Showing 57001 words to 60000 words out of 63115 words

Chapter 20 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

danyi magana.
Ta ce Allah.
Su wa kika ba?
Ta dan kalli jakunkunan
Na ba baba shadda goma, su goggo atamfofi uku uku, itama luba na bata lesuka da kayan
shafa, baba ma na bashi turaruka, an dibar ma dangi yankunnaye da atamfofi suma, sannan na
bada *Hajiya ta* leshi uku, atamfofi biyar.
Cewa zakiyi kin rabar da kaya kaf! Sai kawai Tayi murmushi shi fa ya kirata da mai rowa yanzu
kuma ta bayar yace ta rabar.
Ya kalleta yaushe rabon da ya ga murmushin ta?
Haka ya dan jata da fira har daya saura sannan ya ja mata kofa ya tafi dakin sa.
Yana fita ta saki ajiyar zuciya *Ohh madaki ikon Allah*
Barci ya dauketa saboda gajiya ga kuma kuka anci.
Shi ko sai kusan uku ya samu yayi barci yana ta gyare gyare.
Cikin kunnenta aka kira sallah, ta tashi da sauri ta shiga tayo wanka gudu gudu ta sanya wani
material ruwan kwaiduwar kwai,sai da ta gama sallah sannan ta dan shafa mai ta zauna lazimi,
shidda da rabi ta shiga ta wanke kewaye, sannan ta zo ta gyara gadon ta jera jakun kunan duk
ta dan gyara fasalin dakin sannan ta kunna abin turaren kamshi mai kamar kwanon glass ga
sanyin A.C, ta dauko wasu turarukan ta na cikin lefe ta feffesa ma labulan daki., nan da nan
dakin ya rikice da wani irin kamshi.
Ya dan kwankwasa, tayi saurin zama kamar tana lazimi kafin ta ce *Shigo*....Yana sanye da
jallabiyar da ta siyo mishi, ya dan turo a hankali sanyi da kamshin dakin ya daki hancin sa,

.......ina kwana, ya dan lumshe ido *Morning sweetheart* yayi suka bisa gadon mamee ta ce
idan kin gyara gado baki so a bata miki, ta mike tana ninke abin sallah tana murmushi.
Shi ne kika bari na makara ko? To Alhaki kanki.
Ta dan saci kallon sa kadan, ya tashi zaune miko mun littafin can, tana zuwa ya damko
hannunta, kilibabba kina ta wani satar kallon miji kedai umaimah baki waye ba, ta kyalkyace da
dariya tana noke fuska,
Ya cacumota bari dai in fidda miki kunyar nan ta daina takura mu........ Ta fasa ihu wayyo na
shiga uku wallahi na daina wayyo mameee.......... Ke tsaya saurara wasa nakeyi ya tallabo
fuskarta, wasa nakeyi ya jaddada mata da kai.
Duk illahirin jikin ta ya rikice da kyarma.
Ya kwantar da ita bisa kirjinsa yana bubbuga bayanta, ya hakuri wallahi wasa nakeyi.
Ya dan runtse ido, lallai yana da babban aiki wannan tsoron na umaimah yayi yawa.
Ya dagota, ki saki jikin ki dani ki yarda dani please bana son wannan tsoron da dararewar.
Ta danyi murmushi, ya ja hancin ta yar rainin wayo kamar ba matsiwaciyar yarinyar nan ba.
Kwanta muyi barci...... Ta zaro ido mamee zan gaido.
Ya dan muskuta ya cire jallabiyar daga shi sai vest da dogon wando ta dan basar don tana
motsawa zai jata jikin sa.
Ya mika mata, malama to lunke tunda cirewar ma kin kasa taimakawa, ke kam kina ban kunya,
idan miji zai cire riga sauri akeyi a cire mishi kar ya wahala...... Ta danyi murmushi . ita dai duk
bata amince da shi ba.
Ya maida kansa bisa filo don Allah kizo mu koma barci....... Bana ji. Ta ce a hankali.
Ya fizgota ke bazan dauki wannan gidadancin ba.
Na shiga.....yayi saurin rufe mata baki da hannu shiru kiyi barci.
Tayi lamoooo kirjinta na harbawa, ya kai hancin sa a wuyanta lallai amaryar nan kina zuba
kamshi. Gabanta ya fadi ta fara raba ido.
Yana ta faman zolayarta, a hankali a hankali taji ya fara saukar da numfashi alamar barci ya
daukeshi.
Ta saki ajiyar zuciya ciki ciki a hankali. Ta bashi kamar minti biyar sannan ta zame jikinta a
hankali ta maida mishi filo, har zata fita taga yadan ja kafarsa alamar kamar yana jin sanyi, sai
ta koma a hankali ta rufe shi da bargo sannan taja kofar ta fice,
Ta sauka, dakin mamee tayi ma tsinke, bata ciki ta zagaya dakin baki wadanda basu kai ga
tafiya ba su naryam hamza, hafsat, Aunty Aisha, duk dai aminan ta suna nan.
Sai kawai ta fada toilet ta wanko shi fes!
Sannan ta shiga gyara mata dakin, duk wani sako da loko sai da ta sharo shi,
Sa'annan ta goge ta feffesa abun kamshi, ta kusa karasa gyaran wodrop kenan taji mamee ta
rafka salati bayanta.
Mi zan gani ni *Rabi*, uwani??????
Ta yi sauri ta isa kusa da ita tana murmushi tare da zukunnawa *Mamah* Ina kwana,.
Ta kamota ta mike, wanene ya turo ki wannan aika aika? Ina madakin?
Ta dan dukar da kai *Yana barci*........koma sama maza ga kalaci can an hau dashi...... Kuji
mun yarinya ni jikar buzaye kai *Uwani* al'amarinki sai ke.
Ta danyi dariya kai mamah bari in karasa gyaran...... Ke bani son iyashege kinji zaki koma
daki ki huta ko sai..... *Kai mamah* ta fada kamar zatayi kuka, ta dauko kwadon zuba shara ji fa

abinda na sharo dakin nan in banyi ba waye zaiyi?
Su mansurah ta bata amsa. Ta zumbure baki ta juya tana ci gaba da lunkewa.
Ta matso kusa da ita, zaki wuce ko sai na kwakkwada miki wannan ludayin da ke hannuna.
Maza kije ki tado mun shi kice yazo su Aunty salma zasu tafi dasu Hafsa....
Ta danyi murmushi Allah dawowa zanyi ko na kirashi ta wuce ...... Ta bita da kallo tana yar
dariya *Uwani* ....... *Uwani* ikon Allah.
Allah dai ya baku zuri'a dayyiba. Wannan kuruciyar taki gara yazo ya daukeki kubar kasar can
kya dan natsu kisan kin girma ja'ira.
Tana buda kofa ya farka, amma sai yayi shiru cikin bargo.
Ta zo tayi tsaye kansa tana alwalar kuda, ya fara dariya saboda tabbas yasan kiransa zatayi.
Ta dan juya *Kazo inji mamee*, yayi shiru
Ta kara cewa, shima ko motsi,
Ta ce *Madaki*........ Ya lumshe ido kamar bakinta sunan ya fara fitowa,
Kaji mamee na kira shima yayi shiru,
Ta dan sa hannu ta yaye bargo kawai ya fizgota ta fada saman sa,
Innalillahi dama kana jina?
Ba'a sani ba, ke dai ba kauya ce an fada miki ko a kauye yanzu ana tada miji haka?
Ya kara matseta, haka zaki dan hawo sannan ki dan mun kiss kamar haka...... Ya mata a goshi
sai ki fara cewa *Honey*......... Kina dan shafani.......ta wuntsula ta sauka ya kyalkyace da
dariya.
Mikon rigar in saka, tana daukowa ta wulla mishi ta sauka da gudu ya fara dariya.
Shi ya kai su Aunty bintar airport da kan sa.
Kiri kiri mamee ta hana umaimah saukowa dole ta tafi daki tayi zaune.
Ya shigo da sauri rike da kayan kalaci, yarinyar nan abinki akwai son kai shine kika gama cika
cikin ki ni ko in gane?
To zo muci mamee ta koroni yau.
Tayi murmushi nima koroni tayi.
Ya kyalkyace da dariya kyaleta gobe kamar yanzu mun bar mata gidan.
Ta kalleshi da sauri,
Ya kai dankali a baki *Dubai zamu honeymoon*......................

*Good morning*

*Maman Abdallah*😘😘😘😘😘

Godiya ta musamman ga *Salamatu dahiru* ( MZ)

Ayi mun uzuri yau post daya zanyi. Wannan.
💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣3⃣4⃣

*Gareki AYFA ( AYSHER BAITEE )*�😘😘😘😘

*Mrs Faruq*

......... Ta zumburo baki.
Ya kalleta da kyau bazakije ba ne ko kuwa Dubai din ke bakya so?. Ki fadi kasar da kike so
umaimah you have that right.
Ni ba tafiyar ke bana so ba zolayar nan ta jirgi idan zai tashi nake tsoro wallahi hanjin cikina
kamar zasu fito........ Har kwanciya yayi saboda dariya ta yi murmushi wallahi ka fiye mugunta
kai kuwa.
Sai da yayi mai isar sa sannan ya ce ba irin wancen jirgi zamu hau ba, wannan na daban ne
sha kurumin ki wifee.
Ta ce *Hmmm*
Ki matso muci ko na kamoki yanzu nayi miki dura,..... Ta matso da sauri saboda tasan duk
abinda madaki ya ce zai yi to zai iya, suna ci yana janta da fira.
Wayar sa tayi kara, gaban sa yayi mummunan faduwa ganin sunan samira, ya dauka idan ta
gane mace ce ya shiga uku, ya ki dauka shima matsala.
Ta dan saci kallon sa ganin waya nata ringing har tana niyyar katsewa, ya dan bata fuska ya
daga yana kallon fuskar ta..... Hello Aunty har kun isa?
Samira ta dauke wayar daga kunnen ta tayi saurin kallon screen din tana zargin ko ba
*Madaki* ta kira ba,
Yaji shiru, yaci gaba da cewa amin na gode Aunty Allah yabar zumunci ya latse wayar. Dai dai
ta mayar da ita kunne itama.
Toooo faa! Ta fada tana zaro ido, wai ya akayi? Ta mike tsaye, lallai abinsa azimun ne wannan
yarinyar tsoron ta yakeyi kamar rai da ajali. Abinda yafi na shafa ma kaina lafiya da *Matashin
yaro* idan ya nemeni welcome idan bai nemeni ba kuma umma ta gaida asshhaa ina dalili.
Ya kalleta tana ta tura dankalin da kyar sai kawai ya sha mur, ke juyo ki fuskance ni.
Gabanta ya dan fadi ta juyo tana kallon sa kanta a kasa,
Na lura sai na biyo miki ta bayan gida sannan zamu shirya ko? Kin dai san yanda mukayi jiya
da ke ko?
Ta daga kai *Eh*
To ina nan akan baka na babu abinda zan miki, sai dai dole ki sauarara kin kindaya miki
sharudda saboda yanda na ke kokarin tsara zaman namu bazai taba tafiya dai dai ba.
Kin dai San yanzu ke matata ce ko? Ta daga kai *Eh*
Good to bazan jure wannan makurewar ba wallahi kinji na rantse. Na farko anan zan kwana yau
nida ke saman gadon can...... Ta zaro ido wallahi na tuba zan yi yanda kake so.......... Jira da
Allah malama, kawo man ke akayi in kalla? Na ce ba abinda zan miki kin kuma San abinda
nake nufi da hakan sai dai bazan iya hakurin wannan makurewar ba, idan kin hana in taba ki
baya yanzu dai baki da iko.
Magana ta biyu zaki ringa bani abinci daga yanzu a baki har in koshi, sannan ba maganar
zama nesa dani ko kusa dani kin ga nan? Ya bugi cinyar sa nan ne mazaunin ki Allah. ......zatayi
magana ya daga mata hannu *umarni nake baki* ba wai ina neman shawarar ki ba.
Tayi narai narai, sai magana ta uku idan ina barci zaki tasheni dole kema ki kwanta kusa dani
kina shafani a hankali kina kiran sunana har na farka ko kin gane?
Ta daga kai *Eh*

Good taso ki dawo nan toh ya janyo hannunta , tayi sukutii ....ya kalleta wallahi ki ware kawai
don baki ga komai ba game da dokokina ba.
Ta fara debo dankalin zata bashi ya ce hajiya ajiye chokalin da hannu ake ba mai gida
abinci........
Na bani kawai.....ta fada azuci.
Da ta bashi ta kara debowa sai ya rike hannun ranki ya dade ba a sauri *Slowly*........ Ya kashe
mata ido.
Ta yi dai sukuy, yana koshi ya gyara zama sannan ya rungumeta kamar jaririya yana bata, (
yau na ga ta kaina ni umaimah ) ta fada kamar ta nutse.
Karfe biyu ya shirya ya ce mata zai je cikin gari.
Tana fitowa ta kira su bilky ta kwashe bokitan gara duka ta ce a mayar sashen mamee hada
manshanu.
Tana ciki tana harhada kudin gudunmuwa bata san wainar da suke toyawa ba, umaimar ta
shiga . Tana ganinta ta washe fuska 'yar halak yanzu nake tunanin ki a raina.
ta zauna tana tayata harhadawar mamah kuma ba sai ki kirani ba?
Tayi dariya kawai, ashe gobe zaki kara katari da nutumen? Duk sukayi dariya sannan ta turo
baki wallahi bana kaunar abinda ka kara hawa dani jirgi mamah ki ce a bar tafiyar don Allah.
Uwani ina ni ina hana tafiyar da an gama komai gobe goben nan?, to ki shirya mu tafi tare don
Allah mamah......... Ke bani son iyashege, haka kawai sai in biku?
Ta langabe idanunta suka kawo ruwa wallahi zanfi jin dadi idan muka tafi da ke don ni tafiyar
gaba daya bana so........ Ta ajiye kudin hannun ta kafin ta kamo hannuwanta duka biyun.
Uwani ki kwantar da hankalinki ba abinda zai faru sai alkhairi, idan kuka tsaya garin nan
tabbas ke kanki abin sai ya dameki saboda fitar nan da kika ga yayi office ya tafi, wallahi
matukar madaki na garin nan bazai huta ba.
Kuma kema dama ce gareki da zaki San me mijinki keso meye baya so........ Bata san lokacin
da bakinta ya kucce ta ce humm ba.
Bata bi ta kanta ba taci gaba da cewa, kuma kya gano gari kiyo kallo tunda naji yawo zakuyi
kasashe don jirgi ai sabawa zakiyi wancen ma don karonki ne na farko.
Ta fara janta da yar firarraki har ta dan saki.
Suna zaune falo ya shigo tara da rabi har ta gota, uwani da mamee ya fada yana murmushi, ina
so inji yanda firar ku take kasancewa yanzu su uwani an zama matar madaki,
To rasa kunya beran tanka,zaka fara ko?
Uwani tashi ki tafi daki kada ya hanaki sakewa kinji, tayi zumbur ta wuce simi simi ya bita da
kallo iyye yarinya sama tayi yau bad akin mamee ba…….itama mikewa tayi ta wuce ciki, yana
waigowa yaga har ta kusa shigewa y ace mamee ina zuwa? Ko waigowa batayi ba barci nake ji
kasan akwai gajiya tayi ciki. Ya danyi murmushi kai mamee karshe ce wallahi.
Tana ta kakkabe kakkabe tama rasa me zatayi hankalinta a tashe wai gado daya zata kwana da
madaki. Ta yi kasa da murya ba abinda ke cikin aure sai fargaba, takura, zullumi da tsoro.
Wallahi kamar in gudu nakeji………….ki tafi ina?
Tayi firgigi ko kadan bata ji shigowar sa ba. Ta danyi kasa da kai, ya kamota zo nan meke tayar
miki da hankali kike tunanin guduwa?
Ya bata rai umaimah dana san baki kaunata da ban aure ki ba…..Allah bah aka bane, to

menene?
Tayi shiru, ya zauna bakin gado ita kuma ya dorata bisa cinyarsa, umaima wallahi aure da kike
ganin sa babu abinda ke ciki sai jin dadi, farin ciki,walwala da nishadi. Shi yasa Allah SWA cikin
suratul rum yake cewa : kuma na halitta maku matan aure sannan na sanya soyayya da
nutsuwa a tsakanin ku lallai wannan ayar mutane ce masu yin tunani. Saboda haka ki saki jikin ki wallahi zan jiyar da ke dadin da ba’a taba jiyar da wata mace shi
ba, zan shagwabaki yanda ake shagwaba yaro daya tilo wanda iyayensa suka samu bayan sun
dade suna rokon haihuwa kuma daga shi basu karaba, zan kula da ke yanda duk baki
tsammani na jiyar da ke dadin da ba kowa ce zata sameshi ba. Abinda duk kike tsoro sai ya faru yau, gobe , jibi ,next month,next year ke any time but zai zo
miki lokacin da baki tsammani lokacin da baki tsorona, lokacin da kika saba dani, lokacin da
kika san dadin madaki…….. kawai ki saki jiki dani wannan shine abinda nake bukata umaimah
saboda ni mutum ne mai son kula, kuma ina sha’awar taba jikin ki wanda baki isa ki hana ni ba
duk tsoron ki duk wata makurewa da zakiyi.
Tun kafin in fara gwada miki karfi kawai ki ware hajia, ya tallao fuskar ta. Ya harareta wallahi
matukar baki rage wannan kunyar ba tabbas zan gaggawar wancakalar da ita a wuce wurin….
Kinji ko?
Ta daga kai tana murmushi.
Kilibabba irin ku kunfi jaraba sumimu kasau, ni yanzu gashi dai na karya record yau idan kinji
wayoyin abokai dana amsa wani dan iska ma cewa yayi zai zo ya rakani in kaiki asibiti. Basu
san cewar ni madaki ba haka nake ba lokacin da ake tunanin da zanyi abu sai na kiyi ko laifi
akayi man lojkacin da ake tunanin zan dau mataki sai anyi shiru, wallahi umaimah sai kin zauna
zaki fahimceni bani da fitina da kike ganina na mugun miskili ne ni kawai ke baaki gane bane
saboda yanayin chakwakiyar mu ko kuwa? Duk suakayi dariya,
ta ce wai chakwakiya, eh mana ko kin manta yakin da muka gabza kika farden hannu? Ya
kyalkyace da dariya kai naga bala’I ni ummaru.
Tayi murmushi, ya mike ya fita sai gashi da gyalen hajia wanda ta bata aro lpkacin da suakyi ma
juna wankan miya a fatin asma’u, ta fara tafa hannu tana salati, daman yana hannunaka? Ya yi
murmushi ke wannan gyalen ai kusan haukatani yayi lokacin da muna cikin fitinar idan na dauko
shi zuciyata har hayaki takeyi don azaba. Da kuwa na kamu da son ki da kin gudu kin barni sai
na zo na daukeshi ina bege. Ta kyalkyace da dariya ta ce wai bege.
Nan da nan ta sake kawai suka hau fira hada tafawa, sai kusan sha biyu ya watsa ruwa yayi
yayi da kyar ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0