Showing 36001 words to 39000 words out of 63115 words
ta iya siyasa ta gama karto cewar *madaki* fushi yakeyi da umaimar. Duk da bata
san dalilin Fushin ba,
zaman falo dai ya gagari umaimah yanzu saboda kunya , mamee na zaune ya shigo da
sauri ya haye sama tayi saurin kwadawa umaimah kira ta zo da gudu saboda yanayin kiran.
Ta ce maza hau sama ki dauko mun kwalin ruwa. Ta ce to ta wuce domin tasan bai gidan.
Ta na hawa shi kuma zai sauko saura kadan su hade yayi baya da sauri, har zaiyi magana sai
kuma ya fasa kawai ya raba ta ya wuce.
Ta bishi da kallo *Wai fushi yakeyi dani?*
Me na mishi? Sai kawai taji itama ranta ya baci.
Mamee na hangoshi ya taho tasan bai kula ta ba.
Gaban ta ya fadi ko uwani ba ta karbi soyayyar tasa bane.
Ita ma umaimar ta sauko rai a bace ta ajiye mata ruwan ta shige ciki. *Ikon Allah ta kame baki*
Ta rasa me ke mata dadi, duniya ta yi ta zumbure zumburen baki.
Mamee ta shige kewaye ta ringa dariya sosai.
Har bayan magriba umaimah taki tafiya gida,
Uwani yau bakya gudun dare? Mamee ta isketa daki zaune ta rabka uban tagumi,
Ta mike yanzu zan tafi cikina ne bana jin dadin sa, ta sumke dariya, assshhha cikin ne yau
ma? Tayi shiru ta dauki hijab ta wuce kawai.
Tana zuwa gida ta bude waya ta tura mishi sako da turanci saboda bata iya rubutun Hausa ba,
*Pls what did I do?*
Ya na ganin message din ya tashi zumbur dama kishingide yake.
*good kin fahimci kinyi wani abu kenan*
Wani ya kara shigowa , *Sorry*
Ya bi wayar da kallo yana murmushi *naki wasa ne yarinya*
Tafi mintuna talatin rike da wayar amma bai maido amsa ba ta kara tura mishi:,
*I know whatever happened, Should not have happened the way it did, But, I am really sorry
on my part, My intention was not this from the start, So please forgive me!*
Tsalle ya buga yana wani irin ihu. *Billahil azim ta kamu*
Ya koma ya kwanta *Sai kin fada da bakin ki yarinya*
Tayi shiru, kai jama'a wannan da me yayi kama nifa bana son yawan fushi. Anya zanji dadin
zama da *madaki* a matsayin miji?
Ta yi saurin sauya zancen *tabb duniya akwai namijin da zai taba birgeni bayan shi?*
Ta kara tura mishi sako,
*Please forgive me for what I did, My intention was pure I admit, I did not want to hurt you a
bit, I am really sorry for what I did!*
Ya kara tashi zaune yana kara kallon rubutun , yarinyar nan yaushe ta iya turanci haka?
Wani sakon ya shigo har kyarma yakeyi,
*Madaki , Things are not the same without your company, I am missing you a lot, and I told
you sorry, Please forgive me and start a new chapter, This won't ever happen again!*
Ai sai yayi mutuwar zaune, motsi ya kasayi duk illahirin jikin sa kasala ne,
Da ta kara jin shiru sai kawai kwalla suka zubo mata ta kashe wayar,
Lokacin da hankalin sa ya dawo sai kawai ya nemi kiranta yaji *Switched off*
Ya dora hannu aka ya ce *na gama banuwa*......Ya ziri makulli kamar mahaukaci ya fito, yana
zuwa falo agogo na bugawa karfe sha biyun dare, ya koma da karfi bayansa ya daki bango ya
runtse ido cikin wani irin radadi.
Dukkansu babu Wanda ya sami damar runtsawa,
Karfe shidda tayi sammako, shi kuwa tun biyar ya gama shiri ko da ya fito sallar asubah bai
shiga ciki ba yana zaune bisa dan dakalin kofar shiga.
Daga nesa ta hangoshi zaune, Sam baiyi tsammanin ta ba yasan zata kai takwas zuwa tara,
kansa duke yana lazimi ta iso,
Yaga alamun tsayuwar mutum ya dago da sauri , Ta rike kugu idanun ta sun kawo ruwa *Wai
me na maka?*
Saura kadan dariya ta kufce mishi. Ya sha mur *laifi*
*bana baka hakuri ba?*
Ya dan dukar da akai don gaf yake da ya kwafsa,
Yaushe?
Tayi shiru tana kokarin maida kwallan bata so su zubo kafin ta ce, jiya na maka text.
Ya tabe baki ya dan watsa hannuwa ban gani ba.
Meye kika ce a text din?
Ta fiddo waya a hasale ta budo page din *Duk gashi* duba gashi kuma yaje na tabbatar tana
faman scrolling.
Ya kyalkyace da dariya. Ta bishi da kallo nan da nan ta tsargu kunya duk ta baibayeta ta balla
mishi harara ta wuce ya janyo ta ta fada jikin sa.
Lallai ana kauna ta *kut*
Ta fara kokarin zamewa ya ce *ke kilibabba* dadi na san zai halaka ki ne abinda kikayi missing
kenan duk kin rikice.
Ya kamo hannun ta zo muje in baki labari nima ai na wahala....ya rike hannun ta sukayi ciki
yana dariya. Suna shiga ya tarar da mamee zaune tayi tayi ta fizge ya riketa gam,
Ta yi sukutii... Kamar da gaske sai mamee tasha mur *ina zaka je da ita?*
Ya jata da karfi zasu wuce ya ce gyara zata mun sama.
Ta daka mishi tsawa zaka saketa ko kuwa?
Bana hanaka yi mata wannan zillar ba? Har yaushe zaka kyale yarinyar nan ta sarara?
Uwani wuce ciki daga yau na sa miki doka baki kara hawa sama...........
í ½í¸ƒí ½í¸ƒí ½í¸ƒí ½í¸ƒ
*maman Abdallah* í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜
[1/26, 10:10 AM] +234 813 180 9991: í ½í²‘ AUREN FARI í ½í²‘
0⃣2⃣4⃣
DAFATAN ZAKU SAKA TA ADDU'A AKODA YAUSHE HAJIYA RABI BADAWI MAMAN
IBRAHIM DA NURY
.............. Ke tsaya ya daka ma umaimah tsawa, ya isa gun mamee da sauri , kiyi hakuri mana.
Na ce kamun laifi ne?
Tunda ka rainani to bazata kara rabarka ba har ka gana mata azaba......wace azaba mamee ya
marairaice, gyaran da zatayi mun shine azaba?
Ta kalli umaimah Na ce ki shiga ciki ko?
Ya mike tsaye ke kina hauka ne? ya kara daka mata tsawa ......wai mamee menene haka? Ya
kalli umaimah dake niyyar shigewa ya ce wallahi kika shiga zan fiddo ki .......wai mamee
menene haka? Duk ya rikice, ya kalli umaimah dake makale a bango Malama kiyi mata bayani
...ya juya mamee wallahi bazan mata komai ba gata nan tambayar ta. Kinyi shiru mamee....me zance tunda ka rainani ka nuna ban isa ba? Duk lokacin da ta hau
saman da kuka take saukowa ka zageta tsaf ka gama.......Qalu innalillahi mamee ki sassautan
mana.
Ya maka wa umaimah harara Wai bazakiyi magana ba?
Ta ce me?
Mamee na tuba dakin can yayi kura....... Shin naji na amince gyara kake so? Zauna ga kujera
Uwani je ki gyaro ki dawo
Simi simi zata wuce ya mike Ta koma kawai bana so......fuuu yayi sama.
Uwani jeki ciki abinki kinji ko?
Tana juyawa wayar ta tayi kara tayi ciki da hanzari. Hello
Sato ki taho don Allah
Tabb wallahi mamee na falo.......ke da waye a waya?
Tayi saurin latsewa......ni... Nida luba ta juya tana kakkabe gado.
Ya zaro ido Wayar ma hanawa zatayi?
Ya sauko da gudu gudu yayi sa'a ta fito falon , tana hangoshi ta kara tsuke fuska.
Ya zauna kusa da ita, wallahi mamee yarinyar nan ki tambayeta yanzu bama fada ko kadan.
Da zakayi hakuri mu bar maganar nan..... Saboda me?
Ko magana ta fatar baki idan ta sake hadaku sai na...... Tsaya mamee ki rufa man asiri na
tuba.
Ta hasala Sam baka bin magana ta nayi nayi ka fiddo mata kakiya ka zauna kana tokalo fitina
da yar cikin ka...... Ya mike yana murmushi Aure Aure this is your only problem.
To ai UWANIN TAKI NAKE SO NA AURA
Ya koma ya durkusa ita na ke so!
Duk bakin mamee ya kulle farin ciki ya baibayeta.
Yayi hanyar dakin ta yana fadin Yanzu ai kya taimaka kiban ita inyi magana ko?
Tana duke tana share carpet ya shigo tare da janyo hannunta....tayi saurin turjewa, ya kalleta
wallahi daukar ki zanyi matukar kika man gardama. Ta bishi yaci gaba da bambami kuna neman
haukatani ku rikitani ke da mamee..... Ya na zuwa falo wayam babu mamee, ashe shigarshi tayi
baya da sauri don tabbas Madaki sai dai taji kunya shi da gaske yake. Suna zuwa babban falon sa ya zauna bisa kujera two sitter , ta tokare tsaye shi kuma yaki
sakin hannunta, ya kalleta ta zumburo baki tana fushi.
Me akayi? Ya bukata yana hararar ta,
Gaskiya abin nan zai dameni yanzu mamee tace kada in zo gashi ka kawo ni ta yaya zan
sauka saboda Allah?
Ya ficikota ta zauna cinyar sa da karfi, ke kwantas na fada mata mun jone ya karasa maganar
yana murmushi tare da kashe ido daya.
Mun shiga uku ta zabura me ka ce mata?
Ke ban son rashinin wayewa baki lura yanda za... Read more
[1/27, 7:42 AM] +234 806 091 7227: í ½í²‘ *AUREN FARI* í ½í²‘
0⃣2⃣5⃣
Ya fi mintuna ashirin bai ce qala ba kafin Ya dago kai yana murmushi, ko alokacin jahiliyya
ranka shi dade ban taba jin anyi haka ba.
Hasali ma idan son yarinyar kakeyi kaine zaka tarar da iyayenta komin kudin ka komin mulkin
ka ba iyayen yarinyar zasu kawo kansu ba kamar yanda mukayi yanzu.
Aure rahama ne yana daya daga cikin dokokin Allah da manzon sa cewar a girmama aure a
kuma daratta shi, umaimah marainiya ce ni na saki nono mahaifin ta ya kama.
Wallahi matukar nayi mata haka ba la'antar Allah kadai ba tsinuwar dangi da mutanen gari
bazasu taba sanya ni in zauna lafiya ba.
Amma ina mai baka hakuri idan abin da na fada bai ma dai dai ba.
Ya juya Allah shi gafarta malam ga maganata akwai gyara?
Ba liman yayi magana ba *madaki* ne yayi
Hakika babu gyara ga maganar ka baba.
Kuma naji dadin maganganun ka . kafin in sanar da kai dalilina ina son ka amsa mun tambayoyi
biyu zuwa uku,
Na farko me yasa kabar gidan ka sakaka babu kula?, ya akayi duk yaranka na makaranta
banda umaimah?, sannan minene ka gwammace tabi gidaje aiki akan zaman gida bata aikin
komai. Saboda ko kafin umaimah ta fara aiki gidana ta dade da fara bauta gidajen unguwar
mu? Yayi shiruuuu.... Kafin ya nisa, idan ma na boye muku to bazan boyewa mahalicci na ba.
Na farko ina iya kacin bakin kokarina a kan gida matsala daya aka sami da na karo mata ta uku
shine cin mutunci ya fara shiga har matan nawa suna zagina ko su sanya 'ya'yansu manya su
nemi sa'in sa dani. Sai na yanke shawarar idan na fita kasuwa tun bayan fitowata sallar asubah
sai talatainin dare sannan zan dawo. Umaimah kuwa, gaba daya daukota ma da nayi shi ne ya kara jagula duk wata matsala, ko na
fita na barta zata tafi makaranta to bata zuwa, tsinke wannan idan na siyo da sunan ta tabbas
ranar na janyo mata masifa da ni kaina shi yasa na tattara na watsar.
Aiki gidaje kuwa shi ne in da tafi ko ina samun natsuwa, zata ci zata sha zasu bata tsumma ta
daura. Wannan shine dalilina na barinta tana yi don kada yunwa ta kassarata.
Ya juya gun su liman Malam kunji da kunnen Ku?
Hakika munji yallabai. Suka fada. Ya ce good,
Baba, kayi hakuri amma maganar gaskiya dalilin da yasa na kiraka anan shine da ka kuskura
an daura Aure na da umaimah wallahi da sai na sa an daureka don ka tabbata baka San
*Hakkin Dan Adam* ba, idan kuma baka amince ba to shi yasa na kira malamai don kamar
yanda na ji bayanin ka na tabbatar akwai rashi ko karancin ilimi sai Suyi maka wa'azi.
Ina Neman afuwar ka baba....... Ya sunkuyar da kai haba haba babu komai, babu komai.
Liman yayi gyaran murya, to Alhamdulillah, shi musulunci sauki gareshi kuma Aure kamar
yanda ka fada ne babba. Namiji ga gidan sa shi *Linzami* ne, shi yasa Allah SWA ya ce
*ARRIJALU QAWWAMUNA ALAN NISA'I....* a wurin Allah wannan ba hujja ba ce, Suka fara
mishi wa'azi daki daki hakkin iyali, hukuncin Wanda ya zalunci maraya da sauran wa'azi. Iyakar kunya malam bawa yaji ta, sannan ya tausaya ma kansa akan saken da yayi.
Ya sallami su liman sanna ya ce wadannan kudin baba ka dauki dauri biyu ka ba aminin ka
daya, Ku kara jari. Zamu je da kai can gida kaga inda umaimar take domin hankalin ka ya
kwanta....... Babu damuwa.
Malam nasidi ya ce nikam zan koma rumfa mun baro yaro marar wayau.
Mansurah ta dunga tuntsurar dariyar keta,
Wai ke ya akayi ne? Sai da tayi mai isarta sannan ta fada masu.
Bilki ta zaro ido anya kina cikin hankalin ki kuwa? Kin manta duka gidan ko ina akwai kamara
da yallabai ke ganin komai?
Kina tunanin zaiyi shiru bazai bincika ba?..... Bata rufe baki ba mansura ta baza da gudu tana
zuwa ta tarar da kawar khausar ita kadai, daman ta wuto su a kitchen. Ta ce kije inji khausar
tana fita tayi saurin bude jakar ta mayar da kayan dai dai lokacin da dayar ta fito toilet.
Tayi waje da Sauri, ta bita da kallo cikin tsarguwa.
Suka fara mata dariyar har taji babu dadi, ke kin fiye sauri irin gidan nan an fada miki haka
kawai zaka bigi gaba kayi tuggu? Ko kuwa duk wannan feleken da daukakar da uwani ta samu
an fada miki haka kawai ta shigo zikau bata shirya ba? Bilky cikin dariya ta ce, ai idan baki fitar
da ita ba ke kya fita saurin me kikeyi? Suna gama cin abincin suka tafi.
Ita kuma ta kabbara sallah, raka'ar karshe mamee ta fara kwala mata kira, tana karasawa ko
addu'a batayi ba ta ruga sanye da hijab din mamin domin ita da gyale tazo,
Gani mamah, Aunty murja ta kalleta Tun daga sama har kasa *Ina kika sami gadararriyar yar
aiki?* Aunty jamila ta yamutsa fuska, yaya mai mutane.... Saboda samun wuri yar aikin ce da
hijab dinki?
Ashe jita jitan da mukeji da gaske ne tabdi.
Lallai zamu kowa Aunty yaya da bayani....... Au har kunji labarin uwanin?
Kwarai kuwa ance ta raina kowa ke da madaki ma tsoron ta kukeyi to........ What? Aunty jamila
kuna hauka ne?...... Mamee ta daga mishi hannu. Sam bata yarda ya raina mata yan uwa ko
Kadan.
Babu Wanda yaga shigowar sa. Sukayi sukutiii don tsoron sa sukeyi kamar me.
Baba bisimillah ya daga murya. Umaimah ta zaro ido baba ta tareshi tana yar dariya.
Mamee ta kalleshi alamar tambaya *Baban ta ne* ya fada tare da zama bisa kujera.
Mamee ta washe baki kai maraba maraba. Ya nuna mishi kujera ya dago suka hada ido da
aunty murja, kawai ta mike ita ma jamilar tabi bayanta.
Munafukan banza ya fada cikin rai.
Bayan gaisuwa da mutunta juna. Mamee ta kalli sadauki wallahi kayi kokari kayi Kyan kai.
Wanin uwani bai taba zuwa gidan nan ba. Ta mike tsaye sannu baba.
Mamee zama zakiyi na sameshi ne akan umaimah ta zauna anan zuwa bayan sallah kada
zaryar tayi mata yawa ga azumi.
Mamee ta fadada fara'ar to ya amince da hakan? Umaimah dake kusa dashi ta taunkulo cinyar
sa tare da girgiza mishi kai wai yace A'a . sai ya kwashe da dariya ya kai mata duka aka,
kaniyar ki da mintsili na....... Mintsili????? Me zasuyi ba dariya ba. Wallahi mintsili na tayi wai in
ce A'a. Mamee ta kasa magana don dariya, madaki ya kalleta *Yanzu baban kike mintsili?* ta
zumburo baki ta noke kai,
Uwani hoo, mamee ta fada
Ba zaki zauna ba kenan?
Baba ya amince kyaleta mamee ita tana tausayin kanta ne?
Ta bishi da harara,
Inji waye uwani zaki zauna ko kuwa...... Haba hajiya shawara za ayi da ita? Ya mike tayi
zamanta can din me takeyi daman ai barci ne kawai ke maida ta.
*Madaki* ya buga kafa *Good papa* mamee ta baka mishi harara. Malam bawa dai kansa
kasa yana ta murmushi.
Su Aunty murja na labe, anya wurin can babu alamar tambaya?
Hmmm ai muna ganin ikon Allah ni jamila.
Ya mike zan tafi Allah ya kara arziki. Ta mike ai nima lokacin tafiya ta yayi gobe na dawo da
kayana duka,
Madaki zaiyi magana mamee ta daga mishi hannu dole yanaji yana gani tabi baban ta.
Suna zuwa suka tarar da