Showing 30001 words to 33000 words out of 79519 words
baki tayi tare faɗin "Mama alrdy night fa wazai ganni yanzu?" girgiza kai kawai Mama tayi tare faɗin "yaro man kaza be carefull dai"Afnerh ce ta ƙarasu hawa wajan hannunta ɗauke da basket ɗin abincin a tare sukai hugging ɗin Mamansu tare da sakar mata peak a ko wanne kumatunta shafa kansu tare cike da soyayya tace "Allah yay maku albarka"da "Ameen" suka amsa tare da ficewa daga gidan.
Da kallo ta bisu tana jin wani zafi da kuma raɗaɗi na damun zuciyarta tana jin har abada wannan baƙin cikin na zuciyarta bazai taɓa guguwa ba dashi zata mutu,ɗauke kai tayi jin idanunta na cicciko da hawaye.
Suna tafe suna shirya cikin tafiyarsu mai nutsuwa a haka har suka ƙarasu Get ɗin gidan cikin ladabi Fannerh ta gaisar damai gadi yayinda Afnerh ta ɗauke kanta tare da shige cikin gidan tana gaf da shiga ɗan ƙaramin parlour'n Fannerh ta cimmata tsaki Afnerh tayi tare da faɗin"talkative"girgiza kai kawai tayi kana suka shiga parlon bakinsu ɗauke da sallama.
Tsaye suka ganshi gaban t.v yana ƙoƙarin kunnawa shuru yay masu bayan ya amsa sallamar tasu cikin ransa.
Sanye yake cikin baƙin wando 3 guater ko riga babu hakan ya bawa ƙyaƙƙyawar surarsa bayyana skin ɗinsa Afnerh tabi da ido ganin ko'ina yalwataccen gashi ne yay kwance luff cikin white sharning skin ɗinsa ga wani sahihiyin ƙamshi dake fita a jikinsa kamar daga zama suka ji saukar daddaɗar muryarsa "stop looking"shine kawai abinda ya faɗa lokacin daya gama kunna t.v
Afnerh daskarewa tayi a wajan tare da mamakin mamallakin muryar domin wajan mutum guda ta taɓa jinta cikinsu babu wanda ya samu jarumtar ce masa ƙala duk da cewa basu ga fuskarsa ba amma sosai yay masu ƙwarjini.
A hankali ya juyo tare da sauke ganinsa a kansu ƙarar da Afnerh ta ƙwala ya sashi saurin runtsa idanunsa tare da toshe kunnuwansa.
Gaba ɗaya jikin tane ya shiga rawa sabida bayyanar ƙyaƙƙyawar fuskarsa wani irin shock ne ya kamata tare da bugawar zuciya hannunta ta ɗaga ta shiga nunasa ganin hakan yasa Fannerh tayi saurin riƙeta tare da jijjita"Afnerh" Afnerh" Afnerh" bakinta ne ya shiga mutsi a ƙoƙarinta nasun furta wani abu amma ta gagara hakan sabida numfashinta daya ɗauke ta saki basket ɗin hannunta tare da faɗawa jikin Fannerh babu numfashi.
*DAN GIRMAN ALLAH DA ANNABI IDAN KIN KARANTA KINJI DAƊI KIYI SHARE PLS*
F@y@l
_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*
*18-19*
*_Wattpad_*
nimcyluv
Before we ask
God for anything we must first thank him for everything 🙌🏻🙇🏻♀️
*Dedicated to MaimunaAbdullahi* still waiting for ur hurt coffee I luv u my jerry🥰🌹
Not edited.
.....Cikin tsoro da firgici haɗi da ƙaraji Fannerh ta shiga girgiza Afnerh tare za kiran sunanta "Afnerh pls wake up pls Hadnerh,ganin Afnerh ko mutsi ba tayi ne ya sashi taɓe baki tare da juya zai shige cikin bedroom ɗinsa sai kuma yaga rashin da cewar hakan ko babu komai baƙin Fauwaz ne kuma Fauwaz ya zama jininsa bazai taɓa iya wulaƙanta jinin abokin nasa ba.
Bak damu da yadda surar jikinsa da take a buɗe ba a hankali ya taka tare da ƙara sawa wajansu cikin muryarsa wacce bata fita sosai sabida tsaɓar rashin son maganarsa,lumshe gajiyayyun idanunsa yay tare cije lips ɗinsa ya ƙara mutsa bakinsa tare da ware laɓɓansa yace.
"ke Aljanu gareta halan?" baƙin ciki ne ya kama Fannerh har bata san lokacin data wurga masa wata uwar harara ba tare da faɗin"what Aljanu fa?Allah yay mata tsari dasu"ƙara taɓe fuska yay irin ko'a jikinsa ɗinan "ok farfaɗiya take kenan?"ya ƙara jefa mata wata tambayar cikin sauri Fannerh ta ɗago kanta tare da zuba masa baki ta saki ganin gama ɗaya ya maida hankalinsa kan T.V tamkar bashi yay maganar ba.
Ganin ta ɗauke daga garesa ne yasa ta juya tare zuwa wajan freezer tare da saka hannu ya ɗauko gorar ruwa mai sanyin gaske cikin gajiyawa da kukan da Fannerh take ya lumshe idanunsa haɗi da saka hannu ya shafi ƙwantaccen gashin da yay luff a ƙirjinsa a haka ya ƙarasa wajan da suke,tsaki yaka cikin lion sound voice yace "oyya gefe"yana faɗin hakan ya sunkuya tare da riƙe gefen rigar Afnerh ya jawota haɗi da jinginata da jikin sofar dake parlon,murfin gorar ruwan dake hannunsa ya ɓalle kai tsaye ya sheƙa mata ruwan a jikinta.
Wata wawiyar ajjiyar zuciya ta sauke tare da ƙanƙame jikinta jin wani a zababban sanyi daya ratsa jikinta lokaci guda a galabaici ta shiga faɗin.
"shine wallahi shine tabbashi shine my heart dream shine mafarkin zuciyata a kullum dashi nake ƙwana nake dashi bana da burin daya huce na kanga a gaske,a kansa na guji dukkan waƴanda suka ce suna sona wallahi kaine eyes ball ɗinka sune suka ƙara tabbatarmin da haka,fatana da kuma muradina haɗi da cikar farin cikin zuciyata shine Allah ya bayyana min kai ubangiji kada ya ɗauki raina sai naga wanda zuciyata dake mafarki a kansa sai gashi na ganka when all is gone a lokacin da komai ya ƙare yanzu kaine duniyata kaine jindaɗi na,kaine muradina,kai farin cikina,kaine mahaɗin rayuwata,kaine bangwan da zan jingina naji daɗi a raina,dan Allah ka taimaki zuciyar data mace a kanka tun kafin tasan waye kai"ta ƙare zancen lokacin da take fashewa da wani irin razanannan kuka mai taɓa zuciya.
Lallai "SO" masifa ne a duk halin da mutum yake ciki baya hana zuciyarsa bayyana abinda yake so da kuma muradin kasan cewa dashi koda ace bazai samu wannan abunda ƙaddara ta haɗa Afnerh da Fahad duk a cikin mafarki wanda a kullum tana tunanin mafarkinta gaskiya ne dalilin hakan ta sauya sunanta daga Afnerh zuwa "Hadnerh" suna mafi soyuwa a gareta.
Lallai marfin Afnerh ya zamantu gaskiya domin gashi ubangiji ya haɗata da mafarkin zuciyarta ko hakan na nufi wani sabon shafin ƙaddarar wani daga cikinsu?.
Ganin ta fita a hankalinta kuma ya gama tabbatar da abinda take faɗa gaskiya wanda tasa ƙwaƙwalwarsa ta tafi wani dugun tunani dasun tunasar dashi wani alƙawari da yay a baya wannan wanne alƙwari ne?wa yaywa shi?wannan sune tambayoyin da suke ƙasan zuciyarsa amma babu amsa.
Cikin sanyin jiki tare da kasala ha saka tattausan hannunsa tare da ɗurawa saman fuskarta a sanyaye ya shiga goge mata hawayen dake zuba cikin idanunta.
Haɓarta ya ɗago tare da zubawa oval face ɗinta idanu kafin ya taɓe baki tare da saurin saki fuskarta,kamar bazai magana ba sai kuma yace.
"فاذكروني اذكر كم واشكرولي ولآ تكفرون. (آلبقرة ١٥٢)".
"ku ammabace ni zan ambace ku,ku gode mini kada ku butulce min (baƙara aya ta 152).
Numfashi ya fitar tare da ɗaure fuska ganin kallon da take masa,lumshe ido yay sosai maganar da yay tayi masa kafin ƙara saki numfashi tare cije lips kana ya ware laɓɓansa tare da faɗin.
"mai yasa kika zama mai butulci wa Ubangiji?ya baki komai na rayuwa sai ɗan wani buri dake banne a zuciyarki amma ki kasa yiwa ubangiji tasbihi da kuma neman sauƙi daga wajansa,nayi tunanin kina da hankali ashe sakalyace?kulna ƙarajin kuka domin baya maganin damuwa akwai dubban mutanan da suka fiki shiga damuwa da kuma ƙuncin rayuwa su kuma suce me?idan mutum bai gode ni'imar Ubangiji ba amma ya gode azabarsa,ki zama mai ta wakkali kuma me yarda da ƙaddara ki ɗauki hakan matsayin ƙaddararki da ubangiji ya jarabceki da ita danya gwada imaninki kinji ko?
Ajjiyar zuciya ta shiga saukewa tare da zure jikinta waje guda tare kafa masa idanunta tana ji dama ta dauwama a haka tana kallon baiwar zati da kuma surar da ubangiji yay masa.
Raguwar ruwan daya zuba mata ya kafa a bakinsa ya shiga ƙwanƙwaɗa saida ya shanye tas sannan ya cire gorar ruwan daga bakinsa.
A fili ya saki ajjiyar zuciya sosai ruwan yay masa daɗi maƙoshi tare da magana a zuci"Rabbi ka shayar damu ruwan alkausara".
Cikin nutsuwa ya juya tare da zama a kan duguwar sofa ganin gaba ɗaya ya gaji ga wani bacci daya keji ne ya sashi ware idonsa tare da mannasu a kan Fannerh wacce ta zubawa Afnerh ido domin sosai ta kejin tausayin ƴar uwarta ta, saukar muryarsa data jine ya sata ɗago kai tare da zuba masa ido dan baza taɓa iya cewa taji abinda yake faɗa ba.
Ya tsuna fuska yay tare da ɗauke kai ya maida kallonsa wa Afnerh wace take zauna ko mutsi ba tayi sai ajjiyar zuciya take saukewa a kai²,Tausayin tane ya kamashi cikin taushasshiyar murya yace.
"mai kuka aban abinci ina jin yunwa"cikin sauri Afnerh ta miƙe jikinta har rawa yake dan ba tayi tunanin hakan a wajansa ba,kallo ɗaya tayi masa ta fahimci shiɗin mutum ne wanda bai damu da magana ba sannan shiɗin miskiline uwa uba girman kai amma sam bata damu da hakan ba indai zai nuna mata ƙauna zai zauna da ita zata iya jure duk wata halayya tashi.
Basket ɗin abincin ta ɗauka tare da ƙara sawa inda yake zauna tana zuwa ta zauna ƙasan sofar tare da ɗaukan plate ta buɗe wata wamer nan ƙamshin abincin ya daki hancinsa cikin saurin ya lumshe idanunsa wanda hakan ya zame masa ɗabi'a.
Zallar chips ɗin tare da ɗaukan wani glass cup ta siyaya masa fruit salad ɗin,cikin rawar murya tace"gashi"yi yayi kamar baiji abinda ta faɗa domin ya fahimci itama bata son magana sosai.
Turo baki tayi kamar zata fasa ihu tace"the food is ready"ware manyan dara-daran idanunsa ba tare daya kalleta ba ya zamu da ƙafarsa ƙasan sofar tare da sakkowa ya zauna a kan capert bai damu da zaman da yay kusa da ita ba,dan ko ajikinsa impact bai ɗauketa wata babbar macen dazai damu kansa danya zauna musanta halima shi mata duk kallon maza yake babu wata macen da zaiji wani feelings a kanta.
Zamansa kusa da ita yasa taji wani mugun shock ya kamata take wutar sonsa da ƙaunarsa ta ƙara huruwa cikin zuciyarta,tabbas ya cika namijin da dukkan wata ƴar mace ta ganshi za taji ƙaunarsa a lokaci guda,ware ƙofar hancinta tayi tana ƙara shaƙar ƙamshin dake fita daga jikinsa a sanyaye tayi magana yadda shine kawai zai iya jin abinda ta faɗa banda Fannerh da take tsaye sai kuma Fauwaz wanda zuwansa gidan kenan.
"kai ɗin gwarzu ne"
Girgiza kai kawai yay tare dayin bisimillah ya saka zara-zaran ya tsunsa tare da fara cin abincin,Fannerh tunu taja basket ta zubawa habibinta abinci sunayi suna shira.
Fahad bai wani ci abincin da yawa ba ya ture ko fruit salad ɗin bai sha ba ya miƙe tare da shigewa cikin toilet ya ɗauki lokacin kafin ya fitu suna zaune ya fitu sanye da bathrobe jikinsa na ɗigar da ruwa a haka ya ƙarasu wajansu tare da kallo Fauwaz taɓe baki yay shi a dole soyayya yake cikin ransa"ƙaddararka soyayya da underage"a fili kuma yace "boddy goodnight"ɗaga kai Fauwaz yay tare da murmushi kafin yace"Na ɗauka zakuyi hira da Afnerh"kallonsa yay da alamar tambaya sai kuma yace"wani abune haka?"dariya Fauwaz yay tare da kallon Afnerh wacce take turo baki gaba tare da fidda wasu sabbin hawayen ɗauke yay tare da faɗin"eh wata abace gata nan a bayanka ai"tsaki Fahad yaja dan ardy yasan wace Afnerh ɗin tun ɗazu yaji sister ɗinta na kiran sunanta,baice masa komai ba ya juya zai shige bedroom ɗinsa tayi saurin miƙewa tare da sakin kuka danji take zuciyarta kamar zata fashe,waro manyan idanunsa yay ganin kuka baya yi mata wani ƙawataccen murmushi yay lokacin daya tuna da Lili ko magana ce bata gamsheta ba yanzu zata saka maka kuka harda birgima bare kuma faɗa cije lips ɗinsa yay tare da ware laɓɓansa a fili yace"i'm still waiting for u my sunshine bby"jin haka yasa Afnerj da katawa da kukanta tare da zuba masa idanu ta gefenta ya huce ko ƙara kallonta baiyi ba.
Sun ɗan jima a gidan kafin su ɗauki basket ɗin tare da yiwa Fauwaz sallama suka koma gida.
Da kuka Afnerh ta shiga gidan tana zuwa ta faɗa jikin Mama tare da fashewa da kukan cikin kiɗima ta fara tambayar abinda ya faru,cike da nutsuwa Fannerh ta shiga gawa Mama komai har rashin ko in kula daya nunawa Afnerh ɗin.
Da ƙyar Mama ta rarrashi a Afnerh tare dayi mata alƙawarin ita da kant zata amsar mata soyayyarsa.
*** ***
Wajan satin Najma uku kenan gidansu Faisal dukkan wani jin daɗi Ammi na bata shi,amma batun farin ciki wajan Faisal babu shi kullum rashin kulawarsa gareta ƙara yawa yake.
Misalin 7 na dare shiguwarsa daga sallah kenan ya zauna a babban parlon gidan tare da kunna karatun Sudais cikin suratul Maryam,sosai karatun yake masa daɗi kuka yake sashi nutsuwa domin baƙin ciki da damuwarsa suna nan kwance ƙasan zuciyarsa saima abinda ya ƙaru.
Lallai Ƙur'ani haske ne aduk zuciyar data ƙawatu da son karanta shi kuma dukkan wanda ya dogarar da alƙur'ani bazai taɓa taɓewa ba.
Ƙamshin turaranta daya daki hancinsa shine kawai ya tabbatar masa data ƙarasu parlon ganin tare suke da Ammi ne ya sashi sakin fuskarsa tare da zubawa abin idanu gani yake kamar yau ya fara ganinta idanunsa da suka cicciko da hawayene yasa yay saurin ɗauke kai tare da faɗin"barka da dare my luv"cikin so da ƙaunar ɗan nata ta zauna gefensa tare da shafa sumar kansa tace"yawwa yaya aiki?"..."mungode Allah" shine kawai abinda yace..ɗaga kai Ammi tayi tare da faɗin Najma zauna ma..ruwan hawayen data gani kan fuskar Najama shine ya hanata ƙarasa abinda tayi niya cikin kulawa tace"lafiyanki lau?"wasu hawayenne suka ɓalle mata ta shiga girgiza kanta kafin ta durƙushe gaban Ammin tace"Ina son komawa gidanmu domin na gaji da zama da Faisal,banyi iskanci tun ina budurwa ba haka bazanyi ina matar aure ba,amma yasan da cewa nima mutumce kamar kowa kuma dole akwai haƙƙina daya rataya a wuyansa,bansan mai nayi masa amma baison haɗa gado dani😳hakan kuma illah ce wa rayuwata koda ace bashi da lafiya ya kamata ace ya faɗamin tunda niɗin matarsace bawai zaman dadiro muke dashi ba".
Ai maganarta tamkar saukan ruwan dalma haka yake jinsu cikin zuciyarsa baƙin ciki takaici ladama na aurenta babu wanda baiyi ba,hakan kuma ya tabbatar masa bata da kunya ko kaɗan sannan ita ɗin ba matar sirri bace,cikin ɓacin rai Ammi ta kalli Faisal wanda idanunsa yake a rufe ruf tamkar maiyin bacci tace.
"ka tabbatarmin niɗin ban isa da kai ba kuma baka ɗauki maganata da muhimmanci ba,ka sani indai ni nayi cikinka nayi naƙudarka kuma na shayar dakai ruwan nono a yau basai gobe ba nakeson ka bawa Najma dukkan wani haƙƙinta da yake kanka idan kuma ba haka ba wallahi Faisal zan sallamawa duniya kai badan kaga mahaifinka baya nan ba kakemin wannan abun to kaje dani dakai za'aga wanda zaici riba".
Idanunsa ne yay jajur tamkar gauta sosai kalaman Ammi suka daki ƙawon zuciyarsa meyasa Ammi ba zatai masa uzuri ba?mai yasa ba zata fahimci zafi da raɗaɗin abinda yake damunsa ba? Mai yasa ba zata fahimci abinda zuciyarsa da gangar jikinsa suke muradi ba? Runtsa idanunsa yay da ƙarfi tare da miƙewa cikin zafin rai ya kalli Ammi yace
"zanyi dukkan abinda kikeso koda bakan zai baƙanta raina,zanyi abinda kikeso Ammi koda zuciyata zata buga,zanyi abinda kikeso koda hakan zai zama sanadiyar rasa raiana,tabbas inajin hakan shine ƙaddararta kuma shine silar rasa raina,zanbar duniyar kamar yadda Lubna da iyayenta suka bari inaji a raina I think my Lubna is calling me, I think it's time to go tabbas lokacina na zuwa wajan mahaliccina yay Ammi kuma insha Allah indai kece kike haifeni kika kula dani da yardar ubangiji bazan bar duniyar nan ba saina tabbatar maki da kalamanki zanyi tabbas zanyi abinda kikeso Ammi"
Yana faɗin hakan yasa hannu ya riƙe Najma tare da janta da sauri a haka suka ƙarasa flat ɗinsu,tsoro da fargaba gaba ɗaya sun cika zuciyar Najma babu kalaman da suma tsaya ma sai "tabbas zabar duniyar kamar yadda Lubna da iyayenta suka bari"me hakan ke nufi wace duniyar zai bari? Ina zaine'inane inda Lubnan da iyayenta suka tafi"tambayoyin da suke zuciyanta kenan amma babu wanda zata tambaya ƙara ta saki sabida cillata da yay kan gado kanta ya daki fuskar bed ɗin a zafafe ya cire rigar jikinsa tare da long jeans ɗin dake jikinsa ya rage daga shi sai boxer cikin saurin ya faɗa kan gadon,babu ɓata lokaci ya zare zanin dake jikinta babu wani romance haka yay bisimillah tare dayin Addu'a ya shiga jikinta.
Zafin da raɗaɗin da ta jini yasa ta fasa wata mahaukaciyar ƙara ta shiga ya ƙushinsa tare dayi masa Allah ya isa ganin hakan bazai mata ba ta shiga cizonsa tare daya ƙushinsa.
Faisal bai rabu da ita ba saida yay mata lilis yay mata fata-fafa sannan ya zare jikinsa tare da sakin wani mahaukacin kuka kamar mace sunayen Allah ya shiga kira tare da salatin Annabi hannunsa dafe da saitin zuciyarsa wata bugawa da zuciyarsa tayine yasa shi faɗin "La'ilah ha'illahu Muhammadur Rasulillah" wani gudan jinine ya fitu ta hancinsa da bakinsa lumshe idanunsa yay yana mai ƙara jadadda sunayen Allah a zuciyarsa,dai² lokacin da Ammi ta buɗe ƙofa ta shigo yay dai² da lokacin daya saki wata shaƙuwa mai ƙarfi.
*Dan Allah dan Annabi kuyimin share dan Allah wlh bbu lokaci groups sunmin yawa sai kuna taimakawa🥰👏🏻luv u all*
Team Najma
Congratulations🤾🏻♀️💃🏻
_The secret issues_
*💖JUYAYI💖*
*20-21*
*WATTPAD*
Nimcyluv
*Telegram* https://t.me/joinchat/U6Qw0BuhKkqh5GZ8RadieQ _Masoyan *NIMCYLUV* ga mahajarmu na telegram yana da kyau kuyi join domin samun littafai cikin sauƙi da kuma amfanuwa da_
*programs* _ɗin daza muna gabatarwa kuma dukkan wani posting ɗina zai kuma can zai zama VIP group ɗina na musamman kuyi share zuwa wasu groups ɗin dan nuna ƙauna dan Allah._
......Jinin dake fita ta hancinsa da bakinsa ne yasa Ammi saurin fasa ƙara tare dayin kansa tana zuwa ta durƙushewa gabansa ta shiga girgizashi tare da kiran sunnansa "Faisal"