Showing 27001 words to 30000 words out of 63115 words

Chapter 10 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

yasan *kyas* zata jefeshi da jakar taki karba.
Sai ka bude mun ko malam?
Ya fita da sauri ya fara fiddo *ice cream* din sannan ya bude mata, ta duro da karfi saura kadan
ya kwashe da dariya amma ya kara tamke fuska,
..... Ungo ki kaiwa yan gidan ku tsaraba.....
Ta yi saurin ja da baya... Tabb in ce ina na sameshi?
Ki ce ubangidanki ya ji Kansu ya siyo..... Wai kai idan baka nemi ci mun fuska ba Baka jin dadi?
Kaji Kansu kamar yaya?/na rokeka ne?
Sai kin roka? Ko an fada miki bana sane da ta'asar da kikeyi wa mamee idan an kawo mata?
Nasan suma haka suke da shegen kwadayi kamar ki. To bazan karba ba bama bukata, kawai ta
juya ya yunkuro zai dankota ta kwasa guje.
A zaure ta boye kudin cikin zani. Sannan ta shiga.
Kamar kullum kowa na tsakar gida ana zazzaune har an fara kiran isha'i. Fitila ta haske ko ina
abinka ga karamin gida.... Ko zama batayi ba taga mutum ya fado...
*KE NI ZAKI BARI DA BOKITI A HANNU BAKIN TITI?*
Ta zabura, tare kwalalo idanu...........

*maman Abdallah*

😘😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:14 AM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣8⃣

*Godiya ta musamman ga Bollywood addict members na gode da addu'o'i da kaunar Ku. Kamar
su Rumaisa, sanah, secret writers, Hanan, khadycute da duk wadanda ban ambata ba ina
yinku*😘😘

.... Ta zaro ido, yau na gama shiga uku ni umaimah, ya ajiye ice cream din da karfi ya tunkareta
tayi baya baya ya hada da bango hannuwansa duka a kafadunta,
Duk illahirin gidan kowa ya mike kamar an tsira mishi allura kusan mutum hudu zuwa shidda
suka hada baki..... *Alhaji umar madaki*????
Me yasa kike da taurin kan tsiya, Ke bakya tausayin kanki ko? Tayi shiru tana kyarma.
Ya daki bango *ki kiyaye ni zan wahalar da ke matukar baki sauya hali ba.*
Har ya juya ya dawo da sauri, bakwai idan ta wuce miki da minti daya gobe baki je aiki ba sai
na 6atar dake sannan idan kin cika ke din mai taurin kai ce ki ajiye jakar nan kada kiyi amfani da
ita, wallahi ko da kuskure baki dauketa ba sai na baki mamaki.
Ya juya ya fice yana huci.
Goggo hansatu ta kai mata wani uban duka *don ubanki bishi ki bashi hakuri kar ki janyo mana
masifa matsiyaciya mai halin munafukai* ta ingizata da karfi, ashe bai fita ba zaure ya lafe tana
zuwa ya fizgota tare da toshe mata baki yana magana rada rada.
Wannan dogon layin naku zaki bi? Ke me yasa baki da tunani ko kin manta motata nacan
farkon layin. Idan kin bini wazai maidoki?
Ohh ni dai na bani. Wannan masifa har ina?
Tayi tayi ya saketa ya kiya, kwallan da take faman hadiyewa suka shatato.
Ya banka mata harara inda kikafi auki kenan ya juyata ta kalli kofar shiga gidan sai kawai ya
ingizata *shiga maza* ya fice da sauri.
Tabi bayan shi da kallo, duk yau bai bata haushi ba, amma tana tausayin kanta.
Lokacin da tashiga an kachame rabon ice cream,
Kowa ya bita da harara, goggo jummai ta ce ke kuwa meye hadinki da *madaki*?
Tayi narai narai gidan sa nake aiki, matar data zo kwanaki mahaifiyarsa ce........duk suka
zaburo *gidan sa*???
Ta ce eh, yanzu ma ita ce tasa ya rage mun hanya shine....... Shine don ubanki kikayi mishi
mugun halin naki ko? Tsinanniya mai mugun hali.
Wallahi goggo ban san bokitin.....ke ar can munafuka ko baki akayi ki kawo mana mugun
halinki zai barki ne? Shi mai kudi an fada miki yana da wannan mugun kudurin ai sai talaka irin
ki jakka.
To kin daiji sharuddan shi idan kikayi wasa halaka ki zaiyi sakarai kuma wallahi ko cigiya.
Mai bakin jini ke duk inda kika raba sai an tsane ki anji ba a kaunarki. Kai ina ma amfanin

yarinya irin ki shegiya, Goggo tayi karaf, ai idan ina fadi bekena ake gani.
Irin su shatu ne munafukai, idan an kirasu cin arziki sai su zake Suna nuna isa kuma ta banza
tunda baka dashi.
Luba dake zaune tana ma ice cream cin tuwo da hannu ta ce,
Kun tuna mun wata munafukar yar ajin mu. Usaina 'Yar gidan kansila kawar mabaruka ce tare
suke komai, to labuda kuma kawar mabaruka ce ta janyo ta itama taci arziki.
Kawai sai ta fara kiran ta da *mamana* ai kuwa usaina ta ringa jin dadi tana zabga mata abin
arziki, shi kenan tana ganin wuri sai ta fara ma labuda bakin ciki tana gaba da ita, idan gaban
usaina ce faran faran da sun kebe tayi mata magana sai ta kyaleta, ai kuwa kowa ya karto
tsinanniya aka fara bincike sai gashi an gano ba sunan *uwarta usaina* ba makirci ne da
kwadayi irin na munafukan mutane.
Kinji ko? Goggo ta fada, muma Allah kadai yasan abinda ake bamu bata kawowa munafuka.
Ice cream din da umaimah bata sha ba kenan ta nufi salloli.
Tana gamawa ta tafi gidan Alhaji yakuba.
Hajiya na ganinta ta ce me akayi miki kamar kinyi kuka?
Ta kakaro murmushi tayi tayi amma ta kasa sai kawai ta fashe da kuka, hankalinta ya tashi
kwarai,
Umaimah ya akayi?
Ta dago fuska sharkaf, wallahi na rasa in da zan sa kaina inji sanyi.
Ya akayi?
Kin san nazo na karbi dubu biyar ko? Abinda ya faru....ta fada mata.
To shine yau ya bani da cikon wancen dana wannan watan kin gansu amma INA tsoron kai
kudin nan gidan mu sunyi yawa, idan suka saba ina kai kudi da yawa ranar da ban kai ba na
shiga uku saboda wani irin birkitatten mutum ne.
Ikon Allah, yaro ba mutum ba sai ya girma, duk abubuwan naku yazo da yarinta umaimah,
kuma wallahi kin mun Kyan kai tabbas *da* da mahaifi sai Allah kinyi zurfin tunani da baki fada
mata ba, maganar kudin nan ma wallahi naga hankalinki,
Shi kam yayi wauta da yarinta a matsayin sa bai kamata ya biye miki ba, ina shi in ke?
Ta ce *Hmmmm* kawai
Ta fiddo kudin ta mika mata shine na ce bari in zo duk abinda kika gani.
Ta karba *Au yo ai ke lissafin naki hada riba ya dora* nake ga dubu Dari ne.
Tabb wallahi baki basu sarka zan siya miki dasu.
Sarka? To ke kuma fa me zaki dauka?
Tayi murmushi wallahi bani taba miki kudi kinji na rantse. Wadancen ma suna nan zamu ajiye
tsaron lalura. Daga wannan watan idan ya baki zan fara miki siyayyar kayan kitchen ina
ajiyewa, ki ringa basu dubu biyar din.
Allah yana tare da maraya. Kuma kayanki nacan duk na bayar dunki saura leshi da atamfa na
ajiye zuwa gaba.... Wallahi nabarwa farida nima na rantse bazan karba ba.
Ta rasa me zata ce mata .
Tayi saurin canza zancen *kuma Hajiya zata sanyani makaranta.* ta kamota ki bari don Allah,
Allah har an fara mun lesson ma Dana gama fahimta zan fara zuwa. Amma tace inyi shiru ,
Nima abinda zance kenan. To Alhamdulillah ai kyawawan dabi'un ki umaimah bazaki taba
wulakanta ba.

Suka sha fira, umaimah ta fito zuciyarta fes! Duk wata damuwa ta rageta.
Lokacin da ta shiga kowa ya kwanta, itama tabi lafiya, amma jiya wayau, barci sama sama
tunani ya hanata runtsawa.
Goggo ce ta tada ta karfe biyar da rabi, *Barcin ubanwa kikeyi* ta kai mata duka tayi firgigi,
shegiya kafaffiya duk gargadin da yayi miki shine yau ma kika gyara kwanciya? Idan ke zaki
janyo wa kanki da sauki muma tana iya shafar mu ja'ira mai taurin kan tsiya. Ki tashi kiyi man
wanke wanke da shara. Haka ta yi sallah ta hanzarta kada ta makara,
Daga bakin gate ya hango shigowarta tana ta uban sauri rataye da jaka, yana tsaye sama
yana kallon ta har ta shige ciki. Yayi murmushi ya koma daki ya kwanta.
Ko da ta shiga babu kowa falon tayi ciki tana gunani, masifa ce kawai ko nazo ko banzo da wuri
ba ina abinda ya dameshi tunda ba jirana yakeyi ba. Idan ta gaskiya ne ya zauna falo mana.
Mtsew taja tsoki.
Tana shiga mamee ta tashi zaune 'yar halak kinki ambato wallahi yanzu nake shirin kiranki a
waya.
Tayi murmushi gani ta samu ne?
*Dan kifin nan* zaki siyo mana irin na rannan kiyi mun faten dankalin ki......hahahaha lallai kinji
dadin sa. Kuma kamar wasa na kwatanta dana gani a *Arewa 24*
A a da dadi kam, ki siyo mun tumatur irin manyan nan. Tayi murmushi kwadon ne ko?
Kin tuna mun da *lansir* ....ai fa ta fada tana laluben inda kudin suke, ta dan juyo nawa zan
dauka don zan siyo kwakwa da danyar citta...... Dauki dubu biyar ai lissafi yanzu kika fara.
Duk sukayi dariya, kifin na nawa?
Dubu daya ko yayi kadan?
Kuma zan dauki har dubu biyar? *lansir* din da na hamsin ma mugun wajiba akeyi dashi?
Ta yi yar dariya kedai dauki hakan nasan yalo, soyayyar aya duk suna can suna jiranki, suka
kara dariya.
Yi sauri ko kya dawo.
Saboda duk kasuwan kowa na sammakon siyayya saboda juma'a ce sai goma saura ta dawo,
tana shigowa ta tarar dashi zaune ya hada gabas da yamma. Simi simi zata wuce ya daka mata
tsawa...
*Daga ina kike?*
Ta yi chak!
Ko ba kya ji?
Kasuwa, ta fada kai sunkuye
Ya banka mata harara tare da yamutsa fuska *kasuwa?*
Ya mike , ta yi sauri ta bude jaka wallahi kaga mama ta aikeni na siyo kifi, tumatur, lansir ta fara
fiddo kaya ruwan kifin duk sun bata jakar da na tumatur.
Ya zaro ido *What?*
*Umaimah kina hauka ne jakar *200+ kika sako wannan shits din*????

Barkan mu da rana
*Maman Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘

[1/26, 9:59 AM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣9⃣

...... Kayi hakuri ledojin ne sukayi mun yawa shine naga meye amfanin jakar....
Ya finciko ta baki fahimci me nace ba? Kin San kudin jakar nan kika sako mata wannan
tarkacen?
Ya girgizata *dubu dari biyu da hamsin* Ta zaro ido na shiga uku, ta zazzage kayan da sukayi
ragowa tana kyarma, *dubu dari biyu da hamsin* kudin kawai take maimaitawa duk ta gigice sai
kawai ya rungume hannu yana kallon ta cike da takaici,
Tabar jakar nan ta shiga kwashe kayan tana kaiwa kitchen, sannan ta dawo ta dauki jakar tana
dan sayar kallon sa,
Ta tarar komai an hada mata har dankalin an fere, ta shiga hadawa,
Koda ta gama ta kawo musu bisa table bata tsaya ba sai tayi ciki. Ya bita da kallo, *yarinyar
nan muguwar bagidajiya ce mtseww*
Mamee ta kalleshi cike da kulawa lafiya?
Ya ce ba komai,
Ta zuba faten zata fara sha, ya kalleta
Meye ke kamshi haka?
Faten dankali ko zaka sha?
Ya danyi jimm, eh kamar hakan.
Tayi murmushi kilibabbe,
Wasa wasa sai da ya share plate biyu, a lomar karshe ya kalleta mamee dama shi kika mun tayi
last time na bar dadi haka?
Tayi yar dariya au kajiye ma bakin ka kenan.
Gaskiya ya mun dadi ayi. 'Yan aikin nan naki na bada wuta kwanannan.
Na lura masu kalacin safe sunfi sauran iya abinci fa, last week ma na ci wani Dan bread da
SOS ya mun dadi a office kamar na kuma waya.
Ai uwani na kokari kam don yanzu kalaci inba ita ta hada mun ba bana jin dadin sa saboda
yan makulashen nan.
Uwani? Ya bukata,
Uwani fa ai karambanin ta ya wuce inda duk kake tunani, duk abinda ta ga wani yayi sai ta
kwatanta.
Ga tambaya, ai tana da kwalwa.
Lallai idan akwai saura zanci da dare a ajiye mun.
Ta kalleshi da sauri *a ajiye ma Kana nufin a *dumama*? Yayi murmishi haka na ce mamee,
Umaimah kuwa tana baya ta debo uban *klin* ta zuba a katuwar roba tana ta gurzar jaka,
mamee ta kwala mata kira,
Ta antayo da gudu hannun ta duk kumfa,
Ya bita da kallo duk ta jike hijab dinta,
Naga hannunki kumfa me kikeyi agogo? Mamee ta bukata tana kallon ta cike da kulawa.
Tadan murza hannun kumfan ya fado kasa tana satar kallon sa, jaka nake wankewa...... Ya
dago *what a ruwa kika saka ta?*

Mamee yar nan taki wallahi duk abinda nayi mata kar kiyi magana.
*Da tayi maka me?*
Ki tambayeta gata nan, ya nuna ta da yatsa,
Uwani me kika mishi?
Ta dan kara kame jikin ta tana dan in ina....... Uwani matso nan saki jikin ki. Ta kalleshi wallahi
bani son takurawa yarinyar nan da kake yi madaki tsoron ka takeyi kamar me dubi yanda jikin ta
duk ya rikice da kyarma ina dalilin wannan azaba?
Ta kamota me kikayi mishi?
Jiya ne ya ban jaka ban san cewar mai tsada bace shine....... Ki faro mata daga farko.... Ya
katseta.
Kai bana son shiga uku kai ka fada man mana.
Mamee yarinyar jiya zan tafi stadium na hadu da ita hanya zata je gida na taimaka mata na
rage mata hanya na ganta da kudi a hannu na ce bata sawa jaka ta ce bata da ita, na biya na
siya mata mai tsada shine yau ta yo cefane da ita duk kifi da karikitan data siyo ciki ta zubo
shine......... Shine me? Ina ruwanka idan wuta ta saka ta Ina ce kai dai ka bata ko?, zai yi magana ta daga mishi
hannu kai bani son rashin gaskiya, daman ka siya ne don ka uzzura mata, duk tsadar ta ina ita
zata san haka?
Ta kalleta kin rage dan faten? A a duka na juyo shi sai Wanda na diba a plate...... Sai ki ajiye
mun shi kar ki taba.
Mamee ta bishi da kallon takaici,
Ko bakiji ba? Ta ce to zata juya, mamee ta kamota je ki ci fita batun sa,..... Haba mamee .......
Zakayi mata kurulla ne?
Sai kawai ya mike ya nufi kitchen din ya dauko. Wai madaki meke damunka?
Ai mamee idan na zauna gidan nan wata rana ma cewa zakiyi ba ki haifeni ba sai uwani ya
wuce sama da plate din.
Ungo wannan je karasa cinyewa kyaleshi. Kullum ganin kansa yakeyi yaro karami shi yasa
nake burin yayi *Aure* gaban umaimah ya fadi *wai ya zanyi naga madaki da wata?*
Tayi ciki tana karasa wanke jakar,
Ta ringa jiyo hayaniyar mutane, ta sami mamee daki ta ce, kamar baki nakeji falo.
Wannan fitinannen ke meeting ai shirin zuwan su ne jiya na wuni baya ina gargadin su
mansurah, manya manyan manajojin sa ne,
Au, ta fada a takaice.
Firatan ya ki hawa sama duk ya takura kowa.
Madaki kuwa yasan yau wuni zaiyi tare dasu gashi baya son umaimah ta tafi bai sani akwai
maganar da zaiyi da ita.
Karfe uku aka fara shirya musu abinci kamar yanda ya tsara, umaimah an dage aiki baji ba
gani, magana yakeyi amma hankalin sa na gunta idan ya hangota ta fito.
Ashe shima cikin manajojin shi daya ya hangota nan da nan hanakalin sa ya dauku. Ya dan
juyo yana sosa keya,
'Yallabai ni fa na hango iri.
Ya maida hankalin sa gareshi sosai saboda shine babban manager da yake ji dashi a Lagos
yake,

Iri na me?
Dai dai ta fito ya ce waccen yarinyar....... Ya sha mur *Bana son maganar banza* abinda ya
kawo ka kenan?
Nan da nan ya kame kansa saboda suna bala'in tsoron sa.
Suka tafi zuwa dining, Sun fara cin abinci kenan sai gata da tray an nado kaji gasassu. Rashin
sani ta ajiye gaban manager ya dago kai tare da dan murmushi ita ma ta mayar mishi, ya ce
sannu....... Wata fizga yayi mata sukayi ciki ya kaita har kofar dakin mamee ya ingizata *wallahi
kika kara fitowa sai na bata miki rai* ya juya. Ta bishi da kallon takaici, su manager na ganin haka jikin kowa yayi la'asar ya dawo yanata
mazurai ya nuna ma kowa plate *serve your self*
Kowa sukuku ana ci ana tattaunawa. Yana sauraron kowa yana kurbar lemu yaki cin komai.
Umaimah kuwa tana shiga ta ce mamah mun gama bari na dan huta , suka fara fira,
Bayan sunyi sallah suka dauko gyada mai bawo soyayya data siyo kasuwa ta juyo ta a tray
suna ci.
Gashi an rufe kofar baya ya ce kada Wanda ya bude, ga shidda ta wuce tana son tafiya gida,
ta rasa yanda zatayi. Kamar mamee ta karance ta, Uwani yau ko fira za a mun naga baki fara
wannan saurin naki ba gudu gudu.
Ta danyi murmushi, na ga har yanzu suna falo kada ya ce ina mishi sintiri.... Ke kama hanya ki
tafi gida kinji gobe kin san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0