Showing 9001 words to 12000 words out of 44681 words
Chapter 4 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
ta ce “ashe kin tashi? Bari na sa a haɗa miki ruwan wanka in kin
gama sai ki ci abinci”
Ɗan murmushin yaƙe na yi na ce “to” sai ta ƙwala kiran ƴar aikinta bayan ta zo ta faɗa mata
aikin da za ta yi sai kuma ta dube ni kamar mai son tantance wani abu kafin ta ce “kayanki suna
ɗakinki an jera a drower”
Abun mamaki kasa yi mata muso na yi ko kuma na tambaye ta yaya na samu ɗaki a nan
gidan.Ita ce ta yi min jagora na isa can ɗakin wanda tuni an haɗa min ruwan wanka a baho,kar
ku ji zancen wasa a ranar nan Zuly ce ta yi min wanka tamkar wata ƴarta ni kuma na kasa yin
wani kataɓus.Duk da ina tune na yi mafarki amma sam tunanina bai bani na tsarkake jikina
ba,saboda controling nasa ake yi.Bayan na fito ita ce ta bani kayan da na saka,sannan aka
kawo min abinci kamar yadda ta shaida min tun farko.A cikin abincin nan Allah kaɗai ya san irin
kalar maganin da aka saka min amma a haka na ci,kar ku tambaye ni maganar sallah don
dama can farko ni ɗin na kasance mai wasa da ita ba kullum nake cika biyar ba sai in Umma ta
yi min faɗa wannan yasa ko kaɗan ban samu ƙarfin zuciyar yunƙurin yinta ba.
Ina cin abinci Zuly na yi min hirar yadda aikina zai kasance a gobe da kuma yadda tsarin
yake,sai kuma ta soma nuna min yadda ake yin aiki da wata ƙatuwar waya bayan nan kuma ta
kira ƴan aiki biyu suka yi min tausa da wani man da aka tanada don yin tausa sai dai shi sun
garwaya shi da gubar tsafinsu. Har cikin ɓargon jikina nake jin yana ratsa min ,a sannu a hankali kuma bacci ya ɗauke ni nan
ɗin ma mafarki na yi gani nan a wani ɗakin taro duk turawa ne ciki ni ɗaya ce baƙar
fata.Masayar turanci kawai muke yi kowanne na yaba kamfanin da yake yin aiki,bayan mun
gama meeting kuma sai muka je muka yi wanka cikin swimming pool maza da mata haka duk
muka shiga ciki babu wata suturar kirki.Ina farkawa wannan karon babu kowa a ɗakin sai ni
ɗaya,sannan babu wani haske sosai shuru na yi ina daidaita tafiyar numfashina.Daga nan
kwance na ga lokacin da wata baƙar inuwa ta fita amma ban iya tantance ta mace ce ko ta
namiji.
Kamar minti biyu sai ga Zuly ta shigo tare da kunna ƙwan lantarki,na lumshe ido tare kuma da
buɗe su.
“Ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai saura ”shine abin da ta ce min.
Da mamakin jin wai har dare yayi gari ya waye na ce “kina nufin yanzu safiya ce?” wani irin kallo
ta yi min kafin kuma ta fita,na sauke ajiyar zuciya na tashi na shiga toilet sai a lokacin kuma na
lura da an canza min kayan jikina zuwa na bacci.
Cikin bahon wankan na shige,ina tunanin kaina a can ƙasan zuciyata sai dai fa na kasa tuna
wace ce ni daga ina nake abu guda kawai ke cikin ƙwaƙwalwata shi ne aikina da kuma Zuly sai
oganmu wanda nake jin mugun tsoronsa ya samu wuri a zuciyata ya zauna daram.
Bayan na gama wankan sai na fito,da taimakon wasu turawan masu aikinta na kimtsa cikin
wasu arnan kaya riga da wando waɗanda suka ɗame ni sosai suka fitar da shap ɗina.Tamkar
wata ƴar tsanar roba haka na koma na yi kyau sosai,gashin kaina kuwa an dunƙule min shi
tsakiya sai aka ƙara min da ribbob na gashin doki ta yadda ya sauka har gadon bayana.
Zuly ta shigo ita ma cikin shiga mai kyau sai dai na fi ta haɗuwa kasancewar na fita kyawun
fuska da na jiki.Jaka ta miƙa min da sabuwar waya irin ƙatuwar nan wacce ake aikin ofis,kafin ta
ce “mu je” ta kamo hannuna,dakyar nake tafiya saboda yadda ban saba hawan takalmi masu
tsini ba.
Da muka fito harabar gidan nan na ga ikon Allah don kuwa ba gidan da muka zo ba ne ni da
Zuly,wannan tamkar aljannar duniya haka yake.Hatta motocin da ke wurin sun sha banban da
waɗancan,cike da girmamawa aka buɗe mana gidan baya muka shiga abun mamaki har da
masu take mana baya.Sai da muka hau babban titi ne sannan na gane nan ɗin fa Turai ce ba
Afirka ba,wani kamfani ne muka je tun a bakin ƙofa Zuly ta tsaya kafin ta ce “ki nutsu ki aiwatar
da aikinki kar ki wani damu jin cewa ke ce baƙar fata a cikinsu” kai na jinjina mata kafin
Bodyguard biyu su take min baya har zuwa ɗakin da za a yi meeting ɗin.
Direct kujerar da ke ɗauke da sunana na je na zauna,suna ne wanda ba wanda uba mahaifina
ya saka min ba a'a Oga ne ya canza min shi ba tare da na san ta ya aka yi kuma na gane nawa
ne ba.Leena shine sunan da ke jikin ɗan ƙaramin allon gabana,sai da na yi gyaran murya
sannan na danna wayar hannuna wacce ke ɗauke da dukkan bayanan da za mu tattauna a kai.
“Sunana Leena daga ƙasar Kamaru,wakiliyar kamfanin El Mansoor a yau mun kawo muku wata
babbar haja wacce muke fatan za ku ji daɗinta sosai fiye da sauran business namu na baya” ina
kawowa nan sai na yi shuru ina yi musu murmushi su kuma duk fuskokinsu sun nuna zaƙuwar
jin abin da zan ce ɗin.
Na ci gaba da cewa “a ƙididdiga ta malamanmu na spirituality sun gano cewa dayawan mutane
a yayin yin bahaya mutum na zubar da kaso hamsin cikin na abin da ya shafi taurarinsa marar
kyawu,yayin da kuma zubar da yawu a lokacin da mutum ke tsugunne kan salanga yake ɗauke
ɗigo biyu na sinadarin tauraronsa mai haske.In muka haɗa hamsin da biyu sun tashi ɗari
cicif.Na san dayawanku za su tambaya ta ya aka yi aka samu ɗari? To amsar mai sauƙi ce duk
tauraro mai haske ɗaya yana daidai da kaso hamsin na baƙin tauraro,da za a saka su a injin
markaɗe a garwaya su to tasirin farin tauraro ne zai ƙwace kaso mafi rinjaye.Kun ga shi kenan
mun samu tauro ɗari kenan” duk shiru suka yi suna nazari amma babu wanda ya iya cankar
ainahin gamsashiyar amsar kawai sai suka fara yi min tambayoyin yadda za su yi su zuba
hannun jarin wanda dama ni shi nake jira.Sai na soma yi musu bayani dalla-dalla “iya adadin
kuɗin da mutum ya zuba iya adadin taurarin da zai samu,kenan kowa sai ya aiko min da saƙon
abin da ya yanke ta adreshing email namu”
Ina kawowa nan sai Zuly ta shigo ita da wasu masu aiki su biyu suna ɗauke da tray,amma ita
Zulyn ce ta ajiyewa kowa kofin shayi a gabansa tana ajiye min na ɗauka na soma kurɓa ina
kallon yadda suke shawara a tsakaninsu.
Ba a kuma ɗauki lokaci ba kowa ya soma faɗin abin da zai zuba na hannun jari,bayan nan duk
sai aka watse aka bar ni daga ni sai Zuly wacce ta danna wa oga video call tana murmushi tare
da yi masa congratulations akan aikin da na yi nasara ba tare ni na san muhimmancin meeting
ɗin ba ko kuma ina jawaban da na kawo suka dosa ba.
Yadda suke murna yasa ni ma na ji sanyi a raina,ina jin oga na cewa “ku tawo gida mu yi
shagalin murnar a nan”
Yanayin fuskar Zuly ya ɗan canza ina ganin lokacin da ta saci kallona ta wutsiyar ido kafin ta ce
“oga kana ganin lokaci yayi da Luby za ta ga zahiriya da idonta?”
“Eh mana! Ai ba zama za mu yi muna kashe kuɗi wurin controling memorynta ba kawai ku dawo
yanzu,sai ku same ni a can filin hutawana ”
Da ƴar damuwa a fuskarta ta ce “oga ko dai ka tarbe mu a can ɗin,don ina gudun Luby ta yi min
tirjiya ko borin hauka”
“Ki yi yadda na ce” yana gama faɗa ya kashe,sai a lokacin ne ni kuma na jefo mata tambayar
da ta ɗaure min kai “Zuly wace ƙasa ce nan? Ta ya aka yi muka zo nan?”
“Ki taso mu je,yanzu kin samu amsar tambayarki in mun koma Kamaru” ta faɗa tare da nufar
ƙofa,sai na take mata baya ina mai ci gaba da yi mata wata tambayar “amma ina ne nan?” ba ta
bani amsa ba har muka shiga mota muka isa gida.
Da umarninta kuma na bi bayanta zuwa wani ɗaki wanda babu komai a cikinsa sai wani madubi
da aka rufe da jan ƙyalle.A gabana ta buɗe shi tare da ɗaukar wuƙa ta tsaga yatsanta jini ya
soma ɗiga sai ta shafi madubin nan take yayi ƙara ƙiiiii tare da buɗewa ya fitar da hoton ƙofa
amma fa ba ƙofar ba ce don ba ka ganin komai sai wani farin abu kamar gajimare.
Jikina ya ɗauki rawa na ce “ina ne nan kuma Zulaihat?” na yi tambayar ne jin tamkar tunanina
ya dawo normal,iya ni ɗaya kawai ke sarrafa shi.
“Ba mu da saurin lokaci Lubna ki zo mu tafi” ta faɗa tana kamo hannuna da niyyar shigar da mu
cikin madubin,a tsorace na ce “mu je ina? Wai cikin madubin? Zulaihat wannan ai tsafi ne.Ina
kika kawo ni? ” ba ta bani amsa ba ta wani fizgo ni muka ratsa mirror ɗin sai gamu muna yawo
cikin wani iska kafin kuma ƙyaftawar ido na gan ni a cikin ɗakin Zulaihat a cikin falo.Tuni zaren
carbin tunanina ya tsinke,dukkan jikina rawa yake yi min ina son yi mata tambayoyi amma ina
tsoron jin amsoshinsu don ban so a ce abin da nake zargi gaskiya ne.
Ita kuwa Zulaihat sai ta yi fuska tare da haɗe rai ta ce “ki tashi mu je Malama oga na jiranmu”
Cike da masifa na ce mata “babu inda zan je! Gidanmu zan tafi”
Nan ta yi wata dariya kafin ta ce “au haba? Kenan? To wuce ai ga ƙofa nan sai ki tafi”
Sam ban damu da gyatsen da ta yi min ba sai na fita daga ɗakin na fito harabar gidan,babu
kowa a bakin get sai na je na buɗe ƙofa da zumar fita nan na yi arba da wata lukutar masifa don
kuwa ruwa ne maƙil a wurin tamkar za su taɓo sararin samaniya,babu shiri na koma can cikin
falon sai na tarar da ita tana shan ayaba cike da shaƙiyanci ta ce “har an dawo daga gidan ko
kuwa an fasa zuwa?”
Idona ne suka kawo ruwa shaaa,ina kallon Zulaihat wacce da dukkan alamu babu ɗigon imani a
ƙirjinta.Miƙewa ta yi tare da ɗaukar key ɗin mota ta ce “mu je” dole dangi na ƙi yasa na take
mata baya muka shiga motar .Mai gadi ya buɗe mata gate yana wani murmushin da ya tabbatar
min bakinsu ɗaya shi da Zuly duk munafukai ne,gudu sosai ta yi har muka isa gidan Ogan.Muna
shiga ana kiran sallar magrib,a zaune muka tarar da shi kan kujeru na alfarma ya saka ɗan
madaidaicin table a gaba mai ɗauke da cake wanda aka yi wa kwalliya kamar ba ci za a yi ba.
Tsoron Ogan ne ya ƙara ratsa ni,amma duk da haka ita ɗaya kawai ta gaishe shi.Ya amsa yana
kallona kafin ya fara jawabinsa “Luby na san zuwa yanzu kin fara gane aikinki, sannan kin san
cikin me kika shiga,da kuma su wa kike tare da su.Sai dai ki sani a tafiyarmu ba gudu ba ja da
baya,kamar yadda kika saka hannu a yarjejeniyar tsarin aikinmu za ki yi komai da family suka
buƙata wato ƙungiya,to ya zama dole ki yi shi.Sam family ba mu da matsala,ba kamar sauran
ƙungiyoyin da kika sani ba ne,mu sam ba mu da buƙatar jini sai in dai mutum ne ya kawo taurin
kai muke ɗaukar mataki mai tsauri a kansa.Abin da muke so ba komai ne ba sai abin da bai da
amfani wurin al'umma,kamar dai abin da kika gabatar a yau wato kashi/bahaya sai kuma sperm
ko yawu ko kuma audugar mata da suka riga suka yi amfani da ita shi kenan fa.Mene ne
matsala a nan?” ya ƙarashe tambayar yana mai kafe ni da idonsa masu mugun dafi.
Wasu sabbin hawaye suka zubo min kafin na zube a gabansa na ce “don Allah ka yi haƙuri ka
goge sunana daga ciki, wallahi na yi ma alƙawari babu wanda zan faɗa wa wannan labarin ko
da kuwa iyayena ne”
Yayi wani murmushi ya ce “tuni ai iyayenki sun san da aikinki,don yanzu haka mahaifinki na
asibiti an yi masa gyaran ƙafa sannan mun aika saƙon cewa yau ke ce za ki yi gadi a babbar
pharmacie ɗinmu ta saida magunguna.Ko ba ki yarda ba?” yayi tambayar yana mai jawo
wayarsa ya kunna min video duk abin da ya faru tun daga lokacin da aka ɗauko Abbana har
izuwa lokacin da suke asibiti an yi masa aiki ga Ummah nan zaune kusa da shi fuskarta cike da
farin ciki.
Wani irin tausayin kanmu ne ya kama ni,tabbas sun yi min dabaibayin da ban isa na warware ta
sauƙi ba.
“In kuma kika ce za ki bijire minti biyu yayi yawa zan aika mahaifinki barzahu” oga ya faɗa .
Cikin razani na dube shi,sai ya gaskata maganar ta hanyar cewa “ƙwaran gaske ,kamar yadda
kai ki ƙasar Turai bai yi min wahala ba haka zan katse igiyar numfashin mahaifinki don haka kar
ki kawo min wasa ki zo ki yanka cake ɗin nan kafin ya sha iska”
Yana gama faɗar haka sai Zuly ta miƙa min wuƙa,ba don na so ba na yanka cake ɗin wanda
yayi daidai da jin wani mashi ya caki zuciyata tamkar ma zuciyar tawa ce na yanka.
Mu uku muka cinye cake ɗin duka,kafin Zuly ta ja ni mu koma can gidanta.....
Ga masu son fara yin payment 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[02/04 11:51] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
06
Da muka isa gidanta dakyar na samu na yi sallar isha'i,ita kuwa magrib kamar yadda lokacinta
ya wuce to haka ta wuce ni don ba zan ranka ta ba.
Gida nake son tafiya,amma da dukkan alamu ba zan samu wannan alfarmar ba.Haka na yi
shuru cikin ɗaki ina tunani iri-iri da kuma mamakin yadda Zulaihat ta koma muguwar sheɗaniyar
marar imani.Na goge hawaye masu ɗumi da suka zubo min lokacin da tunanin yadda na ga
iyayena suna farin ciki ya faɗo a kwanyata.
“Luby sai fa in kin so ne za ki damu,kamar yadda oga ya faɗa miki mu family sam ba mu da
wata matsala.Kin ga fa babu wani abu da za a nema wurinki in kika cire lokacinki,ni ban ga abin
damuwa ba a aikin da babu kashe mutane ciki sannan ko jinin ɗan tsako ba mu buƙata”
A lokacin da ta yi min wannan magana sai kuma na ga fa kusan tana da gaskiya,duk da cewa
su ɗin matsafa ne amma dai fa ba su kashe mutane.Amma abin da ya fi bani mamaki bai fi ta
yadda suke son abubuwan shirme ba,cikin son sanin dalilin haka na jefo mata tambayar “Amma
Zulaihat me za ku yi da kashin mutane?”
“Don Allah ki bar ce min Zulaihat ɗin nan,ki kira ni da Zuly sannan maganar me za mu yi da
kashin mutane ke ce a ba ki san amfaninsa ba shi yasa amma da shine ai ake yin takin zamani
ana kaiwa gona don yin noma”
Na ja ajiyar zuciya da yake ni sokuwa ce sai na yarda da maganarta,kuma in faɗa muku gaskiya
sosai kalamanta suka yi tasiri a raina don sai na ji na kuma yarda zan yi aiki da su.Ban taɓa
sanin illa ne ba sai da na haɗu da ke Haule na ga irin abubuwan da kike yi na ban mamaki.
Jin na samu ƴar nutsuwar ruhi sai na je na yi wanka da ruwa masu ɗumi,da na fito na sha
salade na fruit sai kuma a lokacin ne Zuly ta bani wayata wacce take sabuwa dal.Wani irin daɗi
na ji ganin ta canza min waya amma layina ne a ciki,ta yi wani murmushi tare da zama kusa da
ni ta ce “kwaɗayin na gan ki cikin daula yasa na kawo ki cikin family,dubi yadda jikinki yayi kyau
cikin ƙanƙanen lokaci ”
Na ɗan yi murmushin farin ciki kafin na ce “ni dai ki koya min yadda ake aiki da ita” ta yi ƴar
dariya kafin ta soma nuna min,muna yi muna taɓa hirar makaranta da kuma ƙawayenmu wanda
muka yi aji guda.Duk wani wanda nake da labarinsa sai na faɗawa Zuly aikin da ya samu ko
kuma halin da yake ciki.Ban taɓa tunanin cewa rahoto ne take haɗawa ba don farmakarsu sai a
ranar da ni ma tawa mission ɗin ta zo,zan faɗa muku yadda komai ya wakana sannu-sannu.
A daren nan sosai muka jima muna hira kafin duk mu kwanta, washegari Zuly ce ta tashe ni sai
kuma ta hana ni na yi wanka sallah kawai na yi na saka kayana waɗanda na fito da su daga
gida sai jakata.
Fita muka yi muka shiga mota ta kai ni asibiti da tambaya muka samu ɗakin da su Ummah
suke.
Ina ganinta na je na rungume ta ina tambayar jikin Abba wanda ke bacci.
“Da sauƙi sosai yanzu likita ya shigo ya duba shi tare da yi masa allura,ya aikin Lubna? wannan
fa?” Ummah ta faɗa tana nuna min Zuly .
“Ah na manta ban gabatar miki da ita