta dawo gida.
Tana dawowa ta sa me aiki ta shirya lafiyayyen abinci dama bata girki Bata aikin