Showing 36001 words to 39000 words out of 44681 words

Chapter 13 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki

tuƙo
motar yayi parking nata daidai ɗakina,nasa sabon key ɗin da headmaster ya bani na buɗe
sannan muka shiga .A gajiye yake wannan yasa ya soma shiga wanka,ko da ya fito tuni an
soma kiran sallah da sauri na ɗauke idona ganin ya fito babu riga daga shi sai farin towel ya
ɗaura a ƙugu.
A ɗan daburce na ce “ Uncle ga kayan buɗa bakinka”
Bai ce komai ba sai gefen katifa da ya zauna haka nan ya ƙi saka kayan,da kansa ya zuba
zoɓon don dai ni ba zan juri kallonsa a haka ba na shige toilet na ɗauro alwala .

Da zan fito sai da na ɗan ziro kai don ganin ko ya saka riga sai dai karaf muka haɗa ido da
shi,yana nan kuma a inda na barsa.Ya sakar min murmushi yayin da ni kuma na fito cike da
kunya,kaina sunkuye na ɗauki dadduma na soma yin sallah ko kafin na gama ya canza kaya ,a
nan ɗaki shi ma yayi sallah gefena kan nasa daddumar.
Hannuna ya kamo da nake ta yin Azkhar ɗin yamma da ban samu na yi bayan sallar asar
ba.Wani irin sanyi ne nake ji yana ratsa ni ga tuwon tafin hannunsa sai wani matse min nawa
yake .

“ An gama yi wa Uncle ɗin fushi?” ya tambaye ni yana murmushi mai sauti.
Na ce “ ni ban yi fushi ba”
“ Kalle ni” ya faɗa ,a hankali na dube shi ɗin idonmu ya sarƙe cikin na juna ina son kawar da kai
amma tamkar wacce ya yi wa dabaibayi na kasa.A hankali na soma sauke ajiyar zuciya ,tsawon
lokaci muna a haka kafin ya buƙaci in zuba abin da na dafa mu ci.Jiki duk a sanyaye na zuba
muna ci muna aukin kallon juna har muka gama,ana kiran sallar isha'i na miƙe don gabatarwa
amma ya katse ni “je ki yi ɗahara ki sake alwala”

Ban musa masa ba don ba ya daga cikin halayena yin gardama a gare shi.Da mamakina kuwa
da na shiga toilet alwalata ta karye iya ɗan kusanci da muka samu kawai,amma sam ban kawo

shi wai don wannan niyyar yasa ya ce na je na sake alwala shi yasa ko da na fito ban wani ji
kunyarsa ba na haye dadduma,shi ma sai da ya sake yin wata alwala kafin ya yi sallah.


Hira muka soma yana tambaya ta meeting ina basa amsa cike da sakewar fuska kafin na soma
jin cikina na yin ciwo,tun ina daurewa har na kasa.
“ Je ki kwanta” cewar Uncle ,ina cije leɓe na haye katifa tare da yin rairan ina duban sama dafe
da cikina.

Jakar da ya zo da ita ya buɗe sannan ya ɗauko wasu kwalabe yayi wani haɗi cikin kofi ,kafin ya
cika bakinsa da ruwan ya zo ya ɗora shi kan nawa.Na buɗe bakina na dinga haɗiye ruwan
maganin a hankali ina lumshe idona har na shanye duka,ina jin yadda Uncle ya soma tsotsar
lips ɗina amma banda wani ƙarfin hana shi dukkan jikina ya saki kwanyata ma tamkar ta rabu
biyu tunanina yana gushewa yana dawo wa kamar wani network.

Wani irin zazzaɓi ne nake jin yana rufe ni a sunnu,na ware idona a hankali kamar na jariri sabon
haihuwa ina kallon Uncle da ya gama tsotse min baki.So nake na faɗa masa ina jin sanyi amma
babu bakin magana,tashi na ga yayi yasa key ya rufe ƙofar sai a lokacin ne kuma Inna A'i ta
faɗo min a rai.
Jakar kayana ya buɗe ya je ya ɗauko kayan baccina,irin rigar nan mai buɗewa ya saka min
bayan ya zare ta jikina sai rumtse ido nake don ko bra ban saka ba saboda muddin ba fita zan
yi ba takura min take.Shi ma irin rigar ya saka sai dai bai ƙulle tashi ba,ina ganin ya kashe
hasken ɗaki ya kunna wutar ƴar ƙaramar waya sai ya ɗauko ƙaton blanket ya rufe ni kafin shi
ma ya shigo ciki.Hannuna mai sanye da zobe ya kamo ya riƙe kafin yayi min rumfa da ƙirjinsa
mai cike da yalwa gashi ta kwanta sai santsi take.

Wannan karon yana ɗora bakinsa kan nawa ji na yi kamar ya jona ni ga lantarki,tuni na ji duk
jijiyoyin jikina sun dawo aiki.Na ƙanƙame shi gam ina yin numfashi da sauri-sauri,yayin da shi
kuma ya ci gaba da shan yawuna kafin ya soma shayar da ni nasa can kuma ya cire bakinsa ya
mayar da shi daidai kunnena yana cewa “faɗa min wa ya baku abinci jiya?” Dukkan jikina rawa yake saboda sabon yanayin da na tsinki kaina,na tallabo bayansa da kyau
na ƙanƙame shi ina jin lokacin da igiyar rigata ta since ƙirjinmu ya mannu da na juna sai na ji
kamar raina zai fita tsabar shock.Murya na rawa na ce “ headmaster ne!” ina gama basa amsa
ya ƙara lalubo bakina wannan karon har da romance yana yawo da hannunsa a duk sassan
jikina.Ni dai duk abin kamar a mafarki nake jinsa ba zahiri ba saboda tunanina ba zaune yake
daram ba,ban san lokacin da na yi bacci ba bugun ƙofa ne ya tashe ni.Na ware idona a hankali
sai na ga Uncle a tsaye bakin ƙofa yana murza key,yana gama buɗe wa sai Inna A'i a tsaye
kamar wacce aka fiddo daga rame.......


My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

Zuwa page 10 zan gama free page in sha Allah,za ki iya yin payment ɗinki tun yanzu.
[06/04 15:24] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________


08

Da wani irin sauri na gyara rigar baccina wacce na tuna sosai Uncle ne ya saka min ita .Na miƙe
tsaye ina mai ci gaba da kallon Inna A'i wacce ta shigo ƙafafunta fututu kamar wacce aka fiddo
daga kabari.Tana shigowa Uncle ya maida ƙofa ya rufe,sannan ya je ya zauna kan dadduma
hannunsa riƙe da ƙaramar casbi.
“ Innarmu daga ina kike?” na samu kaina da tambaya.
Sai ta dubi Uncle Salem,ni ma sai na dubi bangaren da yake ina mai tambayar kaina ‘shi
wannan a nan ɗakin ya kwana ko me?’ a nan take kuma kwanyata ta soma kawo min gogagen
kilishen abubuwan da suka faruwa sai dai ba su fita sosai ba dishi-dishi ne ban ida tantance
taƙamaimai abin da ya faru ba a tsakaninmu.

“ Bari har na yi wanka Nafisa, lokacin sallah ma ya gabato ” Inna A'i ta faɗa tare da nufar toilet.
Yadda na ji idonsa na yawo a jikina yasa na kai dubana gare shi,sai na ga ashe cinyoyina ne
yake kallo bai ƙyaftawa.Duk sai na ji babu daɗi don dai bai saba yi min haka ba,na je na ɗauki
hijabina na saka na yi tsaye har sai da Inna A'i ta fito daga wankan sannan na shiga saboda

fitsarin da nake ji ya matse ni.



Wani irin tsoro ne ya kama ni ganin ina yin fitsari baƙi ƙirin da shi tamkar wani Lipton .Wani kuka
ne ya ƙwace min tare da tashi ina yarfa hannu,ban san ta ya aka yi har Uncle ɗin ya ji kukan ba
sai gani na yi ya shigo toilet ɗin sam kuma a wannan matakin da nake cikin tsoro ban ga aibun
shigowarsa ba .

Wani irin sihirtacen kallo yayi min a tsakiyar idona da suke tsiyayar da hawaye kafin ya ce “ ki yi
wankan tsarki ki fito, wannan dattin ciwon cikin da kika yi ne jiya ko kin manta har magani na
baki?” yayi maganar yana jan ruwa fitsarin ya wuce,sai a lokacin na ji kunya tare da gyaɗa
masa kai alamun na yarda.
Murmushi ya sakar min kafin ya fita,sai a lokacin na cire rigar baccin da hijabi.Wankan tsarkin
na yi kamar yadda ya umarce ni kuma sai na ga ya kyautatu ɗin na yi shi.Bayan na fito sai na
ga yana bai wa Inna A'i magani da murfin roba,ya fi kala uku maganin kafin kuma ya miƙe ya
fita.

★Uncle Salem

Jiya a lokacin da Inna A'i ta ɗauki wayar Nafisa ,a cikin muryarta kawai ya ji hucin wani ruhi da
ke jikinta.Bai kuma yi wani dogon tunani ba ya fahimci tabbas da matsala,can gida ya koma ya
tattaro duk maganin da ya san zai buƙata kafin ya ɗauki hanyar garin Ƙwargwam.Abu guda ya
sani shine ba zai iya rabo su daga ƙauyen can ba tun da har Innarsa Delu ta yarda ta bar su
suka wuce alhalin kuma ta fitowa Nafisa a siffar ruhi.
Ko da ya zo kuma bai ga Inna A'i bai yi mamaki ba,ita kanta Naf ɗin ƙwayar idonta kawai ya
kalla ya hango yadda guba ke son game dukkan jikinta.Abu biyu ne yasa ya bata maganin,na
farko don ya ji wane ne ya ciyar da Inna A'i don samo mafita,na biyu kuma don karye abin da
aka baiwa Nafisar a cikin shayi ta sha. A jiya ba don yana son ceto Inna A'i ba babu abin da zai hana shi ya mayar da Nafisa cikakkiyar
mace,sosai moment ɗin ya ja shi zuwa ƙarshen shauƙi.Ba tare kuma da ya fita ba daga nan
inda yake kwance da taimakon zoben hannunta ya lalabo Inna A'i a can wani ƙasurgumin daji
tana yi ta tafiya ita ɗaya kamar mahaukaciya saboda tun bayan fitarta zuwa mayar da
kwanukan gidan headmaster a nan bakin ƙofar ɗakinsu ta ji kamar ta zurma cikin rame kafin
kuma ta tsinci kanta wani wuri.Dukkan detail ɗin nan Uncle Salem ya gansa daki-daki,wanda
kuma ko ita Inna A'i aka tambaye ta ba za ta kawo shi ba.

Yadda ta ji muryarsa kamar daga sama shi ya sa ta juyo baya ta fara dawowa gida kuma,ko
lokacin da ta buga ƙofa daga cikin ramen ta fito sai dai Uncle ya toshe duk wata ƙofa da zai sa
A'in ta fahimci wani abu.

Yanzu kuma da ya fito, tsugunawa yayi ya ɗiga wasu ruwa cikin ramen kafin ya rufe kwalbarsa
ya saka a aljihu.
Masjid ɗin makarantar ya nufa wanda ake ta kiran sallah,yana isa ya shiga sawun gaba bayan
yayi nafiloli sai ya zauna har lokacin sallar yayi .Tuni kuma masallacin ya cika aka tayar bayan
an gama ne Uncle Salem ya juyo yana kallon headmaster wanda ya zauna kafaɗa da kafaɗa da
shi.Ya saki wani murmushi kafin ya ci gaba da yin Azkhar ɗinsa,har sai da ya gama kafin ya
basa hannu ya ce “ Assalamu alaikum ”

Headmaster cikin mazgewa ya miƙawa Uncle hannu suka yi musabaha wacce yayi da na sanin
yin ta,don kuwa akwai kumfan magani a hannunsa na karye sihiri.
“Wa'aleykum Salam ! Fatan an sauka lafiya?” ya amsa tare da saurin janye hannunsa.


Uncle Salem ya ce “ lafiya lau alhamdullah ! Na zo duba wurin da matata ne za ta yi aiki ita da
Kakarta sai kuma na ga wuri yayi kyau”


Cike da takaici headmaster ke kallon Uncle ,don kuwa tun zuwansa jiya akan idonsa na ɓoye ya
sauka.Sannan sarai ya san da shi ne ya warware zare da abawar da ya ƙullawa Inna A'i,amma
saboda ya iya munafurci shine zai ce masa wuri yayi kyau.
Cike da iya tako shi ma headmaster ya ce “ ai kuwa dai school Ƙwargwam na kula da
malamanta har ma da ɗalibai”


Uncle wani murmushin ya sake yi kafin ya ce “ ni ne shaida,amma me yasa kuka bata ɗaki mai
lamba uku bayan ita sabuwar zuwa ce?”
“ Ɗakin nada matsala ne?”
“A'a kawai na tambaya ne”
“In ba ta sonsa ai sai a canza mata”
“ A'a na faɗa ma wuri ne mai kyau,kuma lamba ukun ai ita ce daidai da ita surukar Inna Delu
guda” Uncle ya faɗi haka ne ya na saka idonsa cikin na headmaster don yi masa gargaɗi kan
cewa kar ya sake cutar masa mata in kuma ya ƙara yin kuskuren haka shi da shi shege ka
fasa.Da sauri kuma ya miƙe ya barsa nan.



Bayan na gama sallah haka na tsure Inna A'i da tambayoyi sai ta faɗa min inda ta je amma sai
kwana-kwana take yi min daga ƙarshe ma ta shige kitchen tana cewa “bari na haɗa mana
breakfast ”
Na ce “ yau fa Litinin ko kin manta azumi muke ni da Uncle ”

“ A'a yau ba za ki yi ba,ki bari har Alhamis ” Uncle ya faɗa wanda ke shigowa.Na dube shi da
mamaki jin yau shine ke cewa na ajiye azumi,“ Uncle ina yi fa” na faɗa kamar zan yi kuka ina
kallonsa.Ya ɗauke kafin ya ce “a'a akwai maganin da za ki sha yanzu kafin ki ci komai” sai yayi
gaba ya ƙarasa gaban jakarsa ya fiddo wata kwalbar zuma.

Ido tab hawaye nake dubansa,ya ɗago ya kalle ni kafin ya ce “za ki zo ki sha ko sai na zo nan
na ɗauko ki na matse miki baki tare da ɗura miki shi?”

Jin ya fito a Uncle Salem ɗinsa mai tsanani yasa na ƙarasa gabansa na yi zaune tare da
tanƙwashe ƙafafuna.Da wata ƴar ƙaramar cokali ya soma bani zumar har sai da na sha bakwai
da ita kafin kuma ya soma bani wasu sauran maganin,ɗaya kuma ya ce “ wannan kuma sai in
kin ci abinci za ki sha” sai ya miƙo min na karɓa ina gunguni.
Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ Naf sai yaushe za ki girma?”
Kamar suɓutar baki na ce “ ranar da ka yi min aure”

Shuru yayi bai ce komai ba,ni ma sai na rashin kunyata.Na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa sai
na ga ashe ni ɗin ce yayi ƙuri kamar mai kallon tv.Zan yi ƙasa da kai yayi saurin tallabo haɓata
ya ce “ da gaske kin shirya zaman auren?”
Na lumshe ido ina dariya,ya ce “ faɗa min na ji saboda in na koma gida na yi wa Daddynki
magana a soma shirin biki”

Na ɗan cinno baki gaba na ce “ni da ko saurayi banda” kamar daga sama na ji bakinsa kan
laɓana, wannan karon dai kam cikin hankalina nake.Cike da razani na buɗe ido kafin da sauri
na tashi daga gabansa jikina na ɗan yin rawa,duk da ba yau ne ya saba yi min kiss ba amma a
goshi ne ko a kumatu ya saba min sannan an ɗauki lokaci mai tsayi rabon da yayi.

“Nafisa?” na ji muryar Inna A'i,da sauri na nufi kitchen ɗin ina jin daɗin kiran nawa da ta yi.Ina
shiga ta yi min wani kallo sai na ji na tsargu na yi tunanin ma ta gani ,a ɗan daburce na ce “ ni
ma ban san me yasa Uncle yayi haka ba,shi ba giya yake sha ba ballantana na ce bai cikin
hayyacinsa ”
“Ungo ni ki je ki sha ya fi wannan surutun da kike yi min marar kan gado,duk duniyar nan akwai
mai sonki sama da shi Salem ɗin da har za ki yi tunanin zai yi abin da zai cutar da ke” Inna A'i ta
faɗa .
Na karɓi kofin kunun tare da komawa can gefe na soma sha sam na ƙi yarda na koma can,ita
ma ba ta matsa min amma ina shanyewa sai na fito don tuni gari yayi haske sannan lokacin da
za mu je bakin aji ƙarfe bakwai ne.

Ina fitowa na gansa a zaune ido rufe yana wani jan numfashi tare da ɗan game fuska haɗi da

yamutsa ta.Toilet na shiga na yi wanka,da na fito sai na tarar ba ya nan.A gaggauce na shirya
tsaf,na zuba takardun da zan yi amfani da su da abin rubutu.
Inna A'i ta fito tana min wani kallo kafin ta ɗauke kai,“ki je yana mota yana jiranki ku yi sallama”

Jiki a sanyaye na fita ganin irin yadda ita Innarmu ta canza min fuska wacce nake ɗauka uwa ta
biyu.Hijabi na saka kafin na fita,gidan gaba na buɗe na zaune na sunne kai tare da yin shuru
ina wasa da zoben hannuna.Kujerar da nake zaune a kai ya ɗan buɗe ta ja baya,da sauri na
kalle shi yadda na ga idonsa sun kaɗa sun yi ja yayi bala'in bani tsoro.Murya na ɗan rawa don
duk a tunanina kuka ne yayi,na ce “Uncl...” sauran maganar ce ta maƙale jin bakinsa kan nawa
abin ma bai tsaya nan ba ya soma shafar hijabina ta sama .Hawaye ne suka soma zubo min ,ba
yau ne farkon jin cewa uba yayi mu'amala da ƴarsa ba na sha jin ire-iren labarun nan a kafar
BBC amma ban taɓa tunanin akwai ranar da abin zai zo kaina ba don ban taɓa banbance
Daddy da Uncle ba.Duk abin da yake yi ko motsi ban yi ba da yatsana ballantana na yi yunƙurin
hana shi ,hawaye kawai nake yi don babu bakin kuka saboda Uncle ya mayar da shi sweet
ɗinsa.Sama da minti goma kafin ya janye daga gare ni amma ina jin hucin saukar numfashinsa
kusan fuskata da na rumtse idona.Shashekar kukansa da na ji ta yi kuma bala'in tayar min da
hankali fiye da abin da ya gama yi min,na buɗe idona ina kallonsa shi ma hawayen yake fitarwa
kafin ya kama hannuna dukkan biyun ya ce “ don me Naf? Me yasa kike horar da ni da yawa?
Me yasa ba ki ganin zazzafar ƙaunar da nake yi miki? I love Naf! Ina sonki,ina buƙatar ki a kusa
da ni haƙurina ya ƙare”

Tamkar wacce aka bugawa guduma a kai haka na ji ,kalamansa kuwa kusan tarwatsa min
kwanya suka yi sam kasa fahimtar abin da yake nusar da ni na yi.“Wuce ki tafi ki kula min da
kanki”ko ida rufe bakinsa bai yi ba na ɓalle murfin motar na fito.....


My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login