Showing 30001 words to 33000 words out of 63115 words

Chapter 11 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

akwai lesson kuma na safe.
Taji wani kwarin guywa ta fito simi simi *ya daka mata tsawa bana ce karki fito*.......tayi baya
guje
Mamee ta ganta kamar an jefo ta. Ke lafiya waya biyoki?
Tayi shiru tana kallon kofa.
Ya mike tsaye, kowa na iya tafiya gobe ma karasa by 8:00am. Yana gama fada ya haye sama
da sauri.
Mamee ta ce muje ta taso ta a gaba. Ba kowa falon umaimah tayi turus.
Kama hanya ki tafi gida yanzu kyaji kiran sallah.
Ta ringa hada kafafu don sauri gudu gudu ta fito tana rufo kofa taga mutum tsaye.
Ya figeta sukayi wata hanya, me yasa ke kullum kin fi so kiga ina miki hayagaga?
Ta sunkuyar da kai.
Ya bita da kallo wai yarinyar nan yanzu bata biye mun?
Da ke nake magana . tayi shiru, idan kika kara fitowa nayi baki sai ranki ya baci daga yau.
Ta ce toh a hankali. Ya kalleta sosai, ko bakiji ba?
Naji, ta ce kanta a kasa.
Ya dan saketa ga jakar ki can da kika ki karba ta tsaraba na ce maikudi ya kaiki gida kije yana
jiranki...... Ta kalleshi da sauri maikudi drivern sa da baya tuka kowa?
Ta girgiza kai bana shiga.
Dalili?
Haka nan,
Idan na ce dole fa?
Malam bafa zan shiga motar ka ba, kawai sai aga cewar waccen motar ta ajiyeni wane kallo za
ayi mani?
Zai kara magana ta hada hannuwa don Allah ka kyaleni haka nan na kai makura..... Har jakar

bazaki dauka ba?
Ko na karba zan raba ka da su ne ba tare da nima na amfana dasu ba to meye amfamin
amsar?
Ya kalleta har zaiyi magana ya ingijeta ya wuce....
Ta bishi da kallo ohh wannan akwai bahagon mutum ta wuce tana yan tunane tunane.
Ya wuce masallaci yana magana kasa kasa cikin fada, gidan nasu zan je in kyare masu warning
duk shegen da ya yi amfani da kayan inci uwashi. Ai na karanci matsiyata tun jiya.......

*Mukwana lafiya*

😘😘😘😘😘😘😘😘
[1/26, 9:18 AM] +234 813 180 9991: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣0⃣

....... Tana shiga ko zama batayi ba goggo jummai ta nuna mata tulin kayan wankin ta ita da
yara,
Ko sallar magriba batayi ba ta shiga yi don ko hijabi ta nufi cirewa ta tabbatar sai ta daketa,
Karfe takwas da rabi taci dunin wankin sosai, duk suna bisa tabarma ana ta shewa ita ta basu
baya.
Tsit taji gidan yayi kamar wuta ta dauke ta juyo da sauri, katti ta gani ko wane da bakaken kaya
tadan ware ido nan da nan ta gane ko su waye, ta mike zumbur dai dai shi ma ya shigo wasu
na binsa a baya.
Duk su goggo suka makure sun kasa ko motsi ganin ko wane da bindiga,
*Sannu da zuwa*..... Ta fada hannunta jage jage da kumfa, ya kalleta Tun daga sama har
kasa sannan ya fara waiwaye ya hango tulun wankin da ke ajiye da kuma Wanda ke a robobi
manya.
Ya sha mur *Zuwa na yi in miki gargadi na karshe*
Tunda mamee ta na ce sai kin mata aiki to babu yanda zanyi domin duk abinda takeso bana
kin sa matsalar bazan taba daukar *Kazanta ba* duk yan aikin gidana babu kazama irin ki, ya
nufeta kamar zai shaketa tayi baya ya dan bita, *Kinga wannan jakar?* kaya ne a ciki Su zaki
ringa sakawa kina zuwa aiki na san ko kala nawa ne don ni na siyo, ko wane turare, sabulu, mai
da duk abinda ke ciki nasan kamshin sa da adadin da zaiyi.
Ya fizgota na sanki da *Taurin kai* ki bada ko toothpaste ne kiga yanda zan *halaka ki da
Wanda kika ba din*
Su goggo kowane ya zaro ido tare da hadiye wani dunkulallen miyau.
Ya kalli lubabatu dake bakin tabar ma *Ina ne take kwana?* ya daka mata tsawa. Ta tsira
hannu *Gashi can*!
Ba tare da yayi magana ba cikin kattin wani ya yi ciki da jakar.
Ta kalleshi cike da takaici wannan mutum akwai wulakantacce ni zai kira *kazama*? Ji yanda
yazo yana mun hayagaga har gidan mu ban tsira ba. Kai ohh ni umaimah na jefa kaina a jafa'i.
Ya kalleta sosai *Ki rufawa kanki asiri ki bi doka ta* ya juya kawai duk suka bi bayansa.
Ta bishi da harara ta wuce wurin wankin ta.

Lubabatu ta saki ajiyar zuciya, goggo jummai ta ce yau naga masifa, wannan matsiyaciyar
yarinya zata janyo mana bala'i.
Kowa na tofa albarkacin bakin sa amma goggo hansatu ko motsi sai da luba ta lura sannan ta
tabo ta *inna*..... Tayi firgigi ta ce *Wayyo mun shiga uku*....... Duk aka kwashe da dariya ta
mike da gudu ta suri buta tayi kewaye.
Umaimah me zatayi ba dariya ba. Ta ce su goggo manya wannan 'yar barazanar ta firgitata da
sune yake ma wujijjigawar da nakesha wataran mussai zasuyi. Ta kara tuntsirewa da dariya sai
kawai ta ganta tsaye gabanta tana nishi idanu duk sun fito, kyayi dariya don ubanki hankalin ki
ya kwanta ki kawo mana ajalinmu har gida. Ta shiga bambami kowa ya dunga zagin umaimah.
Ta waigo goggo haka fa yake da wannan masifar ta babu gaira, saboda Allah luba bana tsafta
idan zan tafi?
Duk suka kwalalo ido *Anya yarinyar nan bata tare da aljannu?* firar yau batayi tsawo ba kowa
ya shige daki.
Sai goma saura ta gama tayi salloli, ta kura ma jakar ido gabanta ya fadi *Ohh ni umaimah*
Ta juya luba kinyi barci?
A a ido na biyu.
Au, kuma kikayi lamo? Tashi mu danyi fira bana jin barci wallahi.
Ta janyo jakar ta bude sai kawai ta dafe kirji *Na shiga uku* wasu irin kayana ta gani ta ce luba
zo ki gani.
Mi? Tabb um um , sai kawai ta bata baya kada ma ta hango wani abin ya birgeta. Tayi
murmushi ta dauka wasa takeyi sai ma tayi mata banza.
Duk sai taji babu dadi *wannan ai mugun hali ne* ta fada a hankali. Kiri kiri yazo ya firgita
jama'a. Dogayen riguna masu kyau wasu matsattsu wasu budaddu, turaruka, Mayan shafa wani
abin ma bata San ya ake amfani dashi ba,Gyaluluwa kai kaya barkatai , kunya ta kamata ganin
brezias mtsew ta buga tsoki ta rufe jakar. Luba dai na jinta tayi lamo.
*Madaki* kuwa suna fita yaji kamar ya koma ya dauko umaimah su tafi gida. Yarinyar nan tana
wahala gidan can. Wanki hada na yara?
Amma mutanen nan akwai matsiyata, zasuci ubansu, ya kuta.
Sai na gama ci masu uwa sannan in dauketa in mayar da ita gidana zan fara nemo waye uban
tukun shima dayan *shashashan*
Yayi dan murmushi Matsoratan banza duk sun rikice ganin bindiga. Sai na mayar dasu
ma'aikatan ta a gidan *nasu wasa ne*
Da safe ta fito da shirin ta normal zata tafi , tayi karo da goggo lami, ta kalleta sama da kasa
Sai kawai ta fizgota ta fara bugu, duk mutanen gidan suka fito lafiya?
Ta kallesu tana nishi Ku dubi duk gargadin da yarinyar nan tasha jiya a haka zata tafi. Kowa ya
dauki salati nan suka yo kanta mai kulli nayi mai kwanya nayi, suka tasa ta a gaba tana ta
kwalla har gaban jakar , goggo tasa hannu ta fiddo wata bakar riga tasha ado da duwatsu rigar
ta yi kyau matuka da dan gyalenta karami, suka tsareta ta saka, sanan suka dauko turaruka
suna feffesawa suna ci gaba da dankwasar ta *Shegiya mai kunnen kashi* baki gudun wahala
baki gudar ma wani.
Ta kalli kanta ta kallesu tana kuka goggo haka zan fita da wannan dan mayafin in ratsa

gari?........ Gam goggo hansatu ta buge bakin , wannan shegen bakin zai yi shiru ne? Idan ba
da shi da uwaki zaki tafi?
Ta jefa mata wasu golden brown din takalma maza kisa ki tafi suka rufe jakar, duk tulin kayan
babu wanda ma yabi ta kansu har su birgesu.
Karfe bakwai da rabi ta shigo tayi sama da gudu cikin bacin rai don kagare take ta iso gidan,
yana kwance daki bisa gado yana ta sharar barci, haka kawai yau yaji barci kamar me,
Ta dunga bugun kofar da karfi ya tashi firgigi da jallabiya tunda ya dawo sallar asubah.
Ya kasa magana ya taso da sauri ya bude a hasale, yana ganin ta yayi turus yaja baya tayo
kansa tana bala'i, me kake nufi dani ne, ya dunga baya baya tana binshi, ka firgita man iyaye
ka rikitatsu ka kara jefa ni masifa, *Why are u increasing my problems?* ya zaro ido jin tayi
turanci, yana kaiwa ta bango Sai ya daga hannuwan sa sama *am sorry* ta daki kirjin sa bazan
yi ba wallahi na gaji da halayen ka ...... Ya ce, Ammmmm.... Ta kura mishi ido.
Kayan nan sun miki kyau. Ya bita da kallo tun daga sama har kasa yana dan murmushi, taja
tsaki tare da juyawa ya fincikota ya maida ga bangon fuskarsa daf da tata ya sunkuyo, ya zaki
tayar dani barci ki gudu ai yau muna nan.
Ta zaro ido..... Ya balla mata harara kilibabba an kwana tunanina zaki wani taho a 360 kina
wani borin kunya.... Ya buge bakin zatayi magana naji ba haka bane kwalliya aka zo nuna mun
in yaba ko?
Ta ture shi da karfi zata gudu ya maidota tabaya a jikin sa ya leko da kansa ta wuyanta, *Ke
bakya godiya idan an miki abin arziki ko?* tsikar jikin ta ya tashi ta rasa in da zata sa kanta, ya
lumshe ido yana shakar kamshin jikin ta.
Duk sukayi shiruuu kowa najin abin da yakeji a zuciya.
Shine mai karfin hali ya dan saketa amma Sai ya ruko hannunwan ta muje can kasan ya dan
fizgeta..... Ta jiyo muryar mamee ta yi saurin turjewa ya kalleta *ya dai?*
Kai ni dai sakeni don Allah.
Ya kara fizgarta bazan saki ba haka zamu sauka sai kawai ta zukunne *Na tuba wallahi ga
mamee can*!!!! ...... Shi ma ya zukunna kina jin kunyar ta ne?..........
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣1⃣

https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH

....... Ya kyalkyace da dariya ta bishi da wani irin kallo. Mamaki ya baibayeta wai meke damun
*madaki sometimes?*
Ta langabe don girman Allah kayi hakuri ba don ni ba wallahi bazan kara ba...
Baza ki kara me ba?
Ta yi shiru, kinji?
Don Allah ni dai kayi hakuri.
Okay naji zanyi amma da sharadi kullum da kinzo zaki wuce sama ki fara gayar dani kafin ki

shiga inda mamee take kin amince?
Eh na amince duk ta kagara ta sauka,
Ya kalleta idan kika saba menene hukuncin ki?....ka rike albashina na amince,
No! Banda wannan... Ta kalleshi cikin kosawa duk abinda kaga dama na amince kayi man.... Ko
menene? Ta daga kai eh na amince bama zan saba maka ba kayi hakuri ,
Kiyi man alkawari duk abinda nayi miki zaki rama. Ta kalleshi ya daga kai *yes*! Idan na mareki
kema zaki dalla man mari. Ta sunkuyar da kai na amince, no! Kiyi rantsuwa Kice wallahi zan
rama. Ta dan kalleshi kaikaice *wallahi zan rama*
Ya danyi yar dariya *Good girl* ya maida hannuwan sa baya yadan kishingida kin ce ko
menene fa?
Haka na ce ta fada tare da yin hanyar falon mamee. Ya bita da kallo yana yar dariya.
Saukowa takeyi mamee ta bita da kallo har ta kusa karasowa kusa da ita, sai mamee ta dauki
salati..... La'ilaha ilallahu mahammadu rasulullah tana tafa hannuwa *Uwani?* gabanta ya yi
wani mummunan faduwa....
Kallon ki kawai nakeyi ina tunanin ina muka sami 'yar balarabiyar budurwa tun da sassafe
kuma daga saman bene? Ta karasa maganar tana yar dariya.
Ta zumburo baki kai *Mamah* ta kyalkyace da dariya wallahi da gaske nake waya baki
tsarabar makka ko kudin naki ne kika kwashe kika siyo..... Kai mamah wai ya akayi? Ta karasa
gunta tana yar dariya.
Ta dago fuskar ta anya *Uwani na ce yau*? Kai wallahi kinyi kyau. Ko kefa don Allah ki ringa
sauya shiga amma kullum cikin kodaddun kaya kamar almajira kina fama da hijabi balam balam
kai kace matar liman. Duk suka kwashe da dariya.
Allah kullum ina son miki magana amma bana son kiji babu dadi tun da ban san tanadin naki
ba.
Ta mike zuwa ciki tana yar dariya ta bita da kallo ohh uwani yarinya ce har yarinya talauci babu
abinda baya boyewa kuma sai ta zamo tana da hakuri da rashin kwadayi.
Kamar kullum *Mr Samuel* yazo ta fita lesson. Yana bala'in jin dadin koya mata saboda bai
taba tambayarta sau biyu ba, ya dade baiga mai kokarin umaimah ba.
Ya kalleta da yake bayajin hausa ko kadan wata biyu ta gama kwarewa da turancin sa tana
ganewa kawai wajen maidawa ne wani lokacin take samun matsala amma yana gyara mata to
an wuce wurin.
Ya kalleta yana murmushi *primary certificate din ki ya kammala* zan bawa oga shawara ya
sanyaki js 3 kawai ina da tabbacin zaki iya. Kinga da kin je SS2 kawai kiyi WAEC.
Ta washe baki haba? Lallai naji dadi. To wane school zasu amince? Ta bukata , yayi
murmushi *Madaki international school* ta zaro ido yana da makaranta?
Makarantu dai ai duk kasar nan babu inda baida branch.
Yanzu haka private university yake ginawa, kano, Kaduna, Abuja, Lagos da katsina. Zaiyi
lunching a lokaci daya.
Tabb lallai ta fada.
Ya kalleta ke ai kilan anan cikin gida zakiyi ta ki.
Ta kyalkyace da dariya sai kawai taga mutum kamar an jefo shi ya kalleshi *koya mata kakeyi
ko maganganun banza?*
Ya mike yana kyarma no sir is part of our lesson...... Shut up, ya kalleta 6ace man da gani

kada in miki rauni...tayi ciki da gudu.
Ya nuna shi da yatsa *Ka shiga hankalinka*
Ya fara bashi hakuri. Lesson din da ba a kara ba ya hana.
Washe gari kamar yanda tayi alkawari ta wuce sama direct yau idonsa biyu, kwankwasawa
daya tayi ya ce *Shigo*
Tana bude kofa ta durkusa ina kwana?
Ya dan harareta da Allah malama shigo ciki.
Ai kaji matsalar, nasan bazai taba amsa gaisuwa ta ba. Ta fada a zuci tare da shigewa ta rabe a
bago.
Kinga leda can da jaka ki dauko, uniform din ki ne da school bag. Ta washe fuska ta nufi wurin
da sauri.
Monday zaki fara zuwa idan kika saki kika kasa maida hankali sai na miki bugun kudina don
bazan yi asara ba.
*Ta durkusa guywa biyu* na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara arziki mai amfani.
Ya dade yana kallonta har ta ji ba dadi tunda kanta a kasa yake.
Ya ce amin.
Magana ta karshe makarantar *mix* ce wallahi kika kula wani namiji kin gama karatun daga
ranar..... Ta banka mishi harara ya zaburo *Au baki dauka ba?*
Ta kwashi kayan tayi waje da gudu tana fadin *Nima so kake in tsofe irin ka ba aure*?
Ya biyota da gudu yana iyye yarinyar nan kin gama rainani ji kakeyi daf daf daf....da da da....
Karar gudu dai dai mamee na fitowa tayi bayanta wayyo mamah ..wayyo zai dakeni.
Ta tattare kai tsaya wallahi ka taba ta sai ranka ya baci. Me ta maka?
Umaimah daga bayanta ta ce uniform ya bani zan fara zuwa makaranta litinin wai idan na kula
maza na gama daga ranar. Don na ce so yake in tsofe kamarshi ba aure shine ya biyoni zai
daka......
Mamee ta zaro ido ta kalleshi sai wani mazuran borin kunya yakeyi. Sai kawai tayi murmushi,
kayi hakuri toh bazata kara ba.
Mamee yarinyar nan fa ..... Na ce kayi hakuri *uwani shige ciki* ta ruga da gudu kuwa.
Ya bita da kallo kamar yanda mamee itama ta tsareshi da idanu.
Fakam fakam yayi sama.
Ta koma ta zauna bisa kujera *Haba wallahi koda naji* fitinar nan ta uwani da madaki ta isa
watan *Son ta yakeyi shi ne yaketa wannan haukan*
Wani sanyi ya diri zuciyarta bani da matsala da uwani wallahi. Ta rike haba *ohh*....
Ta yi ciki ta tarar da ita zaune. Ta na ta nishi.
Ta kalleta taji ta kara sonta fiye da *da* wannan kauna da nakeyi ma uwani ta isa, ashe
surukuta zanyi da ita.
Ta zauna kusa da ita, uwani?. Ta kalleta kawai, ki daina biye mishi kina wannan mugun gudun
wata rana sai kinyi wa kanki rauni. Idan ya taso ki tsaya kiga zai kasheki?
Duk sharuddan da ya kindaya miki to kibi su babu kuskure matukar kina son Ku zauna lafiya
ya daina wahalar da ke.
Ta ce toh, ta kalleta wai rigunan da yawa kika siya haka naga ta yau tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0