Showing 24001 words to 27000 words out of 44681 words
Chapter 9 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
budurwa ce.
Wajen wani koren fure muka ratsa sai ya soma yin rangaji yana motsi tamkar wani mai
rai,Lubna ta kai hannu za ta tsinko amma Aliya ta buge hannun tare da cewa “ ba ki ji na ce ba
a taɓa komai ba?”
“Na manta” ta faɗa tana dariya.
Sai da muka yi yawo sosai kafin mu kamo hanyar fita,nan ne na ji tamkar na taka wani abu mai
motsin rai.Ina ɗaga ƙafata sai na ga wata sarƙar diamond mai shegen kyawu sai ƙyalli take,kallo
ɗaya na yi mata ina shirin kawar da idona amma wani abu ya ja hankalina a tsakiyar sarƙar
harafin H ne aka zana sannan ga wasu duwatsu masu kaloli da aka ƙawata harafin.
Na duƙa na kai hannu na ɗauki sarƙar,ko da na ɗago sai na ga tuni su Lubna sun kai bakin
ƙofa.Kamar wacce aka yi wa dole haka na saka sarƙar a wuyana tare da gyara ɗan ƙaramin
hijabina sannan na ɗan ruga na cimmar musu.
Ko da muka fito waje sai Aliya ta ƙara mayar da mu can wurin nan mai datti.
“Yanzu ya za a yi kenan?” Lubna ta tambaya.
Aliya ta ce “mafita guda gare mu a yanzu shi ne mu je can gidansa”
Kamar wacce aka tsikara na ce “na san gidan” duk suka kalle ni da mamaki,amma tun da abin
da suke so ne kawai ba su tambaye ni ta yaya ba sai muka ɗau taxi ni ce na dinga nuna masa
hanya har muka isa gidan.
Bayan mun sallami mai taxi muka fito muka yi cirko-cirko,unguwar tsit take sosai ma na yi
mamakin ta yadda aka yi Meelat har ta iya ganin maƙwabtan Alhajin.
Aliya ce ta soma juya hannunta mai power ta ɓalle kwaɗon da aka rufe gidan da shi,su biyun
duk suka shige ciki yayin da ni kuma na tsaya ina kallon wata matashiyar budurwa wacce ke
zabaya tana leƙena ta wata can saman benen ɗaki.
‘Wace ce ita kuma waccan mai farar fata kamar fulawa?’ na tambayi kaina a zuci,ban kai ga
samo amsa ba na ji kururuwar su Lubna daga can cikin gidan.A guje na nufi ciki sai na tarar
suna gurmuzu su da wani gogon Biri duk yadda Aliya ke da power ta kasa tsayar da shi domin
shi ma an tsafe shi.Abun mamaki ina shigowa sai ya tsaya cak tare da zubewa ƙasa yana wani
irin abu kamar yana gaishe ni,ƴar kallon-kallon muka fara yi mu ukun .
“Haule ke ma irin wannan protector ɗin gare ki? Na ga duk jikinsa yayi sanyi” Aliya ta yi min
tambayar da sam ban ma gane mene take nufi ba hakan yasa na share ta na ce “ga ɗakin
akwatin gawar nan” na nuna musu shi da yatsa sai suka nufi ƙofar yanzu ma Aliya ce ta buɗe
ta. Sai bayan sun shiga na take musu baya ina mai waiwayen Birin da har zuwa yanzu yana a
yadda yake.
Kiciniyar buɗe akwatin suke amma sun kasa,don power Aliya ma ta ƙi yin aiki.Sai na zo na
kama musu amma ta ƙi buɗuwa,Lubna ta ce “ina ga akwatin nan jini ne makullin buɗe shi”
Duk sai muka kalle ta,kai ta jinjina ta ce “wannan tambarin Family ne” ta nuna wani logo da ke
jikin akwatin.
“To jinin wa za a tsaga?” na yi tambayar.
Aliya ta ce “in dai haka ne da na Lubna za a yi amfani duba da ta taɓa zama cikin ƙungiyar,na
san har zuwa yanzu zanen hannunta bai goge a rubutun da suka yi ba” sam ba mu yi tunanin
wannan babban kuskure ne za mu tabka ba,haka Lubna ta tsaga yatsanta ɗigon jininta ya ɗiga
sau uku a jikin tambarin nan take akwatin ya soma buɗe kansa a hankali wari da ɗoyi yasa suka
ja baya,yayin da ni kuma na toshe hancina tare da matsawa ina leƙen akwatin.Yana gama
buɗewa na ji an tunkuɗa ni ciki na faɗa yayin da kuma akwatin ya rufe ruf da ni a ciki.Cike da
tashin hankali na soma kiciniyar buɗe shi amma ya ƙi yi,ina jin muryar Aliya kuma na cewa
Lubna “don me kika yi haka? Yanz...” ban ji ƙarashin maganar ba sakamakon ƙanƙame ni da
gawar ta yi tana yi min maganar da ta birkita lissafina.Daidai nan free page ya ida in kina son ci
gaba sai ki tura 500 via2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBABK sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
Yanzu nake rubuta shi Ni ma banda complete in kin biya group ne zan saka ki
06.Apr.25
[06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.
*FCWA*☀️
________________________
01
Ra'ayi riga in ji ƴan magana, wannan haka yake a lokacin da matasa sa'anina ke sha'awar fita
waje domin yin dogon karatu tare da burace-buracen ababen ƙyalƙyalin duniya ni kuma shiga
ƙauyuka ne ra'ayina domin koyar da yaran da ke cikin duhun jahilci.Sunana Nafisa,matashiyar
budurwa ƴar kimanin shekara ashirin da biyu a duniya.Na fito gidan sarauta,a jinin masu izza da
taƙamar dukiya sai dai ni sam ba wannan ne a gabana ba.Duk da na sha wahalar shawo kan
mahaifina kan ya bar ni na yi karatun zama malamar makaranta amma kuma fafur ya hana ni
fita aiki wanda hakan ba ƙaramar barazana ba ce da cikar burin nawa.
Fuska shaɓe-shaɓe da hawaye na nufi ɗakinsa,shine kaɗai tilo da na san zai iya yin magana
mahaifina yayi amanna da ita ba tare da gardama ba.Ko sallama ban yi ba ballantana neman
izini kawai na tura ƙofar,kamar kullum yana zaune kan dadduma yana jan casbi.A gabansa na
zube kamar raƙumar da ke jin ƙishi,ya ɗago fararen idonsa ya zube su a kaina kafin cikin
tattausan furuci ya ce “Naf !”
Baki na turo gaba idona na sake zubo da wasu sabbin hawayen.
“ Yau kuma wa ya taɓa ki?” ya tambaye ni cikin nutsuwarsa wacce ke ƙara masa ƙwarjini.
Cikin kuka na ce “Daddy ne wai ba zan yi aikin gwamnati ba”
Yayi murmushin da ya bayyana fararen haƙoransa waɗanda kullum suke shan gugar asuwaki
kafin ya ce “ki je zan yi masa magana” da sauri na girgiza masa kai na ce “ a'a Please uncle ka
tashi mu tafi yanzu kafin masu hura wuta su ƙara masa ƙaimi” na faɗi haka ne saboda ahalin
gidanmu suna da ɗagawa sosai ta yadda suke ganin kamar ƙasƙanci ne a ce jinin gidan ya je
yana aikin gwamnati,aikin ma koyarwa.
Ya buɗe baki zai yi magana na yi saurin kamo tafin hannunsa wanda yake lutuf da tsoka sai
taushi kamar na mace,hannun nasa ya duba da sauri na sake shi saboda ba tun yau ba ya yi
min hani da hakan ba wai iya gare shi ba kawai a'a hatta ƙannaina maza ya hana ni raɓar su ko
kuma taɓawa a tsakaninmu.
Na sunne kai wasu hawayen na sake surnano min suna ɗiga kan farin hijabina.
“Nafisatu?” ya kira ni cikin wani salo,ba tare da na ɗago ba na ce “ na'am uncle”
“Me yasa ra'ayinki ya banbanta da sauran danginki? Me yasa kike son yin aiki alhalin
mahaifanki sun tanadar miki komai na rayuwa?”
Na ɗago na dube shi kafin na ce “ uncle kai ma ba ka son na yi wannan aikin jahadin na shiga
ƙauyuka ina wayar da kan al'umma? Saboda me uncle? Kawai don iyayena suna masu arziki
shi kenan sai na yi kwance na dogara da dukiyarsu? Me yasa ni ba zan yi aiki ba?”
“ Saboda ke mace ce!” ya bani amsa yana kallon idona,ji na yi kamar ya watsa min ruwa zafi
kawai sai na tashi na fita a guje ina gwanjin kuka.Ina shiga babban falonmu duk sai na tarar da
ƴan uwana kuwa suna ta cece-kuce akan maganar,ɗakina na wuce direct na haye gado na
kwanta rub da ciki amma abin mamaki sai na ji tamkar kan cinyar mutum ne kaina yake amma
sam ban bai wa hakan muhimmancin ba na ci gaba da rera kukana,har na fi jin haushin rashin
goyon bayan Uncle Salem kan na Daddyna.A hankali na soma jin ana shafar gashin kaina
wanda ke luluɓe da hijabina,ido na soma lumshewa ba tare da na shirya ba yayin da kuma na
soma sauke numfashi akai-akai.Ban sani ba ko na shiga duniyar mafarki ne ko kuwa zahiri ne
amma sai na tsinci muryar wata dattijuwa na yi min gatana haɗi da bani tarihin ababen tsoro
kamar yadda na fi ƙaunar kallon horror film.
★A can ɓangaren Uncle Salem kuwa Nafisa na fita da gudu yayi saurin tattare littafansa kafin
ya gyara zaman hiramin kansa ya fito.Direct ƙofar da za ta sada ka da babban falon ya nufa
bakinsa ɗauke da sallama,tsit duk falon ya ɗauka kafin duk su yi ƙasa da idanunsu saboda
yadda yake da matuƙar muhimmancin da kuma girma a idonsu.Cike da girmamawa suka soma
gaishe shi “ Barka da fitowa Daddy ƙarami“ domin haka suke kiransa in ka fidda Nafisa da take
ce masa Uncle ita ma ɗin shine da kansa ya koyar mata da hakan.
“Fatan dai ba ƙara ta ba aka kai wurinka,a toh don na san ba kasafai za a gan ka a nan ba”
cewar Daddy yana ɗan murmushi yana kallon babban abokinsa,amininsa kuma ɗan
uwansa.Uncle Salem ya ce “tun da ma ka sani ai shi kenan sai a fara shirya mata abubuwan da
za ta buƙata in ta je can”
Daddy ya ɗan nisa yana kallon yaran wurin duk sai suka tashi suka kama gabansu,sai a lokacin
kuma Uncle Salem ya zauna suna fuskantar juna.
Duk shuru suka yi na wani ɗan lokaci kafin Daddy ya ce “ ba wai yadda kake tunani ba ne
aboki,ina da dalili na daban da yasa ban so Nafisa ta yi nisa da gida”
Uncle Salem ya murmusa ya ce “tun muna makaranta ake faɗar wannan kalmar akan kana da
dalilin ƙin yin wani abu amma har yanzu ba ka taɓa faɗa min mene ne dalilin ba.Abdul Hameed
ka sani cewa su yara da kake gani sun fi son bin zaɓinsu kan na iyayensu,kuma kai ma in ba ka
manta ba...” sai kuma yayi shuru. Yanayin fuskar Daddy ta ɗan sauya kafin ya ce “babu damuwa zan bari ta je ɗin, Allah ya bada
sa'a ya kuma tsare ta akan abin da nake tsoron faruwar” da “amen“ kawai Uncle Salem ya
amsa kafin ya miƙe tsammm ya nufi ɗakin Nafisa,ya tura ƙofa tare da yin sallama sai kuma yayi
tsaye cak yana buɗe ƙofofin hancinsa saboda kalar wani ƙamshi da ya dake shi da bai taɓa jin
irinsa a wannan duniyar ba....
[06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.
*FCWA*☀️
________________________
02
Tsaye yayi yana kallon yadda take bacci tana wani taɓe baki kamar mai kuka yayin da goshinta
ke fitar da gumi.Ya furzar da wani huci kafin ya ƙarasa ya zauna bakin bed ɗin,a hankali ya cire
mata hijabin nata wanda ya ɗan jiƙe saboda zufa.Sumar kanta wacce take baƙar ƙirin ya soma
shafawa yana tofe ta da addu'a,a hankali ta soma sauke ajiyar zuciya tana wani motsa idonta
kamar mai son buɗe su.
Kamar wanda ke wasa da maciji haka ya soma shafa farar fatar fuskarta wacce ta yi ɗan ja
saboda kukan da ta yi.Wata irin azababiyar ƙaunarta ce yake jin tana bijiro masa,ji yake tamkar
ya ɗauke ta ya haɗiye tsabar so.
Sam bai san abokin nasa ya shigo ba don ya lula sosai a duniyar tunanin muradun ruhinsa,sai
jin saukar muryarsa yayi “ sai yaushe ne za ka sanar da ita ɓoyayyen sirrin da ka binne
abinka?”
Uncle Salem yayi saurin ɗagowa ya dubi Daddy ya saki ɗan murmushin da ya zame masa jiki
kafin ya ce “ har yanzu Naf yarinya ce aboki,zan ƙara mata lokaci ” sai kuma ya mayar da
duban nasa ga fuskarta a iya kallon da yake jifar ta da shi ya isa ya fallasa ma sirrin da ƙunshe
a zuciyarsa.
“ Shekarunta ashirin har da biyu fa,lokaci na ƙurewa girma na sake zuwar ma amma har yanzu
ba ka ajiye iyali ba aboki” Daddy ya faɗa cikin rashin jin daɗi.
“ Shi aure ai ba sauri yake so ba,a'a fahimtar juna aboki.Ka yi tunanin yadda Naf za ta ɗauki
lamarin ne in ta ji cewa ni mijinta ne alhalin a uba ta ɗauke ni?”
Daddy yayi murmushi kafin ya ce “ to ai kun fi kusa,ban iya na sani”
Uncle Salem na shirin yin magana aka shigo haɗi da sallama,Ammy ce hannunta riƙe da kofin
ruwa.A mutumce ta gaishe da Uncle Salem wanda a girme ya girme mata sannan ta dubi
mijinta hasken idaniyarta ta ce “ ga maganinta yau ba ta sha ba sam” ya karɓa ita kuma sai ta
fita.
Kan dakalin gado Daddy ya ajiye maganin yana mai kallon Nafisar wacce har zuwa yanzu take
baccinta yayin da kuma hannun Uncle ɗinta ke kan sumarta.
“ Aboki me kake ɓoye min dangane da Naf?” yayi tambayar cike da kulawa.
A ɗan rikice Daddy ya ce “ no babu komai zan je na duba wasu takardu in ta tashi ka bata
maganin” yana gama faɗa ya fice,shi kuwa Uncle Salem kai ya girgiza tun suna yara suke tare
amma har izuwa yanzu bai san dalilin da yasa abokin nasa ke ɓoye masa wani babban sirri da
ke ɗawainiya da rayuwarsa.Tun da Nafisa ta soma tasowa yake lura da yadda hankalinsa
kocokwam ke kanta hatta makaranta in ta je ya dinga kiran waya kenan yana tambayar
labarinta,yana ɗaya daga cikin abin da yasa kuma ya basa aurenta tun ba ta san kanta ba
amma har yau ya ƙi sanar da shi mene ne sirrin.
Ganin kamar baccin nata irin wancan ne da ta saba yi ,sai Uncle Salem ya ɗauki kofin maganin
ya cika bakinsa da shi kafin ya taɓe bakinta yana ɗura mata shi kamar yadda tantabaru ke ciyar
da junansu,a hankali kuma take haɗiye ruwan maganin da shi ne ya haɗa mata shi a haka har
ta shanye shi tasss.Da ya kai ƙarshe sai da ya ɗan lashe mata lips kafin ya miƙe ya
fita,sashensa ya nufa ya rage kayan jikinsa yayi wanka ya fito ya shafa turare kawai sai ya
ɗauki system ɗinsa ya soma aiki yana duba saƙonnin sojawan da shine ya tura su mission a
daji.Reppot ne iri-iri wasu na murna wasu na jimame,tuni kansa ya soma yin hayaƙi yana jin
cewa da buƙatar ya je can ɗin da bada wata sabuwar atisaye.
★ NAFISA
Ban san iya lokacin da na ɗauka ina bacci ba,ko da na tashi da ƙamshin turaren Uncle Salem
na soma cin karo wanda ya game ko ina na ɗakin.Na turo baki gaba kafin na dubi hijabina
wanda na san da shi ne ya cire min shi ko shakka babu.Wanka na shiga,bayan na fito na yi
sallar azahar don sallah na ɗaya daga cikin abin da na fi so a kaf cikin abubuwan ibada ita da
azumi wannan kuma horarwa Uncle Salem ce tun ina ƴar shekara sha uku yake saka ni yin
azumin Litinin da Alhamis,tun ina kukan yunwa har na kai na saba.
Ina zaune kan dadduma Ammy ta shigo,“yawwa kin sha maganin ashe ” shi ne abin da ta fara
cewa.
Shiru na yi ina tunanin yaushe na sha magani amma ban tuna ba,amma tabbas da na tashi na ji
bakina na zaƙin zuma.Na sake turo baki don kuwa tuni kwanyata ta hasaso min ina baccin ya
bani magani.
“ Ammy ni yunwa nake ji” na faɗa kamar zan yi kuka,“ Sai ki je ki ci mana,ki taso ki kaiwa Daddy
ƙarami abincinsa” ta faɗa tare da ficewa .Ina kukan sangarta na fita zuwa falo,cikin gunguni
nake cewa Ammy “ duk ga ƴan aiki nan amma shine ba za su kai masa ba sai ni ”
Ta dube ni da mamaki kafin ta ce “ au! Dama can ƴan aiki ke kai masa abinci?”
Ba tare da na ce komai ba na nufi dianing na ɗauki ƙaton tray ɗin da aka jera komai nasa,na
ɗauka tare da fita ina tafe ina turo baki har na isa sashen nasa dakyar na lalubo sallama can
ƙasan maƙoshi na yi.
Bai amsa ba sai ɗagowa da yayi yana kallona kafin kuma ya mayar da dubansa kan system
ɗinsa.Hakan yasa na ji haushi na ajiye tray kan table har na juya zan tafi na ji ya ce “ Naf!” na
tsaya cak ba tare da na juyo ba ina jiran abin da zai ce sai kawai na ji tsayuwarsa a bayana.Da
sauri na juyo muna fuskantar juna,idona tab tsoro nake kallon nasa da nake hango tsantsar
ɓacin rai a cikinsu.
“ Ka yi haƙuri!” na faɗa murya na ɗan rawa.Bai ce komai ba ya kamo hannuna ya zauna da ni
kan kujera,“ ki zuba abinci ki ci” shi ne abin da ya faɗa sam babu wasa a maganar sai ya je ya
zauna ya ci gaba da aikinsa.
Ni kuwa kallo na soma ƙarewa kyakkyawar fuskarsa mai cike da yalwatacen saje da ɗan
madaidaicin gemu,kan jajayen laɓansa na tsayar da ƙwayar idona waɗanda ke yin furucin da
babu sauti da alamu wani abu yake karantawa.
Tamkar wacce aka yi wa dole haka na ƙanƙance ido ina karanta bakin nasa,na waro ido jin
tamkar har da muryarsa ke yi min raɗa a kunne tana sanar da ni abin da yake cewa ɗin.
“ Ba ki ji abin da na ce ba?” ya jefo min tambayar,da sauri na mayar da hankali kan abincin haka
na zuba