Showing 21001 words to 24000 words out of 86820 words
ya ja mayafinta ya daketa wani ya
mareta wasu Kuma duk Magana ta banza yarinya tun tana karama Matukar tana talla za a
dinga Yi a gabanta,tunda waje ne na maza idan Suka taru akwai kalaman banza da bai dace taji
ba amma za a dinga Yi a gabanta wasu ma su dinga janta da Harkar banza irin wannan ke
sawa Yan talla suke lalacewa yau da gobe zata Saba har ta daina kunya,sannan ga gogayya da
maza mutane manya daban daban zai sa idonta ya bushe ta dawo Bata da kunya Kuma bata
tsoron kowa kadan daga illar talla ga ya mace,Aslam yace hakane Nima sai yanzu naga hakan,
Uhm ta furta tana kallon Wayar hannunsa me tsada
Sabeer ne yayi sallama tare da shigowa shima,Sai yau Siyama taga Sabeer,gaida shi tayi
Yana binta da kallo ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa ya zauna yace ko kece Siyaman?
Charity tace ae yace Sannu mun gode fa,Sabeer ya dameta da kallo,Aslam Yana
kallonsa,Siyama mikewa tayi tace zata tafi,sai yaushe? Aslam ya tambaya tace sai an ganni
Kawai yace muje na rakaki Suka fito tare suna tafiya a hankali suna hira tana ta bashi dariya.
Nusaiba aka sauke a taxi ta tsaya tace Charity sai da Kika sake biyo mu Nan dan masifa
yanzu ba kudin da za a baki to,Tsaki Siyama ta ja tare da furta banda lokacinki
Nusaiba,Nusaiba ce tace zo wahalalliya Ina son magana dake,Charity ta ja gefe Nusaiba tace
tunda taku tazo Daya da Aslam dan Allah kisa ya sakeni,ki fada Masa Ni takarda ta nake so ya
sawwake min na gaji bazan iya rayuwa da shi ba,Siyama ta kalleta tace ki kalli Namiji irin Aslam
hadadden mutum Kamar shi yayi kansa kice Wai kin gaji da shi,ae dan Allah ni na gaji bana son
auren ya sakeni,kinfi so ki Zama bazawara ae gwara haka ke karuwai ma suna nan su da
karuwanci suke Yi suna zaman su a duniya Lafiya bare ni Dan an sakeni na Zama
bazawara,wlh idan Bai sakeni ba Kara Zan kaishi wajen Yan Hisba,Siyama juyawa tayi tare da
komawa wajen Aslam ta fada Masa abinda Nusaiba ke so saki,yaji Matukar ciwo ya danne,Yana
komawa gida tace wallahi yau ba zaman lafiya sai ka sakeni,Aslam yaki kulata rigarsa ta rike ya
samu ya kwashe ta da Mari ya sake zabga Mata Mari Wanda ba shiri ta sake shi tana kuka
wallahi sai ka sakeni,yace baki ji kunya ba mahaukaciya aure wata hudu na sakeki Baki da
hankali,kuka Nusaiba takeyi sosai yaki sakinta haka Suka kwashe satikai kullum da masifar da
zata fito da ita a saketa sabo da bai da kudin da zata karba yanzu Kuma sai takalo rashin
mutunci iri iri shi Kuma yaki sakinta,harda daina kwana a dakinsa ta dawo palo a nan take
kwana kullum.
Yau Mama ce tazo gidan tana zuwa ta saki ihu a palon tace a Nan yata take Zama daki nawa
ne? Nusaiba dake zaune tace daya,Daya tal yanzu idan da kwana zanyi bani da wajen bacci
kenan tab amma Aslam ba karamin azzalumi bane ka ajiye bawa me rai a nan, Nusaiba tace
zauna Mama bari na Miki girki dama bana dafa Masa abinci,Mama tace kinyi dai dai tana zaune
Nusaiba ta dafa Mata shinkafa da Miya harda kazar da ya siyo jiya Mama taci ta tauna Kashi ta
sha ruwa me sanyi ta sake zuga yarta tace Kai Kai kamarki a wannan gidan daki Daya sai Palo
kujerun ma ba na kasar waje bane ba Yan Dubai ba Yan nan Kano ne,Nusaiba tace kalleni
Mama yanda na girma nayi kiba nayi wani fresh kowa ya ganni yaga kalar hutu amma
matsiyacin ya makale yaki sakina,gida ko filin tsakar gida babu kalli tv din ma karama sai kace
ta Office din principal din makarantar sikandire cewar Mama,wani takaicin Aslam ya sake rufe
Nusaiba,Mama Kuwa sai sake zugata takeyi,tashi tayi ta leka kitchen ai wani ihu ta saki tace
hodijam inji Dan fillo wannan kina samun balance kuwa? Sai dai manage Mama shi yasa bana
shiga
Suna haka Aslam ya shigo sanye cikin wata shadda Yar ubansu grey color cikin kayansa na
baya masu tsada ya saka ya shigo da takardun makarantarsa,Mama ta Bata rai tare da kallonsa
shekeke ta tabe baki tace kamar gaske akwai kudin Kai karya bata Yi ba,Aslam ko kulata baiyi
ba ya wuce bedroom dinsa,Mama tsabar rashin son zaman lafiya tace sai na dawo kwana
zanzo na kwana biyu haka,Nusaiba tace Allah ya nuna mana Mama sannan ta fita ta tafi
gida,Aslam ya fita bai dade ba ya dawo da Leda a hannu yayo cefane harda Naman rago da
yawa,tun kafin yayi magana Nusaiba tace wlh sai dai ka dafa da kanka Kuma abinci daga ni sai
uwata na dafawa mun cinye,bata ko rage Masa ba gashi Yana Jin yunwa Charity bata da waya
bare ya Kira ta, tashi yayi ya fita bai ko saurari Nusaiba ba ya shiga Napep zuwa gidan su
Charity
Yana Fitowa daga Napep Suka hadu da Shehu Baban Nusaiba,Shehu da fara'a da murna
yace surukina gobe nake so nazo gidan naka jaje wlh ashe haka Abu ya faru marar Dadi,Aslam
ya duka zai gaida shi yace tashi tashi Aslam ubangiji ya maida alkhairi,yace ameen,Shehu
yace ya Nusaiban iceko lafiya kuke? Aslam baiyi kasa a gwiwa ba ya zayyanewa Shehu
komai,Shehu Baki ya rike yace wallahi ban San me ake ciki ba abin wato har ya Kai haka,duk
uba bazai so a saki yarsa ba amma tunda Nusaiba take maka haka na baka dama ko nine iyaka
abinda Zan iya kenan na saketa,Dan Allah kayi hakuri Kai mutumin kirki ne,har gobe Ina ganin
mutuncinka Kuma bazan fasa zumunci da Kai ba ko da ace baka tare da yata,Aslam yaji dadi
da farin ciki,Shehu yace ka kyale Maman Yarinyar tunaninsu daya taho muje gidan Yar uwata
ka huta a can,Shehu yaja Aslam zuwa gidan Yar uwarsa Alawiyya ba nisa da gidansa ita me
rufin asiri take aure komai nasu me kyau ne,kana ganin Aslam zaka Yi tunanin da kudinsa tunda
Yana da sutura,palon Alawiyya Suka shiga babbar dattijuwa yace mijin Nusaiba ne,Alawiyya
tace Shehu ai na gane shi,Aslam ya gaishe da ita ta fita ta kawo musu lafiyayyen girki Aslam
dama yunwa kamar zai mutu baiyi Kara ba ya zage yaci ya koshi shi da Shehu Kamar ba
surukai ba suna yin Sallar la'asar Aslam yace zai tafi Shehu ya rakoshi har kofar gida Suka Yi
sallama shi ya koma cikin gidan wajen Yar uwarsa,Aslam Kuma ya karasa kofar gidan su
Charity,Yana tura yaro ciki sai gata ta fito zata siyo manja,taga Aslam ba zato,Murmushi ta saki
kayatacce tace Ina yini ya amsa da fara'a tace Ina kaje haka? Yace cefane nayi tace baza ta
dafa ba nama ne zai lalace shi yasa nace Bari na kiraki ko ki dafa min ko kizo ki dauka ki kawo
gidanku kuci Kar ya lalace,Charity tace nama guda wa yaki dadi har kasa yawuna ya tsinke,ya
saki Murmushi ba shiri,ciki ta koma tace Aunty ga kudin ki aiki yaro Aslam yazo nema na,Aunty
tace Kuma dan Iskanci sai ki dawo da kudin,Bata tsaya ji ba tace ki fadawa Kawu matsala ce a
gidan zanje wajen Nusaiba,Aunty tace to a kula dai tace to,ta fito tare da cewa muje Suka fito
tare Suka Mike suna tafiya suna Hira har yaji sanyi a ransa
Titin kwalta zasu tsallaka Yana ta tunani ya tafi bai kula da mota ta kusa zuwa inda yake ba
Siyama ce ta taho da gudu ta fisgi hannunsa tace mota da sauri suka tsallaka suna tsallakawa
motar ta wuce da mugun gudu,ta kalleshi tace tunanin me kake Yi haka ta furta tana kokarin
zare hannunta a nasa Wanda ya damke hannun nata cikin nasa Yana Jin wani shock da bai
taba jinsa a jikin wata ya mace ba,Napep Suka shiga zuwa gidansa Siyama ce ta biya kudin ta
hanashi ya biya kudin,suna zuwa Nusaiba chatting take abinta ga ledar kayan nan a
gefe,Siyama tana zuwa tace ke ballagazar matar aure shashashar matar Aslam, kallon Charity
Nusaiba tayi Kawai ta ja tsaki,Siyama ta zari ledar Aslam ya zauna tace Ogana me za a dafa
Murmushi ya saki yace kiyi farfesu Kawai sai Dan abincin dare,an gama ta furta tana kallon
Nusaiba tayi fatali da kafar Nusaiba dake mike a hanya tace matsa can Yar banza Yar
wofi,wawiyar banza,Dariya Aslam ya shiga yi Nusaiba ta galla Masa harara tace dan uwarki ba
Charity kike ba ko Ngozi kike nafi karfinki wahalalliya me bauta a banza, Siyama ta yiwa
Nusaiba dakuwa ta shiga kitchen tare da kunna gas ta Fara aikin girkin sai wurin magriba ta
gama farfesun ta ebi dan kadan a roba me murfi ta rufe,Ta fuskanci yana son tuwon danyar
shinkafa shi tayi Masa da miyar danyar kubewa ta Gama komai yayi Alwala zai fita masallaci
tace na gama, yace Banga kinci ba tace gashi na eba ta nuna Masa robar, tare Suka fita ta
shiga napep shi Kuma ya wuce masallaci.
Nusaiba tunda tana zuwa restaurant bata damu da abincin Aslam ba Sufyan Yana mugun
kashe Mata kudi yanzu burinta Aslam ya sake ta,washe gari Mama Shehu ta tambaya tace zata
je kauyensu ya barta tana tafiya sai gidan Nusaiba da Yar Jakarta wai tazo zata kwana biyu a
gidan yarta,Nusaiba ta dauki Jakarta ta Kai bedroom ta hau girke girke Aslam Yana zuwa yaji
kamshin girki na tashi yasan da dalili shigarsa bedroom kenan ya iske Mama a ciki yaga Kuma
jakar tata tabbas kwana zata yi, mamakin suke mugun bashi,Mama ganin ya shiga ta fito,a
gabansa a palo Suka zubo abincinsu Suka ci Suka koshi ko tayi basu Masa ba Yana Jin yunwa
sai fita yayi yaci a resturant bai dawo ba sai 10pm lokacin Mama da Nusaiba sunyi Shirin bacci
sun kwanta a saman gadon me gidan sun shige bargo tare,Aslam ya dan leka ya girgiza Kai
yace idan baki da kunya Mama kin hadu da Dan zamani,bedroom din ya Shiga Mama ta bude
baki,toilet ya Shiga suna ji Yana wanka Mama tace yau na shiga Uku da fitsararre,sai da yayi
wanka ya fito daure da guntun towel,Mama Hannu ta dora a Kai tare rufe Ido tana yau na shiga
Uku yau Naga jaraba,cikin bargon ta Danna kanta,turaruka ya fesa ya zura Jallabiya arsh,Kawai
Saman bed din ya nufa yace Mama Dan matsa gefe kadan gadon zai iya daukar mu mu uku ba
damuwa,Mama taga da gaske hawa zaiyi ya kwanta ta dirga kasa harda faduwa tace amma Kai
ba dan arziki bane ban taba ganin suruki marar tarbiyya ba sai kai ta fice Palo tana cewa
Nusaiba Miko min jakata a Daren nan Zan koma gida,Nusaiba ta mike tana hararar Aslam ta
dauki jakar Mama da tarkacenta ta fito,Aslam ya kwanta a saman bed dinsa tare da Jan tsaki
yace iskancin banza tunaninku ku kadai ne Yan iska uwar banza ya lulluba da bargonsa,Ita
Kuwa Nusaiba a daren ta fita ta samawa Mama Napep ta koma gida,Shehu sai ganinta yayi ta
dawo,yace ya na ganki ke da Kika ce Zaki kwana a kauye,Mama tace Wlh mutan gidan da naje
domin su sunyi tafiya basa gida shi yasa na dawo,Shehu yace ke Kika sani kuma.
Washe gari da wuri Nusaiba ta Kai karara Aslam Office din Yan Hisba tace so take a fadawa
mijinta ya saketa bashi da lafiya baya iya biya Mata bukatar Aure sannan ma ita ta daina sonsa
ya Fadi abinda ya kashe zata biya shi ya saketa,Aslam yana gida ya fito zai fita Kawai yayi arba
da jamian hisba mutum biyu suka Mika Masa takarda ana nemansa a Office din Hisba yasan
Nusaiba ce kawai Sabo da haka Kawai sai ya nufi can a Napep.
Wacece Raudat
Raudat Ibrahim Waku 'yace ga Ibrahim Waku hamshakin me kudi ne dan asalin jahar Gombe
Wanda ke zaune a Oyo state,tunda kasuwanci ya kaishi can ya shahara ya Zama hamshakin
me kudi na gaske ya tattara da yaransa su Raudat gaba daya ya koma Oyo da Zama,matarsa
daya tal Hajiya Rahmatu itama Yar Gombe ce, yaransu biyar Raudat ce babba sai kannenta
biyu maza biyu mata,Raudat tana gama secondary ta samu Saurayinta Hussain dan Kaduna
state,Hussain talakawa ne a zahiri ba son Raudat yake ba irin masu auren Mata ne dan kudinsu
dan ace Kawai ya auri Yar me kudi,Baban Raudat tunda yaga Hussain da Kuma cewar baya
sana'a ko kadan yace ta hakura amma taki ji Sam dole aka Yi Mata auren wuri
Bayan anyi auren Raudat da Hussain Baban Raudat shine ya Kama musu gida haya a
Kaduna sannan gara ma kayan abinci mota guda aka ajiye da komai sannan baya Bari yarsa
Raudat da talauci,Raudat komai ita ke Yi a gidan ta koma itace mijin ba karya akwaita da
hankali ga hakuri duk wani kyan haki Raudat tana da shi dai dai gwargwado,Hussain Kawai sai
dai ya kwanta an bashi jari ya cinye an sake bashi har Karo na uku amma sai ya kashe,tunda
Raudat ta aure shi bai taba kwanciyar aure da ita ba Basu taba sex ba sabo da bashi da lafiya
amma yaki yarda fada bashi da lafiya,abinka da yarinya itama sai ta kasa fadawa kowa suna
zaune haka har kusan shekara Hussain ga mugun son Mata bai da aiki sai kula Mata duk
kudinsa Yan Mata ke cinyewa shi Kuma dayar ma da ya aura ya kasa biya Mata bukata amma
Yana hangen na waje,a Haka ko Raudat bata bashi kudi ba sai wulakanci da cin mutunci iri iri
Indai tana son zaman lafiya to ta bashi kudi,abinda yake batawa Raudat rai Shan giyarsa sai ya
Sha giya yazo ya Mata dukan taiya,duk ta rame sam bata San mene dadin miji ba,ana haka ya
fara Mata sharri sai ya shirya zance na karya ya fadawa dan ginsa da abokansa,akwai Sanda
ma yace bata bashi abinci Kuma har zaginsa takeyi,Watarana ma ya dinga fadawa abokansa ai
maza take bi da Aurenta har kunnen Danginsa zance.
Su Kuma dangi ba bincike ba komai suka saka Raudat a gaba Babar Hussain da kanta ta sa
Hussain ya saki Raudat dama bai damu da ita ba itace take sonsa kawai a hakan ma da ya
saketa sai da ta Sha kuka auren shekararsa Daya da Dan watanni ta koma gidansu,tayi jinyar
zuciyarta sosai kafin ta hakura da son Hussain shi kuwa Hussain baya ta tata Sam,Babanta ne
ya maida ta school tayi degree tana gamawa ya samo Mata aiki Babba da NGO su Kuma duk
inda aka turaka aiki dole sai ka je,Kano Suka kawota supervisor ce sune suka rabawa irinsu
sababbin motoci masu tsada,dama Kuma a can Oyo tana da tata motar da Babanta ya siya
Mata,shi yasa tazo kano ta Kama gidan haya har Suka hadu da Affan suke fada Kuma kusan a
tare Suka zo Kama gidan ta Sha Matukar wahala a hannun Hussain kafin Allah ya yanke mata.
Affan
Affan Kuwa asalin Fulanin Zamfara state ne, sunansa Aliyu A. Aliyu,mahaifinsu su biyu Maza
ya Haifa Yusuf shine Babba an haife shi da shekaru hudu aka samu cikin Affan,da cikin Affan
Allah yayiwa babansu Aliyu rasuwa,Babar su tana haihuwa aka sakawa Affan sunan Mahaifinsa
wato Aliyu shine aka boye sunan ake kiransa da Affan, su biyu Suka taso a hannun mamansu a
Zamfara duk da cewar babansu bai mutu ya bar wata kadara ba face wata gona layi biyu,bayan
Yusuf da Affan sun gama secondary School babu kudin ci gaba da karatu,sai Mamansu ta siyar
da gonakin nasu ta hada kudin kaf ta Kira Yusuf da Affan tace kunga kudin nan nasan bazai
isheku kuyi karatu ba ku biyu Kuma ina so a cikinku wani yaje yayi degree a rayuwa ya kuke
gani Kai Yusuf gadon ku ne idan Kuma kowa bazai iya barwa kowa ba to sai dai mu Kama
sana'a da kudin,Yusuf ya kalli Affan yace gaskiya ni bazan iya barwa Affan kudina ba,Affan
Kuwa Nan take yace Yaya Yusuf ni na hakura da karatun dama kaga nine karami na bar maka
kudin gado na halak malak kaje kayi karatu idan ka samu aiki daga baya ka biya min ni nayi
karatun daga baya ai ba'a girma da karatu,Yusuf yayi farin ciki sosai karshe aka Nemo
admission lokacin baya wahala a ABU Zaria Yusuf ya shiga ya gama degree dinsa gashi Allah
ya hadashi da Abokinsa Dan gidan me kudi ya ja shi cikin Harkar kasuwancinsu na siyar da
gwala gwalai har aka zo ma ana tura Yusuf kasar waje yana siyo kayan, a hankali a hankali
Yusuf ya Zama me kudin gaske ya kera katafaren gida a Kaduna gida na gani na fada,ko aikin
gomnati ma bai nema ba,ya manta da halaccin da Affan ya Masa ya kasa tunawa ya sashi a
university,karshe da yazo zamfara da galleliyar motarsa Wai yazo daukan Mamansu zai maida
ta can Kaduna kusa da shi,Mama tace Yusuf Saura Affan Yana ta Zama ba karatu burina ka
biyawa Affan shima yayi karatu ya shiga University yace to zaiyi cikin ikon Allah watan
mamansu Uku kacal a gidan danta ta kamu da ciwon sugar farar daya ta rasu dake Affan shima
Yana gidan Yusuf din tun asali Allah yayo shi da son
Gayu da tsafta ga iya daukan wanka dama Kuma gasu kyawawan gaske.
Bayan mamansu ta rasu da watanni Yusuf ya fara wulakanta Affan kamar ba gidan dan
Uwansa ba,karshe Affan har ya gaji ya fara sana'a haka Kawai sai ya saro irin Guava ya dinga
siyarwa Yana samun kudinsa baya kula kayan Yayansa,ya koma sarar irin su safa da
handkerchief yana bin titin kwalta a hannu Yana siyarwa,ya dawo ya koma koma siyar da su
charger a gefen titi da Haka ya samu ya shiga