Showing 45001 words to 48000 words out of 86820 words

Chapter 16 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

787

Mata hanci me dadi, tace Kai bafa kyau amma shedan
yasa tayi Shuru harda lumshe ida ta zagaye shi da hannayenta dagata yayi sama a haka,dariya
ta danyi ya ajiyeta a kasa sannan ya janye jikinsa tare da furta good night Yau ki kwana kina
mafarkina Kuma ki ganni na aureki Muna soyayya,dariya take kasa kasa tace hmmm ai da na
fika murna Zan hango mu a Palo ina zuba maka abinci,zanyi na ganmu a kitchen Muna
girki,Aslam yace ban iya girki ba fa ni,dole ka dinga tayani Kuwa Indai kana gida,ki dinga Jin
tausayina Baby,ai sabuwar hira Suka dasa ya manta ma Sabeer Yana jiransa a mota,yace
zanzo jibi da dare yanzu na gane yanda zamuna yiwa su Kawu tace to sai kazo dare yayi fa
12am ,yace Kuma Sabeer Yana jirana ba,fita yayi ta tsaya a bakin kofar tace sai jibin Zan jiraka
yace ko kiss Babu?

Tace sai a gidanka yace Allah yasa ta furta ameen Hannu ya Miko Mata ta kai zasu tafa ta
janye,dariya ta bashi ya tafi gari duk ba mutane,sai da ya kule sannan ta maida kofa a hankali

ta rufe ta dawo tana shigowa Kawu ya farka tare da hasketa da touchlight me mugun haske
kamar ta Kama barayi,yace daga Ina kike? tace kofa naje rufewa na zaci ba a rufe ba Kuma ma
Ina zanje babu mayafi,Kawu yace to wuce ki kwanta tace to Sum sum ta wuce dakinta ta kwaso
kayan shimfidarta ta shimfida a gefen Aunty ta kwanta cike da nishadi sai Murmushi takeyi ita
Daya.
Aslam kuwa Yana komawa Sabeer har yayi nisa a bacci cikin motar ya tashi Yana masifa a
Ina ka zauna haka? Na fada maka fa ka shirya jirana domin Zan iya dadewa tunda gidan Zan
shiga nan ya bashi labari a dakinta Suka buya,yace amma ka cika Dan Iska Aslam tab wannan
ai ganganci ne,Tsaki yaja yace ba abinda bazan Yi ba akan Star dita,zaka ga star ya yiwa mota
key Suka tafi gida a gidan su Sabeer ya kwana yau.

Siyama kuwa ta kwanta yau soyayya ta hanata bacci in Banda Aslam ba abinda take tunawa
a ranta Katsam taji Aunty tana kiranta kasa kasa kamar munafuka,Siyama tayi Shuru a zuwan
bacci takeyi,karaf a kunnen Siyama taji Kawu Yana magana kasa kasa tayi bacci? Aunty tace
ae yayi nisa ma baccin,Siyama harda Jan munsharin karya,Kawu yace tashi mu tafi Aunty ta
mike kamar barayi Suka Fara tafiya Sadaf Sadaf suka fada daki,Siyama tace iyye tana dariya a
boye tace an shiga Uku yanzu Kawu dama bai bar Harkar nan ba ya tsufa ai wannan sai
yara,can Kuma tace na tuna Aunty da kuruciyarta itama tana bukata,lallai Kawu dama haka
yake Dan is....bakinta ta rufe tace amma ni ya hanani sakewa da masoyina shi ya ja tasa sun
tafi duniyancinsu ba komai akwai Allah.
Washe gari da safe farkawa tayi taga Auty a shimfidarta kawu ma a tasa,Siyama tace wato
da aka gama sai aka dawo dama haka ake Mana wayo,yau zanga tsiya wlh kaima baza kaji
Dadi ba Allah ya kaimu dare cewar Siyama,Kawu yace ke sai Rana ta fito ne zakiyi Sallah? ta
mike taje da brush tayi tare da Alwala ta koma dakinta bayan tayi sallah taci gaba da baccinta
hankali kwance.

Wani Daren Yana zagayowa Siyama ta koma palon Aunty tace yau a nan Zan kwana Naga ta
tsiya,Siyama tayi baccinta Aunty ba yanda bata Yi da ita ba akan ta koma dakinta taki tashi Wai
ita a nan zata kwana,Aunty fita tayi inda suke kwanciya a tsakar gida ta guntsawa Kawu tace
nifa yau a matse nake da wuri nake so ga Siyama ta kwanta a palon tace ita a nan zata
kwana,Kawu yace rabu da ita bata ji ai,Aunty tace ni a daki Zan kwanta ma can cikin uwar
daki,Kawu yace jeki idan baccninta yayi nisa Zan shigo,ai Kuwa Siyama Taki bacci tayi alwala
ta saka hijab ta Fara Nafeela ai da tayi raka'a takwas sannan ta zauna saman Sallaya,ga dare
Yana yi gashi ko yaushe Kawu ya leka tana zaune a sallaya tana lazimi, window din bedroom
din Aunty Kato ne a bude yake dan tsaf mutum zai wuce Siyama tana can bata sani ba tuni
Kawu ya haura ta window dama matan aure da iya sanin makamar wayo Aunty tasa kawu ya
rufe Mata Baki Kam karma wani sauti ya fita suka gama abinsu ras Kawu ya sake haurawa ta
Window ya dawo saman katifarsa Siyama Bata San me akeyi ba tana Palo,Aunty ta gani ta fito
tace Siyama gwanar addini a dinga sawa da mu,yau zafin da akeyi yafi na jiya bari na sake
sheka ruwa a jikina,Siyama a ranta tace aha yau baza ku Shana ba sai dai ku kwana a haka,
Aunty kam Kawu ta zubawa ruwa yayi wanka tare da tsarkake jikinsa Aunty ma tayi Suka dawo
Suka kwanta aka bar Siyama bau a Palo har bacci ya kwasheta a nan.

Washe gari Kuwa gani Suka Yi Siyama tana ta kwalimar dakinta ta Masa wani uban gyara na
musamman ta kunna turaren wuta ta kulle ko Ina ya dauki kamshi, da Yamma tasan Kawu bazai
bari ta fita ba abinda take so ta yiwa Aslam duk bazai siyu ba dole Wayar Aunty ta dauka a boye
ta Kira kawar Aunty me yin snacks na gidan biki tana yi ma ana order,tace tayi Mata meet pie
me dadin gaske da Samosa sannan ta siyo lemo juice babba ta hado da shi ta bawa yarta ta
kawo mata,idan ta kawo sai ta bata kudin ta kawo Mata Suka Yi lissafi tace ana yin Sallar Isha
take so a kawo matar tace to ba damuwa
Siyama sai gaf da Sallar Isha ta fesa wanka ta saka doguwar rigarta ta larabawa wata maroon
taji ado kawar Aunty ce ta bata da taje aikin Hajji bara rigar tana Mata kyau shi yasa take Adana
ta,ta yafa mayafinta taje ta shafa humrar Aunty ta dan zubo wata a Yar karamar kwalaba,Aunty
tace ke Kuma Ina Zaki je? Siyama tace to bana fita an hanani fita Kawai sai na bar kayana su
rube bana sakawa,Kawu Yana jinsu ya tashi ya tafi Sallar Isha,Aunty ta shiga daki Sallah aka
kawowa Siyama order dinta ta karba a boye ta biya kudin Yarinyar Yar budurwa Siyama ta kalla
tace ungo kudin kice na gode sauri ki ta tafi bana so Aunty ta sani,Yarinyar ta tafi da
sauri,Siyama ta Kai ledar daki ta kwaso plate biyu ta zuba meet pie din da Samosa a plate ta
rufe ragowar ta boye a abinta ta ajiye lemo da cup kusa sannan ta fice,sai ga Aunty ta fito da
Hijab tace zanje gidan kawata Jamila yarta ta haihu sai 10pm Zan dawo ki kula da
gidan,Siyama tace to Kawu fa? Aunty tace baki ji yace yau gidan liman zai je ba abokin babanki
ya gayyace shi walima an Haifa Masa yaro ai Kawunki yau sai an ganshi, tana murna dake
gidan su Jamila ma ba nisa a layin ne tace Aunty a dawo lafiya tace yawwa ta fice,tana fita
Siyama ta fito tayi sauri ta karbi wayar me shago ta shigar da number Aslam ta Kira,bugu daya
ya daga ta matsa gefe tace ka taho kuwa? Yace gani a layin ma Sabeer ya saukeni zai dawo ya
daukeni,tace kace ya dawo tara da Rabi,yanda tace haka aka yi,tana waya sai ganin Aslam tayi
a kusa da ita Yana kallonta,me shagon ta mikawa wayarsa ta Masa godiya Suka jera Suka
tafi,Yana faman kallonta yace yau kin Sha kyau haka ni aka yiwa kwalliyar,Murmushi tayi tace
ae Suka Shige gidan har dakinta bata kulle kofa ba tasan ba kowa ta kawo Masa pie din da
lemo,yace harda tanadi tayi dariya Yana ci yace yayi Dadi kuwa suna ta zuba hirar soyayya
abinsu 9:30 Sabeer yazo suka tafi Siyama harda rakashi har cikin mota Suka gaisa da Sabeer
ta koma gida ta cinye Su samosarta da lemon tayi Shirin bacci tayi kwanciyarta har Aunty ta
dawo.
Haka lokacin na tafiya Aslam duk Sanda yaga damar zuwa sai sun faki idon Aunty da Kawu
suke samu su Shige su Sha Hira ya tafi basu taba Kama shi ba.

Siyama ta gaji da halin Kawu tace wlh yau Zan Bari ya kamamu,ai Kuwa Aslam yazo yana
dakinta dama da shi aka shirya plan din,bai taba kwanciya a katifar ba sai yau,Suka dinga
hirarsu Kamar ba matsala ko an gansu da karfi yanda kowa na gidan Yana ji har dariyarsu ana
ji,Kawu Yana tsakar gida daga shi sai dogon wando da Singlet,Aunty ta mike ta zauna tsoro taji
ma ko aljanune a dakin Siyama suke Hira maganarsu ta fito fili,Kawu yace Siyama ke
Siyama,Siyama Suka Yi kus Kamar ruwa ya dauke can tace naam ta fito har da nuna rashin
gaskiya,Kawu ya mike ta koma dakin da gudu zata turo kofa Kawu ya Danna da karfi Siyama
tana dannawa amma yafita karfi ya Bude ta karfi ya shiga ya Iske Aslam a kwance sanye cikin
shadda Yar ubansu,Kuma ko a jikinsa ko tsoro bai ji ba tunda Yana sani,Kawu ya Fara salati
harda rufe Ido ya fito gashi Yana Jin kunyar Aslam sosai bazai iya ci Masa mutunci ba,Aunty ma

ta leka ta dawo baya tana salati tace kaga abinda nake fada maka ko da alama ba yau Suka
Fara ba na dade Ina zargin Siyama dan Kuwa akwai Sanda takeyin kwalliya ta musamman da
dare to gashi ka gani da idonka har cikin dakinta,Siyama ta fito tana kukan karya Dan Allah
Kawu kayi hakuri dama Kaine ka hanashi zuwa shine nace ya dinga zuwa Muna buya Watarana
ma Sai 2am yake barin gidan nan laifinka ne Kawu,Aunty tace yanzu kaga duk abinda zai faru
ma ya faru,Aslam ne ya fito Kamar gidan Ubansa ko ajikinsa Yana takunsa,Siyama tace ai
Kaine Kawu.....Mari ya zubawa Siyama sabo da Takaici,Aslam ya riketa da sauri,ta juya Masa
Fuska tace tayani gani fuskata Kuwa tana nan,Aslam yace tana nan sosa min wajen,yasa
Hannu ya Sosa Mata,Kawu yace Aslam Ina ganin mutuncinka ka sani Allah Yana ganinka,yata
ce duk abinda ya sameta Kaine wlh,Aunty ta ja tsaki tace mene ma bai faru ba kana gani dai
wlh ka Amince ayi sauri ayi bikin nan tun kafin masifa ta danno Mana gida,Kawu ya tsorata
matuka tunda Aslam yake iya zuwa cikin gida har dakin budurwa su raba dare to komaima zai
faru,Kawu cikin bacin rai yace Dan ubanki kinwa kanki Babu ke ba kayan daki cokali bazan siya
Miki ba,Kai Kuma gobe gobe ka turo manya ka sani ficika bazan kashe ba Kuma babu taro
auren bazawara ma Sai yafi naku armashi in Banda Yan daurin aure kar naga uban kowa a
gidana,Kuma Babu me Kai maka Amarya ana daurawa kazo ka dauketa,Aslam yafi kowa
murna a ransa yace mun Zama turawa Haka ake so ai,Siyama tace Wlh Kawu ba abinda
mukayi Wanda ya sabawa Allah,Kawu yace ai tun daga Kebewa da kuka Yi daki Daya Kun
sabawa Allah kuci gaba da istingifari Kawai mutanen banza sakarkaru Kai ka girma Namiji ka
dinga biyewa mace,Aslam harda durkusawa yace dan Allah Kawu ku yafe Mana,Itama Siyama
ta durkusa baza mu sake ba,,Kawu yace kanku kuka yiwa bazan siya Miki komai ba ko tukunya
baza a Dora ba,Babu shagali ba gayyata,Aslam yace hakan ma yayi mun gode,karma ku gode
ku tashi ku bani waje,Suka juya Suka fice Siyama ta diinga murna,Aslam yace Ni dama ban
damu da wani taron Iska ba,Siyama tace shike nan ba anko ba gayyata ta furta da
tausayi,Aslam yace nan da sati za a daura kin Zama amarya yau bazan Yi bacci ba, Siyama
tace Ina waye ya bani bacci ai sai addua,Aslam yace yanzu an gama yakin karshe ki Fara bawa
kawu hakuri lokacin bashi hakuri yayi ai suka Yi dariya ya Mata sallama ya tafi.
Siyama ta shiga gidan harda durkusawa Kawu tace Mahaifina ka yafe min,sai yau Wai zata
mahaifinta ta bawa Aunty dariya, tace Kawuna ka yafe min na tuba bazan sake ba dan Allah
Kar kayi Fushi dani sai Allah ya tsine min na tuba,tashi ki bani waje Yar banza fitsararriya tunda
nace zan bashi ke Kuma mene na damuna,Siyama tace Kawu ka sa min Albarka to,duka ya Kai
Mata ta tashi da gudu tana dariya ta koma dakinta sai tsalle da murna harda cewa Babana dake
lahira yayanka Amadou Yana rike yarka Amana yanzu,su Kawu suna jinta tana ta hauka iri iri.

Raudat bayan taje gida ta huta suna ta hira da kannenta kanana su biyar da Mamansu,haka
Babansu ya dawo daga Office tana murna yace a'a Raudat zuwa haka ba sanarwa tace Papa
nayi missing naku shi yasa nazo ranar Monday Zan koma,yace Alright ya aikin naki? tace
Alhmdllh Papa na iskeku lafiya yace lafiya lau,ciki ya shiga ita Kuma taje tayi bacci ta huta da
Yamma lis tayi wanka ta fito cikin hadaddun kayanta English fited gown ta Sha me dogon
hannu,kyau Kam ta Sha shi tayi rolling da mayafinta,hand bag ta dakko ta fito tare da yiwa
Umminsu Sallama tace Zan dan zaga gari,Ummi tace to a dawo lafiya ta koma part din Papa
tace papa Zan Dan zaga gari bani mukullin farar motarka please yace duba kasan pillow, ta
duba ta zaba a ciki sannan ta Masa sallama ta fita abinta kannenta suna Aunty zamu je tace ba

Zan je da kowa ba
Affan ta Kira a waya ya Gama bacci ya tashi yayi wanka Yana shiri ta Kira ya daga tace fito
mu tafi,kana nan Kaya ya Sha wani wando pencil creazy da shi me kyan gaske sai riga me Fadi
Yar sarau sarau bata da kauri daga baya ta zobe baya yafi gaba tsayi Suma Tasha gyara sai da
Raudat ta gaji da jira daga cewa Kaya Kawai zai sa ya gama komai Yana ta kalailaitar jikinsa ya
gama ya fito Yana kamshi ana taku dai dai da wayarsa me tsada,tun daga nesa take kallonsa
yanda ya Sha kyau Kamar a turai,Raudat harda kwantar da kanta a saman sitiyari tana
tunaninsa horn tayi kadan sannan taci gaba da kallonsa har ya bude Gaban mota ya shigo,duk
kamshin da takeyi nasa sai da ya doke nata,yace Hajiya Aunty,tace dan Allah ka daina ce min
Aunty ni bana so ka girmeni sosai ka dinga ce min Aunty,yace alright Yana dariya an gama
Hajjaju ta,ta sake kallonsa kamar zata Yi kuka sai kace tsohuwa,yace to Raudat shike nan, tace
haka gatsal kuma,yace to me zance? Ina laifin ma kace min Queen,Queen dina my Queen ya
furta tayi Murmushi tace naam Affan International yanda taji Sayyeed Abokinsa Yana fada
Masa,Dukkan abokansa sai kace Affan International ake ganewa,dariya yayi yace wannan fa
Yan school ne suka saka min,Affan International.

International na wanka ko? Yace yes tana driving tace ni Kuma Affan Appointment,dariya ya
saki suka je wani hadadden wajen cin abinci acan Suka ci Suka Sha sannan ta Kai shi wuraren
shakatawa suna ta yawo cikin nishadi,Affan wani Kara son Raudat yake ji Kamar ya hadiyeta,
sai wurin goma ta kaishi masauki baya so su rabu itama haka, Suka zauna a motar juyowa tayi
kadan tana kallonsa shima ita yake kallo, hannunta ya rike a hankali tsigar jikinsu ta tashi kasa
hakuri yayi tana mazaunin Driver a haka ya rungumeta yace Ina sonki Raudat ya sake
kankameta Yana shakar kamshinta,jikinta ta janye yace please ina kaunarki na Dade Ina sonki
na kasa fada miki dan Allah muyi aure,Raudat tace kana saurayi Ina bazawara ai bazai yuwu ba
Affan International,yace ni ba komai ina sonki haka ba ruwana da wani bazawara Annabi ma ya
auri Zawarawa bare ni,Raudat tace ku da samarin zamani ne sai budurwa,dan Allah ki daina
fadar haka mene a virgin Ni ke nake so,Raudat tace ka bani lokaci to,zuwa yaushe? Koma
yaushe ne in Naga ka cancanta shike nan, Affan yace au yanzu ban cancanta ba sai ma kinyi
tunani,ya kalli Kansa yace mene Nawa bakya so ko bani da kyau ko dirina bai Miki ba? Raudat
tace wane mutum akwai wacce ta Isa ma tace baka Yi ba,Zan baka amsa ai yace Allah yasa
naji Alkhairi tace ameen ya bude mota ya fita tace sai gobe karfe nawa zanzo? 11am lokacin na
tashi a bacci,tace gobe zamu je ka gaida su Ummi da safe sai kace ranar zaka koma kaga
washe gari sai mu tafi,Affan yace ban gaji ba mu Kara kwana biyu tunda kullum zamu dinga yini
tare tace no Monday da aiki yace ni na sanarwa Oga ai farko sati Daya Kika ce,kasan aikinmu
ko yaushe za a iya Neman mu,Aslam yace gaskiya gwara aikin gomnati bazan iya barinki ki
dinga fita haka yanda Kika ga dama ba,a Haka suka rabu Raudat ana ta murna Kamar zata
kashe kanta.

Washe gari Affan harda saka wani yadi me tsada me karamin dinki ya Sha kyau sosai cikin
fararen kaya za aje gaida suruki,Raudat tazo a wata kalar motar har room dinsa ta shiga tana
shiga ya mike,ya ganta da ledan kayan abinci na take away yace ai na karya Ni naci abinci,a
Ina? Yace fita nayi na samu waje tace nace kaje ne da zaka tafi kaci abinci a wani waje Yan
garin nan fa Mata mayun maza ne so kake wata ta nace mak..tunawa tayi ta dauke wuta duf

harda fuskewa tace hmm to ba komai fito muje gidan namu,Aslam ya fito Yana Murmushi ana
kishinsa,katafaren gidan su Raudat suka je dama ta fada a gida wani da suke compound daya
zai zo ya gaishe su yazo garin,Raudat har ciki ta Masa iso,Ummi ta fito ya durkusa tare da
gaidata tana fara'a ta amsa shima Papa yazo Suka gaisa Yana cewa na gode na gode fa shi
Kam Affan ya Masa ya kwanta Masa a rai, Ummi harda Zama ta saki jiki suna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0