Showing 45001 words to 48000 words out of 63115 words
malam bawa mamaki shine yanda *Madaki*
ya saki jiki bai nuna wata kyama ba ko shimfida akayi mishi sai ya yaye ya zauna yanda kowa
ya zauna, babu Wanda baiba girma ba. Wannan abu ya wa malam bawa dadi a rai. Hatta
kananan yara sai da ya raba musu kudi.
Shi kuma duk gidan da suka je sai an basu ko gero ko wake, haka suka dawo da tumbaye
ransa sayau, Yayi yayi malam bawa yabar tumbayen abincin nan amma yakiya.
Hakan ya kara sanyaya zuciyar Madaki kaunar umaimah da tausayin iyayenta ya karu cikin
ransa.
Karfe biyu da rabi ya isa gida suna zaune falo mamee taga ana shigowa da yan buhunna , ya
shigo mamee ta kalleshi duk ya gaji..... Daga ina haka?
Ya zauna wash!
Sannu da zuwa, umaimah ta ce dashi tana satar kallon mamee.
Yawwa my dear ya gida?
Sannu da gida mamee love.... Kai ban son iyashege kaji ko.
Ya tuntsure da dariya umaimah dai tayi ciki.
Ya bita da kallo *Ke dawo*....... Amma ina ta shige.
Ya kalli mamee yarinyar can dole inyi maganin ta ta raina ni,
Naji, ina ka tafi ko wayar ka ba a samu ka shigo da wasu yan buhunna kamar Wanda yaci
kasuwar kauye..... Kin canko dai dai.
Kauye naje mamee.... Kauye?
Wallahi kuwa ya bata labari kaf!
Ta rike baki Allah sarki, wayyo Allah kai masha Allah wadannan mutane sunyi bazata..
Kwarai kuwa.
Gobe zan tafi Abuja zamuyi magana dasu baba Ibrahim muji me zasu ce. Sai in biya Kaduna
...... A a ka bari zan fa da ma su yaya.
Ya dauki waya yawwa kaga missed call dina ko?,......okay ka ganshi? To passport nake so
latest jibi don na gama magana da embassy..... Ya kashe.
Me zakayi da passport?
Na umaimah ne umara zaku tafi kuyo mana addu'a kafin ku dawo na gama wasu gyare gyare.
Don Allah? Kai masha Allah.
Amma naso ka bari sai karshe...... Mamee kuyi hakuri bana so kuyi sallah can saboda daurin
aure ya mike. A ajiye mun kayana kada a taba mun,
Ka fada mata?
Kiyi shiru sai zaku tafi.... Kai ban son shirme komai ayi shiru komai ayi shiru to sai na fada mata.
Ya haye sama kunfi kusa..
Sallah kawai yayi ya kwanta barci.
A saman yasha ruwa cook din sa ya hada mishi tea da sandwich.
Umaimah taji shiru har ta dawo asham amma bai sauko ba ga mamee zaune tana kunyar ta
kirashi sai kawai ta tura mishi text.
*I know for sure that you are my life, Since the time you have left today ,i feel so blue and
nothing interests me, i think you have taken a part of me ,And I really can't survive without you
..I love you and I miss you , You should know that I truly do ,Please come down soon!* Ya maida
mata amsa *When I say thank you, I mean it from my heart, Dear you helped me achieve so
much, You were there from the start, A heartfelt thank you to you, am coming dearest*
Bata karasa karantawa ba ta hango shi yana saukowa, ya sha wanka cikin kana nan kaya *Kai
madaki nada kyau* suka hada ido ya sakar mata wani narkakken murmushi ta mayar mishi tare
da sunkuyar da kai.
Mamee na lura da ita, sai tayi kamar bata ganshi ba ta mike uwani idan kin gama kallon kya
kashe ni kam na gaji...... Mamee barka da shan ruwa ina zuwa kuma?
Au ka sauko? Barkan mu juna, zan dan kwanta ne na gaji.
Yayi murmushi kawai.
Tana wucewa ya ce matso malama ki fassara mun text din ki.
Ta danyi murmushi kawai, ansha ruwa lafiya?
Qalau,
Me kika rage mun?
Kosai.....
Ya kyalkyace da dariya wallahi banci, sai me?
Dan na rogo....
Ya fara dariya.
Ta tashi ta dauko mishi yanballs da samosa, sai dan juice din ta na kwakwa da fresh Ginger,
mamee ta ce kafi son mai dan nama nama gashi idan zaka iya ci don kai nayi.
Ki ce Allah!
Allah kuwa,
Ya janyo cooler iyye yarinyar nan fa zatayi *Caring*
Ta ce hmmmm
Ya fara ci yana Santi
Cewa zakiyi nabar banza na tsaya cin sandwich saboda kiwa.
Gaskiya.
Ya dan zaro wani abu gaban aljihun sa kawo hannun ki in baki tukuici.
Ta mika mishi, ya zo zai kama tayi baya dashi da sauri tare da 6ata rai, wallahi kaga abinda na
tsana a tare dakai.
Ohh am sorry please. Ya kamata ka fidda wannan muguwa tabi'ar a ranka gaskiya domin
wallahi haramun ne,...... I said sorry woo..
Yeah I know but let me tell you, ka fidda fashion a maganar nan ka sanya addini, taba mace
baliga haramun ne , me yasa namiji baligi ko baliga idan sukayi alwala akace shafa ko babu
sha'awa alwalar ta warware?
Addini fa sauki gareshi wallahi ko musulman mu dake zuwa kasashen turawa suna gaisawa
dasu bala'i suke daukar ma Kansu.
Haka ma khausar a school sai da na mata magana ita da kawayen ta kawai kana zaune kato
zaizo ya kai hannu ya dafa ka ko ya kai duka wai abobota.
Ya kamata ka daina bana so na fada ma da arziki, na fada ma cikin fushi to yanzu na fada ma
a addinance wallahi next bazatayi mana kyau ba.
Wallahi na daina kiyi hakuri ungo zobe ne zan saka miki amma saka da kanki Allah ya bada
hakuri ustaziya ta.
Ta yi murmushi.
Shi yasa na ce wa mamee kuje umara tare kiyo mana addu'a kinga sai ki rungumi ka'aba ki
Rokan mun Allah ya yaye man wannan hali.......
Umara?
In shaa Allah.
Jirgi zan hau?
Ya kyalkyace da dariya a'a bisa keke zaku tafi.
Itama ta yi dariyar.
Na gode Allah ya kara arziki.
Aminnnnn my love.
Yau fa da wuri zan kwanta bazanyi kwanan zaune ba.
Ya langabe kiyi hakuri mana haba don Allah.
Okay naji sha daya nayi zanje in kwanta.
A a na yarda sha biyu dai.
Zatayi magana ya canza da cewa,
Don Allah kiyi mana dawafi Allah ya tabbatar mana da alkhairin aure na dake, sharrin da ke
tare dashi Allah ya karemu kinji.
Banda kai za a tafi?
Gaskiya,
Ta bata fuska, dalili
Akwai abubuwan da zanyi ne kafin ku dawo, yanzu haka ma Gobe Abuja zan tafi.
Kai baka jin azumi?
Ko ina ji ya zanyi mai nema ai baya kwanciya umaimah baki ganin ni maraya ne.
Ta balla mishi harara in kaji maraya raggo.
Ka ma gode ma Allah kai kana da mamee ni kuma fa..... Ke kuma kina da *Madaki*
Hummm
Ko baki sona?
Ni kuwa ke son ka....... Ta yi saurin tsuke baki,
Don Allah karasa tawan.
Hahahhaah kaji abinda kaji.
Kedai bakauya ce wallahi.
Naji wayayye.
Ina so in tambayeki, a tsarin gida wannan ya miki?
Ta kalleshi, ban gane ba.
Ina nufin idan munyi aure zaki zauna anan nida ke muna sama mamee na nan..... Yau na shiga
uku ta fada tana tafa hannuwa.
Don Allah ka rufa man asiri ni wace amsa zan baka?
Zai kara magana ta daga mishi hannu nidai canza magana baka da amsar wannan.
Yayi murmushi. To kina iya mun list na abinda kike so batun lefe nake da kamar irin kayan
kitchen,....... Ta mike yau firar taka duk kame kame kakeyi sai da safe..... Yayi saurin tarar ta, ya
hakuri ki dawo wasa nake.
Ta koma tana hararar sa,
Yayi murmushi, ke yanzu baki iya fada man abinda kike bukata umaimah?
Kinji?
To wai me nake bukata saboda Allah, a hakan ma na gode Allah ya kara arziki.
Ko muyi chatting?
Hummm,
Kinji?
Ohh ni! Ta fada,
Kiyi hakuri mana.
Kaini fa bani bukatar komai.
To takalma fa kina son masu tsini?
Ta mike wallahi kaga tafiya ta yau firar taka tafi karfi na,
Yana tunkurawa tayi ciki da gudu...............
*Ayi hakuri da kadan*í ½í¸ƒí ½í¸ƒí ½í¸ƒí ½í±†í ¼í¿¼
*Maman Abdallah taku ce*í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜
[1/27, 7:43 AM] +234 806 091 7227: í ½í²‘ *AUREN FARI* í ½í²‘
0⃣2⃣9⃣
......ya yi murmushi, lallai kina da kawaici da zurfin ciki.
Washe gari ya tafi Abuja.
Yaya kuwa mamee na kiranta tafada mata sai ta hau zage zage wai har yaushe madakin ya
sami mata ba a fada mata ba sai da aure yazo?
Bakin ciki da bacin rai ya taso mata, bata taba tunanin zai yi aure haka da wuri ba amma ga
mamee ita hakan ma ya jima.
Abinda su yaya keso ko motsi mamee zatayi ta sanar dasu, sannan basa iya tsinana mata
komai sai magana da gulma.
Ga hassada, ita hassada mutane basu gane ba, ciwo ce, uwa daya uba daya ana hassada.
Kawai sai dai addu'a Allah ya raba mu da kullihin musulmi da ita.
Yana dawowa bayan an sha ruwa ya ce umaimah ta shirya zai kaita gida suyi bankwana .
Jikin ta yayi sanyi.
Suna fita ya kalleta ko dai bakya son zuwa?
Me ka gani?
Duk kin wani darare,
Ta ce hummm,
Kar ki damu kedai kiyo mana addu'a tare da iyayen mu.
Wai kina ma su addu'a ma kuwa?
Tayi yar dariya kwarai kuwa.
Babana fa?
Hada shi.
Ki ce Allah.
Tayi dariya .
Yau ma anan zaka tsaya? , ya gyara parking gaskiya, kinsan manzon Allah SAW ya ce idan
alheri ya sameku to ku boyeshi har sai idan ya bayyana.
Ita kadai ta tafi ya zauna yana jiranta a mota,
Sallama tayi duk suka mike ana tsallen zuwan ta, yau ita ce hada dauko kujera wai ta zauna.
Dariya tayi kawai ta raba bakin tabarma. Ta kasa boye mamakin ta. Bayan sun gaisa ta fada
ma su abinda ya kawo ta kowa ya fara tsalle ana bata saftu.
Su goggo ta ciki na ciki, amma basu nuna mata ba.
Har zata tafi luba ta ce wai umaimah wanene angon?
Ango? Ta bukata,
Goggo ta dan dungureta ke ban son surutu...... A a goggo kuma fa kuna taso kusan wanene.
Ban gane ba luba.
Jiya wanene yazo wurin baba aka kaishi kauye gaida iyaye?
Gabanta ya fadi, ta tuno dawowar madaki da yan buhunna.
Uhummm kawai ta ce ta tafi.
Tana fita goggo ta ce da luba bita kigano mana ko wanene watakila mai gadin gidan ko direba
ne ta samu, don duk yanda akayi jikin gidan shima yake yanda naga malam nata fachaka.
Ta dawo da sauri anya ita kadai take tama shiga gidan Alhaji yakuba.
Duk suka tabe baki.
Sauri sauri ta tarar dashi ya dan kishingida yana jin gwanja.
Ko zama batayi ba ta ce, jiya kauye kuka je?
Duk da yaji faduwar gaba kuma bai san abinda aka fada mata gidan ba sai kawai ya wayance.
Eh, ina ta so in fada miki kinga na manta.
Jiya na je na sami baba akan ina neman izinin fara nemanki da aure ma'ana ( zance ) kamar
yanda addini ya tanadar kada suji wai wai a dauka ko na raina su or something like that, shi ne
ya ban shawarar in sami lokaci muje kauye na gaida kowa tunda shima yana da na gaba dashi.
A jiyan am free so nayi amfani da daman na ce muje kawai ko nayi laifi?
Tayi murmushi ko daya.
Ya tayar da mota, when last kika je kauye?
Tayi yar dariya gaskiya mun dade.
Shi yasa jiyan akayi ta mamaki wai har kinyi girman da zakiyi aure?
Tayi dariya kawai.
Maimakon gida ya wuce suka siyo ice cream suna tafe suna sha.
Zaki sha ice cream saudiyya mai dadi, ta danyi murmushi kawai.
Me zaki siyo mun tsaraba?
Duk abinda kake so,
A a kawai dai kiyo mun tsaraba da choice naki.
Okay I'll try my best.
Yayi murmushi ya janyo wata leda ungo ga guzurin ki kuyi amfani da dollars sunfi dadin
harka.....
A a duk ka hada kabawa mamee idan ina bukata zan karba wurinta.
Ya kalleta da kyau. *Why*?, nake ga hakan zaifi.
To ai itama ga nata nan ya fiddo wata ledar, ta danyi yar dariya yawwa to hade mana wuri daya
duk ka bata.......ke ban son rashin wayewa malama.
Ta dan harareshi Kaine ba kauye don Wanda ya waye baya gardama kai kuwa kullum sai anyi
musu da kai.
Ya ma rasa me zai ce mata?
Kamar ya janyota ya rungume amma ba hali. Ya dan lumshe ido, Alhamdulillah wani jinkirin
alkhairi ne tabbas Allah ya karbi rokona.
Ya dan kalleta,
Umaimah duk umara ko hajjin da zance wallahi addu'ata ya Allah ya bani mace ta gari wacce
zata soni ta kauna ceni badon kudi ko kyawuna ba, sannan yasa ta so mahaifiyata kamar yanda
nake sonta, ta tausaya mata fiye da yanda nake tausayinta.
Ta danyi murmushi, kaima da wata magana, su iyaye ai na kowa ne, wallahi ko na sona ko
baka sona mamee ta dauketa tamkar mahaifiyata, bata kyamace ni ba, bata taba zargina ko
guduna da duk wani abu nata ba, ta dauki yardar duniya ta dora mun ta yaya zan taba gudunta
ko wani abu ya nemi hadani da ita,? Wallahi ko a lokacin da bama jituwa idan bala'in yayi bala'i naso guduwa sai in tuna yanda ta
amince mun sai na gwammace in hakura da takurawar taka in mata halacci.
Ya runtse ido tare da danna hon....masu gadi suka rugo ya shige da motar,
Na ga irin kulawar da kike bata, naga yanda kuke son junan Ku umaimah wallahi nima na
yarda dake 100%, kuma ban taba zargin ki ba.
Ya kashe mota lokacin da kike mun gyaran daki baki ga kudade ba?
Na gani wallahi.
Ya juya ya kalleta sosai, wallahi ko buhun kudi na ajiye aka taba ina ganewa, lokacin da na
kunna CCTV ina kallon yanda kike kara gyara man kudin hankalina ya tashi domin Wanda duk
kika San ya shiga dakin nan wallahi sai an mun sata, shi yasa na hana kowa.
You are different umaimah, cikin dubu da kyar za a sami goma irinki.
I love you with all my heart, ni kadai nadan yanda nake feeling, ta danyi murmushi ko? Ni ma
haka.
Suka fito tare da jerawa, yana fada mata yanda ya kagara ta zama matar shi. Sai dai tayi
murmushi ta ce *Uhumm*
Mamee na kishin gide falo suka shigo hannuwan sa da ledijin kudin su, ita kuma da dan kingin
ice cream,
Cewa zakuyi kwadayi kuka biya shi yasa naji shiru. Mamee ta fada tana ta kokarin tashi zaune,
Ya dan zauna umaimah kuma ta tafi can kusa da ita, gashi ma na rago miki nayi nayi ya siyo
dake yace a a.
Ya zaro ido ke.....
Mamee ta karba tare da hararar sa na sani uwani nasan babu yanda zaki mance dani.
Ta yi mishi gwalo, mamee na satar kallonta.
Ya nunata da yatsa nafiki iyawa yarinya.
Mamee ta ce kwarai kuwa ka fita iya rowa.
Suka yi dariya ita da umaimah ya sha mur ni zaku hade ma kai?
Ta kama kunne sowie wasa ne ko mamee?
Shi yasan hakan ne,
Ya kyalkyace da dariya dole aban hakuri........ Ohhh son girma kamar maruru!!
Me umaimah zatayi ba dariya ba kaii mamee wai maruru.
Ya mika mata ledojin kudin ga guzurunku, kince kowa na ware mishi gata nan taki karba tace
sai dai na hade duka na baki idan tana bukata sai ta karba.
Mamee ta kalleta da sauri , dalili,????
Zatayi magana ta sha mur ke bani son iyashege yanda nake fama dake anan ina ciwon baki ki
dauki kudi kiyo siyayya haka ma can kike so inyi ta babatu?
Maza karba kada ranki ya baci,
Ta dan langwabe kai, haba mamee ni fa ce uwani, kin manta ni ke rokon kudin tsamiyar
biri......... Ungo ta yi mata dakuwa, naira ashirin hamsin din?
Ta turbune fuska tare da mikewa, so kawai kike yayi mana dariya kin gwasaleni ta wuce tana
zumburo baki.
Ya kyalkyace da dariya na ganku a rana....
Ta harareshi kai tafi can samna, yanzu kai matsayin ka na miji baka iya dabara da lallashi ta
karbi kudin ko?.
Nasan uwani da kawaici wallahi kunya bazata taba barinta ko taga abu ta nuna tana so ba, in
kuwa hannunta suke tafi sakewa.
Ya watsa hannuwa kawai kiyi ta zuwa da ita kina nunnuna mata amma kada ki bari ta siyi zinari
ko zobe, kuci dadi kusha dadi please.
Sai yan kayan kyale kyale sannan kuyo mun tsaraba don ta dawo mun hannu biyu akwai
rigima.
Mamee ta mike kilibabbe sai ka ce tayo ma ba muyo ma tsaraba ba.
Kai Allah yasa maka kunya ni *Rabi'atu* ta wuce ciki.Washe gari karfe sha biyun rana su
umaimah aka tantsa kasa mai tsarki a *Madaki airline* an kame first class anata wulakanci da
rai, da jirgin zai daga yan cikin ta suka yamutse ta kama mamee gammm tace *Wayyooooooo
yan hanjina* Mamee ta tuno umaimah fa bata taba hawa jirgi ba sai ta hau tofa mata ayatul kursiyu. Ta na
warwarewa ta kalli mamee *Kut yau na jiyo kamshin lahira*
Me mamee zatayi ba dariya ba?