Showing 60001 words to 63000 words out of 86820 words

Chapter 21 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

772

kyar take tafiya tana
kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu
ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi.

Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din
Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai
Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking
yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera
tana kallon hadadden Office din tace Sannu da aiki yace yawwa suna haka sai ga wata arniya
ta shigo da wasu takardu sanye da gown ko gwiwa bata Kai ba komin surarta a waje ta Sha
kitson attach tayi kyau gata da hips,Raudah baki ta bude tana kallo shi bai kula bama Signing
ya Mata tare da Mika Mata ta karba ta dauki Hanya zata fita tabi ta gefen Raudah,da yatsa
Raudah ta dan taba Duwawun matar, Affan yace mene Haka beb? Tace wannan wace? Yace
Secretariat ta ce,tace kana nufin kullum sai kaga wannan? Yace mene ne Wai? Baza ka kawo
Namiji ba sai mace to duwawunta kake kallo ko me,kalli fa duwawunta kullum da safe sai ka
ganta Ina can na saki baki hai a bude Saurayina yana nan yana kallon duwawun Chinaza,wlh
Affan idan ka kalli duwawunta bazan yafe ba,Affan yace Wai in tambayeki baki yarda dani
ba,haba Raudah kishin nan naki yayi sau nawa zan fada Miki ke kadai nake da ita,bazan iya cin
amanarki ba,I will never ever cheat on you Karki bari muyi auren zargi so kike kishi ya halakar
dake,Ni wlh Kawai ka canja sakatariya zuwa sakatare Namiji gaskiya ban yarda ba,yace ba
laifin data min baki Isa kisa na sallameta ba Kuma bani na kawota ba Liman ne ai kin san
gidansa tunda munje tare kin gaishe shi je ki fada Masa ya canja ta Indai kin San haka zaki to
karki sake zuwa Office Dina ya mike tare da dukan table sai data tsorata yace tashi ki tafi gida
bana son zargi bana taba ko hannun mace akan kishin banza kizo ki sani gaba ki hanani
sakewa ba ke kadai kike da saurayi ba sannan idan niyyar cutarki nayi ta ya Zan Bari ki gane,
tashi ki tafi bazan cuceki ba Ina sonki babu wacce nake so sai ke bana ko budurwa bare neman
Mata bana son zargi,Raudah mikewa tayi ta Fara hawaye yace oh my God me na miki? tace ni
dai karka kalli duwawunta,yace to naji bazan kalla ba idona ma Zan rufe muje na rakaki mota a
haka ya lallaba Raudah ta koma gida.

Tunda ta koma gida part din Landlady ta shiga suna Hira tace karki yarda da Maza Yar uwa
maciya amana ne duk yanda kike da kyau sai sun kula Mata,ki kula da Affan sosai yanda yake
da kyau Mata bibiyarsa suke kisa Ido akansa idan ba Haka ba wata ta kwace Miki shi,Landlady
ta dinga zuga Raudah,Raudah har da bata labarin sakatariya,tace to ki shiga ki fita a sallameta
a canja masa Namiji ko mace me addini, Raudah ta Fara tunanin ya zata yi ai da yamma ta
shirya sai gidan Liman
Bayan taje sun gaisa da Liman tace Liman wata barna na hango a matsayinka na Malami bai
kamata ace an hada mace da namiji suna kebewa ba da sunan aiki Wai sakatariya me yasa
baza a Kai Namiji ba duk sakatariya sai ace dole sai mace,Liman ya kalleta yace ai an fi son
mace sabo da ita zata iya Zama ko hour nawa ne sabanin Namiji sannan yare sunfi Hausawa

kwazo a wajen aiki,amma tunda Naga Kamar kina da manufa kema bari Zan samu mace me
addini me saka hijab kullum me zikiri a Kai Masa ita,Raudah taji sanyi a ranta ta zube kasa tana
ta godiya.

Washe gari Liman ya canjawa Chinaza Wurin aiki ya kaita wajen Daya manager din nasa
Affan kuma sai gani yayi an turo mace wata baka amma tana da kyau ba laifi hijab dinta har
kasa,ga safa hannu da kafa,suna gaisawa ta saka Nikaf dinta tana magana tana Jan carbi,
Affan Yana kallonta tana motsa baki tana cewa Lailahaillah Lailahaillah tana ta fama. Bayan kwana Daya Suka Fara aiki kullum tana aikin Jan carbi idan ta kama ma a Office dinta
mikewa take tsaye ta Fara dukan kirji tana zikiri Kamar zaka kashe kanta,Affan har ya gaji da
halinta ta cika musu kunne da dukan kirki tana Abu daya tana faman cewa Sayyadina
muhammadu ka kula dani Allah...Allah...Allah tana dukan kirji, ta manta ma Affan aikenta yayi ta
dakko Masa file sai da ya gaji ya taho da Kansa ya isketa tana ta dukan kirjinta tsawa ya buga
Mata tana Adduar bata daina ba tace Sir Allah ya maka gida me kallon bangon gabas,Allah ya
baka mace me zikiri....tsawa ya Mata shut up Ina file din da nace ki dakko? tace Sayyadina
manzo na shi zai agaza min na ganshi, Assalamualaika ya rasulillah.... Affan yana masifa yace
ke lokacin Addua daban lokacin aiki daban,Rabbana.....Rabbana...taci gaba,Affan ya zaro Ido
yace ke tafi gidanku na koreki you are fired,zata roke shi ya daka Mata wata uwar tsawa wacce
tasa ta fice da gudu,nan take ya Kira Liman ya sanar Masa komai Liman ya canja masa wata
macen arniya ce amma Kamar musulma haka take shigarta bata dame jikinta Kuma nutsasiya
ce sai dai ita Kuma akwai bin maza Kamar karya haka take in Banda son maza babu abinda ta
sani, Raudah tana bala'in sawa Affan Ido akan Shige da ficensa

Yau Saturday tana gida amma shi har Saturday Yana zuwa aiki,ya bawa Raudah key din part
dinsa zata gyara Masa,tana cikin palon Affan ta gama gyara dakin tana kwance a kujera sai taji
knocking tana budewa taga wani Matashin yaro da wata jaka me kyau yace gashi Wai a bawa
me gidan inji Farha, Raudah ta karba ta rufe kofar, budewa tayi taga wata flower ta soyayya
tana zuba kamshi ga wani agogo na musamman me tsada,ga wani turare kala biyu,bakin ciki ya
cikawa Raudah zuciya ta dauki turarukan ta fice can baya tasa dutse ta ragargaje su,ta dawo ta
dauki agogon ma ta fita tasa dutse tare da farfasa shi,ta dawo ta jefar da ledar da kafa ta dinga
tattake su sai ga Affan ya dawo ya sameta a haka Yana Tambayarta Lafiya? tace Affan wace ta
kawo maka gift Affan so kake hawan jini ya kashe ni,taya zaka dinga kula wasu gashi har gift
ake kawo maka, Knocking aka musu tare da turo kofar aka shigo Wanda ya kawo gift dinne ya
dawo yace dama wannan sakon na dawo karba ashe ba nan tace na kawo ba gaban gidan nan
ta aikeni wajen saurayinta nayi mistake,Surrender Raudah tayi kunya ta kamata ta kasa ko
motsi har yaron yaga sauran ledar sa flower watse a kasa,Kawai juyawa yayi tare da ficewa,
Affan ransa ya baci shima kasa Mata magana yayi ya juya ya fice abinsa ya shiga mota ya bar
gidan ya bar Raudah tayi mutuwar zaune tana hawayen bakin cikin halinta na kishi da dana
sani,tana so ta daina kishin ta kasa,ga Affan yayi fushi tace Ina Zan sa kaina ta dafe Kai tana
hawaye ta jawo Wayarta ta Fara kiransa yaki dagawa,bugun duniya yaki daga Wayar tata tana
zaune a part dinsa har 11am bai dawo gida ba gashi idan ta Kira sai ya kashe wayar ma gaba
daya, a ranta tayi alkwarin ta daina wannan kishin nata,ga Affan yaki dawowa.

AsmaBaffa[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢� AUREN MU🛢�


76-80



Official

By
AsmaBaffa







Page naki ne

AUTARESS









Kofar gidan da Mum take yayi parking sai gasu ita da Hajiya Zainab sun dawo daga
unguwa,Aslam Suka gani ya fito daga cikin hadaddiyar motar ya dakko Leda da flask,Mum tace
daga Ina haka? ciki Suka shiga gaba Daya Yana cewa daga gida Mana,sai da Suka zauna a
Palo ya gaishe su,ya ajiyewa Mum flask din da ledar a gabanta tare da cewa gashi inji
Siyama,Mum tace me Muka samu Kuma ta bude flask din taga farfesun kaji ledar ta Bude ta

washe baki tace an gode Mata Allah ya Mata albarka,yanzu nasan Ina da suruka,Aslam yayi
murmushi ganin Mum ta Kira Zainab ta kawo plate ta ebi nata ta bawa Zainab nasu,Mum ta
Fara yagar kaza tana cewa wannan yarinya Allah ya mata Albarka,Zainab ma tana ci tace haka
ake son suruka wasu Kuwa Kai da kayan danka ya gagareka,Aslam yace ni baza ku sa min
albarka? Mum tace Kai Dan Allah rufe mana baki muna Jin dadin mu wannan motar ma ta waye
ne nasan baka aro kayan wasu,Aslam yace tawa ce Mana ya Fara bawa su Mum labarin komai
har ya gama,Mum tana tsotse Kashi tace amma ka wahalar damu har hawan jini sai da
yakamani,kiyi Hakuri Mum kin San dalilin da yasa nayi haka yanzu,ae hakan ma kayi dai dai
gashi Yanzu mun samu Yar arziki irin albarka,amma cuta sai da ta kamani,Ki zabi kasar da kike
so Mum na kaiki ki huta,tace ba yanzu ba aure zanyi na tafi da mijina,Dariya ta bawa Aslam
yace kina son aure Mum?wa yaki ibada da ace Ina da mijina ai bazan dinga yawo kasa kasa ba
da sauran kuriciyata fa,Aslam yace Mum na Miki miji, Waye? Ki auri Shehu Baban
Nusaiba,Mum tace Kai nifa bana son kazami Indai tsoho ba me tsafta bane karka kawo min shi
bare wannan Yarinyar tasa marar kunya bada ni ba,dariya Suka yi,Baffa Shehu ai Dan gayu ne
kin girme shi fa sosai sai dai yayi manage dake cewar Aslam,Mum tace tashi ka tafi ka San inda
dare yayi maka tunda magana zaka fada min,Yace Flask dinmu fa? Hajiya Zainab tace ai ba
bata zaiyi ba in ka dawo sai a baka,yace idan tana son amfani da abinta fa matar gidan,Mum
tayi dariya tace duk cikin zumudin Amarya ne rabu da shi Aslam kuwa kitchen ya shiga da
Kansa ya dakko wani flask din da Kansa ya juye ragowar a ciki ya dauke flask dinsu ya rufe ya
musu sallama ya tafi

Wajen Sabeer yaje shima Sabeer tunda yaji ya dinga masifa yace ka wahalar damu wallahi
sai ka biyani dubu dari biyar dina dana taimakeka da ita ai ka fini karfi,Aslam Yana dariya yace
dama badan Allah ka bani ba,yace na fasa taimakon ka dawo min da abata nima na kusa
aure,yace Zan maka transfer din tsiyarka yace da yafi maka Suka Yi dariya tare da tafawa,a
ranar Aslam duk Wanda yasan ya talauce sai da yaje ya tabbatar Masa ba Haka bane,karshe
gidan su Siyama yaje,Kawu da yaji yace banyi mamaki ba tunda dama Sam lokacin baka Yi
kala da Wanda ke cikin wani Hali ba,Aunty tace uhm lallai Aslam kayi kokari da kayi
haka,Siyama tace a gaishe ku,Aunty tace ai munyi waya dazu dazu ta kirani,Kawu kam cewa
yayi fatan yanzu ta kusa haihuwa? Murmushi Aslam yayi cike da kunya bai ce komai ba, Kawu
yace ei kaji kunya Mana yanzu ai da a baya baka ji ba so ya rufe maka ido,Aunty tace Kai Kuma
ga mita tunda an riga anyi ai sai ka hakura, Aslam ya zaro kudade ya ajiyewa Aunty, Kawu ya
raka shi Yana cewa wallahi idan baka kula da 'yata ba sai ka gane kurenka,Indai tayi wata uku
banga tayi kiba ba zaka fadawa mutan garinku,Aslam Yana dariya a ransa yace Zama tayi
Inshaallah,Yana Fitowa har zai je waje Shehu sai ya fasa yace sai nan gaba tukun ba yanzu ba
ya koma gida abinsa.

Aslam Yana komawa gida suna hutawa a Palo Siyama tana jikinsa a kwance me aiki ta shigo
tace yayi bako,Yace Siyama ta koma sama baza a kallar Masa Mata ba,mikewa tayi ta haura
sama,sannan yace a shigo da bakon Jin ance ma'aikacinsa ne,Yana shigowa sai yaga Sufyan
ne ya shigo a firgice ya tsuguna a gaban Aslam yace dan Allah Sir kayi hakuri ka yafe
min,Aslam yace tashi tashi ba matsala ai ba laifinka bane Sufyan na fahimci komai Kai ai baka
da laifi,Sufyan Yana zufa yace ban San matarka bace ka yafe min,Aslam yace please get up ba

damuwa aikinka Yana nan,Sufyan yace ba wannan ba Sir cikin Ina Ina yace ...Ni...Ni...nine na
zuga Nusaiba akan sai ka saketa na aureta,tun tana gidanka nake zuwa Muna fita yawo,ni nake
kaita restaurant munyi soyayya tana da aurenka,a nan ran Aslam yayi mugun baci ya tuna
Sanda ko girki baza tayi ba sai dai ta shirya ta fice ashe tare suke fita,yace dama tare kuke fita
Kaine kake Neman matar aure me yasa mutane wasu baku da Imani ne,Sufyan yace na tuba
dan Allah karka koreni Sir,yace oh yanzu da badan ni bane da shike nan kaci banza ka cuci
mutum,ka daina batawa kanka lokaci da nayi Niyyar kyaleka ashe Kai azzalumi ne ba mutumin
kirki bane me bin matan wasu na sallameka daga aiki,Sufyan hawaye ya zubo Masa Yana
rokonsa yace tashi ka bar min gida cikin tsawa ba shiri ya tashi ya fice,ran Aslam yayi mugun
baci sai da Siyama ta fito ta zauna a gefensa tace lafiya yace Wai ashe Wanda ya auri Nusaiba
tun tana da aurena yake bibiyar min Mata Yana fita da ita,Siyama nan take kishi ya motsa tace
to sai me tunda Kun rabu shi ka kore shi mene na wani cewa Yana bibiyar maka Mata,au dama
matarka ce shine harda tashin hankalinka haka da damuwa akan wata banzar Nusaiba,okay na
gano son abarka kakeyi sai ya saketa ka dawo da ita,Aslam yace Allah ya baki hakuri ni ba
haka nake nufi ba nufina a lokacin ai tana matata ba Wai yanzu ba,Juyawa tayi tace ba
komai,fisgota yayi ta fado jikinsa yace ban yarda ba ai Indai kaji bahaushe anyi Masa laifi yace
ba komai to wlh da komai dawo nan, dariya ya bata amma ta maze tace ka sakeni nace ba
damuwa,yace akwai fa ayita ta Kare a nan baki Isa ba,baki ta turo yayi kissing dinta tare da
furta to kiyi hakuri bazan sake ba Ni dai magana ta wuce ya mutu,tace amma kasan.....kafin ta
karasa yace dan Allah da annabi kiyi shuru Allah ya baki hakuri ni dai Indai akan wannan
ne,Siyama tayi Shuru tana zaune a cinyarsa,yace to ki min magana Mana kiyi murmushi,tace
cewa fa kayi dan Allah nayi shuru to nayi shuru,Aslam yace kai Ina Shan wahala dake ai dai
nace kiyi hakuri, tace na hakura karka sake min zancen Nusaiba wallahi idan ba Haka ba zaka
ga danyen kai,dariya yayi yace to naji bazan sake ba yanzu ma kuskure ne ke kika fassara ni
daban,cike da shagwaba tace mutum Kawai ka kawo zancen wata ballagazar banza bazara
iskar damuna,Boobs dinta ya cafka ya shiga sarrafata ba shiri tayi shuru duk da cewa ba wani
abu zaiyi ba face rage zafi sai ta warke tukun.

Washe gari Sufyan Ya sake zuwa gidan Aslam bai same shi ba ya fita yayi murna dama
Siyama yake so ya gani Yana compound me aiki tace Wai tazo inji Mijin Nusaiba,Siyama Hijab
ta saka ta fito bayan sun gaisa rokarta ya dinga Yi dan Allah madam kisa baki me gidanki ya
maidani bakin aikina,Siyama tace kasan kayi kuskure Babba kaima Wanda gaskiya ko ni bazan
iya Masa magana ba a kanka kayi hakuri tunda yace a'a to fa sai hakuri kayi hakuri Allah ya
baka wani aikin,Yace dan Allah Siyama ki taimaka min,Siyama tace Ina ma Zan iya taimakonka
da nayi amma bazan iya ba kayi hakuri Kawai ta juya ta tafi abinta haka Sufyan ya fita jiki ba
kwari,washe gari Aslam ya Kira Sufyan ya bashi takardarsa ta sallama daga aiki Yana ta
rokonsa amma Ina baya Jin Kira.
Sufyan Yana komawa gida ya iske Nusaiba ta dawo daga gidan iyayenta Wanda ko
tambayarsa bata Yi ba,takardar ya wulla Mata ransa a bace yace Kinga abinda Kika jawo min
ko,kin gani ko Yar iska dabba wacce bata San me take ba jahila,Yar talla, kin Sa na bakantawa
Iyayena kin jawo an koreni daga aiki Allah ya Isa tsakanina dake kuma ki koma inda Kika fito
gidan ubanki na sake ki saki daya,Nusaiba tace ka sakeni ? Yace ae zata Masa rashin kunya ya
hau jibgarta ya Mata jina jina sannan yace wallahi ko hankici baza ki dauka a gidan nan ba baki

zo da uwar komai ba duk ni na siya Miki sabo da Haka ki koma gidan ubanki haka,Nusaiba tana
kuka jiki duk kulun duka tafi karfin ta taba komai Dan kuwa shi ya siya mata,Haka ta mike tana
dingishi zata tafi,Hannunta Sufyan ya fisga ta Fadi a kasa ya dinga janta tana ihu Kamar wani
buhun gishiri haka ya bude gate ya jefata waje ya kulle gidansa ya barta a nan tana ta uban
kuka har ta gaji ta mike da kyar ta shiga Napep sai gida,tana shiga da kyar take tafiya tana
kuka,Mama tana salati ta tafi kanta Shehu Kuwa ficewarsa ma yayi kala bai ce musu
ba,Nusaiba ranar ta Sha gashin jiki da ruwan zafi.

Raudah da Affan suna ta shirye shiryen bikinsu abubuwa na matsowa,yau Raudah Office din
Affan ta ziyarta ba tare da ta fada Masa ba 11am ta tafi da basket na abincinta ta fake da Kai
Masa abinci amma a zahiri so take taga ko Mata na zuwa Office din,Yana Office tayi knocking
yace yes ta Bude kofa ta shigo yayi mamaki yace yau a gari Yana murna,Zama tayi a kujera
tana kallon hadadden

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0