Showing 30001 words to 33000 words out of 44681 words
Chapter 11 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
ba za ki je ba?”
A'i ta ce “ ke wasa take yi miki fa,tuni ai na haɗa komatsaina na ƙulle a buhu” cike da jin daɗi na
ɗauki kofin kunun gyaɗana na fito falo na zauna,tv na kunna na saka horror film ina kallo ina
sha sam ban jin tsoron abubuwan da ake nunawa wani sa'in ma ji nake tamkar ƴan uwana ne.
Ƙamshin turarensa ne ya fara yi min maraba kafin shi ya shigo,na ɗaga kai ina kallonsa .Sanye
yake cikin kakin soja sun yi bala'in yi masa kyau sai dai ya aske gemunsa da sajensa,da sauri
na ajiye kofin hannuna ina turo baki ina kallonsa tuni kuwa ya fahimci dalili don tun ina yarinya
nake faɗa masa ina son saje,sannan Inna A'i ta taɓa faɗa min ranar farko da na fara ganin
Uncle Salem ya cire sage da gemu haka na yi ta kuka ina ɓata fuska sannan kuma na ƙi yarda
da shi .
Da sauri na miƙe zan bar wurin yayi saurin kamo tsintsiyar hannuna yana mai cewa “ oyaaa Naf
ɗin Uncle kar ki yi fushi zo ki shanyen kununki ki zo mu je na yi miki shopping ” jin ya ambaci
shopping yasa na juyo don na san duk cikin shirye-shiryen tafiyata ne.
Na sake turo baki a karo na biyu kafin na ce “amma shine ka aske ...” yayi wani murmushi mai
sauti yana cewa “ zai fito ai,kin ga kar ki yi fushi da Uncle ɗinki” sai ya zaunar da ni tare da
ɗaukar kofin ya ci gaba da bani kunun har na shanye kafin ya ce “ je ki canza kaya ki zo mu
wuce”
Da murna na koma ɗakina,sai dai ban canza kayan ba kawai dai na zumbulo dogon hijabi har
ƙasa.Ina fitowa Uncle Salem ya matso kusa da ni kafin ya ce “ ki canza kaya Naf ” da mamaki
na dube shi,ko ta ya aka yi ya gane ban canza ba.
Na marairaice fuska na ce “ Please mu tafi kar dare yayi” ya ɓata rai yana kallon ƙirjina,sai na
turo baki na koma ɗaki na je gaban madubi na yi tsaye ashe rabon a yi ne ya kai ni don kuwa
ina tsaka da tantance yadda saka hijabin bai ɓoye ainihin shap ɗin jikina ba sai na hango wata
farar mata tana saka min abubuwa a jaka,ta yi zaune daram kan gadona.Na waiga da sauri sai
na ga wayam,ina maida dubana kan madubi daidai nan ta bi ta window ta fice.Da mugun sauri
na je bakin windown sai na gan ta a buɗe alhalin kullum a rufe take ban barinta a buɗe .
“ Naf wai har yanzu ba ki shirya ba?” na ji muryar Uncle Salem a bayana,na juyo da sauri ina
cewa “ yanzu zan shirya“ sai kuma na ga yana buɗe ƙofofin hancinsa ya ce “ wannan wai
ƙamshin mene ne kamar na Gawa?”
Da ido na tsure shi ina kallo jin ya ambaci gawa,a zuci na ce ‘ kenan dai da gaske ne abin da
idona ya gane min? Ko ɗaya daga cikin fatalen da ake cewa sun shigo duniyarmu ne?’
“ Ki yi sauri ina jiran ki a mota” ya faɗa tare da fita.Kayan atamfa na saka kafin na ɗora hijabi
sama,sai da na je na shaidawa Ammy kafin na fita can tsakar gida inda yake jirana.Bayan motar
na shiga na zauna kusa da shi,waya na tarar yana yi sai da ya bai wa direba umarni sannan ya
soma tuƙa mu.
Sai da muka hau titi sosai kafin ya kashe wayar wacce duk rabinta turanci ne da kuma sunayen
makaman yaƙi.Na ɗaga kai na dube shi daidai shi ma ya dubo ni,sai muka haɗa ido hannuna ya
kamo yana murmushi ban san dalilin da yasa ni ya hana ni na dinga riƙe hannunsa amma shi in
ya yi niyya haka yake kamo ni.
“ Faɗa min me da me kike son saya?” ya tambaye ni yana ɗan matsa hannuna,ko kaɗan ban jin
wani abu na daban saboda a matsayin uba na ɗauke shi.Na langwaɓar da kai na ce “ Chocolat
da kuma teddy babba,sai turare da kuma ƙumbar kanti,da lipstick,da uhmm yawwa da sabuwar
waya Uncle Please ” na ƙarashe tare da ciro ƙafafuna na yo sama da su tare da ɗora su kan
nasa,ina jin lokacin da ya ja wani numfashi kafin ya ce “zobe fa?” ya tambaye ni saboda yadda
ya san ina son zobe sai dai duk in ya siya min ban san ya ake yana ɓata ba.Na saki ɗan
murmushi kafin na ce “ na hannunka nake so” sai na soma ƙoƙarin zare wani zobensa mai
shegen kyawu da sauri ya dakatar da ni yana mai cewa “ zan saya miki wani dai”
Na turo baki na ce “ Uncle wannan zoben dai kamar a tare aka haife ku ko kuma wani ɗanka
sam ba ka son rabuwa da shi,ina ga ma ka fi sonsa fiye da Niii!” na ɗan ja ƙarshen ban shirya
ba saboda yadda ya kafe ne da rikatatun idonsa masu matuƙar kaifi .
“ Shi zoben?” ya tambaye ni cikin wata irin murya,ban iya cewa komai ba sai kai da na ɗaga
masa alamar eh.A gabana ya cire zoben daga babban yatsansa na tsakiya sai ya kamo
hannuna na hagu ya zura min shi a yatsana na biyu,a hankali yayi ta shafar zoben yana kallon
tsakiyar idona har ya gama daidaita shi,sam tunanin ta ya aka yi zoben da shi kansa a babban
yatsa kawai ya tsaya masa amma ni kuma a yatsa na biyu? Wannan tunanin sam bai shigo
kwanyata ba sai na shiga yin murna har da wani rungume shi, Uncle Salem ya ƙara jan ajiyar
zuciya a karo na biyu.
Muna isa Mall ɗin ya ja ni izuwa ciki,ana ganinsa da kakin soja duk a soma basa girmansa,ɗaya
daga cikin ma'aikatan wurin aka haɗa ni da ita muka je tana nuna min kaya masu kyau sam ban
san Uncle yayi tafiyarsa ba sai da muka sauko ƙasa ina ta baza ido amma ban gansa ba.Idona
ya ciko da hawaye har zan tambayar mai kula da shiga da fita sai ga shi ya shigo ,ya sakar min
murmushi kafin ya ce “ zo ki zaɓi wayar kafin a kira sallah” ya wani kama hannuna zuwa inda
aka jera wayoyin manyan masu tsada Iphone na ɗauka sai muka zo nan ya biya kuɗi muka
wuce mota yayin da kuma aka kawo min kayana har mota.
Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da ɗan nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru ɗan tsaya
mu yi sallah kar jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu ya parker suka fita
suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa gilashin mota.Da sauri na dubi
wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye tana kallona da manyan idonta da suka
shige can ciki tsabar tsufa.
Banda ko dala a hannuna tun da ban fito da jaka ba,duk a tunanina almajira ce wannan yasa na
buɗe ƙatuwar ledar chocolat da sauran kayan maƙulashe na ɗauko mata cake guda biyu da
kuma jus,ina buɗe murfin motar sai ta ɗan matsa gefe na fito .Fuskata ɗauke da murmushi na
ce “ ga wannan Kaka banda kuɗi hannuna”
Cike da murna ta karɓa kafin ta ce min “ ki san yadda za ki yi ki hana mijinki tafiya dajin nan
rayuwarsa na cikin haɗari tarko ne aka yi masa”
Na yi dariya na ce “Kaka ai ni budurwa ce banda aure”
“Naf shiga mu tafi kin wani fito waje duk ana kallon ki“Uncle ya faɗa tare da buɗe min ƙofa na
shiga ina kallon tsohuwar wacce ke tsaye tana yi min murmushi amma abin da ya bani mamaki
yadda aka yi sam Uncle bai gaishe ta ba alhalin na san shi da girmama tsofi don shine ya koya
min yin sadaka musamman masu rauni irinsu.
Sai bayan na shiga motar ne na lura da ashe tun tuni shi Jabeeru ya zauna kan
mazauninsa.Har muka iso gida da tunanin tsohuwar nan danƙare a zuciyata amma sam ban
faɗa wa kowa ba sallah kawai na yi na fito na soma buɗe kayan ina nunawa Ammy da kuma
ƙannaina biyu Abdul da Mubarak,sai kuma sauran ƴan uwana waɗanda suke cousin ɗina
ne.Wayar iphone ɗin dai ce duk suka yi ta taya ni murnar mallakarta don su duk sun jima da
yinta in aka cire ƙannaina.Bayan an yi sallar isha'i Daddy da Uncle suka shigo a tare nan ne na
ji yana faɗar cewa gobe in Allah ya kai mu Jabeeru direba zai kai mu can ƙauyen Ƙwargwam ni
da Inna A'i saboda shi zai wuce can mission.Sam kwata-kwata ban kawo zancen cewa akan
Uncle Salem wannan tsohuwar ke magana ba shi yasa kawai ban wani damu ba sai ma rigima
da na ɗora masa na cewa to dole da zarar ya sauko ya fara zuwa can inda nake kafin ya zo
gida.
A cikin daren ma sai da na yi mafarkin tsohuwar nan ta sake ce min kar na bar mijina ya
tafi,amma na share batunta na soma shirin tafiya don tuni tun jiya ka saka komai namu a cikin
mota.
Ƙarfe tara tuni mun yi breakfast,sai duk muka fito.Uncle Salem motarsu ce ta wurin aiki ta zo ta
ɗauke shi yayin da ni kuma ta gidanmu ce.Duk lokaci guda motocin suka tashi muka hau titi,ta
windown mota muke kallon juna ni da Uncle muna sakarwa juna murmushi har aka zo
mararrabar hanya motocin namu suka rabu.Sai a lokacin na maido dubana kan titi ina jin abu
biyu,kewar Uncle da kuma murnar cikar muradina ba tare na san abin da ke can yana jirana a
ƙauyen Ƙwargwam.....
[06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.
*FCWA*☀️
________________________
05
Sosai Jabeeru ke sharara gudu kan titin da yake tsit babu kowa kamar an yi ruwa an
ɗauke.Kamar daga sama haka na ga tsohuwar nan mai ƙusumbi daga can nesa ta yi tsaye
tsakiyar kwalta amma duk nisan tazarar bai hana ni ganin ƙwayar idonta ba wacce ke yi min
magana kuma raɗam nake jin sautin muryarta kamar waccan lokacin. “ Me kike jira da har yanzu ba ki sanar da Uncle ɗinki saƙona ba? In wani abu ya samu ɗana sai
na ɗanɗana miki azabar da ba ki taɓa tunani ba ballantana gani a duniya” na shagala sosai da
kallon ƙwayar idon nata sam ban san lokacin da Jabeeru direba ya kawo dab da ita ba,cikin
ƙaraji na ce “ Jabeeru ka taka burkiiii!” sai dai ko kafin in rufe bakina tuni ya ratsa ta jikinta
amma abin mamaki sam bai kaɗe ta tamkar dai iska wannan mai kaɗawa haka gangar jikinta
take.
Jabeeru ya tsayar da motar,ina haƙi ina ƙari na ɓalle murfin motar na fita na je na yi tsaye na
duba can gaba a zatona ko zan ganta sheme a ƙasa sai dai wayam ba komai.Kamar wata
mahaukaciya haka na ƙara yi a guje na duba bayan motar nan ma babu kowa ko ɗigon jini
babu.Da na leƙa ƙarƙashi ma babu komai,tuni sun fito suna tambaya ta lafiya.Kai na dafe kafin
na koma cikin mota na ɗauki wayata don na kira Uncle Salem sai dai sam babu network.Zuwa
wannan lokacin hankalina ya soma tashi ji nake kamar dai gaske wani abu zai same shi.
“ Wai Nafisa lafiya duk kike wannan kai komon kamar mai saffa da marwa?” Inna A'i ta tambaye
ni.
Ba tare da na dube ta ba na ce “ network nake nema ina son kiran Uncle ne”
Jabeeru direba ya ce “ Hajiya fatan dai lafiya?”
“ Jabeeru ina son samun network don Allah,mu je ko cikin dajin nan ne mu duba ko zan samu
tsauni na hawa” na faɗa kamar zan yi kuka.
Inna A'i ta ce “ a'a gaskiya ba zan bari ki shiga daji ba,daga ganin wannan ciyayi ba za su rasa
maciji ba.Ki yi haƙuri mu ƙara gaba na san za a samu”
Jabeeru direba ya yi caraf ya karɓe zancen“ eh Hajiya wallahi sosai ake samun macizai zo mu
ƙara gaba ai mun kusa shiga inda ke da network tun da ga ƙarfen falwaya can ina tsinkaye” jin
yadda suke ta tsorata ni yasa na yarda muka koma ciki sai dai juyin duniya motar ta ƙi tashi a
dole kuma muka sake fitowa Jabeeru ya soma dubawa.
Da wani irin gudu na ratsa cikin ciyayin saboda wasu manyan duwatsu da idona suka hango
min.Ina jin Inna A'i na kirana amma ko waigowa ban yi ba ballantana na amsa mata,da isa ta na
hau can ƙoli ai kuwa sai ga network ya shigo ko kafin na kira Uncle text ne birjit irin waɗanda
ake turowa in an so a kira mutum amma ba a same shi ba.Hannu na rawa na rubuta lambar
Uncle Salem wacce ke zaune raɗam a kwanyata,sai na ji yana cikin kira amma ba a ɗauki
lokaci ba ya ɗaga yana mai jan ajiyar zuciya yayin da ni kuma na saka masa kuka tare da soma
magana “ Uncle Please kar ka tafi tarko suka haɗa maka duk ƙarya ce babu wani kashe
sojojinku da aka yi, Please ka koma gida”
“ Naf lafiya kike kuwa? Wane irin zance ne wannan? ” ya faɗa .Na ce “ ni ma ban sani ba wata
baƙar tsohuwa ce ke son haukata da farko ta ce mijina,yanzu kuma ta ce kai”
“ Ya siffarta take?” ita ce tambayar da ya jefo min.
Na ce “ tana da ƙusumbi...” ko kafin na ida koro masa sauran bayanan ya ja wata ajiyar zuciya
kafin ya ce “ Ok to” yana faɗar haka aka shaida min kuɗina sun ida,daidai nan kuma na ji
muryar Inna A'i tana cewa “ Nafisa zo mu wuce motar ta tashi” tuni na sauko na kama hannunta
muka fito daga cikin ciyayin don sai da ta biyo sawuna.
Muna shiga motar muka ci gaba da tafiya cikin gudun da ya saba,sai da muka yi wajen awa uku
kafin ya tsaya mu ci abinci da kuma fitsari sannan muka ɗora tafiya .Ba mu kai ƙauyen
Ƙwargwam ba sai wuraren sallar azahar lokacin rana ta zo tsakiya,muna shiga garin gabana ya
soma faɗuwa ina jin wani irin yanayi kamar wacce ta taɓa zuwa dama har da wasu tsofin
moments nake gani wanda na rasa daga ina suke ziyartar kwanyata sam ban taɓa kawowa
cewa suna ɗaya daga cikin ire-iren mafarkan da nake yi ba tun ranar da na soma ganin period.
Kamar yadda tun kafin mun tawo Uncle ya bani duk wasu takardun sheda da ya karɓo daga can
makarantarmu haka muka samu wani yaro ya kai mu can gidan shugaban makarantar wanda
yake cikin ƙatuwar school ɗin wacce sosai na yi mamakin yadda aka yi ma aka gina ta.
Da isar mu can sai muka taras da wasu malaman da alamu suma zuwansu kenan .Tarba muka
samu daga wajensa kafin ya nuna mana ɓangaren jerin flat/appartement ɗin da aka tanada
domin malaman ƙetare waɗanda ba ƴan ƙauyen ba.Kowane daga cikinmu ya bamu key ɗin
ɗakinsa kafin mu wuce ,Jabeeru ya tuƙa mota har zuwa ƙofar ɗaki mai lamba uku wato
nawa.Shi ne ya kai mana kayanmu ciki,ɗakin tsaf yake bai da datti kamar an sa da
zuwanmu.Ciki guda ne sai toilet da kuma ƴar ƙaramar kitchen,haka duk muka jera komai
wajensa Inna A'i ta cire zanen da muka tarar shimfiɗe kan ƴar madaidaiciyar kafitar ta shimfiɗa
wata,na shiga toilet bakina ɗauke da addu'a na yi wanka tare da alwala sannan na fito sai na
tarar tuni Jabeeru ya tafi ko sallama bai yi min ba .Dadduma na shimfiɗa na gabatar da sallah
yayin da ita kuma Inna A'i ta shiga toilet ita ma don yin wanka.Ina zaune ina lazumi na ji ihunta
haɗi da yin ƙara,kafin kuma na ji tana magana da alamu akwai abin da take kora can kuma ta
fito kamar wacce aka jefo.
Cike da kulawa na ce “ Innarmu lafiya?”
Cikin masifa ta ce “tsakaka ce na gani kin san ban son ganinta“ ta bani amsa.
Na ce “ ai kuwa inda kashe ta kika yi da kin samu lada ”
Ba tare da ta ce komai ba ita ma ta zo ta yi sallar bayan ta gama ne muka soma taɓa hira kafin
kuma mu ji bugun ƙofa,ita ce ta je ta buɗe sai kuma ta dawo hannunta riƙe da kwanon abinci
tana mai cewa “ kin ga shugaban makaranta ya aiko mana da abinci”
Na ce “ ban jin yunwa amma in kina ji kawai ki ci ki rage min”
Inna A'i ta ce “ ai kuwa ina ji tun da a mota abin turawa ne kawai kika bamu ” tana nufin cake.Na
yi dariya tare da ɗaukar wayata na soma saita app don jiya ban samu na yi ba.Ita kuwa Inna A'i
hankali kwance take cin shinkafa da miyar kajinta tana santin cewa ashe ƴan ƙauye ma sun iya
girki,ashe ba ta san guba ce take ciwa kanta ba.
★ Uncle Salem
Tun jiya da ya rabu da zoben hannunsa yake jinsa wani iri tamkar gangar jiki babu ruhi amma
babu yadda ya iya haka ya haƙura ya bar wa Naf ɗinsa.Tun asali zoben Inna Delu ce ta basa
shi a ranar da ta sanar da shi za ta koma can maƙabarta makwancinta,sam bai san amfanin
zoben ba amma yau da Nafisa ta kira shi ta sanar da shi cewa ta ga tsohuwa mai ƙusumbi
kawai ya fahimci wato sirrin ganin Inna Delu da yake a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro
shi ya ta'allaka ne da zoben.Suna tsaka da gudu ya cewa direban da ke jansa yayi