Showing 24001 words to 27000 words out of 63115 words

Chapter 9 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

duk abinda kike so zan kishi
ne mamee?
Yau kuma? Ta bukata tana ci gaba da kallon sa.
Ya dafa kafadarta mamee *I mean it please* bacin amincewa ma hada shawara na bayar.
Ta fara shi mishi albarka yayi sokoko yana kallon ta yanda ta dage tana nuna tsantsar farin
ciki. A zuciyar sa kuwa kagare yake gobe ta yi yaga kalar murnar da umaima zata yi idan taji ya
amince. Don wacce ta yi marar dalili ce yayi murmushi. *Gobe zata yi mai dalilin kam* daga ni
sai ita bata taba mun dariya ba ko ta mugunta kuwa, sai dai na gani a sace ita da mamee shima
tana ganina zata gintse... Yaja guntun tsoki.
Su goggo nata shagalin nama umaimah na daki ta makure, ohh ni umaimah na shiga uku da
wannan mutume.
Tsikar jikinta ta kara tashi *yarrrrrrrr* tana hasko ta bisa jikin sa kwance, ta kudundune kai a
cinya lokacin da amon muryarsa yazo mata, *am very sorry kiyi hakuri* yau ni madaki ke ba
hakuri. Ya ce yana so mu daina fada gashi a gaban mamee ya mun abinda bai taba ba, ko ya
daina jin tsoron ta? Jikinta ya kara sanyi ta tuno sungumar da yayi mata ya kaita sama, *ohh ni ina na kai kaina ni
marainiyar Allah*
Ta dago kai, nima ina so mu daina fada, idan ba masifa yakeyi ba muryar sa na da dadin
sauraro, yana da masifar kyau gashi dan gayu, da yawa ina son kallon sa amma ina tsoro.
Jijiyoyinta suka kara tsinkewa da ta tuno shi zukunne gabanta yana magana a tausashe. *ohh
ni umaimah* mai kudi kamar *madaki* ta ce *Hmmmm*
Haka ta susuce ta kwana tunanin sa. Ta kagara gari ya waye, daren yayi mata tsawo juyi kawai
takeyi.
Karfe uku yau ta yi wanke wanke da duk abinda ta saba, lokacin da aka kira sallah tana shafa
mai har tayi wanka,
Ta yi tagumi gaban jakar kayanta, wane zan saka?
Ta fiddo wannan ta mayar, sai da ta kare kaf, ta yi tsoki tafi mintuna ashirin da a haka, da kyar
ta amince da wata atamfa roba wacce ta siyo dari tara lokacin bikin *Asma'u* dinkin riga da skirt
ba kwalliya amma kayan na mata kyau. Ta rangada kwalliya saboda gwana ce sosai
karambanin ta yasa ta iya kwalliya sosai da daurin kallabi, idan ana sabga ita ke wa mutane da
dama. Abinda ke hanata yi karancin kayan shafan.
Ba ta hauka tayi ba, bayan ta gyara gira yar hoda kawai ta shafa da dan Jan baki sai kuwa
kwalli data zizara, abinka da ba sabanba umaimah ta yi wani fayau.
Shidda da rabi tabar gidan, bakwai da kwata ta isa.
A gurguje ta gama aikin ta baro mamee ciki ta dawo falo. Kadan kadan ta kalli sama shiru bai
sauko ba, tayi zugumm!!!! Haka kawai yau ganin sa take son yi.
Mamee ta fito uwani shirya mana break yunwa ta gargado ni, ta tashi da hanzari, tanayi tana

waige amma shiru bai sauko ba,
Mamee na zama ta dauko flask kenan zata zuba ruwan zafi ya fito *a slow motion* ta rinka
ganin takun sa, sanye yake cikin wani farin boyel mai zanen kwallo kwallo ya kashe hula har
goshi kansa sunkuye yana faman daura agogo duk falon ya dauka da kamshin turaren sa.
Kirjin ta ya shiga harbawa ta fara yar kyarma ta sunkuyar da kai tana zuba ruwan zafin,
Idanun sa yakai kanta har ya iso bai daina kallonta ba ita kuma taki dagowa,
*Morning mamee! Ina sauri zanje office for an urgent meeting*
A aika mun da break by 11:30am.
Ta dago da sauri har ya kusa kai kofa. Wani abu ya tuko mata,
*Allah ya bada sa'a* inji mamee
Daga can waje ya ce amin ya kara gaba.
Na shiga uku wai me ke damuna?
Ke lafiya?
Ta yi firgigi,
Menene? Ta kara Bukata,
Ta danyi *pretending* cikina ya dan katsa, ta sa hannuwa a cikin.
Yunwa ce maza hada kalaci, ta tsareta. Haka nan take cusawa amma Sam ko dandano bata ji.
Ta fada mata zata fara *lesson ** daga litinin din nan. Ta danyi murna mamin bata damuba
tunanin ta ko cikin ne ya dameta.
Shiru shiru har Biyar da rabi bai dawo ba, hankalin umaimah ya tashi *kadai fa son madaki
nake na shiga uku?*
Ta dauko kayanta ta yi sallama, tana Jan kofa yana budewa yayi Saurin rabewa jikin bango ya
bata wuri alamar ta wuce fuskar sa ba yabo ba fallasa. Ta dan kalleshi kadan ta wuce,
Ta na bada baya, ya bita da kallo kamar ya janyo ta amma ya sha alwashin daga mata kafa
har sai zuciyarta ta dan saki dashi sannan yana gudun kada ya takura mata ta botsare ta ce
karatun ma bata so. Wannan shine rashin sani....
Ta dan waigo har ya turo kofa.
Na shiga uku ya fita harka ta?
Ta juya sukuku.
Abu kamar wasa ya ma rage zama gidan, kullum sai ya ce a bishi da kalaci, abin ya dameshi
amma ya daure, musamman da yaji ta fara lesson. Ga umaimah kuwa ta gama rikicewa, yanzu
labewa ta keyi tana kallon sa ba tare da ya sani ba, wani karin takaici da ya hau sama ya ganta
tana gyara sai ya koma falon mamee. Haka zata leko shi tayi ta kallo, Umaimah fa hada yan kwalla ta rasa in da zata sa kanta mamee tayi tambayar duniya amma
tayi shiru har ta sa mata ido.
Har an yi sati a haka duk susuce, ya dan fara zama akai akai. Amma ba abinda ke hada shi
da ita.
Bayan kwana biyu yana zaune falo shida mamee suna magana, ta koma can gefe ta tsare shi
da ido yana cikin magana ya dan waiga ya hangota ta glass. Gaban sa ya fadi ya kalla sosai shi
din take kallo.
Tun daga ranar sai ya sa mata ido aikuwa ya gano irin kallon kurullar da ta keyi mishi a boye.
A gajiye ya dawo aiki, tana sama tana mishi gyara, koda taji shigowar sa ta watsar da gyaran
ta rugo tare da lafewa in da take boyewa, yana kallon ta don yanzu duk wani maboya nata ya

sani, suna ta labari da mamee tana ta lekowa tana kallon sa da taga zai juyo sai ta koma,
Ta koma kenan ya tashi yayi saman tana lekowa zata kalla ......kwatsam taga mutum
gabanta......

*godiya ta musamman ga*:-
1. Agamcy
2. Rahama nahaja
3. Maryam Yusuf.

*MAMAN ABDALLAH*

😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/25, 7:39 PM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣7⃣

....... Ta tsorata matuka, ga wata masifaffiyar kunya data addabeta.
Ya sha mur, wa kike leke?
Ta yi dabur dabur..... Ta dan ja baya, ya bita, ta kara baya ya bita, table ya to kareta ta yi baya
zata fadi ya tallobota abinda yake so kenan, ta koma jikin sa da karfi ya mata wani riko,
Wa kike leke ina tambayar ki?
Ta daddage ta cije cikin karfin hali ta motsa jikin ta amma rikon da yayi mata bata iya ko taki
daya sai ma ya kara hada ta da kirjin sa sosai, Allah sai kinyi magana zan kyaleki, waye kike
leke?
Ta dago kadan amma ta kasa kallon fuskar sa, ta saki harara *yo ni kai nake kallo*?
Na ce kina kallo nane?
Leken me kikeyi?
Malam ni ba leke nake ba zan dauko bokiti ne na taho na ganka gaba na.
Duk nan sama ba bucket sai kin sauka?
Jiya fa da zan fita wacece na hango bayan labule tana kunno kai???...... Kirjin ta ya harba da
Sauri na shiga uku, idan ina magana da mamee sai ki koma bayana kina mun kallon kurulla ko
shima duk zaki dauko bucket ne?
Cikin ta ya kada, lallai ya gano ni, sai gara in nannade kunyar nan da hauka.
Ta tattakura ta ingijeshi yayi taga taga....
Idan kai baka kalleni ba ta yaya zaka San ina kallon ka?
Allah ya sawake ni banga abin kallo jikin ka ba, wata kila kuma kallon tausayi nake ma babban
mutum kamar ka amma kullum ka tsaya *sa'in sa* da diyar cikin ka, ka kasa fita harka ta........
Shut up.
Ya hayayyako mata karya kikeyi wallahi kallo na kikeyi kullum ina lura dake, shekaran jiya da
kika fita da gudu kika boye bayan flowers kina lekena zan fita ko shima duk tausayin ne?
Ya fizgo hannuwan ta ya rike gam, idan kina da wani abu a ranki ki fidda *kada ki jefa kanki ga
wahala, masifa, da tashin hankali*....... Gaban ta yayi wani mummunan faduwa na shiga uku.
Duk illahirin jijiyoyin jikin ta suka saki.

Ke 'yar abun nan har kin isa kiji tausayi na?
Yanzu dai cika ni!.ta fada a sanyaye.
Ya kalleta sosai shima sai jikin sa yayi sanyi,
Ranta yayi mugun baci gashi yana gani a fuskarta amma ta kasa magana.
....bazan cika ki din ba ki kwaci kanki idan kina da karfi.... Sai kawai tasa mishi kuka.
Ya tsare ta da ido shi kadai yasan azabar da kukan ta ke haddasa mishi.
Ya ci gaba da kallon ta jira kawai yake ta motsa zata gudu ya rungumeta.
Yaga dai bata da halin motsawa ya cire bandir din dubu dari aljihun sa ya birkito tafin hannun
ta ya saka *ga cikon kudin ki da albashin ki*
Yana dorawa ya saketa, tayi kasa da gudu, ta fada toilet din falon don ta gyara fuskarta.
Ya bita da kallo, *Wai ita din nan ta iya boye abu a rai* mtseww yayi tsoki.
Zukunne tayi ta dora hannu a ka *na shiga uku ni umaimah* sai kuka.
Sai da tayi mai isarta tukun ta wanke fuskar ta tafito.
Har lokacin yana inda ta barshi, tana fitowa ya gangaro da sauri, ita kuma tana ganin sa tayi
ciki da gudu.
*Au na kuma yin laifi?* turkashi sai kawai ya koma sama cikin damuwa.
Mamee na baya, sai kawai tayi kwance bisa gado. *kada ki jefa kanki ga wahala, masifa, da
tashin hankali* maganar sa ke dawo mata ta mata amsa kuwwa.
Har yaushe ni umaimah? Ai na gama janyowa kaina duk abinda ka zayyano.
Ta tashi zaune, waya aikeni? Wannan wace irin masifa ce?
Da kwalla sun taho sai ta hadiye. Zuciyarta tayi mata nauyi. Qalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Ta daga hannu sama *ya Allah kada ka jarabeni da wannan masifa. Allah ka tausaya mun ba
don halina da maraicina ba sai don darajar annabin ka SAW*
Kwalla suka shatato mata. Tayi saurin gogewa ta tafi kewaye tayo alwala kawai sai ta hau
kwalliya kada mamee ta gane taci kuka.
*Madaki* kuwa yana hawa sama ya fada wanka shirin kananan kaya yayi .
(Basai na misalta ba kun San dai ruwan designers ne ).
Shiri yakeyi yana Sabbatu. Na gaji da rigimar yarinyar nan *Wallahi so na ta keyi* amma
Girman kan ta zai wahalar da zukatan mu. Ko kuwa ni zan ce ina son ta don ta daukeni
sakarai?
Ni da zata furta sai in fake ta nan koda tana kawo man raini in ce taimakon ta nayi. Amma ina
bada kaina gareta wallahi *sunana sorry*
Yayi guntun tsaki *ina!!! This will never happened*
Yana gama salla ya zo ya zauna yana barazanar karatun jarida.
Biyar da rabi ta wuce ta fito, hannunta cikin hijab ta rungumo kudin da ya bata cikin bakar ledar
data saka su. Har lokacin mamee na baya gun yan aiki.
Ya bita da kallo, tana fita ya mike yabi bayanta.
*Ke tsaya*!
Ta yi chak ba tare da ta juyo ba ya sha gabanta.
Meye kike kuminiya dashi cikin hijab?
*ko ya fara mun zargin sata?* ta dago da sauri tare da fiddo kudin ta warware ranta a bace.
*kudin da kaban ne* ko kana tunanin ina sata ne?
Ya zaro ido....... Ta daga mishi hannu, billahil azim ban taba daukar abin wani....... Shut up joo...

Ke me yasa kin fiye fassara mun magana bai bai? Daga tambaya, ai nasan kudin ne ..... Au
kasan ma sune ka biyo neman magana?
Ke malama taimaka miki zanyi in kaiki gida ko kina tunanin duk da wannan kuminiyar da kikeyi
dasu cikin jikin ki baza'a gane kudi bane? Kin San hadarin tafiya da su a haka?
Ina abinda ya dameka? Koma menene ni kai sama ba kaiba meye zai dameka?.....
Ya cumumiyo ta dole ya dameni mana saboda......yayi saurin kulle bakin sa.
Taja baya da sauri, kar ka kuskura ka kara taba ni zan..... Me zakiyi ya fizgota. Ka duba ka
hango yanda masu tsaronka ke kallan mu.... Ya waiga da sauri tare da sakinta, karki kara zuwa
gidan nan ba jaka daga yau.
Ta balls mishi harara wani mugun haushin sa takeji, a da ina da niyyar siyan ta amma wannan
dokar taka yasa na fasa. Kawai ta juya ta tafi.
Ya nufi bakar jeep din sa da sauri ya tayar, body guards dinsa na ganin haka suka shiga tasu
ya daga masu hannu alamar kar Wanda ya biyo shi.
Ta na ta sauri har an fara Koran sallah yasha gabanta,
Shigo in taimaka miki in ajiyeki gida.
Bana son taimakon ko Kaine ..... Ya fito da sauri ya fizgi hannun ta yayi mota, ta tokare bafa zan
shiga motar ka ba malam... Kawai ya sungumeta yayi ciki ya datse sannan ya zagaya.
Kin fiye taurin kan tsiya ya fada tare da zama, an ce za a taimakeki.... Yau naga ikon Allah na
ce bana son taimakon ana dole ne?
Kwarai kuwa gashi an miki?
Ya fada tare da kallon ta yana harara.
Ta yi mishi banza.
Tuki yakeyi amma hankalin sa na kanta.
Duk ta hasala tun dazun, ko baya lokacin ma da suke fitinar gadan gadan yanayin fuskarta baya
canzawa haka.
Sai wani fushi kikeyi kina turo baki an fada miki gaskiya, bari a kyaleki kiyi *mussai*...... Ya
rama fadin kalmar da tayi mishi baya.
Kan ka akeji dai.
Ta fada.
Me kika ce? Ban sani ba ta fada tana murguda baki.
Kilibabba, dadi ya gama wulakanta ki kin shiga *motar madaki* amma saboda feleke har.........
Allah ya tsareni ai ni napep ko mashin ya fiye mun sau dubu da wannan motar, ya dauko waya,
*hello,..... Yeah fine,.... Okay .... Yeah only 10-15 minutes no only .... Thanks*
Ta tabe baki *yeah* ta kwaikwayeshi ba tare da ya gani ba sannan ta banka mishi harara.
Ya kashe tare da juyowa *ke me kike fada*...Sai naji zafin makara in maimaita...
Ya ci wani uban birki, ta kankame jikin ta tasan *shaka ce* Sai taga ya bude ya fita.
Ya zagayo in da take ya bude, fito mu je....... Ta kwalalo ido *na rantse da Allah kana tabani
zan kwarara maka ihu* ko ka kaini gida ko....ya maida kofar ya rufe Sai yayi locking din ta kawai
ya wuce, tabi wurin da kallo. Taga an rubuta, *shop rite*
Gidan uwar wa ya kawo ni na bani?
Yana nufin Sai ya karaci gantalin sa zai mayar dani gida?
Wannan salon wulakanci da me yayi kama anya mutumen nan bai gama karto ni ba? Allah ya
karto ni gashi abinda yace dani.

Idanun ta suka kawo kwalla *Tawa ta sameni ni umaimah*
Dole in danne zuciyata ko zan mutu....
Duk layin jikunan ba kowa saboda wayar da yayi aka dauko mishi designers kala kala ya ce
wacece *latest?*
Haka aka zabo mishi ta *N250k golden brown* ya biya. Sannan yasa aka kawo mishi katon
bokitin ice cream ya fito yaron na dauke dasu.
Burun taji ya shigo har ta dan tsorata tayi zumbur,
Ya kalleta *ke ar can matsoraciya*
Ya bude bayan motar aka saka.
Ya dankwashi kanta *ke me yasa baki iya sannu ba?* Ta Dalla mishi harara, wai kai idan
hannun ka bai taba jiki na ba baka jin dadi ne?
Kwarai kuwa, kin san ni ko ina yaro bani da abokin fada yanzu da na sameki ne abun ke mun
dadi.
Ta yi mishi banza.
Sannun bazata samu bane?
Eh ta fada rai a bace, ko aiken ka nayi?
Ya girgiza kai ko daya.
Nesa da layin gidan su ya ajiyeta ta kalleshi cike da takaici zata yi magana saboda mashin ko
napep har bakin kofa,.... Ya ce idan na shiga da motar nan akaga kin fito za a tuhumeki a fara
miki surutai ko in karasa?
Ta yi shiru... Tabbas haka ne.
Ta bude kofar taji gam ta yi saurin kallon sa.
Ai ban gama ba ya sa hannu ya janyo jakar, idan kinayi wa Allah karbi jakar nan ba don ni ba
*for your safety*
Ta dan harareshi menene safety?
*ki tambayi Samuel*
Kamar bazata karba ba sai kuma ta sa hannuta fizge.
Ya kalleta kawai ya basar don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0