Showing 51001 words to 54000 words out of 63115 words

Chapter 18 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

ce, Ya turo iyayen sa, munje kauye an yi magana kinga dai
dawainiyar da yake tayi kinga gida kinga dakunan iyayenki jibi nawa, don Allah kada ki bamu
kunya.
Ranar sallah za a daura auren ki dashi.......ta dago ido cikin tsoro baba ranar sallah kuma? Sai
ta fashe da kuka.
Ya bata fuska to uwaki za a jira? Au na baki hakuri shine zaki tayar da hankalin naki?
Ni dai baba a bari sai nan gaba duka nawa nake....... Yaro ba mutum ba . amma umaimah kin
tabbata sakarai.
Yayi kasa da murya ni zaki kunyata ki tona ma asiri saboda ko habaici ya isheni gidan nan ga
shi kinzo kuma zaki kara janyo mun wata maganar. Dama suna fadin asiri akayi daman tallar ki
muka kai sun manta lokacin da kika sami aikin ma bakin su na ji.
Ta ci gaba da kuka kawai duk hankalinta ya tashi, sallamar hajiya ta jiyo har zata mike ya ce
zauna ta shigo nan.
Hakan kuwa akayi suka taru suna kwatanta mata tare da kwantar mata da hankali saboda ita
kanta hajiyar madakin yaje har gida ya sameta.
Ta wuni kwance daki tana kuka saboda shi kanshi dakin an gyara masu shi sosai don yasan
zata dan zauna na kwana biyu.
Karfe takwas yazo, har ciki ya shigo ta dan tashi zaune kanta kasa, fuskarta tayi jawur tasha
kuka har ta bani.
Hankalin sa ya tashi ya karasa kusa da ita ya zauna *Umaimah kuka kikayi haka?* ..... Kamar
ya zugata wasu hawayen suka zubo *Sharrrrrrrrr*...............

*Barkan mu da rana*😃

*Maman Al'Amyn, Amynatu da Abdallah*
😘😘😘😘😘😘😘😘

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣3⃣1⃣

*Dedicated to all auren fari fans group* and you *( DIJA)*😘

....Hankalin sa ya tashi , umaimah ba ki son auren nan a fasa?
Ta yi saurin daga kai alamar eh,
Saboda baki sona baki kaunata?, Gabanta ya fadi.
Kinji?
Tayi shiru, ki ban amsa menene dalilin da baki son auren? Ta goge hawayen *Haka nan* A'a
baiyiwuwa ai duk mai hankali baya yin abu babu dalili.
Tayi shiru, ya kara kallonta *Baki so na ko?*
Ta girgiza kai Alamar ba haka bane,
To menene for God sake?
Kwalla suka kara zubo mata.
Ya runtse ido, umaimah don Allah ki rufa man asiri kada ki raba man hankali biyu.
Ga pressure family, gata mutanen gari ga ki ke kuma da zan raba in ji sanyi kin fara kuka .
Ki kwantar da hankalin ki wallahi ina sonki yanda baki tunani umaimah kuma bazan taba cin
amanar ki ban ko in wulakantaki.
Idan kika ci gaba da nuna damuwar nan zan hakura da auren nan kawai har sai kin shirya,
amma ki sani duk halin da na fada kada kiyi kuka da kowa sai kanki kin amince?
Tayi shiru,
Me yasa dazun kuka hada baki da mamee kika taho ban sani ba?
Na lura Sam ke baki wani doki na ko? Inyi ta rawar jiki akanki kina *Wulakanci da rai*
.......lokacin ne tayi murmushi.
Kin tuna *Kalmar?*
Ta daga kai.
To bani ma'anar ta please.
Ta kara murmushi tana goge yan guntun hawaye.
Kinji? Kaima kasan ma'anar. Yayi yar dariya Allah ban sani ba.
Tayi yar dariya zan fada ma . yaushe?
Tayi shiru kawai.
Umaimah kina fama da mulki. Wallahi Jan ajin ki ya fara man yawa, kin gama gano cewar Ina
matukar kaunar ki shi yasa.
Zuwa na yi in tambayeki dame dame kuke bukata keda kawayen ki?
Hummm, ta ce,
Ai kinji, ke kam ban San lokacin da zaki waye ba, da wata wayayyar ce cewa zatayi , my love ka
bamu miliyan daya, ka siyo mana raguna da katon sa sannan ka kawo mana lemuka da
ruwa...... Ta kyalkyace da dariya ganin yanda ya dage yana maganar mata.
Shima yayi dariyar burin sa ya cika ya sanyata dariya.
Ta ce haka mata ke magana?
To yaya kukeyi?
Ta sunkuyar da kai saboda yanayin kallon da yayi mata.
Ni ai bani da kawaye....... Gayyar da khausar tayi fa? Ta amshi kati yafi hamsin wurina.
Kawayenta zata gayyata, ke ba naki bane?
Um, ta ce ataikaice.

Ya mika mata ledar ga naki kema ki gayyato.....Allah banda kawaye.
Ya kyalkyace da dariya yauni tawa ta sameni *Card* din ma kunyar su kikeji?
Tayi murmushi ganin ya karto ta. Aiki ya dubeni .
Ki fada man kudin zan Baku ko kuwa list zakiyi abinda kuke so?
Kasan Allah bani son komai. Ko abincin gidan nan da ka kawo ma ina za a kaishi?....yarinyar
nan kin fiye gardama. Ya fiddo daurin yan dubu dubu guda uku ya ajiye, sun isa ko a karo?
Ta kalleshi wai kai kudi kaikayi sukeyi maka da baka iya hakuri idan ance ba'aso?
Yanayin yanda tayi maganar yasa shi kyalkyacewa da dariya. Ai ni duk duniya ke kadai nakeyi
ma kyauta kice ba ki so.
Ta harareshi ka dauke kudin nan Allah.
Haba umaimah ke in ba ke ba, wace mata ce mijinta zai mata kyauta ta ce ya mayar bata so?
Au na ma zama matar?
Yayi murmushi cewa zakiyi *Thank you my love*...... Ta rafka mishi filo tashi ka tafi na
sallameka...... Ya kara yin dariya A'a'a hada *playing love?*
Sai kawai ta mike ganin kunya zata kassarata, ni bari in bar maka da kin......ya tare kofa yanzu
ina taba ki zaki birkice mun gashi ke kuma zaki karya doka ta, wallahi idan baki sani ba ki sani
yau idan kuma kin sani kin manta zan tuna miki.
A tarayya ta dake abinda ke saurin hasalani ya bata mun rai shine idan muna magana ki nemi
guduwa ki barni a wurin.
Jikin ta yayi sanyi ta dawo ta zauna.
Ya zauna kasan kafafunta ta zaro ido nidai tashi ka zauna don Allah.
Yayi murmushi, umaimah kin kara kyau wallahi umaran nan ta karbeki ana gama biki zan
daukeki mu gudu ....... Ya zaro ido nan da nan suka ciko da hawaye, ya tashi da sauri ya zauna
kusa da ita,
Bari in baki wani labari, lokacin da muke fada kullum na gama matsarki da kin gudu sai inji
zuciyata zata fashe don radadi ko kuma naga kin fara kuka, sai inji wani zafi cikin rai.
Sai daga baya na gane ashe duk *So* ne.
Ya mike bari na tafi sha daya hada rabi, ai mamee ta kwafsa mun wallahi. Ta barmun ke can
ta assasa sai kin dawo gida gashi ba abinda kikeyi gidan sai kwanciya kina wani kukan maraicin
rashin ganina........ Ta kara dankara mishi harara, Allah ya baki hakuri yi zamanki na yafe
rakiyar. Ka ji,?? Ta fada yana shirin fita, ya dawo da sauri ya akayi inyi zamana ko da asubah na
tafi....... Ta kara hararar sa, yayi murmushi to menene?
Kudin nan wallahi sunyi yawa ka bamu dubu ashirin sun ishemu.........umaimah, wai baki son
kyauta daga hannuna ne ko kuwa ni din ke ba ki so?
Allah ina so, Ta fada kanta kasa tana wasa da yan yatsu, kyautar taka tana wuce misali,
gaskiya sunyi yawa,
Yayi shiru yana kallon ta, yarinya karama amma ta saisaita murya tana zaro magana, taci gaba
da cewa , shagalin biki kawai ka bamu har dubu dari uku? Yanzu haka a garin nan akwai
wadanda suna can sun wuni basuci ba zasu kwana da yunwa, nidai don Allah a kaina ka daina
kashe kudi irin haka ko hidimar da kayi gidan nan yayi yawa. Yayi murmushi, to naji ki dauki dubu ashirin din ki ajiye mun sauran zan karba kinji?
Ta daga kai, ya kara matsowa *What next*?

Tayi murmushi shi kenan,
Ya kura mata ido *Ya sunana?*
Ta kalleshi da sauri, ya daga kai *Yes what's my name?*
Ta danyi dariya.
Allah sai kin fadi sunana yau.
Kaiji ai ina fada kamar wani dana na fari?
Yayi murmushi to ce inji ko kuma wallahi danki na farko in sa mishi umar kuma in hana a boye
sunan.
Ta kara yin dariya duk kunya ta baibayeta.
Ke nake jira ko kuma wallahi yau in kwana dakin nan kin San karamin aikina .......... *Madaki* ta
fada da sauri
Ya fadada fara'ar sa toooooo kema *Madaki* kike cewa?
Lallai. Ya tallabo fuskar ta ya bata kiss *sweet dream* ya fice da sauri, gudu gudu..... Ta zaro
ido *innalillahi*...... Tare da rike kunci.
Bata kara sanya shi ido ba sai dai waya, ta karaci fushin ta har ta fara begen ganin nasa
lokacin sauran kwana uku sallah da kuma daurin auren ta.
Gida ya fara cika da baki, dangin su baba da ga kauye da kuma dangin su goggo.
Umaimah da tace bata gayya sai ga kati ya kare kaf!
Gida dankame da mutane ana zaman jiran kawo lefe, umaimah dai ta hada tarkacenta tayi
gidan hajiya, khausar tayo mata waya gobe zasu taho da kawaye duka, ita da farida da wasu
kawayen faridar ne suka fara yan shirye shirye, ga azumi ga hidimar biki kai Madaki bala'i ne,
Hajiya ta shiga gyara amarya ta dafa mata kaza da auren tantabara sannan ta ringa bata wasu
ruwa tana sha, umaimah da ta motsa sai kuka *Gani takeyi ta gama shiga uku*
Mata cike da gida har la'asar amma lefe shiru dole kowa ta koma gidanta don hada buda baki.
Gashin umaimah har bisa baya yake kadan ne bai karasa hawa kugu ba, ba a gamewa
saboda kullum cikin kalaba take sai ta nade shi ta boye,
Tana zaune dakin hajiya suna buda ba ki ya kirata yazo gida bata nan, ta mike da sauri ta fito,
Ta dai ga motoci amma bata ganshi ciki ba, tana shiga sukayi kicibis a zaure, taja baya,
Ya kalleta ke ban son yawo ina kika tafi?
Gidan hajiya ai acan zamu kwana saboda gidan ba ki ne, ta jiyo cikin gida an rangada guda, to
ki shiga ciki lefen ki ne na kawo.
... Ta kalleshi Kaine ka kawo lefen?
In ba ni ba wazai kawo?
Ta kama tafa hannu na shiga uku nikam kana janyo mun magana, sai kawai ya kasa ce mata
komai don bai san lokacin da zai ma umaimah dai dai ba.
Ta juya, ina zaki?
Gidan hajiya ni bani iya shiga gidannan gaskiya.
Ya kyalkyace da dariya mtseww yarinyar nan gaskiya bata waye ba , eh naji ta wuce, ya bita
baba ya kirani dazun sun bani makudan kudi na kayan dakin ki wai bazasu taba mika ki salin
alin ba tunda na saka komai to inyi amfani da kudin.
Ta ce *Uhumm*
Sun yanka mun sadaki dubu talatin amma na ce zan kara........ Ta juyo da sauri wallahi ka kara
zan maido ma. Ai karancin sadakin mace albarkar aurenta, kai *Madaki* kudi na maka kaikayi.

Ya kyalkyace da dariya to anji ustaziya.
Abokaina zasu zo gobe kada ki saki ki fito, dalili?
Ya sha mur na dai fada miki saboda wurin yan mata zasu zo.
Naji ta fada.
Wai ke ba ki Dan kunshin amaren?
Ta kyalkyace da dariya zanyi mana ai kwana zanyi dashi irin na tsofaffi zanyi duka hannu duka
kafa.
Ya zaro ido ki rufaman asiri umaimah na tuba.
Me zatayi ba dariya ba. Kai ina ruwanka to.
Ya langabe kai kada ki yi man haka bana son sa.
Ta Dan sha mur kamar gaske, shi zanyi, ko ka manta laifin da kayi man?
Ya hada hannuwa biyu Allah ya baki hakuri na tuba.
Kawai kayi hakuri lallan ma na cen na jika shi.
Jikin sa duk yayi sanyi ya CE shi kenan ai.
Ni zan tafi, okay sai da safe ta wuce ciki.
Yarinyar nan ta gama dani , ya rasa inda zai sa Kansa. Bai taba ganin ta yi kunshi ba, gata da
kyan hannu da kafa ga ta fara kullum yana kiyasta ya zata kara kyau idan an mata kunshin
zane.?
Mtseww ya buga tsaki ya wuce.
Washe gari tunda asubah mai kunshin ta tazo , kwararriya ce don duk wani mai kudi da ya
amsa sunanta burinsa tayi wa yarsa kunshi ga biki.
Ta tsantasara ma umaimah kunshi abin da ka kunshi.
Na kafar dawisu ta zana kan ya fara daga karamin yatsan kafa bazar ta hau kan kafafun har
kusan guiywa.Sai kusan azahar aka gama sannan mai kitsonta ta tazo ta yanyara mata
kananan kalabarta.
Khausar Tun karfe tara suka zo. Mai kunshin yan mata daban tana ta masu.
*Madaki* yayi wa faty mamza waya don zatayi ma umaimah *Make up* ranar daurin aure
saboda a ranar za ayi dinner bayan an kai amarya.
Bikin umaimah ya bada kala ga murnar sallah ga shagalin biki.
Abokan sa har daga kasashen turawa shi kansa hankalin sa ya fara tashi ganin mutanen da ya
tara.
Duk hotel hotel dinsa da guest house ya zuba ba ki amma har wasu na hada dakuna mutane
hudu biyar.
Malam bawa ya bada mamaki domin yanda Madaki yayi mishi sai yayi amfani da kudin da ya
bashi ya kara yayi hidima yaba hajiya su aka yi ma umaimah gara, ya kuma dibi wasu cikin
Wanda madakin ya kawo.
Ko mi buhu goma aka kai mishi banda manya manyan bokitan cin cin da dubulan.
Manshanu kuwa daga kauye haka akayi ta lodo wa shi yasa ta sami manshanu fiye da
tsammani.
Sannan aka ware mishi dubu dari biyu za a mishi Karin ango.
A kano suke zaune amma samm basubi al'adar su ba yabi yanda sukeyi can kauye.
Hajiya kuwa sai ta sami katon Kofi ta cika da fura ta tsare umaimah tana kuka amma sai ta
shanye ta banda abinci.

Umaimah taga da gaske akeyi, ta fara kukan wiwi ana gobe daurin aure.
Tun da ya kirata da rana yaji bai kara samun natsuwa ba sai da yazo da daddare.
Kafarta da safa, hannunta cikin hijab, sama sama ya dan bata baki ya tafi saboda wayoyin da
aketa doka mishi.

Mamee kuwa, mutanen ma da bata tunani su ta gani. Gudummuwa kuwa tama rasa in da
zata kudi. Saboda wannan shine bikin ta na farko tun haihuwar Madaki bata kara tara taro ba
sai yau.
Su yaya kuwa sun ja gefe sunyi zaune banda gulma da hassada babu abinda sukeyi.
Ga hidima sunki shiga ciki, sai dai hakan da sukayi bai rage komai ba sai ma kara ma bikin
armashi saboda mutanen arziki ne suka tsaya tare da fidda mamee kunya. Sannan aka sami
wasu daga cikin aminnnan suka ringa yada masu magana nan da nan sai duk kunya da rashin
gaskiya ya kamasu, ko sisi babu Wanda ya ba mamee cikin su amma kullum suka zo gidan
zasu taho da ledoji a jaka su kwashi abinci kala kala, ( kai ya Allah ka raba mu da mutuwar
zuciya, da karanta, hassada , jin zafi da bakin ciki ). Amin.
Gidan sai ya fara gagarar su ganin ko sunzo da zuwan nasu da babu duk daya mutanen arziki
ke fidda mamee kunyar *AUREN FARI* Na danta kwaya daya tilo.
Karfe goma dai dai aka daura auren *umar madaki da umaimah hamza* a babban masallacin
idi.
Yan jaridu, gidajen rediyo da talabijin sai binsa sukeyi amma banda dariya babu abinda yakeyi
ya kasa cewa komai.
Umaimah kuwa da ance fito ga yan jarida sai tayi bisa gadon hajiya ta fashe da kuka .
Da kyar suka kwaci kansa shida abokan sa.
Ya kallesu, muje daukar amarya ko?.......
Ka rufar masa ana dariya don ubanka wa zai baka ita yanzu suna tsakiyar shagli?
Ya buga tsaki wallahi sato ta zanyi zaku rufo wata Ku kawo anjima.
Duk suka bushe da dariya ana ci gaba da yi mishi tsiya.
Duk tunanin su wasa yakeyi sai kawai ya bisu da dariya.
Biki yayi biki su umaimah na daki sai kuka akeyi kawaye na waje ana rawar asharalle,
Kokari yakeyi ya zille amma mutane sun hana,
Da kyar ya samu ya kutto.
Nan ma kofar gidan su umaimar yaga mutane da maroka cike, ya tabbatar idan ya fita ya sunan
sa sorry, cikin bakar jif dinsa yazo daga shi sai driver yasan ko ya kirata bata dauka ya kira
khausar ta fito da sauri.
Ya daka mata tsawa malama shigo mota kada ki hada mun *Go slow* tayi saurin shiga. Jeki
lallabo mun umaimah ki kawo mun ita don Allah.
Ta ce toh.
Tayi tsaye gabanta ta rasa wace dabara zata mata, ta zauna kusa da ita,
Kizo inji yaya Madaki.
Ta harareta cikin kuka,
Ina ga fa zuwa yayi ya tambayeki yaushe za a dauki amarya ya ce ya kira wayanki a kashe.
Ki tashi kin san halin shi in har baki je ba tabbas yanzu zasu kawo mota amma idan kika je
Kice mishi sai zuwa dare ko kuwa?

Uwar wa kike fada mata? Hajiya ta shigo,
Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0