Showing 6001 words to 9000 words out of 44681 words
Chapter 3 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
ido na zuba wa Aliya ko kafin na ce wani abu an turo ƙofa,Maheer ne.Da sauri ta ɓoye
hannunta mai hasken a bayanta,shi kuma ni ya kafe da ido kafin ya saki murmushi ya ce “kar
ma ki ɓata lokacinki ko kin yi yunƙurin fitar da shi ba zai fito ba”maganar ido ce yayi min ya
fice,sai kuma na fahimci cewa ba wai iya ni ɗaya ce wannan karon na ji shi ba har da Aliya
wacce jikinta ya ɗauki kyarma tun lokacin da ta ga Maheer ɗin.
“Wace ce ke?” na jefo mata tambayar,ba ta bani amsa ba sai tashi da ta yi a guje za ta gudu
amma tamkar wata ɓarauniya haka na yi saurin cabko ta na riƙe ta gam ina mai ce mata
“wallahi babu inda za ki sai kin faɗa min wace ce ke”........
[16/03 11:36] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
04
Jikin Aliya ne ya soma yin rawa kamar mazari kafin ta ce,“don Allah anty Haule ki bar ni na tafi
wallahi in ya gano ni ce nan na yi masa kutse zai iya hallaka ni ”
Cikin ɗaga murya na ce “ba fa zan bar ki ba ,gwara ma ki bani labarinki kuma muddin ina tare
da ke to babu abin da zai iya yi miki.Hatta ita gubar da ya bani na sha ba wai don ya cutar da ni
ba ne a'a don ya dinga controling tunanina ne”
Lubna da ke can tsaye a raɓe ta ce “wato kenan kin san da gubar ma a jikinki? Innalillahi
wa'inna ileyhi raji'un! Allah ka tausaya wa rayuwata kar ka ƙara jefa ni cikin wani cakwalkwalin
uƙubar da na tsira a baya”
Na dube ta kafin na ce “don Allah Malama ki zo ki zauna kika wani tayar da hankalinki sai ka ce
baƙuwar ganin abubuwan nan na siddabaru”
Wata muguwar harara ta jefo min kafin ta kalli Aliya wacce har zuwa yanzu hannunta na fitar da
wannan hasken.
“Wace ce ke Aliya?” na sake jefo mata tambayar a karo na biyu.
Kai tsaye ta bani amsa da cewa “ni ɗin almajira ce,na taso cikin Bara na kuma girma cikinta.Ni
ɗin ba muguwa ba ce kamar yadda kika yi tunani,duk da kuwa ina ɗauke da BAƘIN RUHI a
gangar jikina amma ban taɓa cutar da wani ba sai dai na bai wa kaina kariya ga masu son cutar
da ni”
Na ja wata ajiyar zuciya kafin na ce “amma me yasa kike jin tsoron Alhaji?”
“Saboda shi ne babba a gare ni,powersa ta fi tawa ƙarfi sannan a tsarin zubin halitta protector
ɗinsa ya fi nawa tasiri”
Ina jin abin da ta ce sai na dubi Lubna wacce goshinta ke tsatsafo da zufa.Na saki ɗan
murmushi kafin na ce,“na ga powerki irin wacce ake iya sharing nata ne ,ko za ki taimaka ki
gutsurawa Lubna ko da ɗigo biyu ne?”
Aliya ta jinjina kai kafin ta dubi Lubna wacce ke shirin artawa a guje amma na harɗe ƙafafunta
ta hanyar kallo kawai,don ina juya idona ta kasa motsi na riƙe su gam.
Na miƙe tsaye ina riƙe da Aliya har zuwa yanzu,ita ma tashin ta yi da taimakona ta samu ta dafa
goshin Lubana koren hasken ya fita shuuu kamar yadda ake zuba man fetur a babur,yana fara
shiga kuma ta yi saurin janye hannunta.
Na saki murmushi na ce “yanzu dukkan tsoronki zai fice,shi kenan ke ma kin dawo tsagenmu”
Da idonta da suka kaɗa suka yi jawur lokaci guda take kallona amma ta kasa magana,ban
damu ba don na san ƙarfin ikon sarrafa wani yankin power Aliya ne ke ratsa jininta.
An ɗauki kamar minti goma kafin Lubna ta dawo normal,ta ja wata ajiyar zuciya kafin ta ce
“Haule kin kyauta kin mayar da ni mai ido uku,sai dai ki sani yau ba zan bari ki rumtsa ba sai kin
bani labarinki duka”
Na yi ƴar dariya kafin na ce “labarina nada tsayi sosai Lubana amma ke ki fara bamu naki,in kin
gama sai Aliya ta ɗora daga ƙarshe ni kuma sai na dinga baku nawa lokaci zuwa lokaci”
Da sauri Aliya ta ce “eh hakan yayi gaskiya” sai duk muka samu wuri muka zauna.
Yanayin fuskar Lubna ya canza kafin ta ce “ban ma san daga ina zan fara ba,farko dai zan iya
cewa na yarda da karin maganar nan da Hausawa ke yi ' ba duka ƙyalƙyali ne gwal ba' tabbas
na yarda da hakan bayan shekaru biyu da suka gabata na rayuwata.Kamar dai kowacce ƴar
talakawa haka na tashi da burin samun aiki mai tsoka , wannan yasa na kashe kaina wurin yin
karatu tuƙuru.Na bi duk wani matakin ilimi da kika sani,na yi digiri har da digirgir sai dai fa
samun aiki ne ya zama jan aiki.Tun ina ajiye takarduna har na gaji na bari,cikin haka ne Umma
ta sama min gurbin aiki nan wurin Hajiya can farko iya zuwa can restaurant ne aikina ina kai wa
costumer abinci .Kamar yadda kika sani iya wannan aikin kawai ba wani kuɗi ne masu yawa
ba,amma haka nake yi don gujewa zaman banza.Sama da wata biyar ina wannan aikin ,daidai
ɗaya rana ban taɓa cire burina na samu babbar kujera akan karatun da na yi ba.Sau tari ina jin
haushi in na ga masu kuɗi suna shigowa nan su ci abinci na kuɗaɗe dayawa har su bar ragowa
nan.Masu zuwa da ƴan mata kuwa haka zan zauna ina ta kallon yadda maza ke tattalinsu,duk
abin da kika duba a jikin ƴan matan kuɗi kawai ke magana.Sai fa rayuwarsu ta soma burge ni
ina sha'awar cewa ina ma ni ce,zan iya ce muku ma har hassadarsu ke tsarga min musamman
in na ga mace wacce ba ta yi wani dogon karatu ba amma tana da kuɗi sosai nake jin
haushi.Sai kuma ƙarfin imanina yayi ƙasa ina ganin Allah ya azurta kowa amma ni ya bar ni
cikin ƙuncin talauci ni iyayena waɗanda kusan ma a lokacin ni ce ke kula da su saboda Abbana
da ya samu karaya bai aikin komai.
Kusan da wannan burin yin kuɗi nake kwana nake kuma tashi da shi har Allah ya jefo min wata
ƙawata da muka yi makaranta da ita.Ba zan manta ba wata baƙar rana ce wacce ta shiga
lissafin ƙaddarata,ina kwashe plate ɗin da aka ci abinci na ji muryar wata da na sani ta kira suna
“oh Lubna ? Ke ce?” ni ma cike irin zumuɗin nan irin ka jima ba ka ga mutum ba na nufe ta zan
rungume ta amma don wulaƙanci ta yi saurin ja baya tana yamutsa fuska kamar ta ga kashi
kafin ta ce “wai ƴar aiki kika zama bayan duk uban karatun da kika yi? Ki rasa abin da za ki yi
sai tarben customer ?”
Duk da na ji babu daɗi haka na danne zuciyata na ce “to ya zan yi tun da ban samu aikin
gwamnati ba,faɗa min Zulaihat ina kike aiki?”
Ba ta bani amsa ba sai wuri da ta samu ta zauna kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wurin,“me
ke da kwai marar nauyi ? Don yunwa nake ji shi yasa ma na tsaya da motata cikin rana na ci
abinci na wuce” ni kuwa gwiwaina ne suka yi sanyi jin Zulaihat ce wai da mota duk da ban yi
mamaki ba duba da suturar jikinta iya jakarta ma tana iya ciyar da ƴan gidanmu na tsawon wata
biyu,uwa uba kuma wayarta iphone wacce kusan duk masu zuwa restaurant ɗin nan ina
ganinsu da ita.
Jiki na yi min ɓari na ce “jira na je na kawo miki” sai na koma can ciki na haɗo mata abincin da
na san ƴan gayu irinta na so har da lemun kwalba,da na kawo mata sai ta bani damar zama
kan kujerar da ke kallon tata.A kunyace na zauna, Allah yayi min sa'a ma babu kowa.Cike da
yanga take juya cokali cikin plate ɗin kafin ta soma ci tana latsa waya,message ne na
WhatsApp ta soma kunna wa ina saurare kusan duk akan manyan kuɗi ne da kuma kayan da
mutane suka yi oder ko kuma suka saya suka yaba,can kuma ta soma mayar wa na ji tana
zancen za ta tura miliyoyin kuɗaɗe.Ni kuwa ina zaune sake da baki ina kallonta,kuma kar ku ji
zancen wasa wallahi burge ni ta yi yadda take abu na ƴan gayu.Hummm! Faɗar mintinan da na
share a zaune kafin Zulaihat ta dube ni ƙaramin misali an fi goma sha,can ta ɗago ta dube ni da
idanunta da suka sha gashin zamani ta ce “Lubna gaskiya ba zan ɓoye miki ba na ji takaicin
ganinki a wulaƙance kina boyi-boyi,da kyawunki da iliminki.Amma dai komai ya wuce tun da
Allah yasa mun haɗu zan duba na gani”
Ba tare da na san wane aiki ne za ta samo min ba na shiga yi mata godiya,nan ta shiga nuna
min hotunanta da ta yi ƙasashen duniya .Ni kuma sokuwa girman burina sai ƙara farashi yake
ina jin cewa ni ma nan gaba kaɗan zan koma kamar Zulaihat,da za mu rabu sai ta bani lambata
da ke jikin wani ɗan ƙaramin kati mai ɗauke da dukkan address ɗinta da kuma kantinta na
business.Ba ta bar ni haka ba,sai da ta ware dubu goma ta bani shi ma wai don ba ta da canji
ne kuɗinta duk daloli ne.
Da na isa gida kasa bacci na yi,haka na yi ta juyi kan shimfiɗa .Saƙo kuwa na rubuta shi ya fi
cikon casbi kuma sai na goge a ganina sam ba ta cancanci in yi mata text ba.Can na daure na
kira ta, lokacin ƙarfe goma saura kwata na dare,har zan yanke kiran sai kuma na ji ta ɗauka
tana cewa “Lub baby ƴar halak kin ƙi ambato yanzu na gama maganarki wurin oga ”
Na washe baki na ce “na zata ma kin yi bacci,na gode sosai da wannan ƙoƙari me ogan ya ce
?”
“Ki zo gobe nan babban kamfani yana son ganin ki,sannan ki haɗo da takardun karatunki sai
takardar shaidar ɗan ƙasa da kuma hotonki kala biyu ”
Tamkar na yi hauka haka na ji lokacin ba tare da na san ƙaddara ce da rabon a yi ke ja na
ba.Tun a daren na jawo ambalof na shiga haɗa takarduna don dama kusan ina da komai da ake
buƙata in aka fidda hoto.Bacci ɓarawo ne ya ɗauke ni a wannan daren,shi ma rabi da rabi
ne.Tun bayan sallar asubah na shaidawa Umma zancen aikin sosai ita ma ta yi murna.Zuwa
ƙarfe takwas na je gidan hoto aka yi min guda biyu,a nan take kuma aka bani su.Daga nan na
kira Zulaihat sai ta ce na jira za ta zo ta ɗauke ni,ina nan tsaye ina jiran zuwanta sai wata
tsohuwa ta tsaya kusa da ni tana mai neman sadaka .Murnar na samu aiki yasa na zuge jaka
na bata sadaka,tana karɓar kuɗin sai ta soma juya su haɗi da kallona tsakiyar ido ta ce “ƴata ki
koma gida inda za ki je ɗin nan babu alkhairi ” wani irin haushin ta bani kafin ma na kai ga yin
magana Zulaihat ta parker motarta tana yi min horne,da sauri na zagaya na buɗe na shige ina
jin tsohuwar nan na sake jaddada min maganarta amma na yi kunnen uwar shegu da ita .
Fuska a sake muka gaisa kafin ta ce “ke ma dai kin kusa ki faso gari ki huta da yawon raba
abinci a restorant”
Na yi murmushi na ce “ai kuwa dai kin ga ban ma shaida wa Hajiyar na samu aiki ba”
“In an gama miki interview ai sai ki je ki sanar da ita”
Haka muka ta yin hira har muka isa wani katafaren kamfani,duk da ina cikin garin amma ni ban
taɓa ganinsa ba da idona ina dai jin labarinsa.Tun da muka fito daga cikin mota ake gaishe da
Zulaihat,sai na fahimci tana da babban matsayi a wurin .
Jikina ne ya soma yin rawa lokacin da muka shiga ofis ɗin ogan,komai na wurin ja ne tun daga
labulaye capet da kuma kujeru.Hatta kalandar da ke ɗauke da jerin sunayen watanni ita ma ja
ce,haka ma book ɗin nan da mutane ke ɗauke abu mai muhimmanci shi ma ja ne.
Wuri ta nuna min na zauna kafin ta ce “jira yanzu zai fito” sai na sakar mata murmushi kawai ina
mai ci gaba da sauraren bugun zuciyata.Kamar minti biyar haka wani babban mutum ya
fito,baƙi ne wulul kuma gajere yana da ƙiba sosai ga kuma ƙaton tumbi kamar mai cikin wata
tara .
Cike da girmamawa na sauka na gaishe shi har ƙasa,ya amsa cikin sakewar fuska kafin ya bani
umarnin na koma inda nake.Zulaihat ce karɓi takarduna ta miƙa masa,a nutsu ya shiga duba su
kafin ya soma yi min tambayoyi ina basa amsa daidai da abin da na sani.
Ya yi wani murmushi da ya ƙara bayyana muninsa kafin ya ce “Zuly ƙawarki nada kaifin basira
kam,ina ga ita ya kamata mu baiwa kujerar mai kula da baƙinmu na waje ko ya kika ce?”
Ta yi wani murmushi tana mai cewa “ai kuwa ko a makaranta ita ce ta ɗaya,sannan ta saba
jagorantar duk wani abu da ya shafi jagoranci ina ga babu matsala in dai ta yarda za ta yi”
Sai duk suka maido dubansu gare ni,wata irin rikicewar na yi da kuma mamakin ƙarshen furucin
Zulaihat wai in na yarda.To me zai hana na yarda ? Abin da na jima ina nema ɗin shekara da
shekaru.
“Ba ki ce komai Luby” Zulaihat ta faɗa .
Muryata har rawa take na ce “na yarda mana ina so,in dai maganar turanci ce ai kin san nan na
fi ƙwarewa babu wata matsala” ina gama faɗar haka sai ogan ya miƙo min wata takarda haɗi da
jar biro ya ce na saka hannu a ƙasa wanda ke bada tabbacin na yarda da dukkan sharuɗan zan
yi aiki a kamfanin . Hum! Haule kin san dayawa mutanenmu ƴan Afirka muna yin babban kuskure shi ne saka
hannu a takardar da ba ka karanta jawaban da ta ƙumsa ba,to ni ma a lokacin haka na rabbata
hannu na miƙa masa.A tare suka saki wata ajiyar zuciya mai bayyanar da tsantsar farin ciki.
Sai a lokacin kuma ogan ya buɗe ƴar takardar da ke ɗauke da hotunana biyu,ɗaya ya ɗauka
sannan ya buɗe wani fayil mai ɗauke da hotunan mutane dayawa sannan ya maƙala nawa tare
da yi masa wani rubutu can ƙasa.
Bayan ya gama sai ya dubi Zulaihat ya ce “ki kai ta wurin shopping ki tabbatar kin zaɓa mata
kayan da za su fi dacewa da aikinta,sannan inda buƙata har gyaran jiki a yi mata .Kin dai fi ni
yadda ya kamata na bar miki komai a hannunki,sannan zuwa gobe za ta soma aikin kuna iya
tafiya”
Ba mu ƙara cewa komai ba muka fito,cikin yanayin tsarguwa na ce “Zulaihat mene ne kuma na
yin gyaran jiki? Halan datti gare ni irin sosai?”
Ta tuntsire da dariya ta ce “in ba abinki ba ke da za ki tarben turawa in ba ki kama kanki ba kina
ganin za su yarda su zuba hannun jari a kamfaninmu?”
Murmushi kawai na yi na basar,daga nan gidan gyaran jiki ta kai ni cikin wata ƙatuwar inji na
shiga iya kaina kawai ke waje shi ma bayan an gama wannan ɗin sai da aka saka min relax aka
sa ni a tukunyar busar da gashi.Bayan mun gama komai sai ta saya min wata doguwar abaya
wajen matar mai gyaran jikin,na saka sai na dawo tamkar wata balarabiya na yi kyau
sosai.Daga nan gidan cin abinci muka je bayan mun cika tumbinanmu sai muka wuce
mall,yadda na ga Zulaihat na jido riga da wando yasa na yi mata magana don ba zan iya saka
su ba amma sai na ta saurare ni.Bayan su kuma ta saya min har da after dress da kuma sari
,wasu kayan ma ban san da irinsu ba.
Na yi tunanin gida za ta kai ni amma sai ta wuce da ni gidanta,a falo muka zube ta sa masu
aikinta suka kwaso tulin kayan da ta sayo min kowanne da takalminsa.
Sai da aka kawo mana kayan maƙulashe muka taɓa tare da jus sannan na soma duba
kayan,sai dai ban ɗauki lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni a nan take kuma na soma yin
wani mafarki marar kan gado.....
[02/04 11:31] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
05
Mafarki ne wanda sam rabon da na yi sa ina jin tun lokacin isar min da saƙon balaga.Sai da
wannan ya sha banban da wancan,don wannan sarai ina ganin wanda ke tarayya da ni.Ba
kowa ba ne ba sai oganmu wanda yanzu ya gama yi min interview,abin mamaki kuma a cikin
mafarkin bai fi yadda yake yabona ba yana cewa “ashe Zuly ta yi gaskiya kina da taurari masu
kyau masu haske,ke ɗin maƙurar ilimi ce” ban farka ba har sai bayan komai ya kammala.A
hankali na buɗe idona da suka yi min nauyi,sam ni na manta ma a inda nake sai bayan na
watsake ne na tuna gidan Zuly ne nake.
A hankali na tashi zaune ina jin duk jikina na yi min ciwo kamar wacce aka yi wa shegen
duka.Ta zo da murmushinta