Showing 1 words to 3000 words out of 63115 words
ï»¿í ½í²‘ *AUREN FARI*í ½í²‘
0⃣0⃣1⃣
*NA SADAUKAR DA LABARIN GA AUNTY RABI TAH ( HAJIA RABI BADAWI MAMAN
IBRAHIM )*
Sauri takeyi kamar zata tashi sama, hannun ta rike da kwanon miyar manja, tun dazun aka
aketa asibiti kai abinci amma don shiriri ta miyar ta baro gida shine ta dawo dauka.
Fakam fakam fakam tafiya takeyi ba ko jinkirtawa saboda tsoron kada Yaya Abba ya dawo
masallaci a fada mishi yau kuma ga abinda tayi. Ji kakeyi rikichaaaa,!! Karam karam....... Ta
antaya jikin mai tahowa da miyar da ita duk suka afka mishi yayi baya da karfi tare da riketa
gamm bayansa ya bigi bango da karfi miyar ta karasa wanke mishi gaban farar gizna din sa, ya
runtse ido da karfi lokacin da yajin miyar ya watsa mishi a ido yaji wani irin azaba ya ingije ta
silbin miyar ya kwashe ta ta fadi duk ta nade miyar a hijabinta.
Ta mike a harzuke malam wannan wane irin wulakanci ne baka gani zaka jefani cikin miya in
bata sabuwar hijab dita ta islamiya? Bayan asarar da ka janyo mun kai baka iya tafiya kana
duban gaban ka?
Bala'i take zazzagawa yana kokarin goge yajin da ke idon sa. Sam bata lura da mutanen dake
bin bayan sa ba, sai da wani ya finciko ta karfi zai kwada mata mari yayi saurin daga mishi
hannu alamar ya kyaleta. Ta ja baya tare da rike kugu iyyyeee cewa zakayi tafe kake da masu
tare ma fada to wallahi yau sai kun biyani miyata da hijabi na..... Sai lokacin ne ya kalleta
idanun sa jawur ga bacin rai ga radadin yaji ya da ka mata tsawa ke gidan ku ba a koya miki
tarbiyya ba? Wannan tsummar hijabin da banzar miyar manjar ki kike wa mutane rashin kunya
akai? Kin San darajar kayan da kika bata? Ya zaro ido ya na nuna jikinsa.
Kai ka sani ni kasan miyar nawa aka kashe akayi ta? Ko kuwa kasan kudin wannan
hijabin.....shut up!!! Ya daka mata tsawa tare da damko ta. Lokacin ne hankalin mutane ya
dawo kan su. Wani yayi saurin dafa kafadar sa yallabai ba girman ka bane don Allah ka kar ka
biye mata. Ya hakade ta ya gitta zai wuce sai ta chafko hannun sa da karfi kamar wani zaki ya dubeta da
karfi ya kalli siririn hannun ta sannan ya kalleta ita din dukan ta zai iya hadiyewa.
Wallahi duk mazuran ka sai ka biyani zaka bar wurin nan yama rasa me zai mata ya chafki
hannun ya kudundune ta ya jefar suka wuce yabarta kwance tana ihu duk ta tara mutane kanta
asibitin.
Abba da ya fito masallaci ya hango mutane taruru ya tukaro wurin yaga lafiya sai kawai yaga
*umaimah* wani takaici ya turnuke shi ya figeta da karfi sukayi dakin jinyar, tunda tagan shi jikin
ta ya fara kyarma. Suna shiga ya fara wanka mata mari biyu sannan ya tambayi ba asi, tana
gama fada mishi kuwa yasa mata charger ya bata kashi sai da goggo ta karbeta. Abincin sai dai aka siyo mai da yaji.
Umaimah marainiya ce, gaba da baya tana hannun wan babanta gidan banda gallaza mata
babu abinda akeyi ko karatu sun hana a sanyata da tsiya sun kangarar da ita. Matar marikin
nata ce aka kwantar duk da nisan da ke tsakanin su da asibitin kullum itace ke kai abincin safe,
rana da kuma dare.
Kamar mahaukaciya haka ta fito kacha kacha ta nufi gida tana takaicin wulakancewar hijabin
islamiyar data samu da kyar aka yi mata. Haka ta koma gida ta shiga wanke kayan da manjan
ya kasa fita abinda ya kara harzukata tana addu'ar Allah ya kara hada ta wannan dan rainin
wayon. Sati daya, sati biyu....har an share kusan sati biyar basu kara haduwa ba gashi an sallamo
goggo sai ta fita batun sa.
Umaima bata da kiwa ko Kadan shi yasa take cin gajiyar mutane da yawa cikin unguwar ana
yawan kiranta gidaje mai shara, wanke wanke dan wankin yara haka dai idan ta gama abinci,
sabulai mai da tsumma. Gidan su Sam babu Wanda ya damu domin sun dauki hakan kaskanci
da bayar dakai wani lokacin ma sai suyi ta mata dariya tare da habaici. Ita kuwa tafi jin dadin
bautar da takeyi wa mutanen gari suna godewa ba nan da kullum wulakncin safe da rana daban
ba.
Duk satin nan bata zama gida tana gidan Alhaji yakuba tana taya su aikin biki, musamman
gyaran daki domin sun yarda da ita matuka.Har yau ransa a 6ace yake, yarinya karama talaka
kuchaka ta dizgashi, zuwansa asibitin biyu bai ganta ba inama lokacin ya kakkaryata lallai da ya
huce bai zauna cikin bacin rai irin haka ba, ya ringa hasko ta cikin kuchakan kayanta da shegen
yadin da take ikirari da sabuwar hijabi Wanda ko kyallen goge takalman sa yafishi daraja.
Ya buga tsaki ina jiye wayarinyar nan haduwar mu nan gaba....... Au wai baka shirya ba? Don
Allah malam hanzarta kowa ya hallara kai kadai muke jira.
Ya kara hade rai ya mike okay ina zuwa.
Yauma cikin rantsattsiyar gizna yake fara tasha aiki na alfarma tafe yake yana kasaita ran nan
nasa a 6ace. Yanda yake saukowa a benen yasa abokan duk bushewa da dariya baibi ta Kansu
ba kawai yayi gaba abinsa. Mustapha ya yi nuni da baki ji yanda yake hura hanci kamar shine
angon duk suka kara kwashewa da dariya. Hajia ta kira umaima lokacin da ake ta faman tafiya party tace ke bazaki je bane? Murmushi tayi
ta ce eh hajia. Dalili? Maza zo nan ta kama hannun ta tayi ciki da ita wata durowa ta bude kinga
duk wadannan kayan Asma'u cewa tayi a bayar don haka ki zabi Wanda zaki zaka yanzu kije
ayi dake idan kin dawo ko zuwa gobe sai ki zo ki kwashe sauran don ke na ajiye wa....ta zaro
ido ni hajia.
Eh ke fa..
Maza shirya kada motocin su kare, wani paper lace ne milk dinkin riga da skirt ta dauka. Har
zata fita taga hajiyar ta shigo da sauri ta miko mata takalma ungo wurin amarya na roko miki
wannan kuma gyale ne sanya maza ki wuce.
Ko hoda bata shafa ba.
Tana zuwa ta fada mota. Ko da a ka sauke su. Fiddausi kanwar amarya na ganin ta tace yauwa
umaima zo Ku shiga da kayan nan. Ta ce to ta shiga aiki. Dai dai lokacin da sukayi tsaya da
mota kamar ance ya daga kai kawai ya hango ta rungume da lemuka.
Da sauri ya fito sai kuma ya yi turus daya tuna inda yazo.
Muje ko?
Ya rungume hannu a kirji tare da jingina da mota ya ce kuje ina zuwa ...duk suka kalleshi sai
kawai yayi sauri ya fiddo waya yasa a kunne hakan yasa suka fahimci waya zaiyi. Suna
wucewa ya mayar da ita aljihu, ta fito tana ta faman kakkabe kakkaben kaya yayi murmushi
watau yau bata son abinda ka taba kayan jikin ta.
Sam bata lura dashi ba ta zo zata wuce sai kawai taji an fizgeta anyi bayan motoci, ta dago da
karfi sai kawai ta ganshi. Ta fizge hannun ta tare da ingijeshi kana hauka ne zaka kama ni? Zai
yi magana ta juya abinta kayan data fasa dauka kenan ta shiga ciki duk an zazzauna ta hango
kujera can tsakiya ta isa ta janyo zata zauna ashe biye yake da ita kawai ya harbar da kujerar ji
kakeyi *timmm* ya wuce abinsa duk aka juyo hankalin kowa ya dawo kanta ta wunkura da karfi
zata isa gunsa fiddausi ta gani gaban ta. Sannu umaima ke nake nema zo muje ki taya my
serving wani takaici ya turnuke ta ta bishi da kallo dai dai lokacin da ya hau gun anguna ya
zauna ya juyo yana hararar ta.
Kunya duk ta baibaiye ta. Shine ya bude tà ro da addu'a ya bada tarihin ango don haka bata
nan suna can suna shirya abinci.
Fiddausi tace kamata yayi mu fara kaiwa haka .
Umaimah tayi karaf Anty fiddausi kawo in faro daga sama wurin angwaye.
Yawwa Allah ya yi miki albarka umaimah dama kowa baison zuwa saman cen, ta dauki ture ta
fara shiryawa. Zuwa na uku da zatayi ta debi cocktail juice da farfesun kayan ciki ta tafi tana isa
kamar zata ajiye bisa yanda ta faro daga farko kawai sai ta antaya mishi duka ajiki har turen
jikake rikichaaaa ...... Duk Wanda ke high table din tsaye ya mike hankali tashe........
*MAMAN ABDALLAH* CEí ½í¸ƒí ½í²‘
*AUREN FARI* í ½í²‘
0⃣0⃣2⃣
Kamar da gaske ta dan razana laaaaa ban gani ba taja baya zata gudu Ya chafko hannun ta,
Asma'u ta daka mata tsawa haba umaimah baki gani ne? Tayi ta kicin kicin ta kwace hannunta
amma ya ruke su tamau, ba komi ya fada yasa dayan hannun sa ya fizgen gyalen ta ya fara
kwashe plates din dake bisa jikin sa sannan ya ya ci gaba da gogewa, duk illahirin jikin sa ya
baci, yarinyar nan na janyo mun asara amma zan maganin ta a yau.
Biki ya tsaya chak! Yaga kowa ya mai da hankalin kansa abinda ya tsana kenan ransa ya kara
baci. Ki kwashe kwanukan kikayi tsaye, ta kalli kanta ta yaya zata ratsa dubun mutane ba
gyale? Wannan wulakanci dame ya yi kama? Ga kayan duk sun matse ta....ta daka mata tsawa
ko ba kyaji? Ta duka tana kwashe kayan ya yi fit! Da kallabin ta kananan kalaban da ke kanta
suka watso mata ko ina ta mike da sauri zata zazzaga mishi bala'i ya ce yafa gyalen don naga
baya daukar miyar sosai gashi ba towel da zan goge kayan naki sun kama da bargo.
Ji tayi an fizgeta da karfi, tana juyawa taga fiddausi, haba umaimah kinsan waye kika batawa
kaya? Zo muje ki karbo towel mota kikai mishi. Figai figai babu gyale ko kallabi nake binta zarai
zarai idanuna sun kawo wani ruwan bala'i.
Anyi anyi ya tashi yaje ya sauyo kaya yakiya wai zai jira a gama. Ransa kuna kawai yakeyi
amma ya kasa nuna wa duk da fuskar tasa kullum tamau.
Don Allah Anty fiddausi ko kallabinki ne bani in yafa kada in kuma ratsa mutane haka. Har zata
yi musu sai kuma ta kwanto ta bata kowa head ya saka amma wani ikon Allah ita fiddausi ba ta
sanya ba. Tun kafin ta hau saman ta hango kallabin da gyalen a kasan kafar sa yana goge
sauran miyan da suka zuba. Tuni an ci gaba da sha'anin biki amma ganin ta hawo saman sai
hankalin amarya ya dawo kanta, ta mika mishi towel din tare da banka mishi harara.
Baki iya goge masa wai yau meke damunki *UMAIMAH*?
Ya maimaita sunan cikin takaici a zuciyar sa *umaimah* ta duka ta fara gogewa shi kuma ya
kara shan mur, dataga hankalin asma'un ya koma can sai ta fara dangwalo wata miyar dake
ajiye ta na kara yaba mishi a inda bai samu miyar ba. Hada hannu. Ya kura mata ido yana wani
irin mamaki wai yarinyar nan tasan waye shi? Yaci gaba da kallon ikon Allah tasha mur sai
kwaso miya takeyi tana kwaba mishi sai tasanya towel din ta dalaye. Tana gamawa zata mike
ya dankwafar da ita ta koma da karfi ta zukunne, ya kalli abokin sa yace idan bazaka sha
wannan naman ba kaban, ya miko mishi bai ko kalleshi ba yaci gaba da kallon yan rawa, sai
kokarin dagowa takeyi shi kuma ya danne kafadarta da hannu, ya dan waiga yaga kowa
hankalin sa yana gun yan rawa ya sa hannu ya bude gaban rigar ta ya kwarara mata duka
miyar cikin breast ware sannan ya sake ta tafadi ta baya dabas! Ya kawar da kai kamar baisan
komai ba. Na kusa dashi ya kalleta easy! Tashi mana.
Ta mike a wahale miya na zurarowa cikin rigarta duk ta bata ta nama cike cikin brezia.
Kwalla suka shatato mata wannan wulakanci da me yayi kama? Ganin tana kuka yasa yaji wani
sanyi a ransa hakika yanzu ya fahimci 6acin ranta. Ta fita farfajiyar tana faman zubda hawaye
fiddausi ta tareta tare da daka tsawa haba umaima ji yanda kika batan kallabi, ta dubi kallabin
Wanda ya zamo tamkar makwararin juyewar miyar. Zatayi magana ta fizge abinta tayi gaba. Ta koma bayan hall din ta duke tana kuka, kukan takaici ba gyale ba kallabi. Tayi mai isarta, har
duhu ya fara nan da nan taga mutane na fitowa alamar an gama ta kara lafewa jikin bango.
*zan jira a gama fitowa in koma in dauko gyalena da kallabi cikin miya in yafa hakanan amma
bana iya ratsa mutanen can haka* ta fada cikin muryar kuka.
Wallahi ko waye ubansa a garin nan sai na rama wulakanci na ta buga tsoki.
Acikin hall abokan gewaye dashi suna faman ya taso amma ya kasa ko motsi. Baya iya ratsa
dubun mutanen nan haka yanda aka sanshi a gari irin daraja da kimar sa.
Ya kara hade rai na fada muku kuje zan taho nayi waya za a kawo mun mota kuyi amfani da
wacce mukazo ciki key na hannun.... Gashi nan daya ya fada. Ya tabe baki okay you can go
zan taho, zasu kuma magana ya ce please Ku kyaleni wallahi kuna dada sani damuwa.
Dole suka fita, a rude amarya da ango suka iso zasuyi magana kenan ya yi murmushi karku
damu bazan iya fita haka ba idan kowa ya gama tafiya zanje ya kalli Asma'u karki damu da
abinda kanwar ki tayi mun......... Ba kanwata bace yallabai diyar makwabta ce amma tana
shigowa gidan mu kama aiki........'yar aiki? Ya maimaita a rai. ......what ever ba komi kuje nayi waya za a zo a daukeni.
San in ko waye yasa sukayi gaba.
Umaimah kuwa lekowar da zatayi sai taga motar karshe ta fice yayin da wata ke shigowa ta
zuro a guje sai taga sojoji biyu sun fito cikin wacce ta shigo din, tayi cikin hall din a rude, dai dai
zai mike ya hangota ranshi ya bashi lallai gyalen ta biyo, ya kwashesu duk ya cusa aljihu duk da
suke sharkaf da miya. Ganin shi bai wani daga mata hankalin ba domin ta gama rikicewa da
dare gashi kowa ya watse, duddube duddube takeyi tana zare idanu shi kuwa yayi tsaye yaji ko
zata tanka mishi sai kawai tayi hanyar fita ya zabura ya damko ta, kamar tana jira ta harzuka
wai kai *maye* ne? To kurwata tafi karfin ka, meye hadina dakai yauni naga bala'i.... Ina kika ga
bala'i wallahi yau sai nayi maganin ki ya figeta sukayi waje yana dube dube yana faman zare
ido, kawai sai taga jelar gyalen a aljihunsa. Ta kalleshi taga lallai ya fara rasa hankalinshi don
fushi, to me zai Mani? Ganin sojojin nan na tunkaro su yasa ta gantsara mishi cizo a yatsa
kamar zata cire ya fasa kara *kaiiiiii* yana sakin ta tayi wajen *gate* din a dari da sittin.
Daya daga cikin sojojin ya yunkura zai kamota yayi saurin tsayar dashi.
Allah ya taimaketa tana fita ta samu adaidaita da kamar bazai dauketa ba tace party tazo bata
gari suka biyota.
A kofar gidansu ya ajiyeta, ta karbi dari gurin sham'unu mai manja ta bashi, ta shige gida ana
babban falo ana kallo ta sadada taje ta sauyo kayan.
Washe gari wunin biki taki lekawa hajia tayi aiken duniya sai ma tabar gidan.
Karfe bakwai na safiyar walima hajiyar ta aiko kanwarta ba halin kara wata dabarar saboda ta
ce kafarta kafar umaimah. Ko kalaci batayi ba.
Tana shiga tasanya ta gyaran daki tana fada kin San idan bake kika gyara man dakin nan ba
bana jin dadi amma hiratan jiya kika ki lekowa to yau ai kyasha aiki ko fidda dattin tayil dinan
kadai ya isheki.
Ga kayan ki can na kulle miki amma ina gyalena dana ara miki? Gabanta ya fadi tayi dan
kasake kafin tace, yana gida zan wanke ne, to ba komi tayi waje.
Ta shiga gyaran dakin tayi mishi fes cikin yan mintoci saboda bata da nawa, anata shirin walima
ta ce umaimah maza shirya ku tafi walima,
A'a yau bana jin dadin jikina hajia kuma idan na tafi wazai gyara baranda? Ki bari su tafi sai in
karasa gyara miki gidan.
Allah yayi miki albarka ya zaba miki miji na gari, ta washe baki amin hajiyar mu. Tayi waje da
wasu kwanuka ta ce ina zanje mu kara haduwa da mugun nan? Inba rigima irin tau ba inani ina
haye ma irin su?
Su hudu suka shigo tana ta faman hada kayan wanke wanke, kafar dattijuwar ta murguda tayi
kichaaaaa zata fadi umaimah ta saki kwano tayo kanta ta tare sai ta fada jikin umaimah amma
duk da hakan kana jin karar da kafar tayi kat!
Subhanallahi sannu mamah ta fada yayin da dattijuwar tace washhh!
Sai kawai cikin Matan nan wata ta ingije umaimah move... Ta tallabo matar.
Cikin fushi umaimah ta kalleta ta ce *move*? To anki ayi move din ta hankade ta ta tallabo
matar duk suka zaburo kan umaimah, kada wacce ta matso, matar ta fadi a hankali. Sorry
mama suka fada suna ja baya,
Au da taron dangi zasuyi mun? Ashe kuna sonta zaku barta ta fadi? Data kai kasa ai da kun ce
*move* da hujja aikin banza.
Ta juya sannu mamah ita kuwa sai bin umaimah take