Showing 69001 words to 72000 words out of 86820 words
shiga idan ta tuna abinda ta aikata gate din take shafawa da hannayenta tana zubar da
hawaye ta Dade a haka har ta gaji ta juya gida inda ta fito,washe gari gidan Sufyan ta shirya
taje gidan ta zaci gwauro ne bata san Yana sakinta da wata daya ya koma ya nemi gafarar
Iyayensa ya auri tsohuwar budurwarsa Zahrau sun rabu tana sonsa Yarinyar kirki Yar tarbiyya ai
Kuwa Yana aurota bai Dade ba ya samu Offer a land and housing sai dai albashinsa ba Kamar
na Aslam ba amma ba laifi,yanzu iyayensa da Yan Uwa duka komai Yana musu,Zahrau har
Kara takura Masa takeyi akan dole yayi musu abubuwa,Nusaiba tana Shiga gidan taga Zahrau
tana gyarawa Sufyan kwalar rigarsa suna dariya cike da so ai kasa karasawa tayi tasan yayi
aure ta juyo da sauri ba tare da sun ganta ba,ta dawo gida sai kuka Wanda ba shiri Mama ta
shirya ta tafi gidan da Mum take ta manta irin wulakancin data Yi Mata lokacin da Mum tazo a
gyara.
Mama gidan da Mum take ta shiga tana ta kwada Sallama Hajiya Zainab ta tafi gidan biki sai
Mum,Mama tana ta sallama ba ji ba gani Mum ta fito sai taga Mama Fuska ta daure cike da
bala'i Mum tace Wai wace ne ta damemu da Sallama taki ci taki cinyewa,Mama ta marairaice
tare da langabar da kai tace surukata...ohhhhh da baki san ni surukarki bace sai yanzu dan
Allah malama Fadi me ya kawoki sauri nake yi Ina da aikin yi,Mama tace zuwa nayi Dan Allah
Surukata ki taimaka kisa danki ya maida Nusaiba dakinta dan Allah kuyi Hakuri komai ya wuce
zamu gyara Inshaallah dan Allah ki taimaka Mana,Mum wani kallo ta Mata up an down sannan
ba tare data furta komai ba ta tofar mata da yawu tuf ta juya tare da komawa ciki ta bar Mum a
tsaye kikam,gajiya tayi da tsaiwa ta juya ta koma gida dabarunta sun Kare dama duk Shirin da
tace shine kawai zata yi,Nusaiba ana gida zaman gida Wasa farin girki, bayan wasu Yan lokuta
Shehu baya dagawa mama da Nusaiba kafa baya sakar musu fuska da Mama da Nusaiba
wahala suke Sha sauran yaransa yake yiwa abinda suke so kawai,suna haka katsam sai ga
Aslam,Shehu Yana gida yace a'a dana yau Kaine a gidan? Aslam yace ae Abba ya zauna kusa
da Shehu a tabarma ya gaisar da shi ko kallon Mama da Nusaiba baiyi ba Wanda gasu nan a
tsaye sun taho da sauri sun tsaya musu a kai suna magana kasa kasa da ita da Nusaiba,Shehu
yace ashe haka arzikinka dama yana nan ya dawo naji labari Ina ta so ma nazo har gidanka
Allah mun gode maka,Aslam yace Abba Kai na daban ne nasan me kaunata ne Kuma babban
mutum ne Kai idan ba damuwa bana Inshaallah zamu tafi aikin Hajji tare da Kai,Shehu yace
wayyo Allah dadi kashe ni Aslam ya dinga dariya,Nusaiba da Mama harda murna tunanunsu
bikon Nusaiba zaiyi shi yasa ya Fara kashe musu kudi irin da,Aslam yace Kawu ba iya Makkah
zaka tsaya ba Paris da Dubai zaka je inda Nusaiba take mafarkin zuwa yanzu gashi Shehu
Babanta shi zai je Kuma Aslam Yana sani yayi hakan Sabo da farkon aurensu haka tace sai an
kaita honey moon Paris ko Dubai,yace sannan duk Sanda kaji kana son hutawa Abba karka
damu ka hada kayanka kazo gidana ka huta,ko me kake bukata Kawai ka kirani a waya,Shehu
Kamar yayi suman dadi haka yake ji gani yake Kamar a mafarki,yace Kuma tare da abokinka
zaku je Baban Siyama Kawu da Aunty,Shehu yace Alhmdllh na gode na gode ya dinga godiya
Yana murna,Aslam yace Maganar shirye shiryen visa Zan kiraka a waya ya mike ya zaro Yan
dubu dubu ya mikawa Shehu yace gashi kayi amfani da wannan,Mama ta dafe kirji,Nusaiba
Hawaye ya Fara antayo Mata a kumatu,Mama tace surukina dan Allah kayi hakuri abinda Muka
maka,Nusaiba tace dan Allah ka yafe min ka dawo muyi aure,Aslam yayi hanyar barin gidan ya
juyo yayiwa Nusaiba da Mama kallon banza yace mugaye kawai yaja Tsaki ya juya shi da
Shehu Suka fice,har mota Shehu ya rakashi ya tafi sannan ya dawo Yana taku dai dai Yana
doro,Shehu yace Alhmdllh Yana takama a gidan ya zama Dan gayen dattijo aka bar Mama da
Nusaiba da bakin ciki.
Aisha tuni an maida Aurenta da Farooq suna zamansu lafiya yanzu duk Karya da fadan da
sukeyi sun daina sai mutunta juna kowa baya so wani Abu yazo ya shiga tsakaninsu,soyayya
suke me tsafta abinsu su,Nabeela kuwa tana yin Idda ta samu miji wani babban mutum ne me
Mata ta hakura da Affan tasan babu aure a tsakaninsu ma tunda Dan Uwansa Yana raye amma
ta take gaskiya yanzu Kam ta hakura ta auri me Mata Kuma tayi zamanta babu Neman
rigima,Sabeer ma yayi aure ya auri zankadediyar matarsa Habiba.
Raudah da Affan suna soyayyarsu sosai matsalar Raudah kishin tsiya,yau tana zaune a gida
Affan ya fita sai ga Wayar Landlady ta shigo tana ta kiranta dagawa tayi tun kafin tayi magana
Landlady tace Raudah maza maza fito ga mijinki Affan da wata sun shiga shopping zo ki gani
da idonki,Raudah tace what? Na fada Miki maza basu da amana mijina haka ce ta rabamu da
shi na aminta da shi Ashe maci amana ne,gani Ina ShopRite maza kizo kafin ya bar wajen,
Landlady tayi gaskiya domin Affan ne da wata zasu shiga ciki ita Kawai dan ta ganshi da mace
shine tace budurwarsa ce bata San cewar Amaryar liman bace ogan Affan Kuma Liman dinne
yasa Affan ya kaita wajen wata Mata suna business tare da matar Liman,matar daga kasar
waje tazo shine Affan ya kaita.
Raudah hijab ta zurma ta fito da uban gudu tare da bude motarta ta shige ta Mata key motar
taki tashi tayi tayi motar taki ta fito da sauri daga gidan sai ga yaron Affan da machine yazo
gidan zai karbi takardu,da sauri tace dan Allah kaini ShopRite sauri,ya zaci ma wata masifa ce
ta faru ya juya machine ta hau da sauri tana cewa kayi gudu Yi sauri Salahu dan Allah Yana
tambaya lafiya Hajiya? Kayi sauri please duk ta gigita me machine suna ta fyalla gudu a titi tana
kayi sauri ka Kara wuta Yana tsinka gudun gaske a rude yaje ya daki mota Suka watse a gefen
kwalta Raudah ko motsi bata Yi kanta ya fashe daga gefe Yana jini,me machine din Kuwa Suma
yayi Yana farfadowa yasan inda yake sai raunuka da yaji,mutane sun taru akansu aka kwashi
Raudah da Salahu yaron Affan zuwa asibiti,lokacin Affan ma ya koma Office Kawai yaji Kira
Yana dagawa ya mike Zumbur a gigice Yana tambaya a wanne asibitin ya tafi da sauri figi
motarsa sai asibitin,matarsa Kawai yake cewa dakin da Raudah take aka kaishi Yana Shiga ya
iske ta farfado amma ta karye baras a kafa sai kanta an nade daga gefen da bandage,tana ta
kuka a kwance Affan bai ma tambayi me ta fito Yi ba Kawai ta lafiyarta yake Yi,ganin tana ta
kuka ya Fara lallashinta,a gefenta ya zauna tare da maida kanta jikinsa Yana lallashinta tana
hawaye yace Inshaallah Zaki warke kinji,anjima kadan za ayi aiki a dora min ke,ya Isa haka
kukan Affan ko aiki sai mataimakinsa yayiwa magana ya kula da komai ya tafi jinyar matarsa sai
ta warke zai dawo ya sanarwa liman gaba Daya family Suka Zo dubiya har Liman,a ranar aka
dora Raudah ana ta zuwa dubiya har Yusuf da matarsa sunzo,shi kuwa yaron Affan tuni ma an
sallame shi sai da Raudah ta kwashe sati biyu a asibiti Affan shike jinyarta shike Mata komai bai
bari ma yan uwan Raudah sun zauna ba tunda suka zo dubiya,mamanta ce ma ta dage sai da
tayi sati guda a asibitin sannan ta koma.
Wheelchair aka bawa Rauda da sandunan koya tafiya lokacin da aka sallameta,Raudah tana
tuna dalilin fitarta daga gida sai hawaye da kukan takaicin halinta tana nadama da Dana
sani,gashi Affan din yand a yasan bata tambaye shi ba ta fito amma ko zancen bai Mata ba ta
lafiyarta yake Yi ya daina zuwa aiki sai jinyarta shike Mata komai ita Kuwa me zata ce da
wannan bawan Allah tayi dacen miji da wani ne sai dai a kaita gidansu in ta warke a dawo da
ita, motar Affan ce ta shigo gidansa ya fito ya Bude dayan bangaren sannan ya bude booth ya
dakko wheelchair ya dakko Raudah tare da dora ta a Kai tare da rufe motar ya turata a hankali
zuwa ciki,Raudah tana ta zagin kanta a zuciyarta abinda ta aikata,Affan gwani ne wajen gyara
da tsafta sai da ya gyara gidan nan tsaf sannan ya yiwa Raudah wanka shima yayi ya dorata
saman kujerarta suka fito,ya shiryata cikin gown gajera marar nauyi,abinci yayi order aka kawo
musu har gida suka ci sannan ya fita masallaci ita Kuma tayi sallah a zaune saman kujerarta.
Washe gari tana Palo tare da Affan suna kallo Landlady ta shigo bayan sun gaisa Affan ya
koma bedroom ya basu waje,Rauda ta kalli Landlady tana hawaye tace kin cuceni ke ba matar
kwarai bace Kuma ba abokiyar zama bace,sam bakya Dora mutum a hanyar gaskiya gashi nan
abinda Kika jawo min yanzu gashi nice a wahala,Ina zamana da mijina lafiya ke kin kasa aure
kinzo kina zugani bakya taba yabon maza sai dai ki Fadi sharrinsu shi yasa da yawa wasu
matan idan Suka taru basu da aiki sai fadan sharrin maza basu fadan alkhairinsu a haka wasu
Wanda suke zaune lafiya da mazajensu shike nan an gurbata musu zuciya sai su Fara zargin
nasu in ba a yi sa'a ba rashin zaman lafiya ya Fara kenan,Mata in Suka taru basu da aiki sai
zagin maza da halayensu ki sani wata idan bata dauka ba wata dauka zata Yi karshe auren ya
mutu ma,ba kowa ce take auren miji me kule kulen mata ba Kamar mijinki da Kika taba aure
Bmbai yuwuwa kiwa maza kudin goro,na Zama sakarai da ilimina da hankalina na zauna Ina
daukan shawararki landlady kiji tsoron Allah kije kiyi aure ki daina lalata Mana namu,kuma Indai
zugace zata kawoki gidana karki sake zuwa inda nake bani ba bake har abada,kin girmeni
babbar mace ce ke amma baki da tunani, Landlady tasan itama bata kyauta ba tace kiyi hakuri
Raudah wlh aurena dana Yi na fuskanci halin mijina kenan sai nake tunanin kowa ma haka
yake wannan yasa na kasa kara yin aure amma Inshaallah nima na gane gaskiya,Raudah tace
oho Miki ni dai in bada alheri Zaki Zo ba karki sake zuwa gidana yanzu ma ki tashi ki tafi,
Landlady ta mike jiki ba kwari ta tafi,Raudah tana hawaye Affan ya fito yace Wai me yasa
kullum sai kinyi kuka ne kina Jin sauki fa kin kusa fara tafiya da kafafunki Inshaallah.
Raudah tana kujerarta ta miko hannu tare da rike hannun Affan tana hawayenta tace dan
Allah ka yafe min na tuba bazan sake ba,ta bashi labarin komai zugata da Landlady keyi tace
karshe gashi ta kaini ta baro na karye ta fashe da kuka,Affan yace ai Raudah tunda naji kinyi
hatsari nasan kishi ne ya fito dake shi yasa ma ban tambayeki ba nasan baki da wata matsala
face kishi,abinda yasa Kuma bana damuwa so ne a kaina akeyi Kar wata ta kwace ni to ni ai na
Zama dan gata gashi kin jawa kanki kin karye Allah ya takaita ma,haba wifey babu izinina Kika
fito haba Raudah kishi fa idan yayi yawa zargi yake kawowa,da sauri tace wlh bana zarginka
Kawai in ta zugani ne sai naga kamar haka ka yafe min kayi hakuri bazan sake ba babu ruwana
yanzu gashi na karye a banza,Affan ya kyalkyale da dariya tana hawaye ta duke shi a
kafada,yace ai Ni Kika jawa aikin,ki sani bazan taba cin Amanarki ba na Sha fada miki,to yanzu
idan ta kasance Zan Kara kishiya yaya kenan Raudah? tace ai ma Inshaallah baza ta faru b,to
idan ta faru fa? Mutuwa zanyi Kawai,yace kin gani wannan halin naki sai ke Kika ce kin tuba
kuma? Baki ta turo tace ae na tuba bazanyi fada ba bazan ce komai ba Kuma bazan bibiyeka
ba sai dai Kawai aga na mutu,Affan yayi dariya sosai tace ai kana da kyau ko wacce sonka zata
dinga yi ni Kuma bana sooooo....ta karasa da kuka,To yanzu Raudah nifa ba ni nayi kaina ba
Nima tashi nayi na ganni haka,Raudah tace ka kakalo shi Mana tunda kana ta gyara jikinka
kana daukan wanka kullum kayi ta matso kyawunka kana fita gashi nan sai kafi 1h a toilet kana
wanka duk ka goge fatarka kullum fari kake sake Yi kullum gashi nan bature kake Zama,Affan
dariya Kamar me yace to na daina wankan sai na zauna miki a kazami gobe kice Nima Ina
warin hammata,yanzu sai kince kin tuba kin daina ko? Raudah tace Zan dinga yiwa kaina
Addua kaima ka tayani,Affan ya sake sakin dariya tace wannan ba abin dariya bane kaje kullum
kayi ta gyara Suma ba ji ba gani ko wacce Yar iskar budurwa tana zare Ido gashi nan gaf ake
da yaye dalibai daga Yan secondary zasuyi candy gashi Yan University sun kusa gamawa naji a
labarai ance final exam zasu zana Kuma Yan Service sun gama miji suke jira wallahi ta Allah ba
tasu ba, Affan har wani dadi yake ji ana kishinsa yace to ya Isa me Miji,Raudah tace kayi hakuri
na tuba Allah kishi irin na baya da nayi bazan sake ba amma zan dinga dan yin kadan kadan
shi yasa nake baka hakuri kayi hakuri dani Dan Allah har Allah ya yaye min,Affan yace to an
gama Raudah,no your love zaka ce ta gyara masa Yace Okay My love,My one and only, My
Heart,My soul my life Kuma Queen dita,Raudah Murmushi tayi tana Jin dadi tace ga mijina me
jinyata me so na wata tazo itama Watarana ayi jinyarta haka dole naji haushi,kwana nawa baka
Yi komai dani ba lafiya iceko? Affan yace Baby rigima baki da lafiya a karyen zanyi wani xxx
dake,Raudah tace a'a in kana so kayi Zan maka komai Zan daure ai na Fara Jin sauki kafar
basai a lallabata a gefe daya ba,Wai wayo take wa Affan Kar ma yaji Yana so ya Karo aure
tunda bata da lafiya ko yayi sha'awar wata ita bata da lafiya baza ta iya Masa komai ba akan
haka gwara ta daure tunda tana gani idan Yana Mata wanka Yana shiga yanayin bukatar mace
daurewa Kawai yake yi shi yasa gwara ta tari abin.
Affan da wuri ya amshi tayin Raudah yana murna yau zai gagije,ai Kuwa da dare haka kafa
aka sata a gefe Suka jiyar da juna dadi.
Washe gari Raudah tana kallon labarai a tashar hausa suna zaune da Affan taji ance gomnati
ta dage jarabawar waec da dalibai zasu zana Yan secondary school an Kara wata uku nan
gaba,Raudah tace Alhmdllh Yan banzan Yara aci gaba da shiga aji,Me labarai tace kungiyar
Asu jibi Monday zasu Kara tafiya yajin aiki na Sai baba ta gani,Raudah ta kyalkyale da dariya
tace maga karyar gama degree dan ubanku,Affan Yana jinta waya yake dannawa amma sai da
ya tsaya kallon Raudah tana bashi dariya matuka.
Bayan kwanaki ya Fara koyawa Raudah tafiya har ta iya ta Fara takawa da kanta har ta dawo
tana tafiya normal Kamar bata taba karyewa ba,likita yace ta dinga Dan zaga unguwa tana
tafiya a kafa me dan nisa,tare da Affan Suka fito sunyi gayu sosai Affan sanye da 3qrt da t-shirt
komai fari,ita Kuwa Abaya ta sa silver color me shegen kyau tayi rolling suna tafiya a layin suna
zancen soyayya suna nishadi kamar saurayi da budurwa ka gansu gwanin birgewa,Suna ta
nishadi yana tsokanarta,wata Yar budurwa ce tazo wucewa Raudah da sauri ta koma ta
bayansa tare da rufe Masa idanu da tafukan hannayenta dariya sukeyi musamman Affan, sai
wurin magriba Suka dawo gida.
Siyama kwance suke da Aslam a makeken bed dinsu sun gama soyewa suna hutawa ta juya
tare da hugging din Aslam tace My Sugar dan Allah ka biya min makaranta na koma Nima nayi
karatu,marairaicewa tayi da shagwaba please ko ba degree ba ko NCE ne dan Allah kaji, Aslam
yace ni bana son fitarki aje a gurbata min Mata Muna zaman mu lafiya,Siyama tace Ina da
hankali fa Inshaallah babu abinda zai faru wace ma ta Isa ta zuga ni na yarda ilimi Yana da dadi
kaga Zan sake wayewa sex dinnan ma Sai kaga albarkacin makaranta da gogewa nazo Ina
maka style har na tintsira gudi gudi,dariya Affan yayi ba shiri yace ba wayon da Zaki min Yar
nan,Siyama ta sake cewa to yaran mu fa ko Dan yaranmu da zamu haifa zai musu Rana,Yan
dagwai dagwai dinmu jikokin Mum, Yan fararen yaranmu masu Yan kunnuwa Affan yace naji
amma sai kin samu ciki Zaki fara yarona tun a ciki ya dinga Jin turanci,Siyama tace Indai ciki ne
Ina da shi fa,watanmu biyar da aure Ina da ciki,Aslam yace haka ake cikin,da gaske fa nake
idan baka yarda ba muje asibiti gobe,ta ya Kika sani? tace Sanda na dinga zazzabi rannan na
siyo wannan tsinken na pt na gwada Allah ya nuna Ina da ciki,shine baki fada min ba? gobe
Zan kaiki asibiti ai,gari na wayewa Suka shirya sai asibiti bayan an Mata gwaji nagartacce aka
tabbatar tana da ciki na wata uku dai dai,Aslam sai Murna harda kissing dinta a kumatu Suka
dawo gida murna taki karewa,Siyama tace ai mu irin jinin haihuwa ne ana taba mu muke samun
ciki,dariya yayi sai Murna yake zubawa daga nan ya Fara musu Shirin barin kasar.
Su kawu,Aunty da Shehu sai Wanda Affan yasa zai rakasu ko Ina suna filin jirgi,Landlady ma
tazo zata tafi Umrah tana