Showing 27001 words to 30000 words out of 79519 words
be past" jinjina kanta kawai tayi tamkar Yusrah na gabanta a kasa lance ta shige cikin Jakuzzie tare da sakin ajjiyar zuciyar zuciya sabida ɗumin ruwan daya ratsata.
Sosai ruwan yay mata daɗi har wani bacci ne ya fara ɗaukanta ganin jiranta ake yasa tayi saurin yin wankan tare da yin brush ta gabatar da alwala.
Wani long ash ɗin towel ta ɗauka tare da ɗaurawa a jikinta saida ta tsane sumar kanta tare da busar da ita sannan tasa hannu tare da fituwa daga toilet ɗin.
Da kallo Yusrah take binta dashi tare da mamakin baiwar sumar da Allah yay mata musamman leg ɗinta da gashi yake kwance baƙi siɗik sai gyalli yake ko'ina yay luff dashi,cikin sauri ta gama shiryawa tare da gabatar da sallah wani ƙaton hijab ta saka harjan ƙasa yake tana gamawa Yusrah ta riƙe hannunta sukayi waje.
Tun daga nesa ya zuba mata mayatattun idanunsa ko ƙiftawa ba yayi yana jin wani irin magaɗisu na ɗibansa a kanta lumshe idanu yay tare lashe laɓɓansa kamar wani maye.
Kanta a sunkuye suka ƙarasu daining area ɗin duk da jikinta ya gama gaya mata kallonta yake amma saita basar tare da zama nesa dashi cikin baƙunta da kuma sanyin murya tace "barka da gida Momma da Alhaji" kamar yadda taji suna faɗa fuskarsa fal murna yake kallon Lili domin nutsuwarta ta gama yi masa yaji ta kwanta masa fatansa Allah yasa ta amincewa Sufyan kamar yadda yay masa bayani.
"Yawwa ɗiyata yaya jiki?"ya faɗa tare da zuba masa idanu,ido ta lumshe tare da buɗewa kana ta cije bakinta tare da taunesu sai kuma wasu hawaye suka shiga fita daga idanunta ganin Alhajin ya tuna mata da Daddynta.
Cikin sauri Sufyan ya miƙe tare dayin wajanta amma hararar da Momma ta watsa masa ya sashi sosa kai tare da shigewa flat ɗinsa domin bazai jure ganinta haka ba.
Babu wanda ta ƙara cewa komai sai abincinsu kawai suke ci Lili babu abinda ta iya ci sai fruit salad ɗin da Momma ta haɗa mata,saida suka gama ci sannan Alhaji ya kalli Lili tare da faɗin.
"Ɗiyata yayanki Sufyan yazumin da wata buƙata a kan yana neman alfarmar a bashi auranki ni kuma na amince da hakan domin yanzu matsayin uba nake a wajanki kuma keɗin amanace a wajanmu kuma zamanki haka bazai yiwuba tunda Sufyan yana sonki sosai kuma kema kina buƙatar mai kula dake a halin yanzu so I already make my decision to be his wife " a mugun kiɗime Lili ta ɗagu tare da zubawa Alhaji idanu yayinda wasu hawaye masu zafi suka ɓallemata tare da bin kan fuskarta,Kanta ta shiga girgizawa bakinta ya shiga rawa cikin suɓutar maki tace.
*Gadai yau ɗinnan ko suwaye ya suyi na sara tsakanin SARAUTA PLACE da JUYAYI FANS💃🏻🎉🤾🏻♀️ ina zuba idon ganin Comments ɗinku*
F@y@l
_the sicret issues_
*💖JUYAYI💖*
*16-17*
Wattpad@Nimcyluv
*PEOPLE* may destroy your image, stain your personality, but they can't take away your good deeds because no matter how they describe you, you will still be admired by those who really know you matter.
*Dedicated to* Ummu aymana Alkairin Allah ya tabba gareki naga saƙonki ina gdy sosai Allah ya saka da firdausi🙌🏻thanks for the ƙauna Sarauta na maki sonso🥰😘.
No edited🙇🏻♀️.
......"Na amince Alhaji" itace kalmar data faɗa lokacin da wasu siraran hawaye suka shiga zubu mata daga cikin idanunta,gefe na zuciyarta kuma tana yi mata wani irin ciwo haɗi da raɗaɗi da kuma baƙin cikin kalmar data faɗa wanda ita kanta bata san ta faɗe ta ba,Tayi hakanne sabida taimakonsu a gareni inaji suɗin alkairine tunda har suka amince da zamana a garesu rashin amincewa tamkar yankewar zamana a garesu.
Bana da kowa bana da komai su nake gani a matsayin ahalina Momma matsayin Mamy yayinda Alhaji yake matsayin Dad,Yusrah matsayin Najma sai kuma babban jigo wanda tayi rashinsa a lokacin da komai ya ƙare mata tayi kukan rashinsa lokacin da take buƙatarsa yay mata nisa when all is gone ta rasa madafa bata da nutsuwa farin ciki yay ƙaura daga gareta ina zata ganshi domin ya taimaki rayuwarta.
Har abada tunaninsa shine a ranta domin ta fahimci da jininsa take rayuwa duk wani bugun da zuciyarta za tayi haɗi da fitar numfashi basa fita saida tunaninsa sai yaushe ne zata ganshi? yaushe ne za taga garkuwarta? A kullum tambayar da take yawan yiwa kanta ne a ɗan lokacinnan amma babu amsa saidai tai ta tunani ita ɗaya wanda kuma tunanin a gareta bara zanane wa rayuwarta amma babu yadda zata iya tunanin shine abincita da kuma ruwanta haka kuma shine abokin hirarta rayuwa dashi ya zame mata dole.
Faɗaɗa fuska Alhaji yay cike da farin ciki ya shiga sawa Lili albarka dan yasan she never rejecting his ambition ƙara bata haƙurin rashin iyayenta yay domin ta sanar masu komai ya kuma shaida masu aɗan ƙaramin lokaci za'ai bikin yana fita gobe sai sanarwa da Kawon Sufyan yana gama faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa flat ɗinsa.
Kifa kanta tayi saman daining ta shiga sauke ajjiyar zuciya rashin iyaye masifane haka mutuwar iyaye tuzarcine tana jin tausayin mara amma bata taɓa jin tausayin wani mara mai tsanani a zuciyarta ba saida ta rasa nata iyaye hausawa sunyi gsky da sukace duk wanda bai iya kuka ba iyayensa basu mutu ba,ta tabbatar yadda ta kejin damuwa da kuma hali na rashin lafiya da tuni Ahalinta sunyi rufdugu a kanta haka nan ba zata taɓa bacci ba sai a jikin wani nata,saukar muryar Momma da taji ita ta dawo da ita daga dugun tunanin data luula,kasa amsawa tayi sabida laɓɓanta da sukai mata nauyi a hankali ta ɗaga manyan idanunta tare da saukesu a kanta Momma ba tare data amsa kiran sunanta da tayi ba.
Ganin hakan ya tabbatarwa Momma Lubna tana ɗaya daga cikin mutana nan wanda basa son surutu haɗi da takura musamman a wajan wanda basu sani ba kuka ta lura Lubna irin mutananne masu zurfi ciki da kuma riƙe damuwa da kuma haƙurin zama da mutane,ta fahimci ita ɗin irin mutananne masu rama alkairi da abun alkairi ta fahimci ta amince da auren Sufyan ne kawai sabida taimaƙonsu gareta bawai ta amince bane dan tana sonsa da kuma son zama dashi ba cikin tatausan Lafazi ga wanda ake son ayiwa magana ya kuma fahimci abinda ake faɗa masa Momma tace.
"Soyayya abace mai wahala gaske amma idan kayi dace da masoyi na gaskiya mai yarda da kuma amana haɗi da ɗauke kai babu shakka kayi dace da masoyin gaskiya Lubna,akwai ƙaddarorin cikin Soyayya haka kuma akwai alkairai masoyin da zai ɗauki damuwarki ya maidata tashi shine masoyi haka kuma Masoyin da zai baki farin ciki fiye da yadda zaki bashi wannan shine "ƘAUNA" kada ka taɓa zama da Masoyi domin kancewarsa mai kyau ko mai Arziƙi ko kuma Dangi aa ka zauna da mutum a kan ka amince sabida kana sonsa da ƙaunar sabida Allah ba dan wani abuda yake dashi ba,Soyayya nada daɗi musamman ka samu wanda zuciyarka ta amince dashi amma wasu nayi mata wani kallo a kan a bace mai tarwatsa zuciyoyin mutane tabbas Soyyaya nasa mutum yaji inama baizo duniyar ba dalilin yaudararsu da a kai amma abun fahimtar dukkan saurayin daya rabu da mace Ubangiji ya ƙaddara hakan فمن قددر الله حقا قدره ita ƙaddara ta riƙa fata daman shiɗin ba alkairi bane garesu domin ace Matar mutum kabarinsa,duk daɗewar mace a gidansu da kuma yawan shekarunta batai aure ba wannan ba abinda za'a ɗaga hankali bane domin ubangiji ne bai bata mijin auren ba kuma lokacinta ne baiyi ba domin kafin a haifi mace an haifi mijin aureta..."Numfashi Momma taja tare da zubawa Lubna ido ganin tana fahimtar abinda take faɗa mata tana fahimta Thank God domin duk hankalin Lubna na kanta,numfasawa Momma tayi tare da faɗin.
"Wannan fitila na baki keda kanki zaki haska zuciyarki domin tabbatarwa kanki wanda kikeso kuma kike muradi abu ɗaya na sani Sufyan na sonki"tana faɗin hakan ta miƙe tare dayiwa Lili alamar "Goodnight" da hannu wata sassanyar ajjiyar zuciya Lili ta sauke mai ƙarfi tare da lumshe luntsuma-luntsuman idanunta haɗe da taune cute peach lips ɗinta jiki babu ƙwari ta miƙe tare dayin bedroom ɗin Yusrah tana zuwa ta cire zumbulelen hijabin dake jikinta wanda duk ya dameta daman ta sashi ne sabida Sufyan toilet ta shiga tare da ɗaura alwala haɗi dayin brush kana ta fitu tare addu'ar bacci ta shafe jikinta kana ta haye bed ɗin tare da shigewa jikin yusrah ta shiga sauke ajjiyar zuciya duk yadda tasu tayi tunani a kan maganganun Momma amma ta gagara blanket taja masu tare da ƙara shigewa jikin Yusrah domin tana bala'in son ta jita jikin wani few minutes bacci yay gaba da ita.
Wasa-wa yau satin Lubna biyu a gidansu Sufyan sosai suke bata kulawa har yaza mana ta manta da wasu abubuwan da suke faru da ita shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninta da Yusrah wacce ta kewa kallon Najma komai tare suke abu na farko da zai baka mamaki yadda soyayya mai ƙarfin gaske haɗi da shaƙuwa ta shiga tsakaninta da Sufyan saida ta nuna masa ɓacin rai sosai kafin ya daina taɓa jikinta amma idan ya ganta ji yake kamar yay hauka shiyawa bai damu da zaman gidan ba,yafi zama a office ɗinsa yayinda ya tilastawa Alhaji ya dawo da maganar aurensu kusa cikin sa'a aka mai dashi sati biyu kacal.
Hakan yaywa Lili daɗi domin ta gaji da halinda Sufyan ɗin ke nuna mata dan har wasan ɓoye yake wani lokacinma saiya kaiwa Momma ƙararta sannan take fituwa suyi hira amma tunanin ɗan uwanta kuma yayanta yana nan maƙale a ranta musamman yanzu da take yawan mafarkinsa wanda ya zame mata al'ada.
**** ****
Zafin bugun da Fahad yay masa ya sashi ɗaukewar numfashi na wasu sakanni hannu yasa a saman kansa jin laima nabin gefen fuskarsa ɗan waro ido yay cike da tsoro ganin jini kwance a jikin hannunsa.
Yadda yake fitar da wani numfashi mai ƙarfi tare da hurga da dukkan abinda yay karo dashi yasa Fauwaz saurin miƙewa tare dayin wajansa a karo na biyu.
Yana zuwa yaɗan ja da baya tare da zubawa Fahad ido sosai yake jin tausayin abokin nasa musamman idan ya tuna bashi da kuwa komai ya ƙare masa,babban abinda yake damunsa ganin har yau bai yarda Lubna ta rasu ba ƙaddara tazu when all is gone,baya da farin ciki,walwala,ƙwanciyar hankali,bashi da komai sai yau tunani gashi murɗaɗɗan mutum wanda sam bai damu da kuwa ba kamar yadda bai damu da asan abinda ke ƙwance cikin zuciyarsa ba,shi ɗin mutunne mai zurfin ciki da wahala ka gane abinda ke damunsa bare kuma face ɗinsa yay showing abinda yake ɓoyewa a zuciyarsa ba.
A sanyaye Fauwaz ya ƙira sunan Fahad tare da faɗin "how long zaka kasance a cikin damuwa?damuwa bata kamace ka ba a wannan lokacin ya kamata kana maida damuwar zuga Allah ubangiji maɗaukakin sarki shine ke ɗurawa bawa lalura kuma shine ke yayewa,maimakon ka samu sauƙi a ranka saika ƙara samun damuwa cikin ranka,kai musulmi me yana da kyau ka ɗauki ƙaddararka mai kyau ko mara kyau kasan cewa ƙaddara abace mara tabbas,tabbas ƙaddara lokacine bawai kullum mutum ke kasancewa a cikin taɓa akwai lokacin da zaizo sai kaga kamar ba'ai ba,Fahad imaninka bazai taɓa cika ba saika yarda da ƙaddara kaci gaba da haƙuri da kuma addu'a sai kaga ka fita daga cikin JUYAYIN da kake ciki amma ni kaina wannan sicret issues ɗin yana juya tunani kayi dan Allah tun kafin a haifi mutum an riga da an rubuta ƙaddararsa a jikin allon Lauhil Mahafuz allon da babu wanda ya isa ya goge abinda yake jiinsa".
Ajjiyar zuciyar Fahad ya shiga saukewa tare da fesar da wani zazzafan numfashi daga cikin bakinsa,sosai yake ladamar kasancewarsa a raye mai yasa bai tsaya sun haɗa dashi sun kashe ba? Mai yasa Dad ya bashi amanar Lubna?mai yasa Dad ya haɗa dukkan wasu ƙaddarorinsa ya bashi?mai yasa bai duba taƙaddar da Dad ya bashi ba?mai ya kawoshi pakistan mai makon ya juya zuwa mahaifarsa kano?shin da gaske Lubna bata raye? Shin ƴan fashin da suka kashe masa iyaye sun manta cewa sunbar iri wanda zai iya zama shuka harya yaɗu yay furanni tare da zuba ƴar ƴar?mai yasa ya manta ta ƙaddarar da Dad ya bashi ba tare daya duba ba".
All this daya faru ƙaddara ne wacce tana iya faɗawa kan kuwa kuma idan ubangiji ya jarabceka da ƙaddara yay hakanne dan gwana imaninka bawai dan baya sonka ba.
Lumshe idanunsa yay wanda suka gama sauya kala daga fari zuwa jaa wanda har wani ruwa² suke sabida tsananin damuwar da yake ciki,tabbas idan har yana son cimma burinsa da kuma muradin ransa tare da ɗaukar fansa dole ne ya aro jarumta tare da ƙarfin guiwwa ya sama ransa,a karo na barkatai ya ƙara sakin ajjiyar zuciya tare dasa hannu ya dafe saitin zuciyarsa wacce keyi masa matsanancin bugu a hankali ya suma girgiza kansa wanda yake masa ciwo domin duba ɗaya zakai masa kasan cewa kawai dauriya yake musamman idai mutum ya kalli yadda jijiyoyin kansa suka firfitu tare dayin raɗa² saman forehead ɗinsa.
Bakinsa ya shiga mutsawa a ƙoƙarinsa nason furta wani abun amma yadda laɓɓansa sukai masa nauyi ne ya sashi taune lips ɗinsa cikin zuciyarshi ya shiga faɗin."يا الواحد "
"ka kawomin ɗauki da gaggawa" yana faɗin hakan ya ƙara lumshe idanunsa wanda suka suma lumshe sabida jirin dake ɗibansa,ganin hakan yasa Fauwaz ya ɗauko masa gorar ruwa mai sanyi baiyi musu ba amsa domin yana buƙatar jin sanyi a ransa murfin gorar ya ɓalle tare da ƙafawa a bakinsa saida yasha fiye da rabi sannan ya cire bakin gorar daga cikin bakinsa ganin ya samu nutsuwa ne Fauwaz ya amshi raguwar ruwan tare da faɗin.
"Destiny lots of folks confuse of bad management with destiny, destiny is no matter of chance's it not a thing to be waiting for, it's a thing to be achieved, ur destiny change with ur thought".
Wani sanyi ne ya shiga ratsa zuciyarsa tare da ganggar jikinsa zuwa yanzu ya kamata ace ya yadda da ƙaddara kuma ya maida hankalinsa zuwa ga abida zuciyarsa domin yana jin abun a matsayin heart dream first aid box Fauwaz ya ɗauko tare da zama kusa da abokin nasa tare da gyara masa wajan da yaji ciwo ɗago jajayen idanunsa yay tare da mannasu a kan Fauwaz cikin lion voice yace "ka kula da kanka" yana faɗin hakan ya miƙe tare da shigewa cikin bathroom yana shiga ya cire ƙananun kayan dake jikinsa ya sakale saman hanger,tsakiyar shower ya tsaya tare da shakarwa kansa ruwa'n shower'n hannayensa duka biyu ya dafe bango dasu tare da sadda kansa ƙasa ruwan ya shiga duka back naked skin ɗinsa mai kyau da kuma tsari.
Ya daɗe yana sauraran dukan ruwa'n shower'n kafin ya ɗago kansa tare da lumshe idonsa ya saida full face ɗinsa tsakiyar ruwan sosai ruwan ya shiga dokan fuskarsa tare da shigewa cikin hancinsa ta bakinsa saiya zamana kamar wata a zabace yakewa kansa,ɗan tari yay tare da janye fuskarsa jin numfashinsa na ƙoƙarin ɗaukewa alwala yay tare dayin brush kana ya saka bathrope a jikinsa ya fitu kansa na zubar da ruwa tare da ƙwantaccen gashin jikinsa.
Bedroom ɗinsa ya nufa yana zuwa ya fara gyara kansa cike da nutsuwa da kuzari ɗan lokaci kaɗan gashin kansa ya shiga fidda wani ƙamshi mai daɗi shaƙa sumar tayi luff a kansa har zuwa ƙasan wuyansa bai wani shafa mai ba sabida babu irin wanda yake using dashi ganin akwai body spray ne ya sashi ɗauka yare fesawa a jikinsa domin Fahad yana bala'in son ƙamshi baya wasa da turare,yana kammalawa ga buɗe wadrope ɗin kayan Fauwaz ɗan taɓe baki yay dan baison sharing kaya,cikin sa'a yaga ɓangaren wasu kaya sabbi wata coffie ɗin jallabiya ya ɗauka tare da zurawa a jikinsa ya shimfiɗa prayer mat ya tada sallar magrib.
Fannerh na shiga cikin gidansu ta tarar da Afnerh kwance a kan sofa ta zurfafa cikin tunanin da kullum dashi take kwana kuma take tashi har yau ankasa gane abinda yake damunsa cike da zolaya Fannerh tace "pls Hadnerh zoki ta yani aiki mana" ɗago ido Afnerh tayi tare da zubawa Fannerh ido kafin ta murguɗa baki tare da faɗin.
"Kin daɗe baki aikin ba"dry Fannerh tayi kana tace"a'a nikam zanyi tunda bake zanyiwa,na fahimci baƙin ciki kikewa My Husband to be sabida ba Heart dream ɗinki bane ko?"tsaki Afnerh taja tare da faɗin "Na you sabi".
Ganin idanta biyewa Afnerh zata ɓata mata lokaci ne kawai yasa kai tsaye tayi kichen tana shiga ta tarar da Lami mai aiki cikin girmamawa Fannerh ya gaidata tare dayi mata sannu da aiki.
Kayan da zata buƙata ta ɗauka cikin sauri ta shiga yin aikinta wajan 1hour ta ɗauka kafin ta kammalawa pepper soup and white rice sai cipis tare fruits salad sai lafiayyen coconut juice,tana gamawa ta haɗa komai cikin basket tare da barin kichen ɗin daret flat ɗinsu ta nufa tana shiga ta tarar da Afnerh tsaye gaban madubi tana gyara kanta da alama daga wanka ta fitu.
"yawwa beb shirya ki rakani" tana faɗin hakan itama ta shige cikin toilet basu wani ɓata lokaci ba suka gama shiryawa cikin abayarsu iri ɗaya Fanner tasa milk wacce take da adon red flowers Afnerh kuma tasa red mai adon milk ɗin flower kasan cewarta chocolate colour sai abayar tayi mata kyau sosai suna matuƙar kama da juna dake suɗin twints ne Afnerh nada tsiwa sosai sannan bata fiya ɗaukan raini ba amma tana da sauƙin kai,yayinda Fannerh take da surutu sosai da kuma kyauta amma tana da nunƙufarci da kuma riƙo a tare suka fitu daga bedroom ɗin nasu inda suka tarar da Mama zaune a parlour tana kallon tashar zee world lokacin sun fara haska fire and ice kallonsu tayi tare da murmushi kafin ta sauke idanunta kan Fannerh tace"2weeks ya rage bikinki amma still baki bar fita ba?"turo