Showing 48001 words to 51000 words out of 86820 words

Chapter 17 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

781

ta hira da
Affan,shi Kuma an wani nutsu Kamar ba shi ba,kannen Raudat Suka zo Suka gaida shi,last
born Dan yaro Affan yace boy zo Nan ya dauke shi yace ya sunanka? yace Irfan,Yana
tsokanarsa ya Dan dade har yace zai tafi ya rabawa yaran kudade ya fito Raudat ta
rakashi,tace zata maida shi masauki yace da Kansa zai koma shi zai Gane.

Kwanan su Raudat biyar a garin nan suna shakatawa kullum tare da shi suke yini kwanciyar
bacci ke raba su,ranar kwana na biyar Suka dawo gida Kano,Raudat tana shiga part dinta ta
hau gyara shima haka,ta Riga shi gama aikinta shi ya fita kalailaitar masifa,Yana goge kujeru ta
leko ta window ya duka ta wajen saitin windown ta dan yakushi bayansa ta koma ta buya ya
duba yaga ba kowa ya koma yaci gaba ta sake lekowa da cokali ta dan karci bayansa ya juyo
da sauri ya kamata dariya Suka Yi yace dama naji ajikina kece ai tunda Kika yakusheni ban ji
zafi ba naji wani Dadi da shock nasan kece Affan da karya yakushinta ma Wai dadi ba
zafu,Raudat har yau bata bashi amsar tana sonsa ba sai aji take ja Masa tun Yana tambaya har
ya gaji.

Aisha wannan karon tana hakurin dannewa basa fada da Mahaifiyarta suna zaune lafiya Sabo
da sunyi nadama Matukar gaske,aikin gidan kaf kusan Aisha ke yinsa,tana son cikin nan nata
duk da uban dan baya so amma ji takeyi da cikin nan,har tayi kyau ta Fara murmurewa, Farooq
yayi murnar fitowar Aisha amma yaji haushi da aka ce tana da cikin wani ba nasa ba,Aisha tana
ta murna zata samu danta ko ya Kawai tana wanke kayanta dana Ummanta ta Fara zubar da
jini,ta tsorata sosai Suka tafi asibiti har da Baban Aisha aka je, lokacin cikin Aisha ya zube gaba
Daya har ma sai da aka Mata wankin ciki,sabo da taji jiki kwanan su biyu a asibiti sannan suka
dawo gida taci kuka ta koshi sai da Babanta yayi ta Mata nasiha sannan ta hakura,Ciki na
zubewa mutane munafukai suka kaiwa Farooq gulmar cikin Aisha ya zube ta wani bangaren yaji
Mata ciwo ta wani bangaren yaji Dadi.

Bangaren Siyama kuwa sati Daya Kawai dangi aka fadawa Suma kawu yace ba taro Yan
daurin aure ne Kawai zasu Zo,Dangin uwar Babar Siyama ma haka ya fada musu,Babu Wanda
aka ce yazo sai iya maza Yan Uwa,shima Aslam ya fadawa Mum, Mum tace amma nayi maka
farin ciki son ai gwara ma haka ba sai da taron ba babu komai an gode amma duk da haka ayi
order abinci a Kai musu su bawa danginsu Suma mu dai ta bangaren mu tunda dama wannan
iftila'in ya fada maka dama bamu da Niyyar taro sai na Yan daurin aure Kawai Nan Suka Yi kulla
kullarsu da Mum dinsa yanda baza suji kunya ba,Haka aka tura manya da kudin komai da
komai ko Siyama bata sa rai da lefe ba,Aunty dai ta dage tana ta gyara yarta sannan tana zuwa
gyaran jiki, Saura kwana uku biki aka kawo lefe sunyi mamaki akwatina goma cif Kaya na gani
na fada ba abinda babu,aka dinga zuwa kallon lefen a unguwar,Maman Nusaiba taji labari ta
kyalkyale da dariya tace dan karya ne haka yakeyi yanzu ana kaita zaice yaci bashin bank ba
kudi sun shiga uku ta sake sakin dariya,Shehu yace kinyi asarar halinki ke dai Kam tir.

Aslam ne ya fito tare da Siyama yazo zance Suka Yi kicibus da Nusaiba mijinta ya kawota a
mota ya juya,Aslam bai ma ga ko motar ba lokacin yayi nisa tuni ya bar layin,Nusaiba ansha
wanka kana ganinta kasan tana hutawa ko kallonta Aslam baiyi ba ta gefenta ya wuce, har da
kallon Siyama tayi dariya tace an kusa cin bashin banki ki daina murna an kawo Miki akwati
goma Nawa kusan guda ashirin ya kawo amma karshe a ya na kare da talaucinsa, Siyama tsaki
taja,Aslam yaja hannun Siyama yace let's go My Heart Suka wuce,Nusaiba ta bisu da kallo tace
a hau taxi lafiya nasu ko kalleta ba abin Kuma ya Mata mugun ciwo a rai wato Aslam Kamar ma
bai taba saninta ba haka yake nuna Mata ta wuce gidansu dai tana takaici.











AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢� AUREN MU🛢�


61-65




Official

By
AsmaBaffa





Page nakuli ne
Rukey Muaz

Ana gobe daurin aure Siyama tasha gyara sai kamshi take zubawa Kawai ta Sha
lalle,Kawayenta ta gayyata Zulfa'u,Sakna,Raihanatu da Nana sune Kawai a gidansu suke
tayata Zama,sai bangaren Dangin mahaifiyarta Mata su biyar,sai bangaren dangin Aunty Mata
su wurin goma haka bangaren Kawu da Mahaifin Siyama Suma sun kai goma gida ya cika tam
duk da Kawu yace bazai taro ba dole sai da aka zo Masa,haka Aslam ya dinga dariya Jin Kawu
yace bazai taro ba amma iya dangi sun cika gidan haka ya Aiko musu da kayan abinci shinkafa
ta dafawa da danya ta tuwo,mangyada manja,Maggi iri iri,kayan Miya buhu biyu,su
Alayyahu,kabewa, Albasa,Taliya macaroni komai sai da aka kawo da yawa su Aunty Suka
dinga mamaki kamar me kudi haka ya aikowa da Kawu dubu dari biyu,ya bawa Aunty dubu
hamsim haka Siyama ma ya Aiko Sabeer ya kawo Mata kasonta sai,Kawu ne yaga mutane sun
cika gidan ya Kira Aunty gefe yace nace fa ba shagali ba biki ya akayi Yan Uwa Suka cika min
gida to wlh babu wacce zata Kai Amarya ko wacce gobe ta bar min gida,Aunty tace to tunda an
sanarwa Yan Uwa ai ba wacce zaka kora idan Kuma zaka iya bismillah,Kuma biki babu wacce
aka yiwa aure ba dangi sabo da Haka itama Dole Yan uwanta suzo Amarya Kuma ba komai
ango yazo ya dauki matarsa ai dai an daura aure ko to Alhmdllh,Kawu Yana magana kasa kasa
Kar dangi suji yace Ni dai ba wacce na gayyata biki,Kai ka sani cewar Aunty ta juya ta koma
suna ta girke girkensu Kuma ta gayyaci Yan unguwa Wanda suke mutunci da kawayenta.
Washe gari daurin Aure ranar asabar karfe 11am,Aslam shi Kam yayi gayya sosai Suka Zo da
danginsu na jini Yan uwan Uba dana uwa aka taru a masallaci Shehu ma shine wakilin Aslam
shi ya karbi auren Aslam aka daura akan sadaki dubu dari,ana daura Aure Aslam Yana cikin
abokai yaga Affan da liman sunzo Yana sani Aslam da abokansa yace Dan Allah a nuna Mana
Wanda na kasa a samarin Amarya,Sabeer yace waye Muka zo muka kasa Muka cinye shi da
yaki? Affan ya gane da shi suke,yace gani nan ya mikawa Aslam Hannu suka gaisa yace
Congratulations a zauna lafiya,Aslam yace Kar ma a zauna lafiya,Affan yace to fa Yana dariya
yasan kishi ne kawai,Sabeer yace Wanda Muka kasa ayi Hakuri banda gaba,Affan ya dinga
dariya shi ko a jikinsa ya tashi Yana kwambonsa ya wuce,Liman ma ya taya Aslam murna sosai
,Aslam yau anji shadda ta musamman Fara tasha aiki da babbar riga da hula yayi kyau kamar a
sace shi ga abinci da yayi orda fried rice da rabin kaza har da masu rabawa ana ta bawa
mutane a ledar take away a zuwan gidan Amarya ne Suka kawo.

Siyama kuwa ta Sha leshi dan ubansu golden and white,Kawu yace babu batun shagali ko
angon bai je wajen Amarya ba Kawu ya Hana,Amarya tana zaune cikin Yan tsirarin abokanta
suna cin abinci Kamar ba Amarya ba komai bata akeyi tana lashewa da ance gashi zata ci
abinta, sun Kuna Bluetooth speaker suna Jin kidansu suna nishadi tunda ango ya bugo Mata
waya yace sai na Zo daukan Amarya,Siyama tana Jin kunya tace ka daina zumudi fa period na
Fara jiya da dare,Aslam yace ba komai bukatar maje hajji Sallah tunda an daura yanzu
hankalina a kwance yake nasan kin Zama tawa,Murmushi yace 4pm zanzo daukan abata ki
shirya da wuri,Siyama Wayarta ma ta kashe duk sai taji ba dadi abinka da wacce bata taba
barin gida ba kullum kana tare da iyayenka dole idan za a rabaka da gida kaji ba dadi,Siyama

kuka ta Fara Yi tun da wuri kawaye suna tsokanarta ta dauki pad dinta ta Shige toilet tana
hawaye a cikin toilet din ta fashe taci kukanta ta koshi duk ta bata kwalliyar tata sai fuskar ta
wanke gaba daya ta fito idonta yayi alamar Kuka,Aunty tana Sallamar baki ta kalli Siyama Suka
hada Ido tace ke Kuma meye na kukan duk rashin kunyar tana ina? Yan Uwa Suka saki guda
da shewa Siyama sai sabon kuka ya taho,dangi Suka Yi caaa a kanta da tsokana sabo da kowa
ya Santa da baki amma yau Kamar ba Siyama ba,kawaye suna Mata tsiya Kawai ta kwanta a
katifa ta juya musu baya tun tana hawaye har bacci ya kwasheta kowa yazo Ina Amarya sai aga
tana shakar uban bacci tun 12 har kusan 3pm bacci takeyi,ana ta posting pics din ango da na
Amarya a online Wanda suka Zo bikin duk da cewar ma basu dauki hoton tare ba, ai Yan
layinsu suna fara zuwa bikin Suka tasheta da tsokana wata tazo ta Dana Mata duka a gadon
baya ke dalla tashi Amarya da bacci ki tashi kiyi wanka aka taru akan Siyama sabo da mutane
da yawa ana Wasa da ita ta ko Ina caccakarta akeyi,4pm Aunty tasa tayi wanka tare da canja
Kaya wani material ta sa me shegen kyau na lefe,suna bikinsu dai Kafin dare aka Kai Yan biki
gidan Amarya duk me son ganin gidan Amarya Aslam ya turo wasu bakin abokansa sun kaisu a
mota har Aunty taje taga gidan yarta komai yayi Mata itakam,Yan bikin ma suna ta yabawa da
yan uwa,na nesa sun tafi ma tuni sabo da Kawu dama ya fada musu ba taro shi yasa Basu
zauna ba,Aunty Kuwa dama ta fadawa mutanenta Kawu ne zai Kai Amarya da Kansa shi yasa
babu macen data zauna zuwa magriba kowa ya watse sai Yan uwan Aunty su Uku suna ta aikin
gyara gidan,Sabeer ne yazo ya kwashi kayan lefe duk wani abinda Siyama take so ya
tafi,Aslam ce Masa yayi ya bar kayan a motarsa da ita zai dakko Amarya idan sunje gida ya cire
kayan gaba daya,Kamar Aslam bazai Zo daukan Siyama ba sai dare Aunty tace tayi wanka ta
shirya ya yo waya yace gashi nan,Siyama tace ban dade da yin wankan ba fa to ai na Amarya
ne idan Kika Yi yanzu ai kin huta Yi a can,Siyama haka ta fesa wanka tazo ta Gama shafe
shafenta ta saka wani Leshi da Kawu ya dinka Mata na biki me shegen kyau sea blue and black
mayafinta me shegen kyau Kalar kayan da takalmi da jaka komai same color tayi kwalliyarta me
kyau ta shafa turaruka tana shiri Kawu da Aunty Suka shigo Suka zauna a dakin Suka Fara
Mata nasiha iri iri tana ji ta fashe da kuka suna Yi tana kuka kanta a kasa har Aslam yazo tana
kuka,Aunty itama harda hawaye ta fada bedroom dinta ta kwanta tana ta kuka Aunty zata rabu
da yarta,Kawu shi ya tasa keyar Siyama tana kuka kanta a kasa ta rufe kanta da mayafi tana
kuka ya kaita har mota inda Aslam ke mazaunin driver sanye cikin wata shaddar Yar ubansu
ruwan kwai,Shiga tayi gefe ta zauna Kawu ya rufe dama ya yiwa Aslam tasa Nasihar
tuni,Siyama ta sauke glass din motar tana shesheka tace Kawu..... Kawu yace a'a Siyama
karyar rashin kunya ta Kare ki daina nemana gaki ga Aslam aje ayi ta samun ciki idan Kinga
dama ki Haihu sau goma a shekara Allah yasa Albarka,Aslam Murmushi yayi Kawu ya yiwa
Aslam godiya yace su tafi Aslam yaja mota Suka tafi Siyama na kuka.

Affan dawowa yayi gida daga wajen daurin Aure Raudat ta tsaya a jikin window tace Ina kaje
ne haka? Yace yau ki tayani jaje an min gora,Nasha Sanda da Kaye an min mugun Kaye
budurwa ta aka daurawa aure Bata so na wani take so,Raudat taji wani farin ciki tace amma ya
Naga baka damu ba? Juyowa yayi Yana kallonta yace sabo da ke nake so,Raudat baki ta bude
yace yes ke nake so fa na fada Miki kince sai kin duba shike nan ai rayuwa ce harda yin Kalar
tausayi,Raudat tayi dariya tace ai zan baka amsa ne nan gaba,Affan ya girgiza Kai a ransa yace
zanyi maganinki.

Washe gari da Yamma wata budurwa ce Yar kwalisa Fara ta dau wanka ta sa key ta bude
part din Affan kawai ta Shige a gaban Raudat dake Compound,Raudat ta bita da kallo yarinya
Shuru Shuru bata fito ba har Raudat ta gaji ta shigo ranta a bace tace ke wai wa kike jira?
Yarinyar tana yanga tace Affan, Raudat tace a Ina Kika samu key dinsa? tace shi yaje gidanmu
ya bani yace na jira shi, Fitowa Raudat tayi cike da kishi hankalinta a tashe ta zaune a
compound Affan ya dawo da sauri ya fito ya shiga part dinsa Kuma ya rufo kofa,Shuru Shuru ta
ga bai fito ba shigowa tayi ciki ta same shi a zaune shi kadai bakuwar Kuma tana kitchen tana
girki kamshi na tashi,Raudat zuciyarta ta jagule ta rasa inda zata sa kanta a duniya taji san yi
fita tayi cikin fushi ta koma bedroom dinta ta kwanta a saman bed dinta ta Fara hawaye kafin
kace me ta fara ciwon kai ko Hussain bata taba sonsa haka ba bare ma tayi wani ciwon Kai a
kansa amma Affan bayan ciwon Kai harda zazzabi ya lullubeta,Affan Kuwa Yana ganin Raudah
ranta ya baci ya mike ya shiga kitchen yace Safara'u zo ki tafi gida kin gama aikinki, Safara'u ta
fito tace Yaya Affan ka manta sakon da zaka bani na bawa Mallam,Yace af na manta ya mike
da sauri ya dakko Mata kudi yace gashi kice ragowar kudin gidan Mai ne da nace Zan kawo
tace to tare da ficewa,tana tafiya dan Masifa kunnen Raudat taji Sanda tayiwa Affan Sallama
tashi Raudat tayi tare da saka hijab sai palon Affan.

Kishi ya gama cika Mata zuciya ta banko kofar ya mike zai shiga bedroom tace waccen
wacece? Yace wa? Who is she? ta furta da fada tana rawar sanyi yace baki da lafiya ne? Ban
sani ba mayaudari kace min Ni kake so kana zuwa ka kawo wata macen mene baka fada min
ba,Affan yace Yar Liman ce fa uban gida na a'a Yar gidan sarkin musulmi ce karewar limanci si
ba muharramarka bace da zaku kebe dan ubanta tazo tace zata maka girki Kawai kace sonta
kake yi Kuma bana sonka bana bukatarka gaba daya ta juya ta fice Kamar zata tashi sama.
Affan yaji Dadi yace yawwa kin Kama kanki ya zauna Yana murna sosai tana sonsa,washe
gari ogan Raudat yazo zai dauketa zasu tafi aiki,taji sauki ta fito cikin shirinta da simple
doguwar Riga marar nayi ta fito da takardunta,Affan yau hutawa yake a gida yaga Raudat an
dauketa a dalleliyar mota ya zaci saurayi ne ya kule sosai Kamar zaiyi duka.
Yamma nayi ta dawo Affan ya tareta a Hanya waye wancan? wa? Wanda ya daukeki a
mota,abokin aikina nane ai gwara ni ba namiji na kawo dakina ba,Tambayarta yayi a nutse
Raudat mu daina irin wannan kina so na ko bakya so na? Tsayawa tayi tana tunani Kawai ya
juya ya Fara tafiya abinsa tace wait bai tsaya ba ta bishi da sauri tace Ina sonka kayi
hakuri,tsayawa yayi cak Yana murna,gabansa ta dawo ta tsaya tace Ina sonka wlh kayi
hakuri,sabo da murna ma kasa magana yayi,takardunta ya karba yace mu je na Zama mijjn Kan
tace suna tafiya abinsu Suna hira abinsu amma kishin masifa ne da Raudat duk da haka tana
zargin Affan ko suna shiri da Safara'u.

Aslam kuwa tsohuwar unguwarsu yaje unguwar masu kudi ita Siyama tana ta faman kuka a
lullubeta cikin Mayafi har age gida bata sani ba sai da yace fito ta dago da kanta Mamaki ya
kamata tace me za muyi a wannan gidan ta kalli gidansa ne katafaren gida na da Wanda ta
sani Sanda Yana me kudi,Kuma duka ga motocinsa nan har da wasu sababbi ma,masu aikin
gidan tsofaffi Wanda ya sallama ta gani ya dawo dasu kenan,ga inda an Kara gyara shi ya
koma wani irin mugun hadadden gida har ya da a baya tsaruwa,baki ta bude yace Baby fito

Yana Murmushi ya jawo hannunta ta fito tace ba dai duk talaucin da kace ba karya ne? yace ki
saurareni Baby kiji ba abinda ya faru da dukiyata tun daga lokacin da nace Nusaiba ta ebi kudi
a cikin kudina ta bawa Mamanta ta kwashe kudin duka na Fara zargin sabo da kudina ta aureni
badan Allah ba shine nayi Mata haka Kuma ko Mum da Sabeer ban fada musu komai ba
tunaninsu da gaske na talauce,Siyama ta Fara mamaki tace yanzu kana nufin duk banki da
kace sun kwace komai karya ne? Yace ae,Fuska ta bata tace amma ka dauki hakkinmu hawaye
ya zubo mata tace me yasa kayi Mana haka, rudewa yayi ganin ranta a bace,tace ta ya za ayi
ace dama Kawai fada kayi ka shirya zance Muka dinga Shan wahala a kanka muna Jin
tausayinka hawaye ya zubo Mata,yace please Baby kiyi Hakuri ke kin San dalilin da yasa nayi
haka sabo da na San me so na tsakani da Allah kuma gashi na sani ya karasa Kamar zaiyi
kuka kiyi hakuri muje ciki ta shiga yasa me aikin ta shigar Mata da kayanta kaf bedroom din
Amarya,ya zauna Yana aikin lallabata ya Sha fama kafin ta hakura ta sakko hannunta ya rike
kin zauna a Palo Baby muje sama Suka haura sama jikinta a sanyaye tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0