Showing 15001 words to 18000 words out of 63115 words

Chapter 6 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

sa.
Ke bakinki bai mutuwa ko? Ya matseta.... Sakarni malam ko gantsara maka cizo......mansura

ta fito uwani kizo inji...... Maganar ta tsaya ganin madaki, ta yunkura ya kara riketa, jeki ce tana
zuwa, tayi baya da sauri,
Kwalla suka shatato mata, ya bisu da kallo duk tsiwarta bata da wuyar kuka, ya hade
hannayenta dauko kiban sannan ki tafi.
Taga ba sarki sai Allah ta dauko ga hannuwansa duka rike da ita, sai ya bude baki, ta balla
mishi harara sannan ta watsa mishi.
Ya saketa barkanki yarinya da....... Tuni ta shige ciki da gudu yabi bayanta da kallo.
Gani mamah,
Zo nan ki tayani gyaran sarka,
Ya tashi yayi sama cikin nishadi yana tsotsa.
Cewa nayi a kira mun ke kada ya miki wata muguntar. Ai cikin satin nan dai zai tafi Germany
ki huta.
Murmushi kawai umaimah tayi.
Mamee bazata bar yarinyar nan ta zo ba kona kira.
Ya dauki waya hello mamee don girman Allah kibar yarinyar nan tazo ta gyara man daki wallahi
kinji nayi rantsuwa bazan kuma sata kuka ba. Na daina biye mata please.
Ka tabbatar? Wallahi eh kinji nayi rantsuwa.
Shi kenan ta ajiye, Uwani jeki gyara mishi dakin ki sauko.
Bata San lokacin da ta ce innalillahi wa'inna ilaihi raji'un ba. Ta kalleta zuwa saman keda
wannan salatin? To bazaki ba wallahi ina dalili. Kyaleshi ai shi ya jiyo.
Ta langwabar da kai don Allah mamah tunda na gama in tafi?
Tausayinta ya kamata yanzu har tafi sha'awar tafiya gida da zama da ita saboda masifar
madaki.
Tashi ki tafi kinji.
Zumbur ta mike tana murna ta bita da kallo.
Shiru shiru sai kawai ya sauko, baisan ko wacece ba zata wuce ya ce ke ina yariyar mamee?
Yanzu kuwa ta tafi gida..... *what* ? Da daka tsawa har ta dan firgita. Yayi ciki mamee!
mamee!! Ya na bude kofa ya fara masifa,
Kinga abinda na ke fada miki ko? Yarinyar nan fa gida ta tafi.....eh ina sane da hakan. Yayi
turus!
Ka firgita 'yar mutane kwata kwata yanzu bata sha'awar zama gidan nan duk ta tsorata ka
hanata sakewa wannan masifar taka ta yi yawa.
Shine kika bata dama ta tafi? Fine! Kawai ya juya yayi sama.
Gashi ya rarratsa wayar da yake da numberta don bai wani tsaya saving ba, mtsewww yaja
dogon tsaki sai kawai ya fara hada jakunkuna.
Umaimah kuwa tana fita gidan ta mance komai cikin sa'a tana zuwa ta tarar an maido wuta ta
kwashi kayanta ta nufi gidan Alhaji yakuba guga.
Karfe shida na safe tana lazimi ya shigo, mamee zan tafi Germany sai Allah ya mana
dawowa.
Yau ne? Ina ce sai jibi,
Eh akwai shirye shiryen da zanyi ne. Ya mike. Tabishi da kallo a dawo lafiya.....
Ya wuce yana fushi, tunanin umaimah zai zautashi mamee kuma na babbakewa gara yayi nisa
da gidan wata kila zai mance dasu din.

Abinda madaki bai sani ba zaman sa gidan a haka ne saukin sa, domin da ya tafi sai da ya
gwammace kida da karatu kusan zaucewa yayi hatta matan kasar sai suka ringa rikidewa suna
koma mishi umaimah,
Kam bala'i kada fa ace son yarinyar nan nakeyi? Innalillahi ya Allah kada kayi mun wannan
jarabawar .
Umaimah kuwa gida yazamo mata gwanin dadi ta warware, ga kwanciyar hankali ba fitinar
madaki ga cimar dadi nan da nan jikin ta ya canza duk inda yake a dame ya taso, gida kuma ta
kulle ita da lubabatu saboda hasafin da takeyi mata a boye, ko kayanta ma ta daina tabawa, ta
karbi kudi gun hajiya ta yanko wasu yan material masu arha kala kala akayi mata dogayen
rigunakala uku wasu kuma tayi da skirt kala biyu. Sannan ta yanko hijabai ita da mamee kala
kala har ta baiwa lubabatu biyu ciki.
Umaimah na da kokari har ta shiga hizif na talatin ta kuma gama hadisai biyu *haqqul
mubeen* 1&2 ta shiga *bulugul maram*
Duk yaran gidan yanzu ita ke masu kari.
Cikin sati uku ta canza sosai girma yazo mata lokaci daya kirjinta ya cika sosai.
Duk bayan kwana biyu take hawa sama tana gyara masa, haka zata kunna gwanja tayi ta
tikar rawa tana aiki sannan idan ta gama tayi mai isarta sannan ta sauko,
Ko sunan madaki bata son taji an ambata ta gama tsanar sa a zuci yar ta bata kaunar kara
gajinsa.
Gareshi kuwa a bin ba haka yake ba, ya kagara ya dawo wani lokacin yana jin hayaniyarta idan
suna waya da mamee kamar yace mata bani ita.
Ko tambayarta ya kasa yi ina uwaninki.
Ya dankaro mata tsaraba, dogayen riguna, kayan shafa da turaruka, tunda ya siyi kayan yake
tunani idan zai bata me zai ce ko kuwa yaba mamee ta bata kara taki karba? Haka dai ake
kullum ba canji oga umar madaki.
Sanye take da doguwar rigar material fari da flowers pink dinkin ya kame mata kugu ta kaso
kallabi tana faman gyara mishi gado.....
Mamee na falo taga mutum kamar daga sama,
Ta washe baki saukar bazata...??? Yayi yar dariya suka gaisa, ya fara dube dube,
Kamar uwani tasan da zuwanka wallahi, tana ta cewa sai gobe zata gyara ma sama kome ta
gani? Kuma dai ta tafi, yanzu ma ai ta kusa gamawa.....zumbur ya mike ku hau man da
jakunkuna sama yabi bayan su mamee bari nadan watsa ruwa na gaji. Ai dole da gajiya kam,
Daya ke dakin bude yake sai kawai taga ana shigowa da jakunkuna...... Ta zaro ido, tayo
tsalle ta dirko *ya dawo ne*?
*Ga ma shaida*...... Ya fada lokacin da ya kunno kai...........

*maman Abdallah*

😘😘😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣3⃣

..... Yau ni naga bala'i ni umaimah, wannan jaraba har ina? Nikam na debo ruwan dafa kaina.
Kullum abu daya yaki ci yaki cinyewa, kai ina amfanin abinda baya wucewa a rayuwa?
Ikon Allah ashe ya san sunana tsabar wulaknci ne da gadara yasa yake kirana da *ke* ko
*wannan yarinyar* Mi zanyi da wata jaka? Nasan menene a ciki? Duk girman jakar nan ya ce in
dauka. Tabb da alamar tambaya. Bacin daukata sakarai da yayi ina jin hada rashin wayau ma
duk babu yake tunani. Allah gani gareka, Allah kadai yasan gobe me zan tarar ni umaimah. Ka hana kanka zaman
lafiya ka hana kowa?
Ta tuna idan mamee ta aike ta gidan su kawu yanda take tarar dasu cikin nishadi da walwala
amma idan suka shigo bangaren sa kowa jinin sa kan akaifa.
Tana son fita harabar gidan amma shaggun ma'aikatan nan zasu ringa mata dan kira suna
*fine girl* masu jin hausan kuma *yar Fulani*...
Kiri kiri gida ya koma mani kamar wani sansani, kullum zan tafi ina zullumin me zan tarar ga
madaki idan yana gari.
Wani lokacin kamar yana da tausayi amma wani lokacin ya zamo mugun karfi da yaji shin ko
dai yana shaye shaye?
Amma kuma ai baya layi da magagin dasu yaya Abba keyi ko kuwa tasu kwayar ta masu kudi
kwalwa kawai take tarwatsawa?. *NI KAM UMAIMAH NA SHIGA UKU*
Da gudu kowa ya fito masu aiki da mamee. Yayi tsaye yana faman kallon kofa.
Duk sukayi turus!
Kai lafiya? Mamee ta bukata,
Ya kalli yan aikin kuyi *clearing* ya haye sama.
Mi ke damun yaron nan ni jikar buzaye? Abinda madaki kullum kara hauhawa yakeyi fa.
Yarinyar nan ta maidani sakarai ko? Lallai bazan dauki iskanci ba. Wai tana nufin zanyi asara
ne? Ya kalli jakar tabb...
Duk yau ya kasa cin abinci.
Wannan masifa da me tayi kama, yarinya karama ta hanani sukuni? Tunda Allah yasa yarinyar
nan ta shigo rayuwata zuciyata ba kara samun sukuni ba.
Wai duk me ke haddasa mana wannan rashin fahimtar? Nida ita wake da laifi? Ya buga tsaki
ita ce ,
Tana fama da rashin kunya ni kuma bana daukar raini.
Zan saisaita mata zama, ya tashi yayi alwala ya nufi masallaci nan cikin gidan sa.
Takwas da rabi ya shigo zaune take da baki bai ko kalli inda suke ba yayi hanyar sama.
Kai nake jira, mamee ta fada ,
Ya waigo cike da kulawa fuskar nan tashi murtuk, ta mike tayi ciki alamar ya biyota.
Yan mata ne su uku ya kara kawar dakai duk suka bishi da kallo.
*Yaro matashi mai tashen naira*. Kirarin sa kenan a gari. *madaki nada kyau* shi ba fari ne ba
amma saboda hutu, kudi da kuma jin dadi yasa farat daya baka iya gane hakan. Irin kalar nan
gareshi ta bakake mai kyau watan mai haske kamar chakuleti. Amma yana da sumar kai mai
laushi da tsawo. Kullum tana kwance luf luf tana sheki da kamshi. Dan gayu ne na karshe kuma miskili na kin karawa.
Ya kasa yin budurwa saboda mugun miskilancin sa ya ce babu macen da zai yi wa bauta ko ya
bita yana lallashi bare uwa uba har ya mata laifi ya bata hakuri. Duk Wanda ke tare dashi yasan

haka,
Mamee ta kalleshi cikin ido. Gaban sa yayi mugun faduwa yasan doka ce zata saka mishi ko
umarni ko kuma wani gargadi mai amfani.
Kaga yara falo? Kaje ciki ka ga wacce tayi ma duk na san halin ko wace ciki da mahaifanta,
tunda ka ce baka son auren zumunci. Sannan na baka dama har kishi uku kana *failing*
Ya kalleta namee ....wallahi bazan kuma sauraron ka ba, kaje kayi abinda nace kada ka hadu
da fushi na. Haba madaki ya zaka maidani sakarai kana nufin baka aure ko me? Ko kuwa
matan banza kake bi namiji cikakke kamar ka bai yiwuwa ace har yau bakaji son ko wace mace
ba........ai kinyi sauri ne mamee. Ta daka mishi tsawa nayi saurin don iyayenka, kaje kayi abinda na umarceka kada ranka ya
6aci.......
Ba kince kin san halin ko wace ba? Kije duk wacce tayi miki cikin su shi kenan......yasa kai ya
fice kamar ya kurma ihu don takaici.
Tayi kasaké...!!! Wannan taurin kai na madaki ya zanyi dashi?
Ransa ya gama kara jagulewa, tayi wayar duniya ya sauko yaci abinci yace ya koshi. Haka ya
kwanta ga azababben tunani ta ko'ina ga yunwa.
Haka ya kwanta har safe ga cook din sa baya nan yayi tafiya,
Karfe takwas ta iso, mamee tayi kiran duniya yazo ya yi kalaci amma yaki daga waya,
Duk tunanin ta fushi yakeyi, har karfe goma bai sauko ba,
Ta kwala ma umaimah kira, tazo.
Hau sama ki kira man umar.
Hmmm kawai ta fada ta juya. Don bata san me zata fadawa namee ba.
Shin ai duk masifar sa bazai dauki raina ba ko? Wata rana sai labari. Ita kadai ke sabbatu,
tana tafiya, gabanta na dada faduwa.
Ta kwankwasa har kusan sau shida ba ayi magana ba. Tayi tsaye tana tunani kada ta shiga a
kara yar gidan jiya, har zata juya sai taji wani irin kakari daga ciki. Ta saurara da kunne tabbas
shine. To lafiya? kakarin amai taji ta Murza kofar taji ta a datse, ta sauka da gudu ta nufi dakin
mamee tana kwala mata kira mamah! Mamah!! Mansura ta tareta ta zagaya baya fa. Tana jin haka ta yi hanzarin zuwa ta dauko mukulli ta kara hawa saman da gudu.
Kwance yake saman kafet cikin amai ko in ce kumallo, gashi yana fama da ulcer. Ya duke
yana ta murkususu ya dafe cikinsa.
Ta doka salati ta nufi inda yake ta dago shi *baka lafiya?* da kyar ya daga kai *Bani wani abu
in ci please*
Ta sakeshi da sauri ta kara yin kasa, duk an shirya kalaci a table ta hado tea da madara ta
zubo farfesun koda ta hanzarta.
Yana inda ta barshi. Ta ajiye kayan ta kamashi zaka iya tashi? Ya girgiza kai alamar a'a. Ya
hakuri ka daure bana iya dagaka ta yaya zakaci abinci cikin amai?
Ya daddage ya dafata zai mike ta durkushe duk suka fadi gefe. Ta ce wash!
Ungo sha tea din. Ya kasa motsawa. Ta lura tabbas ya gama galabaita sai kawai ta ringa diba
tana bashi.
Yaushe rabon da ya sha tea da madara?
Ta dunga dura mishi da spoon yana sha yaji dadin da ya rabu da ji a rayuwar sa.
Tana bashi tana faman sannu.

Ya shanye duka, ta dauko naman shima ta fara bashi, ganin ya fara farfadowa ta kalleshi
kamar hada yunwa ma ciwon.
Ita ce ma ba ( kamar ). Jiya banci komai ba gashi ina da ulcer.....ulcer? Ai wannan wauta ce ta
fara bambami, gashi ka garkame daki ai da kayi mussai yau.
Ya kalleta sai ta bashi dariya, yayi murmushi kawai.
Wai me ma ya kawo ki dakina?
Ta dalla mishi harara nazo *ceton ka* ya dan tureta zai tashi yayi luuuu ta taroshi da sauri ya
fizge ta bishi da kallo. Me ya kawoki dakina?
Mamee ke kiranka.... Kada ki fada mata abinda ya faru.
Naji ta fada tare da mikewa. Ya tashi da kyar ya dauko magani yasha.
Ta tafi ta mayar da kayan . ya sauko ya nufi dakin mamee yaji kiran.
Umaimah kuwa tana kai kayan ta koma saman ta goge aman ta gyara mishi dakin tasanya
mishi freshener ta canza mishi bedsheet sannan ta shiga kewaye ta wanke mishi.
Tana gamawa ta tabe baki. Allah yasa yau ya zame mishi ishara ya rage zafin rai.
Tana sauka shi kuma yana hawowa, ya kalleta sama da kasa, ina kuma kika je? Me kike mun
a sama.
Ta kalleshi ci ke da takaici, abar hali aci me? Gama rasa me zata ce mishi kawai ta raba shi ya
fincikota ya hada da bango.
Bana hanaki ina magana ki gudu ba?
Ta kalleshi kai wane irin mutum ne?
Irin ki ne.
Ta girgiza kai ni ba haka nake ba........ Ke bakinki bai mutuwa ko?
Ikon Allah, ta fada.
Saboda bana son maganar zan tafi ka dawo dani shin me kake so?
Jiya kin mayar dani sakarai kin pretending na shiga ciki kin gudu ko?
Kin gwammace in rike albashin naki da ki dauki jakar can ko?
Kwarai kuwa na hakura da albashin. Don haka bani wuri in wuce.... Ta ingijeshi ya daki karfen
bene ta baya.
Tana yin step daya ya murdo hannunta ya maidota da karfi jikin sa ya maida hannuwan sa
duka bayanta.
Wani takaici ya diran mata sai kawai ta dora kanta a kirjinsa tana kuka.
Jikin sa yayi mugun sanyi, yayi shiru!!!... Tayi mai isarta tukun, ta dago, yayi saurin sakin ta, ta
kalleshi idanu jawur, na rasa yanda zanyi da masifar ka, munzo na baka hakuri na daina shiga
sha'anin ka, kullum da abinda kake tokalowa.
Bana son hadaka da mahaifiyar ka amma ka kasa ganewa. Kwallah suka shatato mata.
Na gaji na gaji. Wallahi zakayi dana sanin wulakancin da kayi man yanzu. Bani kwadayin
kudin ku. Ina yiwa mutuncin mahaifiyar ka ne.... Kuka yaci karfinta da gudu ta sauka. Ya bita da
kallo kaman ya kamota ya bata hakuri amma baya iyawa.
A sanyaye ya hau sama, turus yayi ganin yanda dakin ya koma, ya zaro ido innalillahi
yarinyar nan ashe gyarawa tazo tayi. Ya dafe kai *ohhhh my God* jikin sa ya kara yin sanyi,
Umaimah kuwa tana baya ta lafe tana ruzgar kuka, tayi mai isarta, sannan ta goge fuska, *In
shaa Allah bazai kara ganina ba* ko mamah ta aikeni zan San dabara amma wallahi bazan
yarda ya kara sanya ni a ido ba. Kuma na rantse da Allah sai ya bani hakuri akan wannan

wulakancin.............. Turkashi.

*MAMAN ABDALLAH*

MU KWAN LAFIYA😘😘😘
[1/25, 8:02 AM] Bahajatu: 💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣1⃣2⃣

Gabanta yayi wani mugun faduwa, ya kura mata ido ta bala'in canza mishi, ya fara taku zuwa
inda take tsaye tana yar kyarma,
Ta fara yin baya baya yana biyota har sai da ta kure ma bango, ya sa hannuwan sa duka ya
dafa bangon yayi mata katanga tare da sunkuyo wa dai dai fuskarsa fuskarsa murtuk..... Ke
baki iya gaisuwa ba? Ko kinfi karfin kiyi man sannu da zuwa?
Ta dago kai aiken ka nayi?
Me yasa kake da neman dalili?
Ta ingijeshi ai fa ka dawo,....ya fizgota da karfi ya buga bayanta a bango. Ai fa na dawo? Ni da
gidana kike fadan aifa na dawo watan baki so na dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0