Showing 75001 words to 78000 words out of 86820 words

Chapter 26 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

764

an daura auren Shehu da Amaryarsa Landlady

kayan daki na gayu da tsada Landlady ta zuba a gidan kana gani kasan ba karya,a ranar da
yamma Kuma ta tare ba kowa a gidan sai Raudah Wanda ma har Affan yazo Daukanta zasu tafi
gida sai ga Nusaiba da Kaya niki niki a Ghana must go ta dawo.
Affan ya dau wankan sugar yana tsaye a jikin mota yana jiran Raudansa Nusaiba sai kallonsa
takeyi har da goge Fuska ko zai kyasa yace Yana sonta,Jakarta ta rike a hannu a Dan gayence
Wai Kar ta kwafsa,zata wuce ta gaban Affan tace sannu lokacin Rauda ta fito taji Nusaiba tana
cewa bawan Allah wani gidan kake nema ne? Affan ya kalleta sama da kasa yace ke lafiya Ina
ruwanki dani karki jawo min matata yau ta hanani bacci mijin tace ne ni nan da kika ganni bani
da amfani wajen Yan matan waje gwara kija tsummar ratuwarki ki Kara gaba gwandala ta baza
kici ba,Nusaiba dariya tayi irin ta samu Hanya tace hmm amma matar taka ta birgeni haka ake
son mace,Affan yace ae ai ta Isa ne kin san wasu ai basu Kai su mallaki miji ba sabo da Basu
iya allonsu ba basu da hali na gari shi yasa ake yawan sakin Mata basu iya Zama da miji
ba,Nusaiba sai taji Kamar da ita yake,yace Amaryar Shehu Muka kawo ai Shehu yayi dacen
mace yanzu zai samu kwanciyar hankali ance uwar gidansa ballagaza ce ita da yarta Basu San
me suke ba ance ma ko a unguwa an tsane su,Nusaiba Kamar ta fashe da kuka bawan Allah ya
tsaya sai caba Mata magana yake,ita bata San ma Affan bai San ko Shehun ba sai dazu ya
ganshi Suka gaisa labari Suka ji a layin ana fada, Raudah ce ta karaso tana hararar Nusaiba ko
kunya Raudah babu akan kishi ganin layin ba kowa sai iya su harda shafa gemun Affan ana
Masa shagwaba tace muje ta juyo ta kalli Nusaiba tana Mata up and down,Affan yace baiwar
Allah ko Zaki Mana wanke wanke da shara a dauke ki aiki kin tsaya kin zuba Mana Ido, Raudah
tace ai wallahi gwara aiki ya kashe Ni idan ba namiji zaka dauka ba Indai macece bana so zanyi
komai da kaina,Nusaiba juyawa tayi tana tuna rayuwarta a gidan Aslam,da kyawun Aslam da
yanda yake nuna Mata so da kauna,kuka ta saki tana tafiya kasa shiga gidansu tayi ta zauna a
kofar gida bakin kofar su tana ta kuka,tausayi ta bawa Raudah taje wajenta tace baiwar Allah
kuyi hakuri wlh bamu fada dan mu wulakantaki ba mun San darajar dan Adam kune bakwa kau
da kai ga mazajen wasu kiyi hakuri idan abinda mijina yace ya Miki zafi,Nusaiba tace ba

wannan ne ya dameni ba,nadama nayi a rayuwata na tafka kuskure,to Allah ya Mana me kyau
cewar Raudah tana juyawa motocin Aslam biyu Suka Yi parking daya motar securities ne daya
kuma shine a bayan motar tare da Siyama,Fitowa yayi a hankali wanka iya wanka ga
kyau,zagawa yayi tare da budewa Siyama mota ya riko hannunta ta fito da dan karamin cikinta
a gaba ya Fara Fitowa ta Sha Abaya ta zuba kyau Kamar ba Yar kasar nan ba,sunyi kiba da
kyau sun Kara wani fresh,da gani kasan sun dan huta a kasar waje, Nusaiba ta bisu da kallo
kawai,Aslam Yana ganin Affan ya koma gaban Siyama ya kareta Wai Kar ya ganta tsohuwar
budurwarsa Kar so ya dawo sabo,Affan dariya abin ya bashi,ke Kuma Raudah da kin ga mace
sai boye Miji a tsiri nunawa lallai ita fa matarsa ce,Aslam zai wuce tsabar kishi harda nunawa
bai San Affan ba,Affan ya Mika Masa Hannu da kyar ya karba Suka gaisa Siyama ta dawo gaba
tace Affan kaine a unguwar tamu,yace Amarya Muka kawowa Alhaji Shehu kawar matata
ce,Siyama ta kalli Raudah tace Sannu Ina yini,Aslam harda Jin haushi dan me zata gaisar da
Raudah ai Raudah ce ta kamata ta gaida Siyama,Raudah ta amsa da fara'a Suka gaisa ta
gaida Aslam ya amsa,Affan yace Nasha Kaye a wajenka mene abin bata rai,tunda ka lashe
zabe Kai fa kace ba gaba,Murmushi Aslam yayi ba shiri ya dai tsaya sun gaisa sosai harda
bawa Affan katinsa yace gashi idan kana so Watarana mu gaisa,Affan ma ya zaro katinsa yace
ga nawa Wai ya nunawa Aslam shima fa babban yaro ne da aikin yinsa,Raudah sai kallon cikin
Siyama takeyi dama itama ta samu nata da Affan,gidan su Siyama zasu shiga Wanda dole sai
ka wuce ta kofar gidan su Nusaiba,Nusaiba tana tsaye tana ta faman kallon Aslam Kamar
mayya,Aslam ya gane itace harda shafa cikin Siyama suna tafiya,Siyama tayi dariya tace dan
Allah ka kyale babyn nan haka kullum hannunka na kai,Siyama tace Nusaiba kece dama ko
magana haba Nusaiba,Nusaiba an sakko tace Charity sannunki tana tabe baki ,Hannun charity
ya rike Suka Shiga gida me kyau Nusaiba bata gane gidan su Siyama bane yanda Kawu ya
gyara gidan yayi kyau ya canja sosai,haka ta Shige gidansu ta iske kannenta duk basa nan sun
tafi sashen amarya,Shehu Yana dakinsa yaji sallamarta,Fitowa yayi yaga Nusaiba a gabansa ta
zube gudun Kar ya koreta ta fashe da kuka ta rike kafar Shehu tana dan Allah Abba ka yafe min
na tuba wlh bazan sake biyewa Mama ba,Shehu yace Nusaiba ki ma biye Mata ni ba ruwana
kece a wahale,Ka yafe min Abba yace dama ni bana Fushi dake na yafe Miki, Yar da na Haifa ai
kullum Addua Zan Miki Allah ya shiryeki ,Nusaiba taji Dadi sai ta share waje ta samu wajen
Zama duk da haka bata leka wajen Amarya ba abinci taci duk Yan uwan Shehu sun tafi itace ta
gyara gidan tsaf tare da kannenta tayi wanka,Shehu Kuwa ana yin Sallar Isha ya wuce
bangaren Amarya landlady anci gayu ta hade cikin rigar baccinta pink ta Sha kyau na
musamman,Shehu duk an gigice anga sabon jini,kajin da ya siya Mata sai da ya siyawa
yaransa ya basu nasu na Amarya Kuma daban,Nusaiba yaushe rabon da taga nama tana
Kauye sai yanzu,kannenta su Ameer sai dariya suke kyalkyala mata.

Landlady wayayya ce wacce tasan ta Kan maza ga iya shagwaba da kisisina Shehu tun a
wajen kwanciyar aure yasan sai yanzu yayi aure da haukarsa Kawai yake yi,washe gari kasa
Fitowa yayi ko kafar gida Yana ta soyayya, Landlady girkinta tayi Nusaiba itace tayi nasu girkin
ita da kannenta,da yamma Kuwa sai ga Shehu a kitchen ya ajiye hula a gefe Yana taya amarya
wanke wanke,Yana gamawa yazo Yana yanka Mata Alayyahu,yau ma Shehu kwanan farin ciki
yayi sun gurji juna shi da Landlady gaba daya Shehu ya susuce ya samu mace Yar gyara
wacce tasan kanta,Satin Landlady daya ta Fara girki da su Nusaiba duk da haka Nusaiba bata

taba shiga gidan ba sai da ta gaji taga kannenta sai shatara ta arziki Aunty Amarya take musu
amma banda ita,haka da Yamma tayi wanka ta shirya ta Shiga bangaren Amarya a ranta tace
gaskiya Aslam bashi da mutunci mutumin nan ba karamin makiri bane shine yayiwa Amarya
wannan mu Kuma ko oho Nusaiba harda goge kwalla ta shiga Palo ac da kamshi Kawai ke
tashi,Abbansu taji a kitchen suna ta Wasa da dariya da Amarya suna girki a hankali tayi Sanda
Kamar barauniya ta leka kitchen din ta hango Landlady akan cinyar Shehu suna kissing,da
sauri ta dawo baya tana rufe Ido ta zauna tana mamaki tace oh duniya ashe Abba dan duniya
ne haka,Amarya ce tace naji Kamar yarmu na sallama ta mike ta fito tasan Nusaiba a
hoto,Nusaiba tana ganin Amarya shegu kudi ba karya sai ta Mata kwarjini har kasa ta rusuna
tace Ina yini Aunty,Aunty ta amsa da fara'a tace sai yau Zaki zo min kema kishi kike taya
mamanki ko banga laifinki ba,Nusaiba mayyar masu kudi tace ba haka bane tana sadda Kai
Kamar ba Nusaiba ba ,Shehu ne ya fito,Nusaiba tace Sannu Abba tana Zama a kujera ya amsa
da fara'a sai rawar kafa yake sabo da anzo gaida Amaryarsa,bedroom ya shige Landlady tace
Nusaiba jeki kular min da abincin can bari naje,Nusaiba ta Shige kitchen Itakuma Amarya ta
wuce ciki tare da Shehu suna soyewarsu aka bar Nusaiba da aiki,Wasa Wasa sai gashi Amarya
bata aikin kirki a gidan nan gaba Daya kusan Nusaiba ce ta Zama Yar boyi boyi ita take Kai
kanta tayi ta dirzar aiki ba tare da an sakata ba sabo da Landlady tana da kudi.








AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢�AUREN MU🛢�


96-98




Official

By
AsmaBaffa

Page naki ne

FUTURE RM









Nusaiba gajiya tayi da rashin mahaifiyarsu ta tattara kannenta suka koma gaban Abbansu
tare da durkusawa,Shehu yace Yaya aka Yi ne? Nusaiba tace zuwa Muka Yi mu roke ka dan
Allah Abba ka dawo da Mama gida badan halinta ba ko don mu,Amarya Landlady tana ji,Shehu
yace babu ruwanku Kar na sake ji Kun min maganarta Indai maganarta Zaku kawo min to karku
zo inda nake,ku tashi ku bani waje ya musu tsawa suka mike sum sum Suka bar wajen,Nusaiba
babu abinda take da buri face ta samu mijjn aure ko ba me kudi ba amma ta rasa me sonta
yanzu duk irin farin jininta yanzu babu ko wani ya fara tunanin zuwa a unguwar za a fada Masa
gaskiya halin Nusaiba da uwarta sai mutum ya fasa zuwa,akwai mutum biyu ma sunzo amma
tun daga zuwa daya Nusaiba bata sake ganin sun Zo ba an zuga su a unguwar ,wannan karon
Ido rufe take Neman miji ko ba me kudi ba ma amma talakan ma ta rasa shi.

Yau tana part din Amarya tana Mata uban aiki Landlady taga tana hawaye,tace Nusaiba
lafiya? Nusaiba ta zauna ta bawa Landlady labarin abinda ta shuka kaf tana kuka tace yanzu
miji nake nema ko talaka ne wlh Zan zauna na rike mijina amma Kinga talakan ma na rasa
duniya me yayi, Landlady tace wlh kin bani takaici ko Mene ke Kika jawowa kanki Nusaiba
yanzu ai an waye kina gani yanzu manyan mata ma kula suke da mazajensu bare Yan matan
yanzu,shawarar da Zan baki ki yiwa iyayenki Biyayya har Maman taki ki samu Wanda Kika
batawa ki tabbatar sun yafe miki sannan ki dukufa da addua ba dare ba rana Allah zai kawo
Miki miji kin samu dama me kyau har biyu kinyi watsi da ita ai gashi nan yanzu son kudi da son
zuciya da hauka sun kaiki sun baro yanzu wa gari ya waya? Nusaiba tace Inshaallah zanyi
yanda Kika ce,Nusaiba haka ta sake gyara halinta tana ta Addua tana yiwa mahaifinta biyayya
amma ta kasa zuwa Neman yafiya wajen Sufyan da Aslam sabo da kunyar abinda ta aikata.

Mama tana Kauye lokacin da Nusaiba ta kwashe kudin tsohuwa Yan gidan Suka samu Mama
Suka zo Suka tasa ta gaba lallai sai an biya su kudin me daddawa Suka kwace karamar Wayar
Mama tare da siyar da ita dubu hudu Suka dauke dubu Uku dubu Daya Suka jefawa Mama
canjinta,ita kanta Mama wahala ta isheta baza ta iya ba gashi lokaci Yana ta tafiya haka ta hado
komatsanta ta dawo ta tafi gidan su Siyama tana rokon Kawu yasa baki Shehu ya maidata
wallahi ta gane kuskurenta baza ta sake ba,Kawu yace ai Kinga irinta yanzu gashi kalleki dan
girman Allah kin dawo sai kace dodanniya ,kin ganki Kuwa sai kace horror ba kyan gani da ace

da dare ne na ganki ai sai na Suma idan nayi arba da kamanninki sabo da zance gamo
nayi,Kawu ya gama Mata tatas sannan yaje ya samu Yan uwan Shehu ya lallabasu aka Kira
Shehu aka zauna dashi akan yayi hakuri ya maida Mama,aka buga aka buga Shehu yace bai
yarda ba,an rasa inda za ayi da Shehu har Mama ta kwashe kwana uku gidan su Siyama
Shehu bai San da zamanta bama,sai da ta daidaici Sanda yake dawowa daga masallaci da
sassafe da sauran duhu ta fice ai Kuwa taci sa'a ya dawo ta tare shi,zubewa tayi a kasa tace
dan Allah Shehu ka yafe min wallahi bazan sake ba na tuba kayi hakuri dan girman Allah,
Shehu ko kulata baiyi ba ta rike rigarsa tana kuka tana rokonsa ya fisge rigarsa ya shige gida
bangaren Amarya,haka ta dawo jiki a sanyaye.

Duk dangi da duk me fadawa Shehu yaji yaje wajensa akan Maganar maida Mama dakinta
Shehu yaki landlady da kanta tayi Masa magana yayi hakuri ya dawo da Mama ko dan yaranta
amma Shehu yace ba ruwanta wannan tsakaninsa da Mama ne dole ta kyale shi.
Kawu ne yace yanzu shawara ta karshe ki tafi gidan Aslam ki roke shi yayiwa Shehu magana
Indai Aslam ya sa baki to aurenki zai koma dai dai amma Indai ba Aslam ba Sai dai na fada Miki
ta bature Sorry Sorry.
Mama tsoro ya kamata tace Aslam din da ya tsane mu ko naje bazai kalleni ba karshe ma ya
ci min mutunci Aslam baya kaunar mu ko daidai da kwayar zarra ne,ai yayi dai dai mene ne
baku Yi Masa ba lokacin Yana auren yarki idan zaki je kije idan baza ki je ba to gobe ki bar min
gida na gaji cewar Kawu,Aunty tace idan tsoro kike ji zan rakaki,Mama tace dan Allah ki rakani
wallahi idan naje Ni kadai Aslam zai iya harbe ni da bindigarsa ni tsoronsa nake ji yanzu ban
taba sanin Shu'umi bane sai da ya rabu da yata sai da ya rama abinda Muka Masa babu irin
bakanta Mana zuciya da baiyi ba abin nan ya min ciwo karshen cin mutunci Aslam ya kashe
kudi me yawan gaske aka Yi min kishiya kalli gidanta kalli namu ta fashe da kuka Aunty sai da
abin ya bata dariya Aslam yayi dai dai cewar Aunty.

Washe gari da Yamma Sunday Aslam Yana gida Yana zaune a center carpet Yana shan lemo
Yana aiki a system Siyama kwance take a cinyarsa tayi dai dai da dan cikinta tana ta Wasa da
botin din rigarsa Suka ji door bell sai da dan cikin Siyama ya motsa sakamakon karar da yaji ba
zato,Siyama tace wash dan cikina zai fasa min ciki ni bana son karar nan tsoratani take yi yace
Zan cireta to tunda baki so amma idan muna sama fa taya za muji knocking? ai idan na haihu
sai a maida yace to ba damuwa,tashi ki bude kofa Siyama direct tace bazan iya ba wlh na gaji
kayi hakuri,dariya yayi yace wannan ciki Ina ganin ta kaina da shi,tashi to na bude Siyama tace
bazan iya ba dan Allah karka tashi naji dadin kwanciyar nan Allah kace su shigo mana,Aslam
yace yau baza kiji kunyar ba kenan? Tace ko Kawu ne sai dai yayi hakuri bazan tashi ba,da
Kansa yace ku shigo Aunty ta bude kofa tare da shigowa bayanta Mama ce sanye da
Hijab,Aslam Yana ganin Mama ya daure Fuska tam ba mutunci,Siyama kuwa bata tashin ba
kamar yanda ta fada,Aunty ce ta harareta ba shiri ta mike zaune a gajiye ba dankwali ma a
kanta doguwar rigace a jikinta Yar kanti tace Aunty Sannu da zuwa,ta gaishe da Aunty ta gaisar
da Mama ta amsa tana washe baki harda cewa Siyama Allah ya raba lafiya,Kitchen ta shiga ta
kawo musu lemo da snacks ta zauna kusa da Aunty ko minti daya bata Yi ba ta kwanta a cinyar
Aunty,Aunty tace ke dagani a kanki aka Fara ciki da kinzo waje ki kwantawa mutum a
jiki,Siyama kin tashi tayi har Aslam ya gaida Aunty Kawai ko kallon Mama baiyi ba ya mike zai

haura sama Aunty tace Aslam wajenka nazo fa,dawowa yayi ya zauna yace Aunty gani,Aunty
tace wata Alfarma nazo nema wajenka dan Allah Aslam abinda Mama da Nusaiba Suka maka
ka yafe musu kayi hakuri Allah ma Yana yafe Mana bare dan Adam ka yafe Mata,Mama ta
karbe harda durkusawa a kasa dan Allah Aslam ka yafe min nasan munyi maka laifi ka yafe min
dan Allah,Aslam ya kalleta shekeke bai ce kala ba,bazai yafe ba,Aunty tace kayi hakuri Aslam
Allah Yana son bawa me hakuri da yafiya,ganin Aunty ce take ta rokonsa Kawai yace to amma
fa bai ce ya yafe ba,Aunty taci gaba tace dama Shehu ne tunda ya saketa yau wajen watanta
hudu yaki ya dawo da ita babu irin hakurin da bata bashi ba yaki yarda kowa a dangi da Yan
Uwa har abokai sunje wajensa akan Maganar yaki amincewa,Kuma wlh ta tuba ta gane gaskiya
a matsayinta na Yar uwa musulma akace yau Allah ya shiryata ai abin farin ciki ne ga mu
musulmai to dan Allah ka sa baki kayiwa Shehu magana ya maidata Kaine kadai zaka fada
Masa yaji dan Allah,Aslam ya gama Jin Aunty yace ni Aunty mene hadina da iyalin Abba
Shehu,Ina yaro me zai kaini shiga zancen manya in yaga dama ya dawo da ita idan bai ga da
ba ta hakura ta koma Kauye inda tafi wayo ni ba ruwana da ai bata san dan Adam me daraja
bane bata taba zaton ma Zan Mata rana ba a rayuwa,Aunty tace bana son taurin Kai Aslam ya
Ina rokar ka kana botsewa,yace Aunty shike nan taci darajarki albarkacinki Zan Masa magana
amma bata da matsayin da Zan taka har can wajensa Zan dai kirashi a waya kawai in ya yarda
tayi murna idan bai yarda ba ruwanta mutum dai abinda ya shuka shi zai girba Kuma Alhmdllh
ko yanzu tun a duniya ba ayi nisa ba sun Fara girban nasu hukuncin,bazai yuwu ka shuka gero
kace zaka girbi shinkafa ba bazai yuwu ba kowa yayi yanda yake so to bazai ga yanda yake so
ba, idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0