Showing 84001 words to 86820 words out of 86820 words

Chapter 29 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

786

haushi sosai yace haka Allah
yace? Ya tsareta da Ido tace kayi hakuri ka yafe min ni tsoron ciki nake yi dan Allah na siyo
maganin planning na dinga Sha ka yarda I promise Ina yaye Muhammad sai na daina sha,yace
to naji karki sake min haka bana so kin San irin hakurin da nakeyi,to ai nace kayi hakuri ta furta
tare da rungume shi ta baya,shanmatarsa tayi ta tura shi saman bed ya fada,tace baka da karfi
dama na fada sai na kayar da Kai watarana,dariya yayi ya dauketa ya jefa ta saman bed da
karfi sai da kashinta yayi kara ta saki kara,yace sorry ya Kika ji to? tace da dana da komai ka
dinga jefar da me Da harfa Da ne dani,Muhammad yana Dan bed dinsa a gefe ya saki kuka ta
dauke shi tana cewa Kai kaci Uwaka Nusaiba,Aslam yace Allah kiyaye ta Zama uwarsa wannan
muguwar, Naga kayanki a jikinta da na hanaki ki bata shine Kika bata ai gashi ta min
kyau,Siyama tayi dariya tace baza ka bani haushi ba Mallam ta zauna tana bawa danta
Nono,Aslam so yayi taji haushi tunda ta bada kyautar kayan nan abun yana ransa, ya dawo ya
zauna a kusa da ita,tana bashi kadan tace ka koshi,yace mene haka wannan ai rowa ce,katon
ciki zaiyi haka Kawai,Aslam yace nono ne yake sa katon ciki ke baki Isa ba dama muguntar da
kike Masa kenan ki ba yaro abu ya koshi harda bata rai ba shiri ta bashi ya koshi,Yana Sha
harda yo aman nono a jikinta,Aslam yace kazama sai karni dole na fara tunanin kishiya,Siyama
sai ta Fara kuka tace shi yasa nace maka bana son haihuwar nan ka nace yanzu ga irinta nan
kana ce min kazama,yi hakuri to ni da yau ma zanbi sahun jaririn ki bani nima na kora,ba wani
nan cewar Siyama,ta tashi ta cire kayan ta zuba a washing machine ta wanke sannan tayi
wanka ta fito,yaron ta kaiwa Nanny ta gyara shi,tana dawowa Aslam ya sunkuceta sai saman
bed daga Nan suka Fara soyewa.

Bayan wata biyu Nusaiba sabo da tunanin rashin miji duk ta rame gashi Ihsan har an kawo
kudin aurenta za ayi bikinta ita Kam shuru,Mama haka take aikin lallashin Nusaiba tana cewa ta
ci gaba da addua,Nusaiba har gidan Siyama take zuwa sabo da Jaririn nan burinta taje ta goya
shi,kaunarsa take yi har ranta,yau Aslam yana gida sai ga Nusaiba ta shigo da sallama,Siyama
ta amsa tace ba wajenki nazo ba wajen Dana nazo na kwana biyu ban ganshi ba,Ina yini
Aslam,yace lafiya da kyar Yana hade rai,Siyama ta kalleshi bata ji dadi ba mutum me kaunar
danka, Siyama ta Mika mata shi tace bari na kawo Miki Pampers a saka Masa yanzu na Masa
wanka,kayan shafe shafen jaririn ta kawowa Nusaiba,ta Fara Shafa Masa mai yayi Mata Kashi
a jiki,Siyama tace ki cire shi a jikinki da sauri,Nusaiba ko a jikinta tace kyaleshi ya gama na
wanke sai da ya Gama ta Shige toilet dake wani bedroom a palon ta sake wanke yaron tas
Siyama ta karbo shi ta maza ta shirya shi da kanta,Nusaiba ta tube kayanta ta wanke tayi
wanka,Charity ta bata wata Atamfa riga da skert kusan sabuwa ce ma tace ta barwa
Nusaiba,Nusaiba ta shanya kayanta ta dawo Palo ta dauki Muhammad yayi bulbul dashi yayi
wayo fari tas da shi, dalilin haka Aslam yace na yafe miki duk abinda Kika min kinci darajar
Dana Muhammad,Nusaiba tace na gode taji sanyi a ranta bata son irin bata ran da yake mata.

Sai Yamma likis ta koma gida, Siyama kuwa ganin Nusaiba ta tafi tace dan Allah wannan
abinda kakewa Nusaiba ka daina Sweetheart,ba dadi tana son danka ka dinga Mata haka Indai

tazo kana nan bata sakewa, kin San fa me ta min Yarinyar nan bai kamata ma ki dinga kulata
ba tunda wani abin a gabanki akayi,ya Ilahi ta gane kurenta ta nemi yafiya me yayi saura
gaskiya ni ka daina Mata haka ba dadi,to nan fada kike min ko umarni kike bani ko kuwa
shawara? tunda kina sonta haka sai aje a maida aure ta dawo ku Zama kishiyoyi sai kuci gaba
da zumunci,Siyama ta bude baki tare da furta haka nace maka? Kawai kace sonta kakeyi har
yanzu zaka dawo da ita shine magana kawai,dansa ta Mika Masa ungo danka ko na fatalar da
shi,ya karbi abinsa ya haura sama Yana dariya a ransa,tace ka dawo muyi magana akwai wani
abu kasa a ranka wannan Maganar bata mutu ba,bai kulata ba tun daga ranar Siyama bata
sake zancen Nusaiba ba, bakinta kanin kafarta har Bata so ma Nusaiba tazo su hadu da Aslam.

Tana zuwa kofar gidansu taga Machine din Salahu masoyinta Wanda ya fece,ko kallonsa bata
Yi ba zata wuce ya dakatar da ita yace Nusaiba dan Allah kiyi Hakuri ki yafe min nayi
kuskure,Kiyi hakuri dan Allah,tunawa tayi yanda itama tayiwa wasu laifi Kuma aka yafe mata
tace ba komai na yafe maka,Yace dan Allah ki bani dama na dawo da Maganar auren mu,dama
gwadaki nayi na gani da gaske kina sona tsakani da Allah Kuma na tabbatar naji labari,Nusaiba
tace waye ya baka labarin? Yace Aslam tsohon mijinku shi yace kin canja yanzu Kar na dauki
zugar mutane idan Ina sonki tsakani da Allah na dawo na aureki ya fada min kinyi nadama ke
yanzu sabuwar Nusaiba ce,Nusaiba Murmushi tayi jin Wai Aslam da Kansa yasa baki a aureta
shi da ya tsane su,juyowa tayi tace in ka shirya ka turo manya bani bukatar yin sabuwar hirar
soyayya da kai ka azabtar da zuciyata,Salahu yace kiyi hakuri na gode Kuma Inshaallah Jibi za
a turo ki fadawa Abba,Nusaiba Kamar bata murna ta fada gidansu sai Murna tana cewa Mama
Allah ya amsa ta bawa Mama Labari,Mama tace Kai duniya shi yasa akace ka taka a sannu.

Bayan wata daya aka Sha bikin Nusaiba da angonta,Ihsan da nata itama ma'aikacin
banki,Mijin Nusaiba gida ne Wanda iyayensa Suka mutu suka bar Masa gado ya gyara shi sosai
ya maida shi na zamani yayi kyau dan madaidaici harda gate dinsa ko Ina tiles tsakar gida
broken tiles ne dagwas, Landlady ita tayi kayan kitchen na Nusaiba da Ihsan sauran Kuma
Shehu ne yayi Kamar yanda uba ke yiwa yarsa,Affan ne da Raudah Suka hada lefe Akwatu
hudu kasancewar Angon yaron Affan ne na hannun dama,machine din ma Lifan Affan ne ya
siya Masa,Siyama ce ta tasa Aslam a gaba da kuka sai ya bata kudi tayi gudunmuwa dan
Dansa da Nusaiba ke so yace me za ayiwa Nusaiba me ya dace, Siyama tana share hawaye
tace a bata jari tunda mijinta baida hali sosai sai rufin asiri idan aka bata sai ta dinga sana'a a
gidanta ko irin dan siyar da su Maggi,omo etc,Nawa za a bata? dubu dari ? Yace to Zan Miki
transfer ki tura Mata kice gudunmuwarki ba ruwana a ciki,Siyama tace hakan ma yayi na
gode,haka ta turawa Nusaiba Suka Yi shawarar kayan da zata dinga siyarwa nan gaba,Ango
Kuma yace in sun Gama amarci zai maida ta makaranta itama tayi ilimi,Nusaiba sai godewa
Allah akeyi ana murna.
Siyama kuwa Private University Aslam ya sata taci gaba da karatunta tana kula da danta
Wanda yayi wayo sosai.
Aisha ta Haifi yarta mace katuwa,Nabeela ma mace ta Haifa,sai matar Sabeer da ta Haifi Yan
biyu duka maza manya,su Aslam sune na hannun dama a nan.

Raudah ce bata Haihu ba har sai da cikinta ya shiga wata goma,Affan yace idan ba dama

Kawai suje asibiti ayi aiki a cire dan,Raudah tace bazai yuwu ka kassara min rayuwa ba in
samu matsala Ina lalacewa wata zaka aura haihuwa ta Allah ce a barni Allah zaiyi ikonsa haka
Kawai ayi min aiki nazo na samu akasi matsala ta afku shike nan sai naji gudar Amarya a
gidana bada ni ba,Affan yayi dariya yace wannan zafin kishi Ina za a kaishi Raudah ni nace
zanyi kishiya Ina nake da wannan kwarin gwiwar ni waye ni,who be me? bayan kin gama dani
sai abinda Kika ce,Suna haka Kamar Wasa Raudah ta fara Nakuda,damtsen Affan ta rike tace
bala'iiii ah'ah Affan....wayyo ta kwala ihu ta rike Mara tace Subhannallahi...mutuwa zanyi..Affan
yace idan Wasa kike ma ki daina,tunda yaji Raudah ta hayayyako Masa da masifa da bala'i
Kamar zata cinye shi karka isheni karka dameni,Malam ka saurara min bana son
wulakanci...yace to da gaske ne nakuda ce muje asibiti tana masifa taya Zan iya tashi ta balla
Masa harara,bata ita yake ba ya dauketa da kyar ya sata a mota,tace kayan haihuwar ko da
yatsunka za a yanke cibin? Affan yace ki dinga bina a hankali Baby, tace Kar na sake Jin kalmar
nan a bakinka,Affan ya koma da gudu ya dakko takarkacen data shirya,ya figi mota tana ta
faman wash wash Allah na har suka je asibiti aka dauketa cikin gaggawa,Affan hankalinsa a
tashe sunfi kafin 1hr sannan aka ce Masa ta haihu,Uwar gidan Liman ce a wajen Raudah itama
Namiji ta santalo katon gaske da gani ya dade a ciki,Raudah ta Sha wahala ba a sallameta ba
sai washe gari da Yamma sannan,Matar Yusuf har tazo,Haka Maman Raudah da kanwar
mamanta sunzo Suka ce tafiya zasuyi da ita,Affan yace bai yarda ba ya dauke jariri ya Hana
kowa

Da kyar ya hakura yace iya sati biyu daga Haka karta Kara ko kwana daya,suka tafi kuwa har
kudin rago Affan sai da ya tura raguna guda biyu sai dai suyi waya da Rauda ko video call yaga
jaririnsa,Ranar Suna yaro yaci Abdallah,su Raudah acan sun Sha shagalin suna,tana cika sati
biyu Affan yaje airport ta sauka da jaririnta ya dakko matarsa Suka dawo gida,sai lokacin suka
nemi yar aiki Nanny dattijuwa me Kamala,Siyama har barka taje mata itama.
Nusaiba Kuwa an Kama sana'ar Omo da su Maggi etc Hannu bibiyu har yasa ta zana waec
da Neco tana Fitowa bata samu direct degree ba sai NCE ya sama mata ta Fara zuwa,Siyama
kuwa anyi nisa a school,Su Nusaiba an farfado kullum Mama cewa take ta kula da mijinta ta
rike shi Hannu bibiyu Kar tayi Wasa da aurenta. Bayan wata biyar Landlady ciki ta samu dama bata taba haihuwa ba yanzu ta samu a gidan
Shehu,Ihsan itama sai ciki har ta samu ciki kullum laulayi da amai,Nusaiba kuwa nata cikin ko
abinci ba komai take iya ci ba sai abinda taji zuciyarta ta raya mata Haka suke fama

Siyama danta har ya fara rarrafe gwanin sha'awa gashi ta tara masa suma an daure Masa ita
kamar yaron turawa kowa ya kalle shi yasan ba karya dan gidan Yan gayu ne,shi kuwa Affan
Abdallansa kaishi yake ana Masa shegen aski style style har sumar tayi yawan gaske Yana
zama,Babu style din da ba'a Masa yaron nan,kayansa ma in aka saka Masa kasan babansa
dan wanka ne yanda ake kwalkwale yaron nan,idan Yana gida har goya shi yake yasa zani ya
daure abinsa a baya Kamar mace haka Affan ke yi, yau ma Yana gida ya goya Abdallah a
bayansa ya daure shi da zani harda jijjiga shi Raudah tana Masa dariya.

Bayan wasu watanni Nusaiba ta Haifi yarta mace Siyama sune na jikin gado,ranar Suna aka
sa mata Jawahir, Nusaiba ana zaune cikin rufin asiri ba rashin ci ba rashin sutura Yar unguwarta

idan zata je ya dauki matarsa a machine dinsu abinsu shar, Nusaiba da shegen Iyayi harda
koyon machine Lifan ta iya sosai sai ta saka riga da wando ta sa Abaya da mayafi taci glass ta
tuka machine taje inda taga dama,Landlady ta haifi Namiji itama. Muhammad din Siyama yayi
wayo ya Fara Kiran Daddy da Mummy Yana tafiyarsa ko Ina dagwai dagwai Amma ba sosai ba,
idan Aslam bazai dade a Office da shi yake tafiya yaron suje su dawo

Yau Aslam yana zaune a dakinsa a kasan dan karamin carpet dake jikin bed dinsu Yana cin
abinci, Siyama tana zaune a saman bed tana bawa Muhammad Nono da yan hakoransa ya
gartsa Mata cizo,bata san Sanda ta duke shi ba ji kake dim dim a bayan yaro,dariya yake yana
kallonta ya dage kafa daya ya riketa da hannunsa dadi ya gama kaiwa yaro,ya zaci Wasa take
Masa sai ya sake cizonta,Siyama ta fisge nononta ta cillo shi kasa aka wani dangwarar da yaro
da karfi yaji zafi ya fashe da kuka tace idan ka sake cizona sai na mareka yaro marar kunya
,Aslam Fuska ya daure takaici ya kamashi yace mene haka Wai ke aljanu ne dake ne? wannan
yaron me ya sani sabo da Allah dan ya cijeki baza kiyi hakuri ba,Siyama tace kaji zafin Kuwa
Ina magana Yana min dariya na yaye shi daga yau yayiwa Kansa bazai sake Shan nono
ba,yace ai lokaci bai Kai ba baki Isa kin yaye min yaro ba,ai Kai sai ka bashi naka nonon ya
sha,dansa ya dauka da yake zaune yana kuka ya lallaba shi yace kyale Mummy taje da
nononta ga abinci yaci gaba da bashi abincin Yana ci,a banza kuma ta huce tazo zata dauke
shi Aslam yace kyale min yarona baza ki dinga dukansa a banza ba,Dariya tayi tace Indai shine
gashi nan rigimarsa ma ta isheka,an Masa wanka? Siyama tace ae an masa,yaci gaba da
lallaba shi Kamar zaiyi bacci sai yaki yi gashi Aslam ana so a Sha soyayya da Siyama yaro yaki
bacci,Light ya kashe ko zaiyi bacci amma yaki yi,saman gadon ya kwanta da shi,Siyama zata Yi
magana yace shiiiit Shuru Shuru...ana ta lallaba yaro har ya fara bacci Aslam ya lallaba zai
tashi yaro ya fashe da kuka,Siyama ta dinga dariya tace matsa ka gani ta kwanta tare da yaron
ta sa Masa nono a baki Yana Sha sai bacci Aslam yace wow tana bawa jariri nono yana cire
Mata Kaya,aka dauke yaro aka maida shi bed dinsa, sai da suka kwantar dashi yayi
bacci,bargonsa Dan karami aka lulluba Masa kansa a waje,tace Yana tashi wajen Nanny Zan
kaishi,Aslam yace ban yarda ba babu Nannyn da Zan Bari ta dinga kwanar mim da yaro komai
dattijantakarta a zamanin nan da duniya ta lalace sai an kula sosai da yara,gashi nan kyuya ta
matanmu tasa suna ta jefa yaransu ga halaka ko a lalata maka rayuwa danka musamman ya
mace sai an kula sosai nawa Zaki ji yaron gida yayiwa Yar wani fyade,Yar aiki ta lalata yarka
tana lesbian da ita,akwai na kirki a Yan aiki Kinga ko wannan Yar aikin na yarda da ita ta dade a
gidan nan I think farko ma a nan kuka taba ganinta,tun Mum tana kasar nan take Mana aiki
amma komai yarda ya kamata a kiyaye,Siyama bargo ta ja musu tace to Allah ya Kare mu da
yaranmu yace ameen shi yasa baza ki aiki ba karatu dai zan bari kiyi Amma kina gamawa shike
nan

Tace to ka tuna min gobe Ina da test ko karatu banyi ba ta mike zata dakko littafi yace ai sai
dai kici Kan jaki amma yau babu karatu sai na aure, yaron ne ya farka kadan ya kwala Kira
Daddy,Aslam yace baya nan,Jin muryar Aslam sai kuka Siyama tace wannan yaron da babba
ne yau sai yaci dukan tsiya,Aslam yace je ki dauki danki ni na gama bangarena bazan sake
daukansa ba na gaji,ya isheni da kuka ya hanani bacci karki haifo wani da wuri wannan kadai
ya ishemu nan gaba idan Muka huta da yawa sai a Karo haba Yara su dami mutum,Siyama ta

tuntsire da dariya tace Kai da kace ayi sauri a Karo yace na janye magana ta yau,kaiwa Nanny
shi,Siyama tana ta dariya tace kace danka bazai kwana can ba,yace Kai Mata Allah ya kiyaye
kaishi,juyawa tayi zata fita yace Madam da kayan baccin Zaki fita ai tana dakin dake palon
kasa,ta fita ta Kai Mata Muhammad,ta karbe shi suka kwanta sai yayi shuru ya koma
baccinsa,ta dawo tace har ya koma bacci,yace dumin uwarsa yake son ji ai Kuwa bai Isa ba sai
in ba da dare ba,ya jawota Suka Shige bargo
Haka rayuwar ta kasance musu cikin farin ciki da kaunar juna sai jarabawar rayuwa da Allah
baya barin bawa ba jarabawa.






ALHMDLLH

Masu Sharhi Ina Matukar godiya wacce ba adadi, gaba Daya yan group din BABU KAUNA
musamman masu bibiyar littafin nan Ina Matukar gode muku


Sai Watarana kuma idan da rai da lafiya cikin yardar Allah na sake muku sabon Novel Amma fa
Zan dade banyi sabo ba sai an huta an huta an gaji sannan.


Copy by Zainab Butalawa




AsmaBaffa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0