Showing 54001 words to 57000 words out of 63115 words
waiga da sauri mama yaya ke kiranta waje,
Au to tashi kije umaimah kinji.
Ta mike suka wuce.
Khausar tayi saurin bude mota ta turata, ita kuma ta shiga daga gaba yaya gata nan.
Ya kalli driver kai muje...................
*Barkan mu da juma'a*
*Maman Al'amyn , Amynatu da Abdallah*í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜
[1/27, 7:43 AM] +234 806 091 7227: í ½í²‘ *AUREN FARI* í ½í²‘
0⃣3⃣2⃣
..... Ta firgita ta daka ma drivern tsawa *Wallahi ka tayar da motar nan zan shako ka ta baya
muyi hatsari.....* ya rikota ke umaimah...... Ta fizge au an daura auran ma bazaka shafan lafiya
ba? Wai meke damunka? Kwallah suka shatato mata.
Gaban khausar ya buga da karfi yaya madaki umaimah ke ma tsawa? *Kut*.......
Umaimah wallahi wallahi idan baka fidda ni motar nan zan bala'in kunya ta ka yau........ Ya
bude kofa da sauri *Allah ya baki hakuri*........ Ta fito da gudu tayi cikin gida.
Khausar jikin ta yayi mugun sanyi ta bude mota zata fita ya kirata a hankalii, khausar, da sauri
ta ce na'am,
Ki kulan mu da ita please , taci abinci?
Saura kadan tayi dariya ta ce au wai yaya abincin zaka je ka bata yanzu?...... Ya dalla mata
wani mugun kallo ke tambayar ki nayi don ubanki.
Tayi sukuy sukuy, eh mama na bata tana ci ko bata so.
Okay jeki kawai.
Ya bita da harara kamar ita ta kashe zomon.
Ta murguda baki kaiji yaya zai huce a akaina. Ta kara jinjinawa. *Kut* lallai umaimah
*Tabbb*.... Haka ta ringa yi har ta shiga ciki.
Yana hawa sama abokai suka yo mishi chaaaaa ya sha mur ya wuce dakin sa. Nan ma cike
da mutane, ya ingije *Ibrahim bababa* ya kwanta ruf da ciki.
Duk aka kwashe da dariya kuzo *Madaki zai fara kuka*.........nan aka yayyabeshi ana mishi
tsiya.
Khausar ta shigo ke umaimah haka kike wahalar da yayan namu? Ina ma laifin....... Khausar
fita don Allah ta daga mata hannu.
*Mamza* tayi tayi umaimah ta tsaya ayi mata kwalliya tace bata so a bari sai anjima idan za
aje dinner.
Karfe uku aka zo a ka tafi da ita gida anan aka mata fada tun tana kuka ana ji har ya kasance
sai dai hawayen kawai ke fita.
Karfe hudu aka dauki amarya, akayi akayi *madaki* yazo su bar gidan ya ce wallahi ba in da
zai tafi.
Haka aka kawo umaimah saman cike da abokansa aka wuce da ita daki, sai leken ta akeyi
kowa so yakeyi yaga fuskar matar *Madaki*
*Bababa* ya kai mishi duka to don ubanka gata nan mun kawo.
Ya balla mishi harara au bata ce *Bata zuwa ba?* ya maida kansa bisa filo *Duk wayon
amarya sai ansha man ta* aka dau ihuuu...... Duk saman benen ya amsa. Hankalin umaimah ya
kara tashi ta fashe da kuka,
Da kyar aka lallasheta bayan magariba aka mata kwalliya shima sai da khausar ta kira
mamee ta waya ta mata magana.
Takwas dai dai aka fito za aje *Dinner* duk ya rikice kagare yake a fiddo mishi ita. Wani
matsiyacin farin boyel ne fari jikin sa kai *Madaki* yayi kyau samira na gefe yake kawai takeyi
tana bala'in son *shi* amma inaaa ya mata nisa yau.
Yanda yake ta rawar kafa yasa ta kara saduda.
Yana zaune cikin mota shida Ibrahim sai faman tsoki yakeyi shi kuma banda dariya babu
abinda yakeyi mishi.
Ya hango an riko mata riga yan jarida anata binsu da camera ya bude mota.......ya riko
hannunsa please *Basar*....... Ya fizge *ubanka ne in basar* kawai ya fice yana zuwa kawai ya
dauketa yayi sama da ita......
Yan jarida har gudu sukeyi kofar gidan ya rikice da ihu.
Ya shigar da ita mota sannan ya amshi sauran rigar da suke riko ya sanya ya kalli kowa yana
yar dariya *Kowa ya shiga mota*......... *Yallabai yallabai*....kawai ya shiga ya ja kofa yana fadin
ban taba ganin banzaye irin yan jarida ba yanzu ne lokacin bayani?
Gabana kake zagin yan jarida madaki?
Ya dafe kai *na tuba* ( mahaifin Ibrahim) tsoron Dan jarida ne.
Ta na ta kame hannu idanun sa ya kai visa kunshi ya zaro ido ya fizgon hannuwan
*Wawwww* ...... *kaiiiii*...... Ya daga rigar kadan yaga na kafan ta duma mishi kulli ya fasa
kara......kai wallahi ban son iskanci zan fita ka nemo driver.......... *Duka na tayi na rantse da
Allah* ya fada yana dariya. Ya juya yaci gaba da Yuki yana fadin *Tamun dai dai* Kyan ka dukan ai.
Ya kalleta *Wallahi na yi sa'a wurin nan tsantsari*...... Bababa ya tuntsure da dariya.
Ya buga mishi harara Allah ya isa ka kara jin firar mu.......... Ta bika, waya hana ka dauko
kurman driver.?
Ya tallabo fuskarta yana murmushi, yau dai a barni in taba inda nake so....... Ta tureshi da karfi
zata ja baya ya fizgota *Wasa na keyi jira* sannan ya Dan saketa,yana dariya.
Ka dai firgitataka gani idan........ Allah ba kai zaka maido mu ba don na lura nayi zaben tumin
dare don ubanka.
Ya kalleta ki ce mun wani abu mana, Ke ko masifa ce yi mun please.
Dai dai mota ta tsaya, ya buga tsoki ni dama suyi partyn abarmu anan ko umaimah?
Lokacin ne ta harareshi, Yayi Har dariya keni ba harara ba *Say something*
Abokan sukayi wajen motar tare da bude su kowa so yakeyi yaga fuskar umaimah, yayi saurin
rungumeta ta soke fuskarta kirjinsa,
Duk suka hayayyako mishi *Wallahi kai mugun dan iska ne madaki*
Kyaleshi ai duk janbakinta zai kare a rigar sa yayi saurin dago fuskar ta hakan kuwa akayi ya
tuntsure da dariya ya kalli bababa ka tuna bikin *sadiq* da aka mun barin miya?
Duk suka kwashe da dariya yace Allah ya kawota yau ma don ubanka.......ya juya fuskarta *ita
ce* .... Duk suka zaro ido aka dau ihu......
Ya kalleta *yau ma kin bata na AUREN ki*
Ta sunkuyar da kai *ita kawai tasan yanda takeji* ga kukan ma yaki zuwa.
Abokanta suka iso aka fito za a shiga.
Sound ya fara tashi na *Because you love me*
Ya kalli wata ya ce malama je ciki kice a sa mana gwanja........ Rawa zakayi yau ne?
Ya kalli umaimah *To gani dai idan ta amince*
Aka kure sautin best wakar sa *Indosa* aka fara taku hannunsa gam cikin na umaimah.
Gunguni kawai abokan sa keyi bayan sa. *Tsakani da Allah madaki ya dauko mace* tabbb
*Ziza*.....:Bashir ya ce *Kai ai wallahi tana da kyau ko hasadun izaa hasada ya ga waccen
yarinyar sai ya ce tayi*
Duk aka kyalkyace da dariya.
Yan mata an sha ankon leshi blue da head silver suna ta tattaka rawa, ya dan sunkuyo *ki Dan
taka please*...... Ta harareshi dai dai lokacin aka basu flasher....
*Dinner* madaki da umaimah ba a taba irinta ba a kano. Da aka yanka *Cake* ya debo ya
bata ta mika hannu aka fara dariya sai zumburo baki takeyi tana fushi ya tabe baki ya sanya
mata aka dau *sowa*, wurin bashi nan ma sai da akayi daru ya kawo hannun ya kai bakin sa da
kansa, ta wurga mishi harara. Abikan sa sukayi ta kyalkyatar dariya *kai madaki yau na shan
harara* shamsu ya fada, bashir ya ce ashe duk kun lura.
Shagali har kusan biyu sannan aka tashi maganar ciye ciye da liki ba sai an fada ba.
Umaimah dai da ance amarya da ango su fito sai tayi tsaye, yayi yayi suyi rawa takiya shi ma
sai ya basar.
A gida kuwa , su yaya bayan an tafi party suka hau sama ganin dakuna ana tabe baki,
Ta kalli jamila duk shi yayi komai 'yar kawai aka bashi.
*Hummm* ai ta raina mu kina ganin damu da banza duk daya sai su *maryam hamza* su ne
gaba gaba dasu ake komai.
Haka suka yi ta gulma da korafi ko *dinner* sai da kowa ya tafi har an fara suka isa, ko wace
ta ledojin ta a jaka na kullar abinda duk aka ci.
A mota suna zaune anata tafiya da mutane, tayi shiruuu kanta sunkuye gani kawai takeyi
tamkar a mafarki.Ya mata rada a kunne *Ko sai na siyi bakin za amun magana?*
Kirjinta sai bugawa yakeyi.
Dabara ta fado mishi, ya dan kawar da fuska ina so in fada miki jiya da sai dai kiji mamee a
asibiti...... Ta juyo da sauri *Me ya sameta?* ya sha mur hayaniyar mutane ce kawai.
Muryar ta duk tayi sanyi ta canza ta ce *Amma da sauki yanzu ko?*
To ban dai sani ba saboda yau din sau daya ma na ganta...... Ta ce hummm
Ya kusa yin dariya. Me na yi kuma? Ko ban kyauta ba dana fada miki?
Amma da ka kara komawa ka dubota ...... Ya kyalkyace da dariya.
Nan da nan ta gano shi.
Ta yi kasa da kai tana murmushi.
Ya kalleta duk kin rame kin sa ma kanki damuwa zaki zo gidan *Madaki*
Ko kuwa ramar ta an dade ba a kawo ki bane?......... Ya mu ta fi ko?
Bababa ya shigo yana kokarin tayar da mota.
Ya harareshi yi ka sauke mu na gaji da kai *Disturber*.
Suna isa, wani abokin sa ya zo suna magana ta sulale ta gudu.............
Bai kara ganin ta ba sai washe gari da yamma an fiddo ta sashen mamee tana gaisawa da
mutane ya hangota lullube, har ya juya zai tafi bashir ya fizgeshi sukayi waje............í ½í¸ƒ
Ba nan na so tsayawa ba na gaji araduí ½í¸ƒ
*Maman Abdallah*í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜ juma@ mabruk
í ½í²‘ *AUREN FARI* í ½í²‘
0⃣3⃣3⃣
*NURY*í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜í ½í¸˜ *only u!*
........ Duk ka tsorata 'yar mutane don ubanka.
Ya kyalkyace da dariya, yarinyar can wallahi bazaku gane ba gwala ni takeyi kamar kwallon
kafa.
Karya kakeyi kai da kace babu macen da zaka bi, baka ba mace hakuri, baka......Alhaji anji.
Suka kwashe da dariya. *waya fada maka barno gabas take*
Umaimah nata, kuka mamee sai lallashi takeyi, jamila ta turo baki *Yaya dubi mutanen ki*....
Ta tabe baki sa ji dashi kilibabbu.
Kinga sarkar da ta sanya jiya? Murja ta fada tana tabe baki.
Jamila ta ce ki duba wuyanta kiga ta yau tafi ta jiya sau hudu.
Aikin banza waccen figaggar yarinyar cinye su zatayi har babu.
Ai kunji tayi shiru har yau taki cewa da mu komai saboda munafunci da shegen zurfin ciki.
Yaya ta fada tana mazurai.
Ku jira Ku gani waccen maryam din data fifita fiye da mu zanci ma uwa munafukan banza.....
Yo yaya bakiga kudi ma ita take ba ajiya ba?
( uwa daya uba daya gaskiya basu duba wa mamee ba. Allah ya raba mu da hassada )
Hassada ciwo ce wallahi, uwa daya uba daya akwai ta kawai ta wasu tafi ta wasu fitowa,
Mamee ta ringa raba atamfofi super, da barguna masu kyau na kasashen waje, ga wasu
robobi, bokitai, glass cups, kai kaya barkatar, su yaya sai tabe baki sukeyi *Karyar banza*
( wai arziki kamar na madaki a kirashi da karya )
Akayi budar kai, kowa na ba umaimah kudi kamar yanda al'ada ta nuna su yaya na zaune
turus!
Bayan an maida umaimah sama suka baje bisa carpet, yaya ce me korafi *Naga ana wucewa
da tuwo mu banda mu?*
Hafsat tayi tsagal, tuwo zakuci? Yanzu kuwa, ta lodo masu har sai da yaya ta ce wannan tuwo
kamar rugaye?
Ta yi dariya tare da yada masu magana ta ce *wai don kuci Ku dauka kamar kullum* Duk
sukayi damama ta wuce bata bi ta kansu ba ta ciko wata yar roba da man shanu ta kawo masu
da ruwa da lemu sannan ta rike kugu da yake takadara ce ta ce *Sai me?*
Yaya cikin yake ta ce tuwon ya mana yawa da akwai leda dana dauki biyu saboda
dumame....... Jamila ta yi karaf nima zan dauki biyun nan........ Hafsat ta ce baku da matsala
yanzu zaku ga tuwo, ta je ta sami ledoji hada Wanda zataci ta lodo masu sannan ta ciko wasu
robobi da miya ta ce duk gashi ai tuwo baya hada fada gidan mamee.
Duk abin nan mamee ma bata San wainar da ake toyawa ba. Kawai masu tare fada ne Allah
ya kawo mata.
Dama hafsat hake take dasu wurin party ance iyaye su fito kawai su yaya suka kalleta suka ce
*Sai kuje iyaye* haka kuwa akayi ta tafi ta dunga rawa daman mamee ta bata himilin kudi ta
ringa watsama ango da amarya.
Ganin yanda hafsat keyi duk sai suka tsargu rashin kyautawa ya dan damesu. Suna gama cin
tuwon suka sulale ko bankwana.
( kai Allah ya ganar da masu irin wannan hali ).
Karfe tara abokai sukayi sukayi su rakashi ya ce wallahi shi zai kai kansa.
Sai da ya sallami kowa sannan. Suka mishi addu'a sosai saboda sunji dadin bikin sa yanda ba
a zato ya bada gidan man shi daya duk Wanda zai tafi yaje yayi full tank.
Banda kayayyaki da ya raba, generator, spare tire , mashin mashin, kai abubuwa barkatai.
Ya shigo karfe goma da kwata, mamee na ciki ita dasu hafsat, ya leka suka gaisa ya fito
mamin ta biyoshi, ya zauna falo, mamee na gaji.
Ta yi dariya da gajiya *madaki* sannu da kokari wallahi ka cika *Da* na gode Allah ya shirya
maka iyalinka ya baka zuri'a dayyiba.
Ammkinnnn mamee love, ya kukayi da mutanen ki?
Tayi yar dariya kai lafiya qalau, girgiza kai kawai kawai yayi yasan fada mishi ke bata son yi.
Uwani duk ta tayar da hankalin ta. Ta fada tare da langabe kai.,
ya danyi murmushi kawai,
Ta kalleshi don Allah ka dubi maraicin yarinyar nan kaji tsoron Allah. Wallahi rikon maraya yana
da matukar muhimmanci ga rayuwar dan Adam. Da mutane zasu gane falala da kuma dunbin
rabon da mutum ke samu idan ya kyauta ta wa maraya lallai da wasu sun ringa bi gida gida
suna sallamawa duk in da yake su dauko. Mamee zan kwatanta na sani.
Ta harareshi na san ka da zafin kai madaki uwani yarinya ce kada ka biye mata don Allah.
Kadai ji yan surutan da yan uwana keyi idan ka rike kanka idan kuma ka banzatar wallahi zan
dauki mataki....... Zan kiyaye mamee.
Jikin sa duk yayi sanyi.
Ta mishi nasiha sosai yayi shiru kawai.
Ta mike mu kwana lafiya sakonka nacen sama an kai. Ta shige ciki.
Ya mike a hankali yana zuwa yaga katon tire cike da gasassun kaji an rufe da foil paper.
Gaban sa ya fara faduwa, kamar bazai iya Shiga ba.
Tana zaune bisa gado kuka kawai takeyi , kukan maraici na ban tausayi.
Ya bude kofar a hankali.
Ta hadiye wani miyau dunkulalle cikin ta ya kada ya bada kulululu.......
Ya zauna shiruuuuu...
Ya dake ya fara magana cikin kakkausar murya . idan kin gama kukan zo nan in magana dake.
Tayi shiru ya daka mata wata tsawa..... Ta matso da sauri.
Ya yaye gyalen malama ki man shiru kinji.
Ta sunkuyar da kai.
Yayi kasa da murya, umaimah kamar an miki auren dole? Wannan kukan naki yayi yawa
gaskiya, ya kamota ya maidota kusa dashi.
Umaimah wallahi ba abinda zan miki kinji har na rantse, zan tafi dakina ma in kwana, amma sai
kin mun alakwarin zaki daina wannan kukan kuma zaki ci abinci...... Tayi saurin daga kai. Yayi
murmushi good.
Sha re hawayen toh, ya fada yana gogewa da hannu.
Jeki yo alwala muyi sallah tukun .
Ta mike tayo alwala sannan shima ya shiga, bayan sunyi raka'a biyu kamar yanda sunna ta
koyar ya dafa kanta yayi mata addu'ar da manzo SAW ya koyar sai ya fita ya dauko naman da
ice cream.
Tana zaune ta zabga uban tagumi ya dan kalleta, ni zan baki ko zaki...... Tayi saurin kai hannu
ta dauko ta fara ci.
Yayi yar dariya *Mrs madaki*...... Ta harareshi ya kyalkyace da dariya ba injini ba inji *yan
jarida*
Da ta janye hannunta sai yace au kin koshi? To kawai in kwana anan......sai ta mayar da
hannu haka har taci sosai, ya mika mata ice cream din sha kiban muyi kama kama inji yara.
Ta dan harareshi kadan, yayi murmushi.
Ya kalli jerin akwatunan lefenta ya ce *umaimah an bani da rowa* haka kika dawo da kayan
baki ba dangi ba? Ana rabawa iyaye da yan uwa fa,
Ai na basu, ta fada kamar mai koyon magana.
Haba? Ya fada ganin ta