Showing 33001 words to 36000 words out of 63115 words

Chapter 12 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

ta jiya kyawu.
Ta yi murmushi mamah wadannan kayan fa *Madaki* ya kawo mun ta zaro ido *madaki* ta
kwashe duk yanda akayi ta fada mata sai kawai ta hau dariya *Au har mutanen gidan naku ma

basu tsira ba?*
Lallai abun nashi azimun ne. Shawara daya zan baki ki daina hawa sama idan yana nan in ba
wani kwakkwaran dalili ba ko gyara idan zakiyi ki bari sai ya fita office ranar da duk bai fita ba to
ki kyaleshi.
Ta ce toh.
Ranar litinin tunda safe ta iso a falo ta tarar da shi nan suka gaisa tayi ciki don shirin makaranta.
Ta dora hannu a kai *Na shiga uku* dan skirt ne bai karasa kai guywa ba hade da karamin
wandon sa sai farar riga yar shirt mai karamin hannu tare da neck tie. Ta zaro ido wai
makarantar su Khausar zanje? Irin kayan su ne ta shirya tsaf, da doguwar safa sai farin takalmi
*camp bus* sai yar hula karama daman tayi sabuwar kalaba kanana amma duk ta hadeta wuri
gida ta kulle, shiru shiru ta fito mamee ta shiga ta ganta tsaye. Ke fa kadai bus ke jira gasu can
suna *oda*
Mamah haka zanje? Ta zaro ido babu ruwansu da ke makarantar duk turawa ke koyawa.....
Kirjinta ya harba. Mamee ta kamo hannunta ta sagalo jakar sai rinjayarta takeyi saboda nauyin
litattafai. Ya bita da kallo wani kishi ya turnukeshi ya daga murya.
Mamee.... Ta juyo da sauri
Sai kawai yasha mur ya kalli umaimah *Ke jeki sanyo doguwar hijabi idan kinje makarantar kya
cire*
Mamee ta dankara mishi harara ke muje ta fizgeta.
Ya taso da sauri suna fita ya hango su baffa cike a motar suna jiranta. *Cikin gardawan can
zata tafi?*
Wuf, ya fizgota hannun mamee ya daga murya *kai isma'ila tafi kawai zan kawo ta*...........Ya
yi ciki da ita yana zuwa falo yayi sama ya dauko key din *private car* din sa.
Mamee na waje tayi tsaye tana dariya kamar me?
*Ta gama tabbatar ma zargin ta* farinciki kamar me tana jin motsin fitowar su tayi baya da
sauri.
Umaimah dai simi simi ta rasa inda zata kanta don kunya tayi shiru kanta kasa.
Tuki yakeyi yana faman tsaki duk karatun nata ya bashi haushi. Kadan kadan yayi tsoki yana ta
sake sake,
Mamee ta ce tohh abin haka yake ashe ina ta wahalar da kaina a waje ashe rabon na tare
dani. In na haukan madaki ba an taba so da *Masifa*? Ta kyalkyace da dariya yau naga ikon
Allah ni jikar buzaye.
Ya kaita har bakin kofar office din principal ya ce ki shiga zasu kaiki class idan an tashi kuma ki
jira zan aiko..... Ta fita da sauri ta kyaleshi.
Ya bita da harara kawai ya juya a guje.
A class din su khausar aka kaita SS1 wurin zaman su daya. Hankalin kowa ya dawo kanta.
Khausar ta gabatar da ita amatsayin yar uwa hakan yayi mata dadi sosai.
Umaimah na cikin matsala da farko don bata ganewa sosai saboda ta riga tasa tsoro a ranta
bata taba zama aji ba. Sai da khausar da wata kawar khausar da suke kira *Yar gata* sukayi ta
karfafa mata guywa. Cikin sati biyu sai ta ware.
Tun da ta shiga makaranta bata da lokacin kanta ga azumi ya kusa,
Idan ta dawo makaranta karfe biyu kafin ta gama wa mamee kintse kintse hudu tayi ta tafi
karatun islamiya shidda tana yi gudu gudu zata bar gidan.

Ranar wata asabar tazo karfe takwas ta tarar mamee da baki falo ta shiga musu hidima yi
wancen dauko wannan. Har ya shirya ya fita ransa a jagule.
Washe gari tana zuwa ta tarar har ya yi wanka yana faman daura agogo ta durkusa kenan ya
ce *ta shi kawai* yau ranar punishment ce , tasan za ayi haka gabanta ya fadi ganin yanda ya
6ata rai. Ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta.
Ya tako zuwa inda take kin tuna da alkawarin da kikayi cewar zaki rama duk abinda nayi miki
ko?
Ta daiyi shiru ya fizgota ta fada jikinsa ...... Jikinta ya fara kyarma ya kai bakin sa kunnen ta
*Kinyi alkawari*..... Tsikar jikin ta ya tashi ta yi baya zata zulle ya maidota da sauri wannan
karon fuskarta ya tallabo kawai taji ya mata *kiss*.............

*Barkan mu da juma'a*
�

*MAMAN ABDULLAHI*😘😘😘
[1/26, 10:04 AM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣2⃣

*INA YABAWA DA KE AKODA YAUSHE 'YAR UWATA , MAI AIKINA KUMA BAIWA TA .
ZALIHA SHEHU SHEMA*( ZALIN 😜)


..... Fiddo duka idanun ta *Na shiga uku* ta fada cikin rai, sumar tsaye tayi yadan ja baya...
Yaushe zaki...... Ta kwasa a guje tabar dakin. Ya bita da wani wahalallen kallo.
Ta zukunna *Ni yau na bani kawai* ta kudundune jikinta tana wata irin kyarma. Data tuna sai ta
tusa kanta cikin cinyoyi ta ce *wayyo Allah* tsikar jikinta *Yarr*
Ta kasa motsi duk ta rikice.
Mamee har sha daya taji shiru ta kirata a waya tana jin ringing ta kara makurewa *ta boye
fuskar ta kamar mamin ce a gabanta* ta ce Wallahi gida zan gudu.
Ta fara bin bango zata gudu mansurah ta hangota laaaahhhh *Uwani* ta kwala mata kira.
Mamee najin haka ta fito taga ko lafiya?
Ba arziki ta koma duk tunanin su lokacin ta zo.
Magana ake mata amma sai sumke sumke takeyi tana kyafta idanu.
Mamee ta rikota uwani lafiyan ki qalau yau?...... Sai kawai ta fashe da kuka ita kanta bata san
kukan ko na menene ba.
Hankalin mamee ya tashi ta jata sukayi daki, tambayar duniya ta kasa magana. Mamin tayi
shiruu zuwa can ta ce *Gida zani bani lafiya*
Uwani baki lafiya kuma zakiyi ta kuka haka? Menene ke damunki? Zazzabi.
Ko dai akaiki asibiti?
A a gida zanje ta durkusa *don Allah mama zanje gida*
Jikin mamee yayi sanyi anya lafiyan uwani qalau? Ta dafa kafadar ta, kiyi hakuri kiyi kalaci
tukun bayan kin sha magani sai ki tafi..... A a zan ci a gida.

Tashi ki tafi amma jira a zubo miki ki tafi dashi.
Duk ta rikice bata son ya dawo tana gidan don taji fitar sa dazun.
Ta wuni daki kwance data tuna sai ta kankame jikin ta.
*Mi hakan yake nufi?* wai ni me ya daukeni? Ta wuni tambayoyi amma ba amsa.
Shi kuwa wuni yayi kamar an mishi bushara a office yau yaba kowa mamaki yanda yake ta
murmushi.
Karfe biyu ya dawo cin abinci yana ta waige waige mamee na dai kallon sa. Mansurah ta fito
ya ce *ke kirawa mamee uwani* yanda yasha mur din yaba mamee dariya amma ta sumke,
Uwani ta tafi gida tun dazun, ya kalli mamee gida, lafiya?
To nidai ta zo mun duk a harmutse yau na kasa gane kanta wai bata lafiya..... Sai kawai ya
kyalkyace da dariya.
Mamee tasha mur kamar da gaske ko kaine ka mata hakin?
Me na mata? Wannan yar taki mamee muguwar bagidajiya ce. Kawai ya haye sama. Guduwa
tayi? Tabb gidan zanje anjima.
Bakauya ta kasa furtawa an bata satar amsa duk tayi failing *Na gaji da wahala*
Kwanciyar ta isheta ana sallame isha'i ta fito zuwa gidan Alhaji yakuba wata kila ta ji dama
dama, ga yunwa bataci wani abin kirki ba.
Tana kunno kai shima yana zuwa daf da kofar , numfashin ta yayi sama
Zata ruga ya kamo hannunta ya hakuri zo muje in baki hakuri na yi laifi.... Ta kankame jikin ta
bani zuwa sakeni *wayyo* yaga da gaske zata rikice mishi ya shigar da ita soron gidan. *ya
daka mata tsawa don ta nutsu* kizo muje inyi magana da ke tafiya zanyi ya fizgi hannunta
kamar ranar da ya kawota farkon layin ya ajiye mota. Suna tafe yana cewa ko agida kike yau zuwa nayi in fiddoki waje. Ta fara kuka,
Yana zuwa ya sakata mota sannan ya zagaya shima ya zauna sai kawai ya tayar da motar ta
kalleshi *Ka rufa man asiri na shiga uku ina zaka kaini?*
Ya kalli agogo yanzu fa bakwai da kwata malama har mu dawo.
Ta durkushe karkashin mota tana kuka don girman Allah ka tsaya, ya ci uban birki. To ki tashi
inyi magana da ke.
Ta zauna,
Umaimah?
Ta kasa amsawa,
Yayi shiru.... Kiyi hakuri da abinda ya faru dazun kada ya dameki kinji?
Ta daga kai,
Ya danyi murmushi to zaki iya ramawa?
Ta kudundune jikin ta,
Kunya kike ji?
Tayi shiru.
Ke ki tashi tambayar ki zanyi naji bana son ki rama na yafe kije can kiji da alkawarinki.
Tambayar ki zanyi saboda Allah zaki bani amsa?
Tayi shiru, ya saisaita murya kamar yanda yake mata magana a da, *Ki zauna sosai ina so ki
fahimceni*
Kina jina?
Ta daga kai,

Kina so in daina takura miki na fita harkarki? Tayi saurin daga kai alamar eh
Yayi murmushi *TO ZAKI AURENI???*
Taji wani tsammmm!
*Ni ina son ki* na lura zakifi gane wannan yaren. Gashi *Na ta ko* har in da kike da *Kokon
barata*
Ya dan karkato *ni umar madaki ina son umaimah*
Ko ban miki ba nayi tsufa da yawa?
Ya koma ya kwanta , kin hanani sakat umaimah tun ina boyewa har na fara *loosing control*
idan naci gaba da shiru *Any thing can happen* ina matukar kaunar ki.
Ya dan waigo malama ki bude baki kiyi man magana. Ta kudundune jikinta kunya kamar ta
narke wurin.
Ya ce *Tabb aiki ja* karki dorawa kanki wahala don yanda na galabaita din nan kin san ina
bukatar kula.
Ko muyi waya anjima?
Tayi saurin daga kai *ohh yauni umaimah ke ma rowar magana* ya fada kamar mace.
To baza ayi wayar ba yanzu zaki ban amsa na miki ko ban miki ba?
Na san dai kwanaki anyi ta labewa ana kallona, rannan kuma na ajiyeki school naga kina
hararar yar kawar ki don mun gaisa.
Kema kuma kinga yanda nakewa maza idan sun koda kalleki, ga dokoki , ya kyalkkyace da
dariya *Umaimah kin kusa haukatani*
Ya dan waigo don Allah kina sona?
Ta daiyi shiru tana murmushi taki yarda ma ta dago kai, ina wayar ki?
Ga ta nan ta fada da kyar.
Zan kiraki anjima ki daga kinji?
Ta ce toh.
Gaskiya bana son tafiya gashi har tara ta kusa, ta daiyi shiru..
Ya kalleta bani number babanki.
Ta fiddo wayar ta sunga mishi, ya harere ta *Ke bani son gidadanci fa* da Allah malama
karanto man.
A hankali take karantowa kadan kadan. Ya ja dogon tsoki wallahi abinda nake gudu kenan tun
farko shi yasa na gwammace muyi ta fadan kamar kaji.
Ya dan kalleta yau saura kwana uku azumi guda nawa zakiyi?
Bata San lokacin data harareshi ba daman idanun sa na kanta, tayi saurin dukewa bata san
yana kallonta ba.
*Kilibabba* malama ki bar wani sunkewa na dade da ganin kaunata a idanun ki.
Wannan kallo haka sai ki sanya dana koma in tada wa mamee zaune tsaye.
An ce man duk CA din ki basuyi kyau ba har 2/20 kike ci.
Tayi murmushi yo turawa ne fa kaji turancin su wani *Rara ra ra ra ra* ya tuntsure da dariya ta
zumburo baki.
Duk turancin da Samuel ke Dan kara miki?
Tabb wallahi ba irin shi sukeyi ba.
To ai kema laifin ki ne kin dage banga me zaki tsinta ba nidai bazan taba barinki kiyi aiki ba,
kawai abinda rai keso.

Tabb ni dai ina so .....ta fada can ciki.
Me kika ce?
Tayi shiru
Yayi dan murmushi kin san dai ban iya jira har ki gama gara ma kisan dabarar da zakiyi wa
mamee don ita kadai zata ban matsala.
Ta dago da sauri *Gaskiya ni dai sai na gama*
Ya yi sa'ar hada ido da ita, *Kin amince kenan zaki aure ni?*
Ta kara dukewa, ya kyalkyace da dariya *ni wallahi ban son gulma*
*Da zaki amince sai naje gidan ku na fada masu zaki kwana a gidana*
Ta dago da sauri *me*?
Ya sha mur ai nasan bazaki amince ba.
Ina wayar ki?
Ta kara fiddo wa,
Ya mika mata sabuwar waya irin tasa *iPhone X8*
Me zanyi da wayar ka? Ta fada a hankali.
Ba ita ba ce kin ga tawa ya fiddo, kawo in mayar miki da *Sim*
Ta mika mishi yayi charaf da hannun.
Ko kiban amsa ko in fizgoki ki dawo nan *sit* din. Kin san karamin aiki nane.
A tsorace ta ce wace amsa?
Ki ce kina sona,
*Nima ina son ka*
Ya saketa yana murmushi ya ci gaba da sanya mata sim din.
Ya duba agogo goma da rabi, ya mika mata wayoyin duka ya ce wannan kya ba wani. Ya
zakulo wata leda wurin kafar sa ga mutumin *ice cream* ta mika hannu na gode.
Naji amma gobe zance zanzo dashi musha tare.
Bata san lokacin da tayi dariya ba .
Ya rike mata suka fito.
Ta fara sauri ya maidota baya *Malama yanga akeyi idan anjera da saurayi ba tafiya buzum
buzum ba*
Kunya ta kamata wallahi madaki ya iya dizgi ta fada a zuci............

*Good morning*

*Maman abdallah*

😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 10:06 AM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣3⃣

........ Luba ta fara barci takai hannu luba tashi.
Ta murtsuke fuska ya akayi?
Ta fara bude leda tashi Musha..... Zumbur tayi, ashe ba ice cream kadai bane hada biscuit

biscuit masu tsada da gasassar kaza.
Ta zaro ido ina kika sameshi?
Don Allah kedai kiyi shiru muci. Ta wuntsilo suna ci suna yar fira.
Ta mika mata tsohuwar wayar ta ungo na baki.
Ta kara fiddo idanu ke umaimah da gaske?
Na taba miki wasa? Allah na bar miki. Amma ina so karki fadawa kowa ga abinda muka ci yau.
Ki debi biscuit din Wanda kike so saura kisa mun jaka ta.
Ta wawusa da sauri kai wallahi na gode. Amma umaimah waya canza miki waya? Zatayi
magana kenan wayar tayi kara.
Ta ce *Ai fa na bani*
Luba ta bita da kallo.
Ta dauka hello. Malama da kika ji shiru ba sai ki kira ba?
Ta yi murmushi, ina gun baba ne zan kira. Kawai ta kashe.
Luba ta bita da kallo *Wanene*? Ke kyale shi ni nasan ma ko waye?
Madaki kuwa ya bi wayar sa da kallo cike da takaici *Haka zamuyi da yarinyar nan*? Ya mike
tsaye *ni zata jama aji?*
Yana kira yaji wayar a kashe.
Kasusuwan luba taje can kasan bola ta tusa ledar. Sukayi kwanciyar su da kyar umaimah ta
sami barci ya sace ta.
Zullumin zuwa gidan kawai takeyi, salon soyayyar madaki na bata tsoro gaskiya.
Shi kuwa tunda ya tashi yake faman zarya mamee na kula dashi tayi kamar bata san yanayi
ba ko kalaci yakiyi gashi sai waya ake mishi office yaki tafiya.
Ransa ya baci matuka, ya zauna tare da dafe kai yayi shiru.... Goma saura ta shigo yana
ganin ta ya mike kawai yayi sama.
Ta gayar da mamee tana ta sunne kai ta wuce ciki. Ta bita ta ido tana 'yar dariya *Wannan
soyayya ni dai an mini kancal*
Ya sauko yana ta fushi mamee sai na dawo..... Ta kalleshi *Kalacin fa ko zaka aiko?* na koshi
ya wuce, ta bishi da kallo.
Koda umaimah ta gama yan gyare gyaren ta sai tayi baya gurin su mansura.
Har ta tafi bai dawo ba.
Da daddare taci gayu ta ce zata je gidan Alhaji yakuba amma tayi tsaye zaure tana jiransa
amma shiru ta fita waje tafi kusan awa daya amma bashi.
Duk sai ta shiga damuwa ta kwanta sukuku,
Washe gari karfe shidda yabar gidan, mamee ta rutsata daki tana janta da labari har ta dan
saki.
Ni uwani kwanakin nan duk bana jin dadin yanda nake ganin ki ko kin fara gajiya dani?
A a mamah ta fada tana yar dariya,
Allah kuwa, sai nake gane kamar kin gaji dani in ba haka bane to ki saki jikin ki kamar farko. Kin
ji ko?
Ta ce toh, tana murmushi,
Ta danyi shiru, uwani na daukeki tamkar 'yar da na haifa don haka ki saki jikin ki kada abinda ya
shiga tsakanina da ke kinji?
Ta ce toh,

Idan kika ga mutum ya bata rai da ke ko ya ce kin mishi laifi kada kiyi girman kai ki bashi hakuri
kinji?
Ta ce toh mamah kiyi hakuri. Tayi murmushi bani ba ina nufin abokan zama kinji? Ta ce toh.
Lallai mamee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0