Showing 9001 words to 12000 words out of 79519 words

Chapter 4 - JUYAYI BOOK COMPELET BY NIMCY LUV

da cewa"maza jeki ga mijinki Lili yanzu ne lokacinki ya suma kada kibar duk wata hanya da wata ƴar mace ko wani ɗa namiji ya shiga rayuwarka har saku a JUYAYIN da zaku kasa gane abinda ke tsakanin,ki zama mace mai jajircewa ki rage wannan shurun naki,ki zama mace mai tsayawa akan ra'ayinta all the best bebyn Boobi no more faɗa tsakaninki da yayanki oyyah go".

Cikin saurin Lili ta fice daga office ɗin babu inda ta tsaya sai compound ɗin asibitin inda ta ajjiye motart,Tana zuwa ta buɗe motar tare dayin bisimillah ta faɗa ciki bata tsaya jiran komai ba ta yiwa motar key da gudu ta fice daga cikin asibitin.

Da kallo dr Layler tabi bayan Lili haka kawai taji wata far gaba mai kama da tsoro sun shigeta,tabbas she still virgin amma tayaya za'ai brother yaywa sister nashi haka,shiyasa a kace duk inda mace da namiji suka keɓe na ukunsu sheɗanne,haka kawai ta samu kanta da son ganin yayan Lili wanda taji tana gaya masa suna Boobi,Lumshe ido tayi lokacin data tuna da farin cikinta wanda ta kejin ko duk mutanan duniya zasu haɗu babu wanda ya isa ya hanata mallakarsa a matsayin mijinta,bata son kowa ya raɓu dashi hatta ƴan uwansa tafi son ace komai nasa itace ta zama ruwa da tsokar jikinsa(uhm abeg Halima muhamman umar come carry ur ƴar uwa😅).
Ji tayi aikin duk ya dameta babu wanda ta keson gani sai dr ɗinta cike da zumuɗi ta cire farar rigar jikinta ganin ardy tym ɗin tashi yaya dan wajan 5:30 wata blue black ɗin abaya ta ɗauka ta saka a jikinta tare dayin rolling da vail ɗin rigar a kanta wani peach ɗin lipstic ta ɗauka a cikin hand bag ɗinta ta shafa saman faffaɗan lips ɗinta mai ɗan duhu tana gabawa ta ɗauki perfume ta shiga fesawa a jikinta dashi saida ta gama komai sannan ta fice daga office'n ta nufi office ɗinsa,A hankali ta shiga knoking amma shuru ba'ai magana ba kasancewar tasan halinsa bazai magana ba musamman idan yasan itace,Murɗa handle ɗin ƙofar ta shiga,fituwarsa kenan daga cikin toilet ya wasa ruwa yana ƙoƙarin saka rigarsa ta shigo ciki,Idonta ne ya sauka a gashin ƙirjinsa da yake baƙi siɗiƙ yay luff sai ɗigar ruwa yake ido ta lumshe ta najin wani abu nayi mata yawo a jiki musamman yadda lafiyayyiyar skin ɗinta ke zubar da ƴan ƙananun ruwa sai shaning take gaba ɗaya surar jikinsa abin kallonce musamman idan kayi duba da lafiyayyiyar arms ɗinsa wacce take a murɗe,lips ɗinsa ta zubawa ido ganin yadda yake ta taunesu tare da lumshe idonsa banda shi babu wanda taga yana yawan taune lips sai Lili ta rasa abinda su keji game da hakan,Murmushi tayi tare da zura lips ɗinta na ƙasa ciki bakinta ta haɗa da haƙoranta ta taune lips ɗinta cikin sauri ta fitu da harshenta tare dayin wata ƙara sbd azabar da taji,Tsaki Fahad yaja jin kamar zata fasa masa kai sbd ƙarar da tayi key ɗin motarsa ya ɗauka yana shirin fita tayi saurin shan gabansa tare da faɗin"Haba Fahad amma yana da kywu ka tsaya kaji me zance maka ko"lumshe idonta yay yana jin kamar ana buga masa guduma aka sbd tsananin ciwon da kansa yake masa,Ko kallonta bai yiba yana ƙoƙarin hucewa yaji ta shige jikinsa tare da sakin kukan munafurci da kissa"meye laifina dan zuciyata tasu wanda ya kamata ace ana sonsa,pls Fahad kaji tausayina wallahi ina sonka sosai dan Allah kada kasa sonka ya jani na aikata abinda bai dace ba"takai ƙarshen maganar tana ƙara ƙaleshi,lips ɗinsa ɗinsa na ƙasa ya shiga sucking a rayuwarsa ya tsani mace mai bibbiko matsifa shifa yana da hankali yasan mai yake tayaya take tunanin zaiso mace kamarta wacce bayyana tsaraici bayayi mata wahala ɗan tsaki yaja kana yasa hannunsa ya zareta daga jikinsa tare da kama hannunta suka fice daga office ɗin,Suna fita yay saurin sakinta tare da rufe office ɗin nasa,Baibi ta kanta ba ya huce harabar asibitin yana zuwa ya nufi wata ƙaramar motarsa mai kyan gaske wacce ake yanzu yana zuwa ya buɗe tare da ɗaga rigarsa ya zauna ya daɗe a cikin motar kafin yay mata key yabar asibitin da sauri.


*Maiduguri road*
A hankali ya shiga buɗe idonsa wanda sukai masa nauyin gaske sbd daɗewa da yayi yana bacci,bakinsa ɗauke da addu'ar tashi daga bacci ya gama ware idonsa da suka ƙanƙance sosai zallar damuwa ta bayya saman kan fuskarsa duk ƙoƙarinsa nason ɓuye abinda yake damunsa amma ya gagara yin hakan,sosai abinda sosai abinda sukai shida Najma keyi masa yawo a brain ɗinsa duk da cewa baisan cewa Yayar matarsa bace gaba ɗaya tunaninsa bbynsa ce,amma mai yasa rauni keson bayyana a tattare dashi mai yasan yake tsintar kansa cikin faɗuwar gaba haɗi da bugawar zuciya,Ganin baya da amsa ga kuma yadda yaji masallatai suna kiran sallar magrib yasa ya miƙe jiki a sanyaye ya shige toilet ɗin dake cikin ɗakinsa,yana shiga ya zare jallabiyar jikinsa tare da saita ruwan shower'n yazu daɗan ɗuminsa,a tsakiyar shower'n ya tsaya tare da sauke ajjiyar zuciya sbd yadda ruwan yake dukan jikinsa yana ratsa duka wata ƙofa ta gangar jikinsa,Ya daɗe ruwa na ratsashi kafin ya shiga yin wankan yana kammalawa yay brush tare da ɗaura alwala ya fitu daga cikin toilet,Wajan dressing mirrow ya nufa ya shiga tsane kansa wani lotion ya ɗauka ya shafa a jikinsa yana gamawa ya fesa body spray,Ganin bayajin daɗi kuma babu inda zashi hasalima matar tasa sai gobe za'a kawota yasa ya ɗauki wata jallabiya mai sauƙin nauyi yasa baya jin zai iya zuwa masallaci dan haka ya shimfiɗa paryer mat ya data sallah.

A can parlo kuma Ammi ce zaune ita da Papa suna ɗan tattaunawa a tsakaninsu,ɗan gyara zama Papa yay tare da faɗin"wai ina son ne i have been see him lpa dai"cikin muryar damuwa Ammi tace"tun bayan ɗaurin aurensa daya shigo ya shige ɗakinsa bai ƙara fituwa ba amma inajin there's a prblm am not sure dai bari na kirasa"ta faɗa tare da ɗaukan wayarta,jin alamin ana sauka daga steps ɗin bene yasa ta ɗaga nan sukai haɗa ido dashi ido ta zuba masa tana son ganin abinda ke damunsa dake Faisal bai iya riƙe damuwa a ransa ba nan take fuskarsa ta nuna damuwar da yake ciki.

Ɗan murmushi yay tare da ƙarasawa wajan mahaifin nasa ya gaidashi,kallonsa Papa yay kafin yace"meke damunka?"..."no Papa i'm ok don't wurry" Faisal ya faɗa lokacin da yake kunna wayarsa,Murmushin jin daɗi iyayen nasa sukai kafin Papa ya miƙe tare da faɗin"follow me"yana faɗin hakan ya huce flat ɗinsa,Jiki a sanyaye ya miƙe tare da bin bayan mahaifin nasa.


*Nasarawa*
Lokaci kaɗan ya ƙarasu harabar babban gidan nasu yana zuwa ya samu wajan yay parking a parking space,cike da nutsuwa da kuma kamala haɗi da juriya da kuma kwarjini ya fitu daga cikin motar hannunsa ɗaukw da P.c ɗinsa wacce yake using da ita kai tsaye cikin gidan nasu ya nufa taɓe baki yay jin gidan shuru kamar babu mutane dan daman yasan Najma tafi kowa tsuru more than Lili,ambatar sunanta da yay cikin ransa yaji gabansa yay mugun faɗuwa,baisan mai yasa ta ɗauki gaba dashi har haka ba bai san mai yay mata da zafi haka ba shida yay amfani da kalaman data faɗa masa a matsayinsa na wanda ya lalata mata rayuwarta wanda ya rasa lokacin da hakan ya faru a duk lokacin daya takura kansa wajan yin tunanin gaskiyar abun amma ƙwaƙwalwarsa bata bashi damar hakan a lokacin kuma ji yake kansa kamar zai tarwatse,sautin waƙa yaji na ɗan tashi daga ɓangaren Lilin girgiza kansa kawai yay dan tabbas idan kaji Lili najin waƙa tana cikin matsanacin farin ciki ba ɗan kaɗan ba,Cike da taƙama yasa kai tare dayin hanyar flat ɗinsa dake ƙarshen gidan,yana zuwa yasa key ya buɗe ɗakin nasa wani ni'imataccen ƙamshine ya daki hancinsa ka sancewarsa bai bala'in son ƙamshi,shi yasa ya ƙara buɗe dugun hancinsa ya shiga shaƙa ya daɗe a wajan kafin ya ɗura ƙafarsa akan italian carpet ɗinsa nan take ƙafarsa ta shige cikin carpert ɗin,daman tun a hanya yay sallar magrib da yaji anayi ƙarasawa yay ya ajjiye p.c ɗinsa inda yake ajjiyeta tare da wayarsa ya shiga zare kayan jiinsa ya zubasu a wani ɓangare dake wadrope ɗinsa,Yana gamawa ya shige cikin bathroom kai tsaye wajan shower yaje ya sakarwa kansa ruwa kasancewar bai fiya son ruwan zafi ba,hannayensa duk biyun yasa ya dafe bango ruwan ya shiga dukan tsakiyar bayansa numfashi ya shiga fitarwa mai zafi jikinsa ya ɗauki rawa ba komai ya haddasa masa hakanba sai brain ɗinsa da take son wargatsa matsa lissafi a lokacin da baya buƙatar wani tunani duk yadda ƙwaƙwalwarsa ta keson sashi tunanin ya hanata faruwar hakan,a haka ya kammala wankan tare dayin brush ya ɗaura alwala jin amfara kiran sallar issha'i,wani light blue ɗin toiwel ya ɗaka ya ɗaura a waist ɗinsa kana ya fice daga toilet ɗin,gaban dressing mirrow ya ƙarasa tare da ɗaukan cump ya fara gyara kansa lokaci kaɗan kansa ya shige gyalli haɗi da fitar da wani sahihin ƙamshi sumar tayi luff har ƙasan wuyansa,wani versiline ya ɗauka ya shiga shafawa tattausar fatar jikinsa yana kammalawa ya ɗauki wani turarw oud ya fesa a jikinsa kana ya ɗauki wani abun baki mai fitar da ƙamshi strawberry ya shiga fesawa cikin baƙinsa ɗan lumshe tsumammun idonsa yay sbd daɗin da yaji yana ratsa shi,jikin sanyin jiki ya ƙarasa wajan wadrope ɗinsa ya ciro wata jallabiya fara tas ya zura a jallabiya ganin jam'i ya huce sa ya shimfiɗa dadduma ya data sallah mai cike da zallar nutsuwa.

Lili
Bayan ta gama wankan haɗi da shirya kanta ta sanya wata ƴar duguwar riga iya laps ɗin tare da saka wani 3guater hakan ya basa ɗan ma dai-dai cin hips ɗinta fituwa yay zamansa cikin ƴar rigar data saka,daga sama rigar tana da ɗan faɗi hakan ya bawa rigar damar zama a faffaɗan ƙirjinta gashin ƙanta ta tattara haɗi da ɗauresa da ribbon ya sauka tsakiyar bayanta a hankali take mutsa ƙaramin bakinta ta shiga rera waƙar wait for me,wayarta ta ɗauka tare da shiga wajan messages wata number ta shiga wacce aka rubuta Soulmate ta fara typing kamar haka.

_i can't live without you, without you what's my worth,if i get separate from you than I will get separate from self (my world) because you are the only one i most love madly,you're the only one my eyes want see you, my ear want hear ur voice, i love you more and more most._

Tana gamawa ta tura masa fuskarta ɗauke da zallar farin ciki ta kusa samun muradin zuciyarta,wani black plate shoe ta ɗauka tare da zura cikin ƙafarta,a haka ta fice daga cikin ɗakinta babu ɗankwali tana ɗan tsallanta na ƙuruciya ta ƙarasa daining area don a nan ta kejin maganar mutanan gidan tana zuwa ta ƙara wajan Dad tayi masa sumba tare faɗin"barka da dare my lovely"kanta ya shafa tare da faɗin"yau mamana bakya son saka kallabi a kanki baki jin tsoron jinnu ko?"turo baki tayi gaba ba tare da tace komai ba ta nufi wajan Mamy tare da shigewa jikinta jinjina kai Mamy tayi kafin tace"our Mama ni ba za'a gaidani bako?"ɗan lumshe ido Lili tayi kafin ta ware manyan idanun nata akan Mamaynta tace"ayya Mamy nina isa kece fa rayuwarta"dry sukayi gaba ɗaya kafin Mamy ta ƙara cewa"to ɗagani mana mutum ya girma baisan ya girma ba haba"ɗan buga ƙafata tayi a ƙasa kana ta juya idanunta kasancewar bata son magana yasa taja bakinta tayi shuru,gefenta ta kallah taga Najama ta zabga tagumi ɗan zugurarta tayi tare dayi mata alama da idanu tace"lpa dai beb?"da idanu Najma ta bata amsa da "i'm ok"jinjina kai Lili tayi kafin tace"i'm gland" ƙamshin da taji yana dukan hancinta tun ɗazu yasa ta ɗaga manyan blue eyes ball ɗinta takai duba zuga kujerar dake farcing ɗinta,A hankali ta sauke ganinta a kansa yana zaune ya sadda kansa ƙasa yana latsa wayarsa sosai yay kyau cikin sky blue ɗin singlet ɗin daya saka tare da wando 3guater cikin sanyi murya tace"Boobi barka da hutawa"jice lips ɗinsa yay dan baiyi tunanin zatai masa magana ba haka kuma baya jin zai iya ɗago kai ya kalleta dan haka kawai ya jinjina mata kai,idan ka ganshi zaka ɗauka wayarsa yake dannawa amma garesa babu abinda yake sai santala-santalan fararen legs ɗinta ya zuba ido ta ƙasan daining babu abinda yake bashi mamaki a jikinsa sai yawan gargasar dake kwance jikin ƙafarta sunfi luff-luff abin sha'awa fatar ƙafar sai shaining take.
Mamy ce ta ɗauki spoon haɗi da ɗebo fatan dan kalin turawan daya sha kayan lambu haɗi manyan kifi sai zabga ƙamshi yake,babu inda ta nufa sai bakin Lili wacce ta lafe jikinta tana jan numfashi alamar zatai bacci,cikin sauri Lili ta janye bakinta tare da shagwaɓe fuska kamar zatai kuka,Dariya Dad yay kafin yace"kinsan cewa Mamana ba tacin abinci da spoon saida hannu"Mamy ma dry tayi sannan ta ajjiye spoon ɗin tayi bisimillah tare da saka hannun cikin plate ɗin ta ɗebu abinci tare da kaiwa bakin Lili bisimillah Lili tayi sannan ta amshi abincin tana lumshe idanunta.
Saida kowa ya gama cin abinci sannan Daddy ya gyara murya tare da kallon yaran nasa sauke idonsa yay akan Fahad da babu abinda ya taɓa sai coffee da Mamy tayi masa,Maida idonsa yay kai Lili sannan yace"Mamana nayi maki abinda kikeso kamar yadda kika nemi buƙata a wajana dole na cika maki ita,a zahiri kinji anyi aurenki da Faisal wannan a gsky al'amari ba dake aka ɗaura ba da ƴar uwarki Najma aka ɗaura Faisal aure"wani ihu Lili tayi tare hantsilawa ta faɗi ƙasa daga kan cinyar Mamy..
*_Nimcyluv ce😘_*



*Wattpad@Nimcyluv* *Tue/Dec/2020 3:43pm*
08119237616

*JUYAYI*

*E 6*

_NIMCY SARAUTA😘_

.....A zaune Faisal ya samu mahaifin nasa da sallama ya shiga bedroon ɗin kasan cewar ya nayin sanyi ya suma,A gefen bed ɗin ya zauna tare da ɗura kansa a shoulder ɗin Papa,Sosai ya kejin faɗuwar gaba haɗi da bugawar zuciya wayarsa yaji tayi ƙara alamar Notification ya shiga yasa ya ɗan zame daga jikin Papa ya ɗauki wayarsa dake cikin aljihu gana shiga yaga alama new messge cikin sauri ya buɗe saƙon ganin sunan BEBY BOO na yawo,Wani ƙawataccen murmushi ya saki mai tsadar gaske karanta saƙonta dai² yake da wanke damuwar da tayi maƙale a zuciyarsa wani sanyi yaji na ratsa shi yayinda ya kejin a kashi ɗari na damuwarsa kasu wajan 90 sun tafi,Yafi 10min ya kallon specail luv messge ɗin da akayi masa kafin yaji saukar muryar Papa a kunansa "Faisal bani hankalinka nan" jin abinda Papa yace ne yasa ya ajjiye wayar hannunsa tare zubawa masa ido,A sanyaye Papa ya kalli ɗan nasa wanda yake alfahari dashi yana jinsa har jini da tsukar jikinsa baya son abinda zaizo ya juya masa lissafi dalilin hakan yake ta fargabar tayaya zai masa magana baya so ace sai ankawo masa yaga kamar anyi masa ba dai² ba,Numfashi Papa yaja kafin yace.
"Faisal khalil Jibaɗo shine sunanka da kake alfahari dashi kuma kamar yadda kake alfhari da sunanka nasan haka kake jin dukkan wata maganata kuma nasan ina da ikon da zanyi maka zaɓan abu domin nayi imani da tarbiyar dana baka ba zaka taɓa watsamin ƙasa ka kunyatani jama'a ba,Nasan baka da burin daya huce Auren Lubna amma ka sani zanen ƙaddararka data Lubna ba ɗaya bace dalilin hakanma aka samu matsala wajan aurenku inda aka juya maka aurenka akan ƴar uwarta Najma,Ina son ka amshi ƴar mutane da amana kayi haƙuri ka samawa kan nutsuwa Har abada Lubna ba zata taɓa zama mata a wajanka ba ina fatan zaka amshi wannan auren hannu biyu".

Wata zufa ce ta shiga zubuwa Faisal lokacin ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa yayinda dukkan wani tunaninsa ya tsaya cak baya jin akwai wani abu mafi muni wanda yake ƙoƙarin sa zuciyarsa bugawa irin wannan,Tabbas banda mahaifinsa wanda ya haifeshi ne ya bashi wannan labarin da babu abinda zaisa yaƙi ƙaryata shi,ganin baya da wani abu da zaiyi a ɗakin Papan yasa ya miƙe a hankali ya nufi flat ɗin zuciyarsa fal tunanin abinda suka aikata shida Lilinsa ɗazu.

Bin bayansa Papa yayi da ido yana mai tusayin Ɗan nasa wanda baya iya riƙe damuwarsa a cikin zuciyarsa,Glass ɗinsa ya mayar saman idonsa yaci gaba da duba Jaridar hannunsa yana yiwa yaron nasa addu'ar samun juriya a cikin zuciyarsa.

Faisal na shiga flat ɗin nasa yasa key ya rufe ƙofar bedroom ɗin nasa duguwar Jallabiyar jikinsa ya zare darect wajan wata drower ya ƙarasa yana zuwa yasa hannu ya jawo drower tare da saka hannu ya ɗauki wani Tablet na Effective Relief from pain and fever kana ya ɗauki ruwa a glass cup yasa maganin tare da kafa bakinsa a saman ruwan ya shiga kwankwaɗa saida ya shanye sannan ya miƙe lokacin zufa ta gama wanke masa jiki,Banda harbawa babu abinda kansa keyi masa ya najin wani matsanancin ciwon kai wanda yake bara zanar tarwatsa tunaninsa na kamashi ga yadda mararsa keyi masa azaba haɗi da raɗaɗi tamkar zata fashe a haka ya sulale ya faɗa kan bed lokacin da ƙyar yake buɗe idonsa sbd tsabar damuwa da tunanin daya gama ratsa brain ɗinsa,Banda juyi babu abinda yake gaba ɗaya Papa yasa tunaninsa a JUYAYI ya shafe 30min kafin baccin ɓarawo ya samu nasarar ɗaukesa.




Rano's family
Jin maganar Dad take tamkar saukar ruwa'n sama da ba'a shirya masa gaba ɗaya tunaninta ya tsaya dan ba tayi tunanin Dad ya ɗauki maganarta da gaske ba harya zartar da hukunci akai kasa cewa komai tai sai numfashinta daya shiga ɗaukewa hakan ya nuna alamar ASMARTA nason tashi,Dama ace mafarkine ta keyi ba gasky ba dama ace idan ta farka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login