Showing 1 words to 3000 words out of 73884 words

Chapter 1 - Dangartakar Zuci Book Compelet

01 Sep 2026

504

[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*
Aishat A muh'd

&
Sumayya salees sadeeq




*BISSMILLAHIR RAHMANUR RAHIM*



_Dukkan godia sun tabbatar ga Allah (SWA), da ya bamu ikon rubuta wannan littafin, tsira da
amincin Allah su k'ara tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), Yah Allah yanda ka nufe mu da
fara rubuta wannan littafin Allah ka bamu ikon kammala shi lafiya_



_wannan labarin littafin bamu yi shi don wani ko wata ba kirkirarren labari ne dafatan masu
karatu xaku biyo mu don jin kalar wannan labarin na *DANGARTAKAR ZUCI*_




*Page 1-2*




Wata er yarinya ce kyakkyawa irin chocolate colour nan tana sanye da wata er farar vest irin
ta yara da yake lokacin xafi ne sai k'aramin wandon vest d'in farare ne sol kalar su sai dai kuma
kash duk sunyi datti kayan sosai duk sun fita hayyacin su ita ma tayi dukun dukun gaba d'ayan
ta, er kimanin 7year's tana 6uruntu a kitchen duk da tsayin ta bai kai ba sai da ta taka kujera
tukunna ta bud'e wata tukunyar miya tasha naman kaji xuk'u xuk'u a ciki wani babban spoon da
plate ta d'auko ta tsomashi acikin miyar sai da ta kwashe naman ciki Kaf gaba d'aya sannan ta
mayar ta rufe tukunyar tare da sakko wa daga kan kujerar.

A k'asa ta xauna ta hau cin naman nan hannu baka hannu kwarya tana sauri don kada a
shigo a gan ta a haka, tayi nisa acikin ci sosai don ta kusan cinye rabin naman sai ga wata er
dattijuwa ta shigo kitchen d'in tana ganin ta sai ta buga salati tare da cewa
" Husna!!! "
Da sauri yarinyar da aka kirawo da husna ta d'ago kanta tuni ta kwa6e baki xata sau kuka cikin
sauri er dattijuwar nan kakar su suna kiranta da hajia maamaa taxo ta fisge plate di'n hannun
husna cikin fad'a ta fara cewa
"yanxu fisabillah husna kin kyauta ki kwashe dukka naman abincin kisa a gaba Kina ci sai kace
naki ne ke kad'ai, yarinya kamar mayya Indai taga nama sai taci "
Tuni husna ta 6are baki ta fara kuka sosai har da majina tana kok'arin xubo wa hararar ta hajia
maamaa tayi tace
"bari yayan ku ya shigo Kinsan baya cin abinci sai da nama koh, gashi kin ta6a wannan baci xai
yi ba wallahi ke dashi ba ruwa na, ja'irar yarinya fita daga kitchen d'in nan kije babar ki tayi miki
wanka ji yanda kika xama yarinya sai shegiyar kaxanta "

Da gudu ta fice daga kitchen d'in tana rusa kuka har da d'ora hannu akai, girgixa kai hajia
maamaa tayi tare da rufe plate di'n naman nan tana cewa
"Bari su na'ima su shigo sa ci don nasan ko Karen hauka ya ciji yayan ku baxai ci naman nan
ba"

A parlour ta tarar da husna mai kuka har ta 6ingire da bacci hannu a baki ga hawaye sun bushe
a fuska banda majinar hancin ta da ta bushe ita ma sai faman ajiyar xuciya take, girgixa kai ta
sake yi a karo na biyu tare da ta6e baki tace
"ohhh ni ma'u yanxu ja'irar yarinyar nan bata tafi Anyi mata wankan ba sai taxo tana yi min
bacci a parlour "
D'an tsaki taja tare da xama kan kujera ta d'auke glass d'in ta ta kwama a fuska tana kallon
tashar sunnah T.v sun sako wa'azin sheik Isah Ali pantami ta nutsu tana sauraren wa'azin.

Acikin nutsuwa ya shigo parlourn da sallama hajia maamaa ta amsa mishi sallamar tashi cikin
matuk'ar gajiya da wata uwar yunwa da yake ji ya nufi kitchen bai kula ta ba kamar 2 seconds
ya fito daga kitchen d'in a fusace ya Kalli hajia maamaa da take xaman jiran abin da xai ce yace
"maamaa uban waye ya cinye naman miyar nan? "
Kai tsaye hajia maamaa tace
"wa kasan xai cinye Idan ba ja'irar yarinyar nan ba husnah ita na kama a kitchen tana ci"
"kenan da kanta ta d'iba "
"k'warai da gaske"

Ya bud'e baki xai sake magana idon shi ya sauka kan husnah wadda take bacci hankali kwance
a xuciye ya K'arasa inda take bai yi wata wata ba yasa hannu ya falla mata mari a gigice ta
mik'e tana xunduma ihu hannun ta dafe da kumatun ta
"keeee kaxama rufe min baki yau sai jikin ki ya fad'a miki"
Belt d'in jikin shi ya fara kok'arin cirewa tuni ta hau rarraba ido jikin ta sai faman 6ari yake
saboda tsabar tsorata don tasan halin Yah ibraheem akwai mugunta

Bata ankara ba taji saukar duka ta ko'ina tuni ta fara xunduma ihun axaba, hajia maamaa kuwa
ko kallon Inda suke bata yi ba K'arshe ma sai ta shige bedroom don ita ta ja, shi kuwa ibraheem
ya d'aga belt d'in ya xuba mata ta biyu Kafin ya ankara sai ga fitsari ajikin kafar shi husnah ta
saki Haba ae tuni ya dad'a fusata yasa kafa ya haure ta ta fad'i k'asa tare da buga kanta jikin
glass table da yake tsakiyar Parlourn ae kuwa ta k'walla wata raxannaniyar k'ara

Mtswww yaja wani uban tsaki a dai dai Lokacin wani guy ya shigo parlourn da sauri duk ya rud'e
ya nufi inda take ya d'ago ta xuwa jikin shi bai damu da dattin jikin ta ba adai dai lokacin hajia
maamaa ta fito daga bedroom d'in don ta kasa xama jin kukan husnah yayi yawa kada
ibraheem yaji mata ciwo...........


Aishat A muh'd
&
Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR ZUCI*🍃




*written by*
Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq




*Page 3-4*




Kallon kafar shi da k'asan wandon shi yayi yanda suka jik'e da fitsari kamar xai fashe da kuka
haka yake ji xuciyar sai tafasa take ya fara cire dogon wandon trouser di'n da yake jikin shi cikin
k'ank'ami Ya yar dashi daga shi sai T-shirt da boxer kawai ajikin shi, suna had'a ido da Yah
Abdullah ya sakar mishi harara tare da cewa "ibraheem me tayi maka kayi mata wannan uban dukan haka? "
D'an ta6e baki yayi Kafin yace

"ka tambayi maamaa xata baka labari "
Yana gama fad'in hka ya fice daga parlourn,sai da yaje d'akin shi yayi wanka sannan ya shirya
ya fito direct part d'in mamee yayi da sallama ya shiga aka amsa mishi ko'ina fes sai tashin
k'amshi yake a rayuwar ibraheem ya tsani kaxanta baya shiri da kaxamai ko Kad'an xube wa
yayi kan kujera ya Kalli mamee yace "mamee I'm very hungry and tired "
Cikin kulawa mamee tace
"Ohh sorry my boy, bari na xuba maka abincin"
Tana gama fad'in hka ta shiga kitchen da sauri ta xubo mishi fried rice nd costlow sannan
pepper chicken sai wani hadadden kunun aya ta kawo mishi cikin sauri ya bud'e plate di'n wani
k'amshi ya doki hancin sa ya lumshe ido tare da sakin wani lallausan murmishi yace
"wow that's my favorite food thank u mamee nah"
Murmishi mamee tayi kawai nan ya fara cin abincin cike da jin dad'i ko five Spoon's bai yi ba
aka bud'e kofar parlourn aka shigo xumbur ya mik'e tsaye tuni fuskar shi ta rine da 6acin rai
tsantsa kallon ta yake kamar xai yi amai cikin tsawa yace
"hey u uban waya kawo ki nan kuma, (Ohh kuji ibraheem da k'arfin hali part d'in su ne fah) "
Cikin mamaki Yah Abdullah yace
"gidan nasu kace uban waya kawo ta to nine "
6ata rai yayi sosai yana wani kau da fuska mamee dai ko kallon su bata yi ba Idan da sabo ta
saba da ganin wannan tsakanin ibraheem da husnah don hka news paper d'in dake kan table ta
dauka tana karanta wa

Kamar ance ibraheem jiyo ka Kalli husnah yana kallon ta yaga wata majina ta fito ta hancin nata
zuuut ta xuk'e ta wato ta shanye ta sai faman rarraba ido take wayyo Allah tuni ibraheem ya fara
kakarin amai da gudu ya fice daga parlourn yana rik'e da ciki da baki, haushi ne ya ishe Yah
Abdullah yace "wallahi sai na saita wa ibraheem kai wannan iskancin nashi ya isheni wlh"
"a'a ba ruwan ka dashi wlh ae da gaskiar shi ji yanda jikin yarinyar nan ya koma don Allah waxai
so ta tsaya a gaban shi yana cin abinci "
Girgixa kai kawai Yah Abdullah yayi tare da cewa
"toh mamee don Allah kiyi mata wanka lokacin islamia ya kusa"
"toh Shikenan "
Tashi tayi tare da kama hannun husnah suka nufi bedroom don yi mata wanka, yayin da Yah
Abdullah ya fice daga part d'in.

Wanka sosai mamee tayi mata tare da wanke dogon gashin kanta irin na fulanin asali a gurguje
ta shirya ta cikin uniform d'in islamia ta fito caras kamar ba husnar d'axu ba, da kanshi Yah
Abdullah ya kai su islamia tare da sauran en uwanta.........



*TUSHEN LABARI*

Alhj ibraheem da hajia Asma'u en asalin garin adamawa ne fulanine na usuli aiki ne ya dawo
dashi garin kaduna d'an boko ne na bugawa a jarida, sun haifi yara 4, muktar, mustapha,umar,
sai autar su fatyma sun bawa yaran su ilimi na addini dana boko sun taso cikin tarbiyya mai
kyau ga nutsuwa suna matuk'ar kaunar junan su sosai.
Gida babba Alhj ibraheem ya gina yayi part 4, kowanne part yana da girma kuma k'asa da sama
ne ya bawa 'ya'yan shi maxa uku kowanne part d'aya idan sunyi aure sai su xauna saboda su fi
xumunci da juna da kuma shakuwa, shi kuma ya xauna a nasu part d'in na cikon na hud'u sai
dai su nasu flate ne babu bene kuma yana tsakiyar na 'ya'yan nashi.
Alhj muktar yayi aure da matar shi hajia halima suna kiran ta da mumy, suna da yara har guda
5, Abdullah, ibraheem wanda yaci sunan kakan su sai khadijah, Amina, Fadila ce K'aramar su.

Sai Alhj mustapha da matar shi hajia zulaihat suna da yara 5, kabeer, mus'ab, ummu aimana,
marwa da autar su habiba wadda taci sunan babar Alhj ibraheem suna kiranta da Ilham.

Da kuma Alhj umar da matar shi hajia zuhra da yaran su 3, yaseer,rufaida da Asma'ul husna
mai sunan hajia maamaa suna kiranta da husna, sai autar su fatyma tana auren wani babban
d'an kasuwa itace matar shi ta biyu tana da yara 2 mata sai namiji d'aya, farida, raudah sai bilal,
wannan familyn suna xaune lafia da kwanciyar hankali ga had'in kai da xumunci hka matan ma
suna xaune lafia xamane na wayayyu kowanne da aikin shi .

Dukkanin su kyawawa ne kunsan Fulani akwai kyau masha Allah gasu farare ne sol gaba
d'ayan su Idan ka d'auke husna da chocolate colour wato mai duhu bata kaisu haske ba amman
duk tafi so kyau gashi kamar su d'aya da ka gansu ka ga en uwan juna, don Alhj ibraheem da
hajia Asma'u auren xumunci akayi musu.
Duk gidan nan ibraheem IB jinin su bai hadu da husna ba ya tsane ta dalilin tsanar kuwa irin
husna kaxaman yaran nan ne duk kuwa da tsabtar mameen ta kuwa brush bata cika yin shi
kullum ba sai mamee ta danneta tayi mata shi ta dole tana kuka da ihu sannan haka ma wanka
don hka shi yasa ko abu ta ta6a ibraheem baya ta6a shi balle yayi amfani dashi da ace duka
yana sa tayi tsabta da tuni husna tayi ko karatu Bata mayar da hankali akan shi sai wasa kawai,
ga shegen cin naman tsiya kamar mayya ko a abinci ta gani ta kwashe ta cinye shi.

Shi kuwa Yah Abdullah duk acikin yayan ninsu yafi bata kulawa fiye da kowa shi yake lalla6a ta
daga shi sai mumyn su ibraheem suna sonta sosai.

Ibraheem yasha siyan abubuwa ya raba wa kanannen shi Amman ban da husna haka xata
k'ara ci kukan ta baxai Bata ba sai dai idan Yah Abdullah yana nan ko Mumy sai su bata, kuma
ba ruwan shi Ko agaban mameen ta kuwa xai ci xalinta baya kiran sunan ta sai kaxama ko
mummuna baka kinfa kowa muni a gidan nan ko abu baya ci Idan husna tana wajen saboda
tsabar k'amk'amin ta.

Hajia maamaa tana bala'in son ibraheem duk cikin jikokinta tafi son shi, shima yana sonta sosai
shi yasa ya dawo part d'in ta da xama gaba d'aya ,Hka kusan sauran yaran ko dayaushe suna
part d'in ta.

Yah Abdullah yana karantar account ne a jami'ar ABU dake cikin garin xaria yayin da ibraheem
yake karantar physiology shima a ABU di'n sai dai Abdullah yana gaba dashi, IB ya had'u ta
ko'ina tun yanxu emmata suna kawo mishi rububi, miskiline na k'in k'arawa ga jan aji yana kuma
da kamun kai ba ruwan shi da irin shiriritar nan na matasa yana da dad'in xama Idan har ka
fuskan ce shi.

Ibraheem muktar ibraheem kyakkyawa ne fari ne sol dashi gashi dogo tubarkallah yana da
hanci ga manyan idanu sajen shi da ya kwanta akan kyakkyawar fuskar shi ba k'aramin k'ara
fito mishi da kyan shi yayi ba gashin kanshi kuwa irin na fulanin asali ne mai laushi da santsi kai
ta ko'ina IB ya had'u

Acikin xuciyar Ibraheem IB yana da wani buri a xuciyar shi wanda shi da *DANGARTAKAR
ZUCIyar* shi ne kad'ai suka san tsawon lokacin da yake cikin xuciyar shi yak'i bayyana shi ga
kowa yana jiran lokaci da ya kamata ya bayyana shi...............

_toh ko mene wannan acikin xuciyar IB sai ku biyo mu don jin wannan abin da IB ya barshi
daga shi sai *DANGARTAKAR ZUCIyar*_




Aishat A muh'd

*&*

Sumayya salees sadeeq
[25/07, 09:00] Aishat A. Muhd: 🍃 *DANGARTAKAR XUCI*🍃






*Written by*

Sumayya salees sadeeq

*&*



Aishat A mu'hd






*Page 5-6*






"Yau ta kama saturday, gaba daya jikokin hajia maamaa suna xaune a babban palour d'inta,ko
wannen su dauke da littafi a hannunsu yayyan su na masu lesson. Ibrahim xaune a gefen
maamaa suna hira da ita, a hankali husna ta bankad'o curtain d'in d'akin tana hangawa, gaba
d'aya ta tsure,ibrahim na daria hankalinsa ya koma bakin kofar, ganin husna na rabe rabe yasa
ya saki wani murmushin mugunta, bata rai yyi ya kalleta, cikin tsawa ya kirata, xonan husna.





"Sanye take da wata multi colour gown iya gwiwarta, gashin kanta daure da blue ribbon sai
sheki yake, school bag ce rataye a bayanta, sai kwalin exotic da ta taho dashi tana sha. Yau
kam husna fes take dan ynx mamee ta gama mata wanka sannan ta kad'o kanta.





"Gaba d'aya hankalinsu yyi wajen ganin husna yasa wasu suka fara tausaya mata, dan bbu
sauki tunda ya abdallah baya nan,dama shi kad'ai ne xai iya dakatar da ibrahim.

"Jiki na bari ta karaso cikin palour harta fara kuka, gaba daya jikinta bari yake dan a dunia tana
bala'in tsoron ibrahim, a hankali ta tako kusa dashi ta tsugunna k'asa, ya ibrahim gani ta fada
tana rawar murya.




"Hannun yasa ya kama kunnen husna ya rike, cikin karkausar murya ya fara magana, husna
dan ubanki mai ya hanaki xuwa lesson tunda xu? Yarfe hannu take dan kunnenta xafi yake
mata. Ya ibrahim har xan taho mamee na ta hanani wai sai ta mini wanka dan Allah kayi hakuri,
wani wicked smile ibrahim yyi ya kalli husna, oya tashi ki mini jump frog, ido husna ta fito dashi
hawayen fuskarta na xuba, dan ita tunda take bata taba yin jump frog ba.





"Ya ibrahim...... Bata karasa ba ibrahim ya dauke fuskarta da mari, a kasa husna ta xube tana
kuka, tsawa ya daka mata ki tashi nace kiyi jump frog.





"Gaba daya maamaa ta tsure dan batasan ganin yarda ibrahim yake dukan husna kamar jaka,
amma bbu damar magana dan bata kaunar bacin ransa. Kabeer da mus'ab ne suka tashi a
fusace suka bar palour dan baxasu iya ganin wannan xalincin ba, gashi bbu damar magana
tunda duk palour din ya girmesu, and a kwai respect a tsakanin su.




"Su khadija, amina, fadila, ummu aimana, marwa, habiba, sai rufaida yayar husna. Gaba dayan
su kuka suke a boye dan kar ya ibrahim ya gani suma ya saka su jump frog din. A hankali
husna ta tashi fuskarta shabe-shabe da hawaye da majina, cire school bag din ta tayi ta ajiye a
gefe ta fara jump frog.




"Motar abdallah ce ta danno cikin gidan, tafe yake yana nishadi, ganin Kabeer da mus'ab yyi

sun fito a fusace daga part din maamaa yasa hankalinsa ya tashi, tabbas yasan akwai abinda
ke faruwa, wani birki ya ci a gabansu bai kashe motar ba ya fito ya na tambayar su ko lpy? Cikin
bacin rai kabeer ya bawa abdallah labarin abinda ke faruwa, bai bari sun kai karshe ba ya nufi
part din maamaa da gudu.




"Ba tare da sallama ba ko kuma tuna cewa ana sallama, abdallah ya bankad'o curtain

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0