Showing 81001 words to 84000 words out of 86820 words

Chapter 28 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

779

dole ya
bita ba shiri,abinci ta kawo Masa yaci ya koshi sannan Suka fara shagali.

Raudah yau ta koma aikinta ta riga Affan dawowa gidan ta gyara a gurguje tayi wanka ta
cakare sannan tana girkinta tasan gaf yake da dawowa, Landlady ta dakko Shehu a
dankareriyar motarta Suka zo gidan Rauda Shehu an faso gari an auri me kudi motocin
Landlady ma har ya koya shi Kansa driving yake ya fita inda yaga dama da motar, Mama Kuwa
sati biyu kenan Shehu ko dakinta bai kalla ba tunda ta dawo,abin Yana Mata ciwo tana gidan
amma bai taba lekota ba sai da ta shafe sati biyu,tana dai ta Shan gyaran jikinta,gashi ta dawo
birni tayi kiba tayi haske ta murje,sai gayu take yi.
Har landlady tazo da mijinta Suka Sha hira Affan bai dawo ba gashi wayarsa bata
shiga,hankalin Raudah ya tashi,bayan sunyi Sallar magriba Suka tafi ba tare da Affan ya dawo

ba,Rauda tayi Sallar Isha ta zuba tagumi taji karar motarsa,da sauri ta mike ta fito taga shine ya
fito ras da shi, dama yasan shi take jira hankalinta sai ya tashi,kankame shi tayi tana murna
tace Allah na gode maka daka dawo min da mijina gida lafiya,Murmushi yayi yace kiyi hakuri
aikine ban gama ba munyi baki gashi wayata haka kawai naga ta dauke ta mutu duf,tace okay
shi yasa naji shuru ya rike hannunta Suka Shiga ciki,wanka ya shiga ta bude toilet din ta Shiga
ta dakko ribbon dinta zata fito yace zo nan My Sugar, tana zuwa ya jawota ciki ya cire Mata
Kaya Suka yi wankan tare,Towel din ya daura ya jawota ya bude ya sata itama a cikin towel din
nasa guda daya tal Suka daura su biyu sai rike towel din yayi bazai dauru ba tana manne a
jikinsa suka fito suna tafiya Kamar masu ciwon kafafu suna dariya bayan sun shirya tace yau
Ina da wani labari me dadi amma muje Dining Suka fito yaga abinci na musamman kala kala an
Masa yace na mene haka tace nasan baza ka iya guessing ba,wata takarda ta Mika masa tana
Murmushi tace read,karantawa yayi bakinsa yaki rufewa ya wani saki dariya ta farin ciki ya duka
a wajen yayi sujjudulshukur ya mike yace My Sugar You are pregnant for 3mnths oh my God
dana Yana cikin mahaifarki,tace kasan kwana biyu Ina zazzabi da tashin zuciya shine na biya
asibiti daga wajen aiki aka min test gashi Ina da ciki,ka kusa Zama Daddy rungumeta yayi yace
dole muyi celebration yau, kissing dinta ya shiga Yi kamar me sannan ya zauna a kujera itama
taja ta zauna ya sake rungumota jikinsa Yana cewa Zan iya Kuwa cin abincin nan yanzu murna
zata barni Kuwa,ai yau Zan fadawa Yaya Yusuf,Raudah tana ta kallon yanda yake murna itama
haka,tun daga ranar Affan kullum kafin ya fita sai ya Dora bakinsa a cikin ya kwararawa dansa
Addua sannan yace Baby Daddy zai fita a Mana addua idan ya dawo ma haka sai yayi Masa
addua yace Daddy ya dawo,Raudah Kuwa yanda take ji da cikin nan nata Kamar kwai.

Aisha ma da cikinta Farook murna ba a magana,haka Sabeer matarsa har ta samu ciki sai
amai take fama,Nabeela ma tana fama da nata.
Yau Shehu ya sanarwa Landlady zai raba musu kwana ya gamsu da shiryuwar matarsa ya
Kira Mama ya kira Landlady ya musu nasiha sosai da yaransa ma ya tarasu sun Sha nasiha
sannan yau ya Fara kwana a dakin Mama yaji ta zam zam Kamar ba ita ba to ta Sha
gyara,Kuma Mama haka suke gaisawa da Landlady ba gaba sai dai dan kishi na Mata Wanda
baza a rasa ba dole.









AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢�AUREN MU🛢�


99-100

Official

By
AsmaBaffa





Page naku ne

Hafsa Abdullahi
Fateema Farouk










Nusaiba tana zaune yau Mama ta aiketa kasuwa zata Yi Mata cefane ta shiga Napep sai
me Napep yace Zan Sha Mai Hajiya tace to,gidan man da Affan yake nan ya shiga,Yaron Affan
Salahu Wanda Suka Yi hatsari da Raudah akan machine dinsa Yana gidan man Affan ya sashi
aiki da machine dinsa a gefe yaga Nusaiba a Napep sai kallonta yake Yi sai ta Masa Kama da
matarsa data mutu da ciki wajen Nakuda,Kawai ganin tana Kama da matarsa yaji Yana
sonta,Yana ta faman kallonta Kamar maye,wajen Napep din ya karasa yace Yan Mata
sannu,Nusaiba rabon da wani Namiji ya kulata a duniya har ta manta sai yau,farin ciki ya
kamata amma ta danne tace yawwa,yace dan Allah ya sunanki? tace Nusaiba yaji sunan
matarsa data mutu mamaki ya kamashi yace ikon Allah dan Allah Dan yi dariya na gani,dariya
ya bawa Nusaiba ta murmusa yace har dariyar iri daya wlh sannu baiwar Allah wallahi birgeni
Kika yi haka Kawai naji Ina sonki Sunana Salahu,Nusaiba a ranta tace ji wani suna dan Allah
sai ace Nusaiban Salahu ko dadi,kallonsa tayi sama da kasa Salahu matashi ne Kamar su Affan
wankan tarwada ba laifi baida makusa kuma Yana gayunsa da tsafta Dan birni ne, a ranta tace
karfa kiwa kanki tace na gode a fili,Yace dan Allah Dan bani number dinki idan ba
damuwa,Nusaiba harda Jan aji sai da ya dinga rokonta sannan ta bashi da kyar tana
yanga,Salahu Kuwa haka yake son mace me yanga sai ta birge shi tuni ya Kara Jin sonta.

A hankali waya Suka Fara da Salahu kafin wani lokaci Salahu ya siye zuciyar Nusaiba yace
shi da gaske yake daga nan ya dage da zuwa zance da machine dinsa yace yafi son bazawara
yanzu sunfi hankali sunga rayuwa,Yana zuwa zance an kusa turo manya aka samu munafukan
layi Suka fadawa Salahu tsiyar da Nusaiba ta shuka aka sake ta,shi yasa ake so ka shuka
Alkhairi duk tsiyar me hassada bazai samu abin fada akanka ba,gashi Nusaiba ta kamu da
mugun son Salahu Kawai taga ya daina zuwa Kuma ya daina kiranta a waya idan ta kirashi sai
yace zai Kira bazai kirata ba,Addua taci gaba da Yi ba dare ba rana tayi ta kuka a boye ba tare
da wani ya sani ba,Soyayya ta sa Nusaiba kuka sai yanzu tasan mene so akan Salahu,sabo da
sauran Wanda ta aura kudi Kawai ta hango Basu samu damar zuba soyayya da ita ba sai
Salahu talaka me rufin asiri.

Tun Mama bata fahimci haka ba har ta gane bata tambaya ba ta rabu da ita,Shehu ne ya
Kama Nusaiba tana wanke wanke tana kuka bata San ya shigo ba,Kujera Fara ya ja ya zauna
ya dakko lemonsa na roba ya balle Yana kurba Yana kallon Nusaiba ya harde kafafu,Mama ce
ta fito tace yau me Zan gani Nusaiba me ya faru,Ka gani Abban Ameer, Shehu dariya ya dinga
Yi Yana kora lemo abin Yana Masa dadi yace sai kin tambaya akan mene yarki soyayya ta fada
talakan da kuke gudu a kansa take wannan an zuga shi ya daina zuciya dama bata San so
bane shi yasa da kudi ne a zuciyarta ba soyayya ba yanzu Kuma da damarta ta gudu ba me
kudi talakan ma Neman sa akeyi Ido rufe to an same shi da kyar Kuma ya subuce ga sonsa
take sosai,Mama taji tausayin yarta Jin Nusaiba ta sake rushewa da sabon kuka tace yarka ce
dai wallahi ba daidai bane,Shehu Yana kora lemo Yana tuntsira dariya Nusaiba da Mama an
shiga wani hali Yana kallonsu Mama tana lallashin yarta.
bangaren Salahu yana mugun son Nusaiba amma abinda aka fada Masa shi ya hanashi ci
gaba da nemanta amma zuciyarsa ta kasa hakura da ita.

Siyama cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe,washe gari Monday Aslam Yana da meeting
ya fita da sassafe ko bacci bata tashi ba nakuda ce ta tasheta, Jin ciwon na musamman ne
Kawai bata nemi Aslam ba sabo da tasan meeting ne da shi akan wani contract zai iya rasa wa
sai ta Kira Aunty,Aunty da sauri tazo tare da Yayarta Suka Kai Siyama asibiti,Kamar jira ake ana
basu daki Siyama ta haifo danta Kato Namiji kyakyawan gaske,Kuma ta haihu lafiya Kamar ba
ita ba, nan da nan aka Mata duk abinda ya kamata zuwa 2pm aka sallame su duk Aslam bai
San me akeyi ba,Aunty gidanta ta wuce da Siyama a can tayi Mata wanka da towel ta koya
Mata sannan tayi na sabulu da kanta,Aunty ce ta wanke jariri tsaf aka sa Masa sabon kaya
farare masu tsada da kyau aka sashi a showel fari Yana kamshi,Siyama ma shiryawa tayi cikin
doguwar rigar atamfa sabuwa a gidanta Aunty ta dakko mata ta shafa turaruka ta zauna taci
abinci ta koshi,Jariri sai cin hannunsa yake Yana Jin yunwa,tana gamawa Aunty tace a bashi
nono,Siyama ta dauki jaririnta tana washe baki ta tsura Masa Ido tace yanzu Aunty dana ne
wannan? Hararta Aunty tayi tace nono akace ki bashi,Siyama ta saka hijab Wai baza a gani
ba,Nusaiba ce ta shigo ganin yaro taga me jego an lulluba da hijab,tace malama ki fito da nono
ki ba yaro,Siyama tace Aunty na rasa bakin yaron fa,Ina Zaki ganshi kin lulluba,Da kyar ta samo
bakin yaron tace Bismillah dan yaro kayiwa ubanka kaka gida,Aunty ce ta maketa a kafada tace
ke dai anyi marar kunya wlh,Siyama tace Aunty ai gaskiya ne shike nan ubansa yau sunyi

handing Over,Nusaiba ta fisge hijab din data rufe kanta,Siyama ta Fara masifa wai mene haka
Zaki ga sirrina ta jawo ta sake rufawa kanta da jariri,Nusaiba tace ga yaron irin ubansa, Sai da
ta gama bashi nono ko koshi baiyi ba tace ya isheka haka karka yi katon ciki, ta mikawa
Nusaiba yaron tace gashi kalli danki Kamar zai ce min Mummy, Nusaiba ta karbi dansu tana
gani tace wannan yaron wayo zaiyi,Siyama tace bakya ganin idonsa Kar Kamar zai Kira
sunana,kalli girarsa cewar Siyama,Nusaiba tace irin ta ubansa ce ya fiki karfin jini,Aunty ce ta
tashi Jin rashin kunyar da suke yi

Siyama a hankali tace ba dole ba ya fini karfin jini ai ansha aiki ayi fama anyi
gumurzu,Nusaiba tace ai aikin maza kenan ni kaina yanzu da kyar nake bacci Sabo da ba
harka yo na Saba da wanga lamari,dariya sukayi sai tafawa suke suna iya shege wani abin
Aunty tana jinsu,Kawu ne ya shigo Suka Yi mukus,ya dauki jariri yace Siyama ashe asibiti aka
kaiki? tace wallahi Kuwa kawu na haihu,Kawu yace to rasa kunya ai na gani,Shuru
tayi,Makwafta da Yan uwa ana ta zuwa barka,Aslam ya Kira yaji ya matarsa tana dagawa yajita
da murna tace Ina gidanmu fa kazo sai ka daukeni mu koma gida,yace lafiya? Kuma shine baki
fada min ba ai na gama meeting dinma Ina hanyar gida tace gidanmu zaka taho bani da
lafiya,da sauri ya juya Kan motarsa sai gidan su Siyama Yana zuwa yaga Nusaiba ta fito daga
gidan ta Shige gidansu wasu matan suna ta shiga wasu na Fitowa harda Maman
Nusaiba,Fitowa yayi zai shiga gidan Yar uwar Aunty harda ce Masa an samu karuwa Allah ya
raya,Aslam yace ta haihu ne? Au baka sani ba ai tun safe Muka kaita asibiti tana nan lafiya
kalau da jariri,Aslam ai ko gama ji baiyi ba ya kutsa Kai cikin gidan,Yana shiga Yan barka duk
sun Gama sun fita Kawu ya shigar da shi tsohon dakin Siyama Wanda yanzu ya Sha kujeru da
tiles,Zama yayi sannan Aunty taje Suka gaisa,Siyama ta mike da yaronta har da pillow din da
take zama a kai,ta Shiga inda Aslam yake,Murmushi ya sakar Mata itama haka jaririn ya karba
Yana kallonta yace Kamar bake ba Anya ma kin Sha wahala Kuwa

Na ganki Kamar wannan ba daga cikinki ya fito ba,dariya tayi tace Allah ne ya amsa Adduar
da kake min kullum Allah ya sauki matarka lafiya to Allah ya amsa Nafeelar da kake yi akan
cikin nan Allah ya amsa, yace ah naga zahiri yace baki ji yanda hankali na yake kanki ba akan
haihuwar nan sai gashi ko waya sai dawowa nayi Naga jariri,Siyama tace ai kana fita daga gida
ko Office baka Kai ba na Fara ciwo Kai nakuda masifa ce na zaci wucewa zanyi har nace da
Aunty a Kira min kai,Aslam harda abin tausayi wai Allah sarki Sannu, kai haka ake nakudar
dama bazan sake haihuwa da wuri ba,Aslam yayi dariya yace baki Isa Yara nake so,Siyama
kamar zata Yi kuka Kamar yace yanzu zai Mata wani cikin tace dan Allah kayi hakuri kayi min
rai wallahi nasha wahala daurewa Kawai nayi amma mutuwa ce Kawai banyi ba harda
hawaye,Aslam ta bashi dariya yace to Mene na kukan Kuma kin manta da dadin da ake ji kafin
ayi cikin,dadin banza mene amfaninsa kaci Dadi ko kaci wahala,dariya ta Kama Aslam,yace
kece fa Watarana kike cewa ayi Miki, to yanzu na gane gaskiya bani ba wannan lamari, tace
kazanta haihuwa Ina haihuwa sai amai na dinga amai,haba ya ake cewa abarnan mabiya ta
taho da komatsai da tarkace tayo shara Suka shirkito kasa daga cikina na zaci kayan cikina ne
duka ai sai amai wayyo kazanta daga yau sai na tsinewa me girman Kai ya taho a cikin wannan
kazantar za ayiwa mutane iyayi,Aslam ya dinga dariyar labarin Siyama an Haihu harda cewa
daina fada min kazantar nan Kar na kasa cin abinci dake,tace dama ni yanzu na Isa na maka

girki kaci ai nayi kazanta da yawa bai ma dace ba wlh Me danyen jego da girki haba kana da
gaskiya karka kaci abincina Allah wannan kazanta haka.

Yaronsa yayiwa Addua a kunne sosai Yana ta kallonsa idonsa tar yace wannan idon naki ne
ba nawa bane,Siyama tace kalli da kyau idonka ne gashi nan a soye,Siyama ta Mika Hannaye
tace bani shi ya gaji uwarsa yake so,yace eh lallai shike nan daga na dauke shi ko minti Sha
biyar baiyi ba Wai na baki danki ya gaji a Ina Kika gane ya gaji,Siyama tace to shikenan rike shi
magana ta kare,Aslam wayarsa ya zaro ya Kira Mum ya fada Mata ya hadata da Siyama ta
Mata barka Mum ana ta murna anyi jika,Aunty ce ta roki arziki ya bar Siyama tayi sati biyu a
gida sai ta koma ba a sonsa ba da kyar dai ya yarda yaje ya kawo Mata kayanta na sawa da
Dan yawa sai na jariri da Suka siyo daga kasar waje komai dai ya kawo,ya jibge Mata kayan
shayi da su maltina,juice,ruwan roba,sai kullum Kuma Yana Hanya da su Fruits da nama da
sauransu.
Nusaiba kullum sai tazo ganin jariri safe da Yamma kamar danta,har zuwa take ta goya
shi,Yau ma tun rana tazo ta goya jariri tana gidan har Yamma,Siyama tace Nusaiba bari nayi
wanka sai na karbe shi ki huta,tace to Aunty tace wanka ma za ai masa shima Siyama ta shiga
wanka Aunty tayiwa jariri wanka ta shiryashi a kayansa wasu milk color yaron ya Kara
wayo,Nusaiba ta dauke shi tana zaune yana hannunta Aslam yayi sallama tare da
shigowa,Aunty ya gaisar Nusaiba ta gaida shi da kyar ma ya dan iya motsa bakinsa ya amsa
shima albarkacin Yaronsa ne da kullum take daukanshi iyaye da dansu,Yana dakin da aka bawa
Siyama kwance akan katifarta katuwa dakin ya Sha gyara Yana ta kamshi, shigowa tayi daure
da zani a kirji tayi wanka,ya kalleta jikinta duk ruwa zanin ma ya jike a jikinta ya manne Mata a
jiki surarta ta bayyana sosai,duk inda ta motsa sai ko Ina na jikinta ya motsa,Aslam yasan ba
samu zaiyi ba yace Wai ni idan an Haihu kyau akeyi ne? Kinga kyau fa Kika Kara kin ganki
Kuwa kullum nazo sai Naga kinfi jiya kyau har bana so na daina kallonki, Murmushi Siyama tayi
tana tsaye tana goge kunnenta da cotton,tace ae ance tana sawa har zuwa arba'in wasu haka
take sasu kyau in suka Haihu zuwa 40 days zaka ga mutum ya dawo dai dai,yace yanzu naji
zance kinje saloon din? tace ae mana naje jiya na kusa da gidan nan gashi nan an gyara gashin
sosai yace okay, yace karbo min dana daga hannun waccen sauri nake yi bacci nake so naje
gida nayi,tace to saurin mene Kuma kayi baccin a nan Mana

Murmushi yayi yace yan barka fa,Siyama tace Kai rabu dasu sai na koma palon Aunty,Yanzu
Zaki suna? ta mike tana cewa Kawu yace babu me zuwa ya bata Masa paint din gida,yace yayi
daidai ai, fita tayi ta karbo Jaririn a hannun Nusaiba,jaririn ta bata ta wuce gida abinta.

Ranar Suna yaro yaci suna Muhammad raguna manyan gaske uku ya yanka Mata,albarkacin
Landlady sai ga Raudah tazo barka da cikinta tsoho itama harda cewa Allah ya bamu ita ku
Nima aga nawa haka Siyama tace Allah yasa.
Satin Siyama uku a wajen Aunty,me aiki ce ke gyara gidan Aslam kafin ta koma ma sai da aka
Masa gyara na musamman,Aslam ya canja furniture na gidan,da Kansa ya dakko matarsa da
jaririnsa Muhammad,Allah yasa me aikin nasu babbar macece ita taci gaba da kula da Siyama
da jaririn nata tana daukan darasi,tun kafin arba'in jini ya dauke taki fadawa Aslam sai tayi
Sallah a boye,Aslam ya gaji yace ban yarda dake ba Baby har arba'in ta wuce ace har yanzu

bai dauke ba,Siyama tace bai dauke ba harda mazewa,yace wallahi sai na duba na gani da
kaina ya jawota tana tirjewa karka gani kazanta baza ka iya cin abinci ba babu kyan gani,suna
ta kokawa yayi dariya yace baki Isa ba sai na tabbatar ba komai,ya dauketa cak ya hau cire
Mata kaya yaganta ras ba komai yace au abin haka ne Baby? yaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0