Showing 36001 words to 39000 words out of 79519 words
gidan cike da mutuntawa Getman ɗin ya buɗe masu ƙofa.
A compound na gidan suka tsaya Fauwaz ya ɗauki wayarsa ya kira Fannerh lokacin ana tsaka dayi mata gyaran jiki taji wayarta na ƙara Afnerh ce ta ɗauka tare dasa a speaker"gamu a compound hope dai Mama na nan dan yace bazai daɗe ba baijin daɗi" dry Afnerh tayi farin ciki fal zuciyarta danta tabbatar yau Mama zata amsar mata soyayyarshi kamar yadda tayi mata alƙwarin.
"ok come in side mana"shine abinda Fannerh tace tare da kashe wayar dan ita ɗagawar Fahad ɗin mugun fusata ta keyi fushinta ya kusa kufcewa a kansa,da gudu Afnerh ya miƙe taje ta faɗawa Mama ita kuma ta shige bedroom ɗinsu tare da sauya kayan jikinta aka fesa uban turare.
Da sallama suka shiga parlour Fauwaz na gaba Fahad na bayansa fuskar nan tasa a haɗe babu yabu babu fallasa,gaba ɗaya suka durƙusa tare da gaida Mama kafinsu miƙe tare da zama kan sofa,"Fahad kaji saƙona wa..."maganarce ta maƙale mata bakinta na rawa ta shiga kallon Fahad tare da nunasa da hannu tace"Fahad kaine..kaine yau a gidana kuma a gabana?"ɗago kai yay cikin sauri zabura yay ya miƙe da sauri ya ƙarasa gabanta tare da faɗawa jikinta a hankali yace "Mamana" sai kuma ya fashe da kuka tare da ƙanƙameta ya shiga rera kukansa a hankali wanda ita kaɗai take iya jin kukansa,lallai ran maza ya ɓaci ba ƙaramin abu zaisa kaga Fahad na zubar da hawaye ba,ita kanta sau ɗaya ta taɓa ganin kukansa lokacin dazai tafi U.S karatu sosai yay kuka kamar ransa zai fita sbd bai son zuwa,bayansa ta shiga bubbugawa tare da shafa sumar kansa "kuka kuma kamar ga ƙwarzon yarona ba ya isa haka nan"ƙara shigewa jikinta yay yana jin kamar ajikin Mamynsa yake,ya jima maƙale da ita kafin ya zame jikinsa ya zubawa Mama idanunsa tare da shagwaɓe mata idan da sabo ta saba da shagwaɓar Fahad.
"Mamana ina Uncle ɗina?"hararar wasa masa tare da faɗin"wanne irin uncle ɗinka kaifa nake shirin tambaya coz wajan watansa guda da rabi da tafiya wajan Daddyka why kuma nida nake nan zaka tambaye ni shi"kallon rashin fahimta yay mata tare da faɗin"u mean Uncle na wajan Daddyna how can that happen? Daddy is no more baya raye wajanwa zashi to"kallon maras hankali tayi masa tare da cewa"wannan wacce lukutar magana ce,waye baya rayen? Idanunsa ne suka sauya kala bakinsa na rawa yace "Mamana niɗin marayane mara gata i lost everthing luv,happiness,care,everthing Daddy,Mamy,Lili babu ko ɗaya cikinsu duk an kashesu"cikin firgici da fitar hayyaci ta ɗaga hannunta tare da sharara masa wasu firgitattun mari,tsabar girman mari saida yay maya lokacin hawayen idanunsa suka sami damar zubuwa daga cikin idanunsa,durƙushewa yay gaban Mama tare da kifa kasan in btw her laps ya shiga zauke numfashi mai zafin gaske jikinsa duka rawa yake.
*** ***
_Maiduguri road_
Horn suka danna da gudu mai gadi ya leƙo ganin sabuwar mota bata gidan ba ya sashi leƙowa tare da faɗin.
"yallaɓai wajanwa kake nema?" kallon Lili Sufyan yay kanta ta leƙo dashi waje tace"Anty Najma fa?"jim ya ɗanyi kafin yace"ayya ai ƙaramin mai gida Faisal ne babu lpa suna Emergency na Aminu kano".
Faɗuwar gabanta ce ta ƙaru lokaci gudu tsoro ya kamata tare da tunanin abinda ya sami farin cikin nata“Astagafirullah”shine abinda tayi saurin faɗa sanin cewa yanzu ya haramta gareta tunda yana auren ƴar uwarta,hawaya ne ya ɓalle mata ta shiga zubar dashi,Sufyan ne ya leƙa yace"mungode Baba"yana faɗin haka yaywa motar key tare dayin ribers ya jata da gudu tare da harbata kan titi.
Lokaci kaɗan suka isa asibitin har lokacin kuka take wanda ita kanta bata san na mene ba,wayarsa ya ɗauka tare da latsata yana sauraran kukanta,ganin bashi da niyar fituwa yasa tayi saurin buɗe ƙofar kafin ta buɗe ya danna mata pin,kallonsa tayi da alamun tambaya"ki tsaya ki gama kukan ko?"share hawayen tayi cikin rawar muryar tace"pls get in"jinjina kansa yay kafin ya buɗe ya fitu itama ta fita, a tare suka jera suka nufi cikin Emergency ɗin.
Ɓangaren Faisal kam tunda ya fita bai ƙara shiguwa ba sai cikin dare,yana shiga Faisal na buɗe idanunsa tare da zubasu a kan mahaifin nata,haka ya tabbatarwa da Papi tambayarsa yake game da Lili,zana yay tare da shafa kansa yace.
"Kayi ta wakkali Faisal cikar imanin mutum shine yadda da ƙaddara,ka yarda Lubna bata raye kuma kowa na haka ne kaci gaba dayi mata addu'a itane abinda take buƙata indai ka yarda kana sonta Rabbi yasfika Allah ya baka lpa ka rungomi matarka ka ɗauki hakan matsayin ƙaddararka"murmushi kawai Faisal yay domin yasan babu wanda zai yarda dashi a kan Lilinsa bata mutu ba,bai taɓa son Najma ba haka kuma bai taɓa tsanarta ba hasalima tausayinta ya keji ganin bata da kowa amma ta zaɓi baƙanta rayuwarsa da kuma duniyarsa,ta zabi ha ɗashi da mahaifiyarsa har tayi mummunan Lafazi a kansa meye laifinsa kodan ya nuna ƙauna da soyayya wa ƙanwata kodan zuciyarsa taƙi yarda ta amsheta matsayin mata,yayi hakanne sbd bai son ya tafi yabarta da marayun yara dan yana tabbacin bazai taɓa tashi ba.
Washe gari da safe Najma ta karasu asibitin tana tafe tana buɗa ƙafa dan sosai tasha wahala wajan Faisal ita yanzu haka maza tsoransu take,wajansa ta ƙarasu tare dajan kujera ta zauna lokacin ya samu bacci zuba masa ido tayi ganin ya ƙara mahaukacin kyau tare dayin wani fari fiye da jiya fuskarsa ta faɗaɗa ta yalwataccen murmushi,wata wutar sonsa ce ta ƙara tasu mata tana jin a duniya tafi kowa dacen mijin ɓangare guda kuma tana jin tsanar Lili fiyeda da,domin ita ta haddasa komai a kanta yaƙi amsarta a matsayin mata a kanta ta shiga damuwa.
Ta daɗe a zaune har bacci ya ɗauketa a jikinsa,wata ƙarar na'oura ce ta farkar da ita daga bacci cikin tashin hankali ta miƙe ganin gudan jini na fita ta hancinsa da bakinsa hannunsa dafe da ƙirjinsa,jikinsa gaba ɗaya rawa yake,da gudu ta tayi waje domin kiran Dr tana ƙoƙarin fita suna ƙoƙarin shiguwa Ammi ce sai Papi sai kuma wani ƙyaƙƙyawam namiji a bayan kafin wata mai hijab ta biyo bayansa,cikin farin ciki Papi yac"indai Lubna ce damuwark daga yanzun ta kau,domin ga muradin ranka a gabanka"
A hankali ya ware idanunsa tare da zare oxcygen dake bakinsa muryarsa na creating yace "Bby..boo"da gudu ta ƙarasu tare da faɗawa jikinsa ta saki wani mahaukacin kuka mai tsuma zuciya,kanta ya shiga shafawa tare da ɗura bakinsa saitin kunnan ta yace "i luv u more most"ya manna mata lafiyayyen kiss a wuyanta.
Kallamar shadar da taji yana faɗa ne yasa tayi saurin ɗago kanta wani ƙawataccen murmushi ya sakar mata fuskarsa ta cika da fara'a kafin yaja idanunsa ya rufe tare da sakin hannunta,gaba ɗaya na'ourorin da suke cikin room ɗin suka shiga ƙara a lokaci ɗaya,kaita shiga girgizawa tare ƙanƙameshi tan faɗin "no pls no Faisal why zakai bacci a lokacin da nake muradin ganinka da son jin muryarka dan Allah ka tashi"
Likitoci ne suka shigu da gudu tare dayin kansa suna zuwa suka shiga dubashi tare da girgiza kai wani Dr yace "saidai kuyi hqr Ubangijin daya samar dashi ya amshi abinsa kum... Ihun da Lili tayi shine ya dakatar dashi daga faɗin abinda yay niya kanta tayo ta shiga dukansa tare da faɗin"wlh ƙarya kake bai mutu kuma bazai taɓa mutuwa" cikin saurin Sufyan yazu ya ƙwace daga jikin likitan tare da mannata a jikinsa ya shiga jijjigata"dan Allah Sufyan kace bai mutu ubangiji kasa mafarki nake ba gsky ba"tana faɗin hakan tayi kan Faisal lokacin har an lullubesa da farin yadi,kafin ta ƙarasa taji saukar wani ƙarfe a tsakiyar kanta ƙara ta saki tare da juyawa da hannu ta shiga nuna Najma wacce take tsaye hannunta ɗauketa da wani ƙarfe cikin kuka Najma tace"wlh kema saikin bishi shegiya mayya aida lafiya muke zaune dashi Wlh nice aljalinki kamar yadda kika sani kuka nayi alƙawarin ganin bayanki"ƙara ɗaga ƙarfenta tayi zata ƙwaɗa mata a kai Sufyan yay saurin riƙewa tare da sauke mata wasu lafiyayyen mari,zafi da raɗaɗin ƙarfin dukan da taji ya sata yin baya lokacin jini ya gama wanke mata fuska nanta sulale ta faɗa jikin gawar Faisal babu numfashi..
_Wlh wlh wlh Allah kenan indai yau mutum sama da ashirin ba suyimin comments ba,kuma dukkan wanda yasan yana karantawa baiyi comments babu shakka zai koma na kuɗi duk nayi alƙwarin free ne amma naga baku da halin kai ina ƙoƙarin na ɗauke kai ni ban fiya kace nace balabu ɗaya nake faɗa,wlh duk wanda yake karantawa yau bai comment ba ya tabbatar kuɗinsa zai kuka domin ko biyar na rabaka da ita nadai rabaka da itan🤷🏻♀️shawara yana wajanku_.
F@y@l
_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*
*24-25*
*_Wattpad_*
https://my.w.tt/jN2GLY5RKcb or Nimcyluv
*_Telegram_*
https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ
يايهاالذين ءامنوا اذكروا الله ذكرا كثيرا، وسبحوه بكرة وآصيلا.
......Cikin tashin hankali Sufyan yay kanta tare da ɓanɓareta daga jikin gawar Faisal,ɗaukanta yay tare da fitar da ita daga cikin room ɗin gaba ɗaya.
Tashin hankali wanda ba'a saka masa rana tabbas ko wanne bawan Allah saiya ɗanɗani cin mutuwa da raɗaɗinta haka da zafinta,kuma dukkan mai rai mamacine,Allah baya barin wani dan wani yaji daɗi a ko'in kake Ubangiji na iya ɗaukan ranka a duk lokacin daya gadama,Allah daya halicce mutum shike da ikon karɓan ransa saida wani yay sanadi.
Papi duk dauriyarsa saida ya zubar da hawaye,a hakan ba ƙaramin ta waƙƙali yay ba domin Faisal yay mutuwa mai kyau mutuwar dako wanne bawa zaiso yay irinta,Ammi kuka tayi harda suma yayinda tsanar Lili ta dira acikin zuciyarta lkc guda tsanarta mai girma ta shiga ko wacce ƙofa ta jikinta,ta tabbatar da baƙin cikin Lilin ya mutu aida bai mutu ba saida tazu,da ƙyar aka samu kan Ammi,Najma kusan haukacewa tayi saida aka yi mata allurar bacci ta wajan 24hours,haka aka ɗauki gawar Faisal aka saka a ambulance suka nufi gida da ita,lokacin mutane sun cika cikin gaggawa aka shiga da Faisal tare dayi masa wankan gawa aka shirya yashi cikin lafiyayyen kayansa kaya na har abada kayan da ya zamewa ko dolen sashi a ranar da zaiyi kwanan ƙarshe a nan gidan duniya,ana gama shiryasa akai waje da gawarsa cikin makara.
Sufyan na fita da Lili babu inda ya tsaya da ita sai wani specail room,aka shiga dubata tare ɗinke inda Najma taji mata ciwo,ganin ciwonta na Asma na shirin tashi yasa sukayi mata allura tare da ɗaura mata drip,ganinta samu baccine yasa Sufyan fita tare dayin harabar asibitin ya shiga motar ya nufi gidan da suka baru dan yana da tabbacin nanne gidan da akai rasuwar,tunda yake bai taɓa ganin mutuwa ido biyu wacce ta tsora tasa tare da ƙara masa ƙarfi imani ba irin mutuwar Faisal,sosai yake gudu harya isa unguwar Maiduguri road yana zuwa ana gama sallatarsa mutum biyu ne suka shiga motarsa cikin saurin suka rufawa motar gawar lokaci kaɗan suka isa maƙabartar,lkcn angama haƙa kabarinsa babba da uwar ɗaki,bisimillah akai tare da sakashi a ciki idan nan bai cika ba sai ɗebu ƙasa tare da dannawa cikin kabarin,daga ƙarshe aka ɓallo ƙatun reshan bishiya aka ciccika a cikin kamarin ana gamawa aka shiga zuba ƙasa saida aka gama sannan aka shiga yi masa addu'a tare da kafa allo aka rubuta.
_Rest in peace_
_Faisal khalil cibaɗo_
_wed/jan/13_
Ana gamawa kuwa ya shiga mota aka barshi shi ɗaya daga shi sai halinsa,mutuwar Faisal ba ƙaramin girgiza Papi taima amma yay ta wakkali tare da rungumar ƙaddararsa,kuwa ya ganshi sai yaga ramar da yay ya faɗa lkc guda idanunsa yay zuru-zuru,ta'aziya Sufyan yay masa tare da bashi ƙaramin card ɗinsa mai ɗauke da adress haɗi da number waya sannan yay masu sallama a kan zaije ya ɗauki Lili su tafi Abuja kar dare yayi.
Sufyan na shiga mota yay asibiti da gudu bai daɗe ba ya isa cikin asibitin,yana shiga daret babu inda ya nufa sai room ɗin da take ƙwance zuciyar cike da tsanar yayarta ta,ƙwance take flat tana sauke numfashi a hankali kana kallan fuskarta kasan bata cikin nutsuwarta musamman idan ka lura da yadda ta haɗe fuskar hawaye yay mata fata-fata a saman innocent face ɗinta,zama yay tare da kama hannunta ya ɗan murza ka ɗan tare da ranƙwafawa ya sakar mata sumba a gefen lips ɗinta cikin sanyin muryar yace.
"Lovely bbyn am sorry bansan zaki tarar da ƙatuwar tashin hankalin nan ba daman kawo ki ba pls for give me ban ƙarawa..numfashi yaja tare da shafa gefen fuskarta yana mai jin wani iri a jiki tabbas da ace matarsa a yanzu babu abinda zai hanashi jin ɗumin jikinta,lumshe ido yay yana maijin wani abu a zuciyarsa mai kama da fargaba,ƙara kallonta yay yace"Lovely bby ina kishinki sosai da wannan mamacin amma bana fushi dashi domin shiɗin abin tausayi ne amma banjin zan iya hqr dake komai wahala komai daɗi dama yau igiyar aure ta shiga tsakanina dake da yau saikin tabbatar da zallar ƙaunar da nake maki ruhi da kuma gangar jikina,amma babu damuwa kamar yadda na jure sati huɗu haka zan jure sati ɗayan ban dama bikin waccan sakalya mai zaisa subar gari".
Haka dai yayta surutu shi ɗaya kafin ya miƙe ya zare drip ɗin hannun ya saɓata a shoulder ɗinsa yay waje,yana zuwa ya buɗe side ɗin mai zaman banza tare da ƙwantar da kujerar ya ƙwantar da ita akai ya sakar mata wani lafiyayyar murmushi"yi baccinki bbyn zuciyanki na buƙatar hutu akwai lokacin da shayar dake zallar soyayyar zan maki madarar soyayyar da babu wani namiji dazai iya baki ita"gefen wuyanta ya shafa tare da rufe ƙofar ya koma side ɗin drever yaywa motar key tare dayin ribers ya figeta da wani irin speed yay waje yabar cikin asibiti yana fita ya harba motar kan titi sai Abuja.
Basu isa Abuja ba sai dab da magrif ganin sun ƙarasu area ɗinsu ya shiga dreving a hankali harya kawo babban get ɗin gidan wani ƙyaƙƙyawan horn yay da sauri Getman yazu ya wangale masa get ɗin,hancin motar ya cilla cikin harabar gidan yana gama parking a parking space ya fitu daga cikin motar tare da ɗaukanta ya nufi cikin gida da sauri jin yadda jikinta ta ɗauki zafi.
Da mamaki Momma ta tsaya tana kallonsa bakinta ɗauke da tambaya amma ta share,bedroom ya nufa tare da ƙwantar da ita har ya saka hannu zai cire hijab ɗin jikinta sai kuma ya fasa yaja mata duvet tare da ƙara gudun A.c'n yay waje.
A nan parlon ya tarar da Momma ita da Yusrah sai haɗa kayan tafiya suke,daman Alhaji baya gari sai ana ƙwana ɗaya ɗaurin aure zai dawo,zama yay kusan Momma tare da ɗura kansa a kafaɗarta ba tare data kallesa ba tace
"Meya faru?" kallonta yay da idanunsa da suka sauya kala sam baison tafiyar nan gani yake kamar akwai abinda zai faru,nan ya shiga labarta mata abinda ya faru,shuru tayi na wani lokaci sai kuma tace.
"Allah sarki wannan bawan Allah tabbas naji wannan mutuwar Allah ya jiƙansa,daman aƙwai ƴan uwa masu irin wannan halin jin ƴar nan inda ta tunda murnar ganin ƴar uwarta amma ji abinda ta aikata mata dole a kira Dr yadu bata before mu huce gobe"
Jinjina kai kawai Sufyan yayi kafin ya miƙe tare da shigewa bedroom ɗinsa,a daren aka kira Dr yadu bata inda ya tabbatar masu babu matsala amma sai zuciya gobe zata farka sbd tsoro da firgicin data shiga,sallama yay masu sannan ya huce abinsa.
Yana fita Sufyan ya kalli Momma yace"amma mai yasa dole sai munyi tafiyar nan ina ganin a hqr kawai ayi auren a nan a bani matana"
Harara ta watsa masa kafin tace"idan bakka so babu dole kana iya zama"tana faɗin hakan ta huce flat ɗinta,ya daɗe yana kallon Lili kafin ya sakar mata sumba tare da tsotsar laɓɓanta ya fice da sauri,flat ɗinsa ya huce shima yana shiga ya faɗa saman bed ɗinsa tare da lumshe ido hannu yasa ya shiga danna mararsa tare da shafawa jin yadda ta kumbura tare dayi masa zafi ya daɗe yana juyi kafin ciwon ya lafa masa ya shiga sauke numfashi a haka bacci ya ɗaukesa.
*** ***
A can Kano kuma bayan tafiyar Sufyan manyan mutane ne suka shiga zuwa wajan Papi ta'aziyya kowa da ƙyaƙƙyawar addu'a a bakinsa,babu abinda za'ace sai halinsa na gari ya bishi domin duk wanda yasan Faisal ansan mutumin ƙwarai ne hankali nutsuwa biyayya uwa uba riƙo da addininsa.
Haka akai ta karɓar gaisuwa har dare yay Papi ya koma cikin gida,yana zuwa yay flat ɗin Ammi amma taƙi buɗewa yay yin duniya taƙi buɗe,rabuwa yay da ita sbd yasan condition ɗin da take ciki a yanzu babbar rigarsa ya cire tare da ƙwanciya akan duguwar sofa cikinsa ya shafa jin yana masa zafi da murɗawa sai lokacin rabosa da abinci tun jiya da safe shima tea kawai ya iya sha,tunanin Lili ne ya faɗu masa a zahirin gsky yana tausayinta domin baisan halin da zata shiga ba,batun Najma kam bai fiya damunsa sbd ba ƙaramin haushi ta bashi ba duk da yana jin tausayinta a cikin ransa domin baisan a wanne hali zata farka ba,a haka bacci ya ɗaukesa.
Washe gari tun shida na safe Anty Kausar ta sauka sbd tun jiya jirginta ya tasu wajan baƙwai kuma Anty billy ta shigo tun daga waje ta fasa wani kuka mai rikitarwa suka ƙanƙame juna ita ƴar uwarta Anty kausar sosai suke kuka kamar ransu zai fita,da ƙyar Papi ya rarrashesu domin har sukai shuru kallonsu yay yace.
"ya kamata kuje wajan matarsa can asibitin"Anty Kausar ce ta turo baki tare da faɗin.
"Allah Papi ban zuwa sam ba taimin ba,ba zance ita ta kashemin ɗan uwa ba,amma tunda ya aureta Faisal baya da sukuni bashi da fara'a kullum cikin ƙunci da baƙin ciki yake,ko vedio call muke haka zai sakarmin kuka yin duniya amma bazai faɗan damuwar ba,Papi idan ba ita ba wake da alhaƙin saka Faisal damuwa"
Ta ƙarasa faɗa tana faɗawa jikin Papi tare da sakin kuka dan gani dake tafi kowa jin mutuwar Faisal ɗin.
Papi ya gama sanin ƴar tasa daka fiya dan haka yace Anty Billy ta shirya ta tafi babu musu ta ɗauki key