Showing 36001 words to 39000 words out of 86820 words

Chapter 13 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

776

Raudat ta Kara
narkewa tace please kayi hakuri,Affan tsigar jikinsa tashi takeyi idan tana Masa Shagwabar nan
tana tuna Masa da Nabeela,Murfin robar ruwan ya balle ya balli paracetamol biyu ya zuba a
cikin murfin ya dan zuba ruwa ya wani narka maganin sai kace zai bawa dan yaye yace tsaya
na baki to Yana kallonta,sabo da shine zai bata kalau take amma tace to tayi wani kasa da kai
lagaf, Hannu yasa tare da dago kanta a hankali harda cewa haa ta bude ya zuba Mata ta
shanye ji tayi kamar ta Sha alawa sabo da shi ya bata, ruwa ya bata a baki ta shanye abinta ta
wani kwanta a saman kujera Yana cewa sannu yaki tashin mota sai data kwashe 30mnt tace
naji sauki har na daina ji sannan ya yiwa motarsa key

yace me kike son ci? tace Ice cream ai Kuwa ya tsaya ya siya Mata wata katuwar roba guda
biyu da su yogourt me sanyi ya dawo ya leko ta windown ta yace abinci fa ranki ya dade Hajiya

Aunty? tace naci a wajen Hafsat,duk da haka sai da ya siyo Mata tsire lafiyayye sannan ya
shiga mota Suka tafi, ana tafiya tana Shan ice cream dinta Yana driving yace ni bazan Sha ba?
tace Sorry gashi yace tuki nake ai tace to sai munje gida,yace ki bani a Baki ,Ido Raudat ta zaro
taji kunya tace bazan iya ba,yace kaji locality me nake ji ba dadi haka sai kace wani suna
Siyama,dariya tayi taki bashi bai ce komai ba har ya kawota gida tayi godiya ta wuce part dinta
shima ya shige wajen Sayyeed,tana zuwa tayi sufa akan gadonta tana tsalle da murna.

Siyama kuwa bayan ta Gama kukanta har kwana uku bata ga Aslam ba tana ta faman
tunaninsa katsam ta fito daga wanka da Yamma yaro ya shigo yace Wai ance Siyama tazo inji
Aslam,da sauri tace kace gani nan, ai ko Mai bata shafa ba ta zura skert da riga na material ta
saka hijab me Kama da doguwar riga har kasa ta tafi wajensa,tana zuwa yaga fuskarta duk
ruwa tayi wani fresh yace daga wanka Kika fito ne? Siyama tace ae Ina yini ya amsa da lafiya
lau,tace rannan kazo Wanda ka gani ba Saurayina bane ba sonsa nake ba,yace in ma kina son
abinki Charity me zance ni zuwa nayi na duba lafiyarki tunda yanzu kin watsar dani kinyi
hadadde,Siyama kamar zata Yi kuka tace ba Saurayina bane tiryan tiryan ta bawa Aslam
labarin Affan,yace hmm kice miji aka miki,a'a nifa ance maka sai na yarda za ayi auren idan
bana so shike nan Kuma bana sonsa,Aslam ya sake cewa bari mu Fara ja baya Siyama tace
kash kajika da wani zance akan Affan din me aka yi aka yi shi wani banza da shi zaka bani
kunya Allah yawa kake yi,Aslam yace to shi kina ganinsa me kudi,kudin me wa yake ta kudinsa
nawa ya tara,Aslam Yana ta bugar cikin Siyama bata gane ba,sai da ya gama Jin komai sannan
yace to Hajiyar wanka in tafi ko na tsaya akwai labari? Siyama tace jeka,yace oh korata ma kike
Yi kenan,Siyama tace nayi Fushi sai ka dinga min wasu maganganu haka marasa dadi,Aslam a
hankali yace Ina sonki Siyama.....Baki ta bude tace so kuma Aslam? Yace ae ba sai kin so ni ba
Kawai na fada Miki mind dina na gaji da hiding, idan Kika bari Kika auri wani laifinki ne na daina
kulaki Kuma har abada ko a hanya gwara ma ki aure ni,Siyama ta rasa wanne irin murna zata
Yi ta boye tace tun tuni sai da ka bari aka turo min wani wajena yanzu ya zanyi da Kawu? Yace
ki San yanda Zaki yi please I love you,ban taba son wata haka ba sai ke sai Ina kusa dake
nake gane ni Namiji ne tun tuni tun farkon zuwanku gidana na zaci ba so bane Kawai yasa
Naga Nusaiba tafi min na aureta,Siyama ta rufe baki a ranta tace zuki ta mallen maza kenan
sabo da ba Nusaiba,ganin bata da Niyyar bashi amsa ya juya ya Mata sallama ya tafi,Siyama
Kuma ta Shige gida da sauri tana zuwa tayi ball da bahon wankansu ya fashe fas,Aunty tace
Yar nan lafiya? Siyama ta kankame hannu tace wayyo Yana sona dadi kasheni cikin farin ciki
ne, Aunty rungume ni dan Allah Zo ki rungumeni, Aunty taki kulata zuwa tayi ta rike jikin bango
tana zan sume Iska zata daukeni wayyo Sanyi dadi Allah na gode maka tayi ihu,Aunty tace
wallahi sai kin siyo Mana sabon baho akan Namiji Kika fasa Mana baho,za a siyo karki damu ta
fada dakinta harda rawar sanyi tsabar farin ciki sai kace tana Jin sanyi haka take karkarwa.

Aisha watanta biyu a gidan Bashir duk ta rame tayi baki ta fita a hayyacinta gashi Hariji
sannan Kuma Babu abincin kirki Yana samun kudi amma ya daina bata ci na kirki,a wata biyun
ta samu ciki amma shi Bashir baya son haihuwa,ga mijinta can Farooq Yana son haihuwa basu
samu ba taje tayi aure Kuma inda ga haihuwar amma ba a son yaran,gaba daya Bashir ya
tsaneta sabo da ciki,ko ya ta bashi haushi sai duka a Haka cikin nata ya zube Aisha tayi barin
Yan biyu twins,tayi kuka sosai ga rama ta kekashe ta bushe,Farooq Kuwa har wasu lokuta baiyi

aure ba ya kasa kula kowa har ya gaji Mamansa ta hada shi Nabeela bazawara ita Kuma
Maman Farooq kawar Maman Sabeer ce a can taga Nabeela,Aisha sai labari taji Farooq yayi
aure tayi bakin ciki tayi kuka ta gode Allah har ta samu wani cikin,Bashir tsana ta dawo sabuwa
dal
Nusaiba bayan ta Gama Idda da kwana uku Sufyan yazo gaida Shehu,Shehu ya sauke shi
yace yaro daga yin iddarta da kwana uku har yaushe ta sanka da zaka ce zaka turo wannan ya
nuna cewar tun tana da aure ka Santa dama kana sonta ko karya ne? Sufyan yayi mukus yace
bazai yuwu ace daga Gama Idda da kwana uku Wai har kazo daga wata uwa duniya kana sonta
Kai ba dan unguwar nan ba a Ina ka ganta sai dai idan dama tun tana da aure kana
zuwa,Mama tana ji tayi gatsal tace yata shi take so kuma shi zata aura,Shehu yace ba matsala
Kai Sufyan gaka ga Nusaiba duk abinda tayi maka karka soma kawo min kara ba ruwana ya
tashi ya fice abinsa,Nusaiba ce tazo tace karka damu dashi Indai Mama tana sonka an
gama,Sufyan Yana murna sosai ya tafi,Bayan kwana uku ya turo da kudin aure cikin sati biyu
Mama ta yanke aure za a daura,Shehu ba ruwansa a ciki sai da daurin aure yazo sannan ya
shige gaba Sabo da yarsa ce ba yanda zaiyi aka daura auren Sufyan da Nusaiba

Nusaiba takanas ta tafi gidan Aslam ta kwankwasa ya zaci wani ne ya bude sai kuwa ta shiga
ciki tana yiwa gidan kallon banza harda cewa to Ina Aslam Dan karya gashi na riga ka aure
Kuma na sake samun wani me kudin Allah ba Azzalumin bawansa bane bazai barni cikin
wahala ba na sake tafiya gida me ac sai naga ta tsiya Kai Kuwa gaka nan tsiya tsiya kalli
wannan dirty smelling House din naka nafi karfinka tana Jan tsaki ta juya ta bude kofa ta fice
tace aci gaba da Shan talauci lafiya,Aslam baki ya tabe ko a jikinsa yace Wanda ya kulaki shine
banza baki da ajin da Zan saurareki,Nusaiba tana jinsa ita Kam tayi gaba abinta.








Masu sharhi Ina Matukar godiya






AsmaBaffa
[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢�AUREN MU🛢�

46-50

Official



By
AsmaBaffa





Page naku ne

MRS SAS
YAR AUTA









Sufyan Isa,Dane ga Isa Yan garin Ajingi ne Kano amma a cikin Kano suke danginsu ne a
Kauye amma uwarsa da ubansa da kannensa guda bakwai suna Kano kofar Ruwa,Sufyan
shine Babba a gidansu talakawane, Allah yasa Sufyan yayi degree ya samu babban aiki na
gomnati yayi aiki da shekara hudu haka Kawai ya ajiye aikinsa ya fito takarar Chairman ya
koma siyasa,bayan anyi zabe ya Sha kasa ko kansilan nadi ba a bashi ba,karshe talauci ya
sake baibaye su ya Shiga Neman aikin kamfani bai samu ba sai da ya kwashe shekara biyar
sannan ya samu aiki a wani kamfanin shahararren me kudi ya bashi C.E.O ga Albashi me tsoka
yana aikinsa sosai bai da wani aibu sai dai dan Adam kowa Yana da Hali me kyau Kuma ba a
rasashi da hali na banza ko ya yake,ana haka ya ginawa iyayensa gida me kyau shima ya gina
nasa gidan me kyau sosai amma bai Kama kafar gidan Aslam da bank Suka kwace ba Babu
hadi ma,
ya mallaki motarsa me kyau har ya hadu da Nusaiba ya aureta Kuma.

Kwana uku da daura aure Nusaiba ta Sha gyara ta ko Ina tayi kyau sai kamshi take yi,ranar
Kuma aka Kai amarya gidan mijinta me kyau kana gani kasan ba gidan talaka bane,zaune take
a saman gadonta dake dama Kawai daga ita sai lefenta da kayan sawarta Amma komai na
furniture ya zuba abinsa.

Sari ne a jikinta Riga da skert maroon ta yafa mayafinsa kyau Kam tayi,9pm angon ya shigo
da Sallama hannunsa dauke da ledar kaji da kayan makulashe,Zama yayi a gefenta yace
Alhmdllh Ni Kam nafi ko wanne Namiji dace a duniya,yau na mallakeki burina ya cika,Nusaiba
tayi Murmushi tare da bude mayafin data rufa a kanta,yace tashi kiyi Alwala,mikewa tayi ta
sheka wanka da Alwala ta fito shima ya shiga,shiryawa tayi cikin kayan baccinta masu daukan
hankali sannan ta daura zani tasa hijab har kasa bayan ya fito shima ya shirya ya sa
jallabiyarsa sannan Suka gabatar da duk abinda akeyi na addini da na al'ada,ledar ya jawo ya
bude musu kaji ne da su Yogourt da sauran kayan makulashe da fruits

Plates ya dakko ya zuba musu ta kalli Naman tace Wai brolas ne ko Maja? Sufyan yace Ina
Zan sani ni da na gansu a gashe na siyo,tace maza dai har abada baza kuci gaba ba,tunda aka
halicci iyaye da kakanni kowa kaza kaza dai ankonta kuke Yi ko wanne ango ankon kawo
kaza,Sufyan Yana Murmushi yace to me kike so? tace Ina laifin ma tattabara tana magana Yana
bata naman a baki tana lamushewa amma tana kushewa,sai da suka koshi suka gama komai
sannan ya dauketa suka haura saman bed abinka da bazawara tsagera zagewa tayi Suka
farantawa juna rai Suka jiyar da juna dadi sosai Sufyan sai yabonta yake yace Yan unguwarku
sunyi sakaki na daukeki shike nan,Rungume shi tayi tana I love you a haka har bacci ya kwashe
su.

Siyama ce ta zubo shinkafa da wake da Mai da yaji sai salat ta toza wani katon plate kamar
mutun uku ne zasu ci tasa a gabanta zaune a tsakar gida saman Sallaya da yamma sanye take
daga ita sai vest fara da English skert wani me kyau brown Mai adon fulawowi fari,jikin nan nata
sumul sumul komai Masha Allah,ta sa Hannu tana ci baza ma tasa cokali ba,Kawu ne yayi
sallama ya shigo sai ga Aslam ma a bayansa sun shigo yasha farin wani yadi me kyan gaske
yayi kyau Kamar baza a mutu ba,ya shigo Yana takunsa na Izza,Aunty ce ta amsa
sallamarsa,Siyama kunya ta kamata sabo da irin abincin data zuba tana ci ya kamata,Aunty ce
ta dakko tabarma tare da shimfida Masa ya zauna Suka gaisa

Siyama tace Ina yini amsawa yayi Yana murmushi,ta mike ta kawo Masa ruwa pure water
Yana faman binta da kallo,Kitchen ta Shiga ta zubo Masa abinci a plate ta rufe ta kawo plate din
salat da Maggi star ta ajiye komai sannan ta koma ta zauna a gaban abincinta,sabo da kunya
Siyama tace Aunty kin siyo min maganin tsutsar cikin nawa Kuwa? Aunty tace wanne tsutsar
ciki sai dai ki boyewa Aslam amma kowa yasan irin mugun cinki,Siyama baki ta turo tace to ba
tsutsar ciki ce ba suke tashi suna neman abinci,Indai suka farka daga bacci to sai na Fara Jin
yunwa shike nan ba zaman lafiya idan ban ci ba Kuma fa,Aslam Murmushi yayi ya kalleta ya
kalli abincin Siyama tana cin abinta,da Ido tace kaci mana,juyawa yayi ya kalli Aunty da Kawu
yaga ai hirarsu suke Yi hankalinsu baya wajensa ya kalli Siyama da Ido ya fada Mata bazai ci
ba harda makale kafada,Murmushi tayi tana leka su Kawu sabo da Kar su Kama ta,tashi Aunty
tayi da Kawu Suka Shige daki suka basu waje,Siyama ce ta leka palon taga sun shige bedroom
da sauri ta jawo abincinsa gabanta ta tona gefa tasa salat da su tumatir ta ebo a Spoon ta Mika
masa a Baki ya tsaya Yana kallonta bai bude bakin ba,cikin muryar rada tace kayi sauri kafin su
fito fa bazan iya baka a gabansu ba,Baki ya dan bude ta zuba Masa Yana ci ta sake lekawa
dakin su Kawu taga dai basu da niyyar fitowa taci gaba da bashi a baki yana ci,sai da ya koshi

Yana Shirin cewa ya koshi Kawu da Aunty Suka fito ai da sauri Siyama ta tura plate din Gaban
Aslam tana basarwa taci gaba da cin abinta,Aunty ta fito sanye da hijab tace Aslam har ka koshi
dan Allah ka cinye ta nan fa ba wajen Kara bane,Kawu yace ke Siyama ku tashi ku koma dakin
zaure ko yafi sakewa a.....kafin ya karasa Siyama ta mike tsaye ta kwashi abincinsa da
ruwa,Shima mikewa yayi ya zaro dubu biyar ya mikawa Aunty yace gashi Aunty Kya sa ko Kati
ba yawa,Aunty tace harda kokari haka to fa an gode an gode Allah ya Kara sutura yace Ameen
Suka koma dakin zaure Wanda ya Sha gyara sai kamshin turaren wuta yake Yi.

Suna shiga Siyama ta dawo ta dauki nata abincin ta wanke hannayenta tare da daukan wani
spoon din ta shiga daki ta saka hijab me hannu ta koma wajensa,tana shiga ta iske shi a tsaye
tace baka zauna ba,yace tsutsar cikina ce ta tasheni,dariya Suka Yi gaba daya suka zauna tace
dan Allah kaci da yawa nasan baka ci komai ba,yace indomie naci Mana,indomie abinci ce?
please....ta karasa da shagwabar da hankalin Aslam ya tashi Yana Mata wani irin kallo cike da
so Wanda yasa yace kin San me tace sai ka fada yana kallonta Ido cikin Ido ya furta Ina sonki
Charity na matsu na jiki kusa dani, Charity tayi Murmushi tace hmm ban baka labarin wata
kawata ba Haleesa wata daya da aure jiya naje gidanta na samu tana sheka amai nace haleesa
lafiya? Charity tana wani magana ana Yi da hannaye ana style da hannaye Wanda sun Sha lalle
me mugun kyau Wai dan Aslam ya gani,tace Ina fada maka ta sake daga hannayen tana
jujjuyasu tace dan ubanki Charity ciki ne dani, ai tunda na bude baki kasa rufewa nayi,tana
bawa Aslam labarin shi Kuma ita yake kallo kamar tv Yana dariya tun dazu yaga lallen amma ya
nuna Kamar bai gani ba shine yanzu labarin ma Sai an sake nuna Masa lallen.

Magana yayi yace ya birgeni haka ake son Namiji kema Watarana haka Zan Miki naki,Charity
ta bude baki kunya ta kamata ta rufe Ido da tafukan hannaye tace ba ruwana ni dai Kawai sai a
ga Yar Baby ta ace Yar gidan Charity ce wallahi haka zance duk Wanda taji yace da mamanta
Charity Kar ta sake ta yarda,Aslam yayi Murmushin Jin dadi yace har na hango kanmu,Ki
fadawa Kawu Zan turo a kawo kudi,Siyama tace da wuri haka? Yace kin San Kuwa yanda
hankalina ya tashi da naga kina zance bazan iya ba wani yazo a samu matsala,Siyama tace Ina
tsoro Kar Kawu yaki yarda sabo da Nusaiba,Aslam yace karki yarda a hanaki aurena kinji dan
Allah bance ayi musu rashin kunya ba dole muyi musu biyayya abi a hankali amma ki dage kice
sai ni,Aslam Yana yiwa Kansa campaign yace wasu tanadi da na mana sai dai munyi
aure,Siyama tace duk abinda ake ciki ka dawo jibi,yace gobe Zan dawo ni ban gaji da ganinki
ba tace Allah ya kaimu,mikewa yayi yace zanje wurin Mum,tace kace Ina gaishe ta yace zata ji
itama ya zaro dubu biyar ya bata taki karba yace bana son musu,ta karba tare da furta na gode
ka manta ledarka da ka shigo da ita tana kusa da Aunty,Aslam yace wayarki ce,waya na siya
Miki Zaki ga Simcard din a cikin ledar ki saka sai na kiraki anjima ya rike hannunta ta zame a
hankali yace Ni kike ma Haka Yana Murmushi tace muna yin aure kazo kayi ta rikewa,an gama
ya furta Suka fito ta rakashi da motar Sabeer yazo ya shiga abarsa ya tafi ta koma ciki taci gaba
da dura abincinta.

Washe gari da safe taje gaida Kawu Aunty tana dakin tace Kawu ya amsa tana kunya tace
Aslam yace zai fito,Kawu yace daga Ina zai fito? Takara zai fito ko kuwa daga daki? tace zai
turo nake nufi,kawu ya gane fa yace baro zai...a'a fa kawu zai turo da manyansa neman aurena

,Kawu yace Yar jakar uba ai na gane so kike ki jawo Mana zagi da abin kunya a unguwa,yanzu
idan aka ji mijin kawarki Zaki aura ai mun shiga uku a layin nan da zagi,Aunty tace sai ace ma
itace ta rabata da gidan mijinta gashi Yanzu ta aure mijin nata ai ki auri Affan yafi Miki
Siyama,Kawu yace rabu da Yar banza Ni baza ayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0