Showing 39001 words to 42000 words out of 63115 words

Chapter 14 - Auren Fari Complete by Maman Abdallah

himilin kayan abinci buhu buhu da jarkunan mai banda kayan shayi
ba abinda babu.
Matan suka tare shi, suna mishi bayani. Ya ce eh na san dasu daga gidan aikin umaimah ne
suka bamu zakka...... Ya wuce ciki.
Umaimar ce ta tsaya yi musu bayanin gidan zatayi azumi. Luba kuwa ta dunga kuka saboda
dan kurmusun da sukeyi cikin dare.
A gidan Alhaji yakuba tayi sallar magriba. Ba karamin dadi taji ba amma har yau kunya ta
hana umaimah fada mata cewar madaki na son ta.
Tana gidan ya kirata a waya yana jiranta a mota. Bata yarda hajiyar ta ga wayar ba tana soke
cikin zane, lokacin da ya kira kuma ta dan fita, ta ce zata koma gida ta shirya kaya. Ta fiddo
mata sunkunan ta ta ce ungo tafi da su.
Yana hangota ya fito tare da bude mata kofar mota, *Barka da isowa ranki shi dade* ta dan
bata fuska *Ya kake*? Yayi murmushi ya rufe yana shiga ya ce lafiya garas tunda gani gabanki.
Ta ce *Good*....... Malama wai lafiya kike wani basarwa ko nayi wani laifin ne?
Ta girgiza kai ko daya naga dai *Kaima haka kake wulakanci da rai* idan ana baka girma.....
Dariya yakeyi har yana kwanciya, *Kai umaimah ke karshe ce* watan wulakanci nake da rai.
Tayi murmushi eh mana suyi ta kyarma suna tsoron ka....... Ya kara yin dariya ai ke bakya
tsoro na ko?
Tayi yar dariya Allah ina tsoron ka..... Ko maganar ka naji sai gabana ya fadi.
Ki ce Allah!
Allah kuwa,
Tabb wallahi nima haka,
Ta kalleshi da sauri yayi murmushi, da gaske nake wallahi dana tunkaro gida sai gabana yayi ta
faduwa. More especially idan fararen kaya ne jikina, a office wani lokacin har zabura nakeyi ina

firgita idan na tuno masifar ki.
Ba wani nan, kullum kai ne ke tokala ta,
Ai matsalar da na ganki sai inji kawai mu kafsa, saboda ko gardama ba'a taba yi dani ba ko
bakiga yanda nake *wulakanci da rai ba*?
Tayi yar dariya na gani kuwa.
Ya kai mata duka,...... Da an canza ma suna yau. Ai nasan hannunka sai ya taba ni.
Ya tuntsire da dariya kin San kuwa dana fara son ki burina kawai mu hadu kina bala'i ni kuma
ina rungumrki......laaaaaa ta ce tana hararar sa.
Meye kika kawo mun a leda?
Ba komai dun kuna ne...... Allah? Cewa zakiyi gayu zan sha, ta dan harareshi *Wai ma*......
Wayar sa ta fara ringing ya duba kamar ba zai dauka ba ta tsareshi da ido, yana dagawa ya
saisaita murya kamar bashi ne ne raha yanzu ba.
Hellooo..... Lafiya, zan kiraki zuwa anjima ya kashe wayar.... Umaimah ta bude marfin mota
yayi saurin fizgota ke ina zuwa?
Ta murtuke fuska zan baka wuri ne don ka sami halin kiran nata ba ma sai anjima ba.......ya
kyalkyace da dariya yanzu dai rufo kofar kafin sauro ya halakamu. *kut*.....kishi umaimah ki ce
na shiga uku. Tayi kicin kicin ita dole fushi takeyi ya kwanto jikin ta ya janyo kofar tare da locking
kawai ya baje bisa kafafunta....... Malam daga ni banda kwari kada ka karya ni. Ya mata banza ya latso lambar da aka kirashi, yasa hands free, hello sir,
Yawwa ina jinki menene?
Dama jirgin nan ne da zai sauka lagos da kaya yazo, na port Harcourt kuma munyi waya in the
next two hours zai iso.
Okay yayi kyau sai ki kira *BASHIR* Suyi magana da Agents.
Okay sir, ya kashe yana kallon umaimah, *What next?*
Ta danyi murmushi yo wani abu na ce?
Sai kince wani abu? Gashi zaki gudu kuma wai ni duk ina kokarin baki full time bana son wani
issue ya shiga lokacin ki.
Wasa fa nake... Ya tallabo fuskarta karya kikeyi wallahi kishi ne.
Ta runtse ido *Wayyo Allah* ya tashi da sauri lafiya?
Kafafu na sukayi *Yami*
Ya kyalkyace da dariya wallahi baki kyautawa yami kamar wani kwanannen abinci?
Ya bata labarin yanda sukayi da Babanta, ta ce, Ohh Allah sarki. Ashe Allah yamun *Alam
nasharaha* ta banka mishi harara ai wallahi da kauye zan gudu.
Ina zullumin gobe wallahi saboda zama kusa da mamee takurani yakeyi banga dalilin da zaisa
ka assasa sai na dawo gidan da kwana ba.
*Baza ki gane bane yarinya*
Gobe zan aiko a daukeki da safen saboda kayanki....... Bana so. Ya yi murmushi to kawo
wannan nayi miki gaba dasu.
Hmmm kawai ta ce,
Sai sha daya saura suka rabu.
Karfe tara ta fito gida amma anan waje ta tarar da drivern shi. Babu yanda ta iya dole ta shiga,
su lubabatu na ta mamaki. Malam bawa kuma yaki cema kowa komai.
Isarta bata tarar dasu Aunty jamila ba madaki ya masu korar kare jiya bayan ya koma ya tarar

sun tsare namee suna mata tambayoyi da maganganu akan umaimah.
Karfe goma ya sauko zai tafi office mamee ina uwani?
Ta na ciki tana shiri,
Shiri?
Eh zan aiketa cikin gari ne.
Okay to tayi sauri na ajiyeta daga nan mu biya office kawai ta dawo miki da sakon,
Kwarai kuwa kaga har na manta da munyi maganar.
Ta fito cikin atamfa dinkin doguwar riga yasha stones, ta yafo dan gyale batayi tunanin yana
falon ba ta fito da gyalen a hannu tana gyara dauri.
Mamee ta washe fuska, fara'ar ta ta karu, Uwani ashe kin dinka atamfar nan?
Nima kuwa yau tawa zan saka kai amma naji dadi. Ta danyi yar dariya, waya miki dinkin nan?
Hajiya ce ta bada mun......au haba?
Ya kasa motsi kamar ya rukota yakeji kalacin da bai karasa ba kenan ya ce muje kawai,
Ta kalleshi tana harara....... Mamee fada mata kada ta batan lokaci ya fara duba agogo.
Zai ajiyeki ne amma zaki karbo mun sako wurin sa.
Ta ce toh, suka fita,
Yana rufe kofa ya janyo ta *Wai ke yaushe zaki waye?* Me nayi?
Ba ko gaisuwa? To sakeni dai ka kalli gabanka, bai saketa ya dan waiga masu gadi ne da
jama'an gida suka taho gaisuwa.
Ya kara riketa ya sha mur,
Haka ya gaisa da kowa duk wanda ya gaidashi sai ya ce *Ranki shi dade barka da safiya*
mutum biyu ta amsawa, kunya ta dunga tsunkulin sa ta baya yayi mata banza.
Suna shiga mota ya shako wuyanta ke wai *Yar fari ce?* ........ *kuma auta* ta fada.
Kina mintsili na gaban mutane.
Allah cizonka zanyi.
Ya kyalkyace da dariya.
Yanzu ni zan gaisheki ko kuwa kece?
Wanda duk ka zaba .
Yayi murmushi ina kwana,
An tashi lafiya?
Ya kara yin dariya naga kin fara *Wulakanci da rai* ta yi murmushi *Wai ma*
Ya na zuwa office ya tarar da dandazon yan jaridu, yaki fita mota ya ce maza ace su tafi sai
karfe biyu su dawo baida appointment da kowa yanzu.
Sai da ya tabbatar sun watse sannan suka fito shida umaimah taki jerawa dashi daya Dan
waigo sai ta nemi kwasawa da gudu ta rike riga,
Ya sha mur meye kikeyi haka?
Eh anji wuce dai muje zan bika abaya.
Murmushi kawai yayi ya wuce body guards sun baibayeshi sunata mazurai.
Dai dai an bude mishi kofa wata matashiyar mata ta iso..... *Yaro matashi*.......ya waigo da
sauri yana murmushi tana zuwa ta fada jikinsa sukayi *Hugging* umaimah ta ja baya da sauri
tare da fiddo ido kirjinta ya buga da karfi.
Tare suka fara shiga office din , umaimah na ganin haka ta yi baya tabar wurin da gudu.
Tana fita harabar office din ta tari mashin tare da fadin *TAL'UDU*................

*Good morning all*

*Maman Abdallah*😘😘😘

https://chat.whatsapp.com/8RrbAeADj5FLV7LZ24rBDH

💑 *AUREN FARI* 💑

0⃣2⃣6⃣

........... Ya waiga bai ga umaimah ba , ya fito da sauri ko tsayawa tayi , babu ita... Ya kira
security din sa da suka zo tare yana tambayar sa yayi damama ya fara dube dube ya daka
mishi tsawa *Are you mad*???
....... Hankalin kowa ya dawo wurin duk aka mimmike tsaye, billahil azim idan baka nemo mun
ita ba a bakin aikin ka ya yi hanyar waje duk aka rufa mishi baya.
Ina yarinyar nan ta tafi?
Ya kwadawa securities din bakin gate kira suka kwaso a guje yarinya ta fita yanzu?...…. Eh
yallabai ta hau mashin....... *What????* Kuna hauka ne *Don ubanku*
Ya dauko waya yayi kiran duniya taki dagawa.
Ya kira mamee kamar yayi hauka,
Mamee yarinyar nan ta dawo gida?
Lafiya, Menene?
Ta dawo?
A'a me ya.... Kit ya kashe
To wai ubanwa yasa kuka bari ta fita.... Ya zaro ido ohh my God *Anya ba ganin samira yasa ta
gudu ba?*
Kaiii kishi umaimah ke gareta sosai??
Tawa ta sameni ya kara kiran nameee...
Ta ce ka ganta? Tana daga wayar.
Ina ne kika aiketa?
Gidan hajiya bara'atu tal'udu.....kit, ya kashe.
Ya kalli driver *Maza dauko mota*.....
Kadan kadan yayi tsoki, rigimar yarinyar nan tayi yawa.
Daga nesa ya hangota hannuwanta rike da manya manyan ledoji suna rinjayar ta, tana shirin
hawan adai daita, ya daka mishi tsawa *Kada ka bari ta shiga*
Kawai taga mota gaban ta, tayi saurin fadawa adaidaita ya sauko da sauri... *ke kina hauka
ne?* mai adaidaita ya zaro ido ganin *Umar madaki*
Ta kalleshi a wulakance daga turu na fito malam muje..... Wallahi ka tayar da mashin din nan
zakayi asarar ta.
Yasa hannu zai fizgota ta ingijeshi na rantse da Allah ka taba ni zan tara ma jama'a, ta daka wa
mai adaidaitan tsawa *Malam na ce muje ko?*
Sai kawai ya fado ciki muje malam..... Ta yi saurin fita ta dayar kofar ta barshi ciki kafin ya fito

ta haye dan mashin......
Ransa yayi mugun baci, suka bi bayanta. Hon sukeyi amma ta ce wa mai mashin din ko
juyawa kada yayi.
Ana sauketa bakin gate shima ya fito, umaimah.... Umaimah tayi banza dashi ba halin ya ruga
ya rikota duk saurin sa ya kasa cin mata,
Falo ta tarar da mamee tana ganinta ta taso uwani me ya faru ne ina kika tafi?...... *Ke kin raina
ni ko?* ya shigo kamar an ingizoshi.
Ta ajiye ledojin gashi mamee ta ce wadancen lesukan basu iso ba.
Tayi ciki abinta ya daka mata tsawa.....amma ko saurarenshi batayi ba tana jin ya biyota koda
ta shiga dakin sai tasa makulli.
Ya yi bugun duniya taki budewa.....
Mamee na jin su tayi zaman ta falo tana fada, *Yara kamar kaji* kullum cikin masifa mtseww.
Ya dawo kamar zautacce mamee zan batawa yarinyar nan rai bana son raini, kinga yanda ta
wulakanta ni bakin titi tabarni cikin adaidaita, mun shigo ina magana ta mayar dani sakarai, a
gaban ki kuma yanzu kinga ta rufe kofa fa....
Me kayi mata??
Ya buga tsoki kawai kishin banza ne na rashin dalili, Samira sardauna ce na tarar office daga
gaisuwa ta gudu.
Au samirar tazo kasar ne?
Nima ganinta kawai nayi.
Ya zauna bisa kujera *Gaskiya mamee ki fadawa yarinyar nan*
Ta kalleshi me?
Tasa ma ranta hakuri saboda yanayin harkokina da ya kunshi kowa jiya fa *Uche* ta kirani a
waya wallahi yarinyar nan ta nemi birkicewa. Me ta dauke ni ne? Mtsew...
Ni zan fada ma uwanin haka? Tabb lallai kana da sauran aiki.
Ta mike ka fidda ni cikin wannan maganar ma can Ku ta shafa.
Mamee.... Kawai ta yi ciki.
Kiran sa kawai akeyi a waya ya kasa dagawa, banda sakonni. Mamee ta ce bude uwani nice,
Mamee na shiga ta nemi maidawa ta rufe ta kalleta tana yar dariya keni tsaya fita ma zanyi
kayan da kika dankwarar man dasu falo na kawo. Ta ja baya ta kasa ko murmushi, dadi kamar
mamee ta goya ta ganin kishin madaki haikan a wurin ta.
Cikin zuciya ta ce lallai uwani kin cika *Diya* zaki gyara man shi da alama.
Don zanga inda za Anyi *So* da zafin rai. Har karo yakeyi da namee zata fita yana kokarin
shigowa, ta kalleshi kamar ta kyalkyace da dariya amma ta basar, ja'iri hada alhakina don
iyayenka, nan na dunga kawo maka yara kana gwasaleni, ta fada a zuci ta wuce ,
Umaimah na ganin sa ta zauna bakin gado ya karaso zai kamata tayi saurin wawuro wata
flower ta glass dake bakin gadon mamee, *Na rantse da Allah ka kuskura ka taba ni zan maka
rauni*
Ya yi turus, ta kalleshi a wulakance, kallo da yafi tsana a rayuwar sa fiye da duk wata kalmar ta
muni da zata furta,
Wai kana mun daukar sakarai? Ko kuwa kana mun daukar makwadaiciya wacce zata bika
saboda dukiyar ka?...... What are you talking about?
Ya daka mata tsawa....ita ma ta hayayyako mishi.

Bani son ka wallahi yau na tsaneka bana kaunar ko ganin ka a rayuwata.
Mtsewww haba no wander ba da aiki sai ka kai hannun ka jikina ashe halin ka ne ko wace yar
iska tabawa ........ *Ke* .....ya daka mata tsawa ..... Ita ma ta tace .. *Enough* tare da mikewa
tsaye ko ka fita harka ta ko kuma na bar gidan nan bari na har abada, kasan dai na isa shari'a
ko? Yaga da gasken gaske yake sai ya fara rokon ta *Umaimah please let me explain*...... *Explain
what?* ta katse shi.
Maharramar ka ce? Ni kaina na fada maka bana so kana taba ni ko kuwa ya hallita?
Zai yi magana ta daga mishi hannu *Wallahi idan baka fita kaban wuri ba zan bar ma gidan
gaba daya*
Dole ya fita,
Ta buga tsaki, duk ya fita ranta, bata kaunar ko ganin sa.
Samira child hood friend din sa ce, sun shaku matuka, yana bala'in shiri da ita yarinya ce
natsattsiya a kasar London tayi aure can kuma take da zama mijinta ya rassu amma bata dawo
Nigeria ba saboda aiki da takeyi, yaranta biyar, babu wani abu tsakanin su, duk Wanda yasan
madaki yasan samira. Mamee bata san fitar shi ba, yana zuwa office ya tarar samira ta bar mishi note na wulakanci
saboda ta kira ta kira bai dauka ba kuma ta tura text ba replay.
Ya rasa abinda ke mishi dadi a rayuwar sa, komai ya jagule mishi duk Wanda ya tunkare shi
sai bala'i.
Washe gari aka tashi da azumi.
Abu kamar wasa sun kwashe kusan kwana hudu umaimah tayi wuri ta kyaleshi, bata daukar
wayar sa bata zama duk inda tasan yana nan.
Yana kwance sama ya kira taki dauka, ya ce wannan yarinya da bakin kishi take, tama ki
saurara ta taji uzuri na. Mamee taki tasa baki nayi rokon duniya ta ce kar na kuma yi mata
maganar ma.
Ya runtse ido kawai dabara ta fado mishi ya tura mata text.
*I know that there is no forgiveness for the kind of mistakes I do. But if you can forget my
mistakes and give me a chance, I'll make everything as good as new. I'd start everything all over
again and make you happy.* Tana ganin message din ta kashe wayar ta ya kara tura mata wani
yaga pending.. Yana kiran wayar yaji ta kashe, Ta harari wayar *Wallahi sai ka gane kuren ka* kai taba jikin mace baka dauke shi bakin komai
ba?
Ban iya wannan iskancin.
Ko aure na ya yi wannan wata rana ya tabo jikin wata yaji tabshi lokacin nawa ya taurare banza
zan zama.
Kishin yarinyar nan yayi yawa, daga *Hugging?*...... Kai na gamu da gamona ni madaki,
problem din ta gama gane na mutu kanta,
Ya tashi zaune, kaii..... Lallai , in ba umaimah ba wace yar iskar yarinya zan ringa bi tana mun
wannan wulakancin, wai ni madaki nake ba mace hakuri tana mun tsawa a kai.
Mtseww *I hate this condition* ya dafe kansa.
Ta tsaneni ko ganina bata son yi? Ga mamee na sane ta zuba ido?
Ya kara tsoki, wallahi zuwa zanyi ayita ta Kare na gaji, ita bata da tausayi ne?

Ya sauko sai kawai ya hangota ashe mamee ta aiko ta,
Tana hangoshi ta juya zata koma ya karaso da gudu ya tari gabanta, ki dubi girman Allah ki
saurareni umaimah .....zatayi magana ya katseta, ,,... *Girman Allah na ce*
Tayi shiru. Haba umaimah wannan kiyayya haka ko lokacin da muke tsahin hankalin ma bakiyi
mun haka ba ballatana yanzu da muke son juna kawai dan kuskure ne da za a iya gyarawa.....
Ta kalleshi *Dan kuskure*
Yayi saurin daga hannu sama, *Babbar matsala* ce afuwan.
Wallahi samira babu wani abu tsakanina da ita, kinji na miki rantsuwa ...... Ni na ga haka tunda
ka mance dani ka mamuke ta,... Kamar zaiyi dariya ya dai tsuke, shin ai don na hugging din ta
ko?
To wallahi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0