Showing 18001 words to 21000 words out of 44681 words
Chapter 7 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
kan tsari”
“Ta ya za a yi na samu sperm ɗinsa ba tare da mun yi sex ba?”
“Ki yi tunani Luby,yin sex da masoyi ai bai da wata illa ya fi ki yi da wanda ba ki so”
“Ba ki da hankali,sai na je na yi zina? Allah ya tsare ni” na faɗa tare da miƙewa,ina shirin fita
wani abun al'ajabi kiran Dr David ya shigo wayata cak na tsaya kafin na juyo na ce “shi ne ke
kirana ” sai ta saki murmushi ta ce “ki ɗauka mana”
Kiran na ɗaga,bayan mun gaisa ya tambaye ni yana son mu yi magana amma don Allah ba ta
waya ba mu haɗu ko da wani restaurant ne.A ranar nan rabon na rabu da alaƙaƙai ne yasa na
yarda da gayyatar Dr David,wani abun mamaki kuma shine a restaurant ɗin Hajiya ne muka
haɗu a nan ne na fara ganinki Haule haka kawai na ji kin yi min sai kuma na ga kina yawan
kallona a duk lokacin da za ki kai abinci a wani teburin da aka buƙata.A tattare da ke na ga
wasu abubuwan na daban sai dai ban san ya zan yi na yi miki magana ba,a nan ne kuma
hankalina ya rabu biyu na yadda zan yi na samo sperm ɗin Dr David da kuma na mamakin
yadda kike yin abu kamar siddabaru.
Dakyar na iya tattaro jarumtar tunkarar Dr David kan cewa ina son sperme ɗinsa saboda an ce
yana gyara fuska,bai wani musa min ba don dama ya kira ni izuwa nan ne don bani haƙuri da
kuma neman alfarmar mu koma soyayya.Mun yi da shi zai kawo min sperm ɗin zuwa dare,da
wannan muka rabu ya sauke ni gida.Duk yadda muka yi da shi na kwashe na shaidawa Zuly ta
yi murna sosai har ta kasa ɓoye farin cikinta,sai kuma na yi mamakin haka amma na ɓoye shi
har lokacin da Dr David ya zo ya kawo min abin da na buƙata cikin wata ƴar kwalba.
Bayan na karɓa ya jefo min wata tambayar da ta hautsana hanjin cikina,“Lubna kin tabbata a
fuskarki za ki shafa shi?” duk da a lokacin na firgita amma haka na mayar da abin tsokana na
ce a'a cikin mahaifata zan ɗura shi don na samo baby mai kama da kai,nan yayi dariya muka
taɓa ƴar hira kafin ya tafi.
Yana gusawa motar Zuly ta parker na shiga muka lula can gidanta,cike da zumuɗi take cewa
“meeting ɗinki na Japan an ɗaga shi,yau za mu je ɗakin sirrin Boss domin gabatar da sacrifice
ɗinki na farko” sam ban fahimci abin da take cewa ba,sannan kuma ban tambaya ba.
Yau ma ta cikin madubinta muka bi muka isa a ɗakin taron,abun mamaki kowa ya haɗu har da
shi kansa Boss ɗin wanda idonsa ke jifana da kallon sha'awa.Ba a ɓata lokaci ba muka
dugunzuma wani ɗaki mai shegen duhu ,babu abu mai haske ko ɗaya in kuka cire wani mirror .
Cikin wata irin busashiyar murya Boss ya kira sunana,hakan yasa na ɗan matsa ba tare da na
amsa ba.Hannu ya miƙo min,na san za ku ce ta yaya na ga haka duk da na ce akwai duhu a
ɗakin.To abin shine da zarar mutum ya kai wani lavel yana samun wani ido a tsakiyar goshinsa
mai gane masa komai da ido normal ba zai gani ba.
Yana karɓar robar sperm ɗin ya buɗe ta,sannan ya dangwalo da yatsansa ya shiga yin rubutu a
jikin madubin *BAƘIN RUHI* shi ne abin da ya rubuta nan take wata irin guguwa da iska mai
ƙarfi suka cika ɗakin na yi tunanin duk za su yi murna sai dai fa akasin haka ne ya faru saboda
kururuwa da suka soma,kafin ƙyaftawar ido wani jan maciji ya bayyana a mirror ɗin yana feshin
wuta kafin kuma madubin ya tarwatse wanda turnuƙin fashewarsa ta haifar min da gushewar
hankali ko da na farka a kwance na same ni kan shimfiɗa Ummah na yi min fifita.Ina ware idona
sosai nan na yi arba da Alhaji wato Maheer,wani irin mugun kallo ne yake watso min yana
hararena.
Ummah ta ce “kin farka Lubna?” ban amsa ba sai dai na yunƙura zan tashi sai dai na kasa
saboda yadda jikina ke yi min mugun ciwo.
“Ki kwanta ki huta” cewar Ummah.
Shi kuwa cike da mugunta ya ce “barta za ta iya tashi,ke miƙe ”
Maganarsa tamkar umarni ne a gare ni,haka na ji ba zan iya yi masa muso ba na miƙe na tashi
zaune duk da kuwa uwar azabar da nake ji.Wani magani ya fiddo cikin aljihu ya miƙo
min,“komai za ki ci ki dinga zuba wannan a ciki,in kuma kika kuskure daidai ɗaya rana za ki
koma hannun waɗanda kika fito”
A lokacin da na ji Ummah na yi masa godiya sai na fahimci tuni ya shaida mata komai,ban yi
mamakin yadda aka yi ya san komai ba don na fahimci yana da power.Sannan a cikin coma ɗin
da na shiga haka aka yi min wahayin komai ta yadda aka yi ya tarwatsa komai,ashe lokacin da
muke yin magana da Dr David Maheer ya shigo restaurant ɗin kuma ya ji abin da nake
cewa.Sannan kuma abin da ba ki sani ba Haule sarai Maheer ya san cewa ke ma ba normal
mutum ba ce,kamar yadda na dinga kallon abubuwan da kike na siddabaru to shi ma idonsa
suna iya ganin duk abin da kike yi” Lubna na kawowa nan da dogon labarinta da take bamu ni
da Aliya sai ta yi shiru,ni kuma numfashi na ja kafin na ce “amma ta ya aka yi ni ban san da
cewa shi ma yana da power ba sai yau? ”
“Saboda ƙarfinsa ya wuce yadda duk kike tunani,kin ga fa shi ne ya kuɓutar da ni daga komarsu
tun lokacin ba su sake waiwayata ba.Haka ita ma Ummah ba ta yi sake kan kula da lamurrana
ba kullum cikin yi min addu'o'i take,duk asubah in ta gama sallah kamar wata ƴar baby haka
take dafa goshina tana yi min addu'o'i ” cewar Lubna.
Na dubi Aliya wacce duk yanayinta ya canza kafin na ce “ya dai?”
“Babu komai! Amma dai a yadda na fahimta ita ma Lubna ta shiga komar BAƘIN RUHI ne
kamar yadda na saba ganin gawarwakin waɗanda suka mutu ta silarsa,su ma jini yana fita ta
idonsu”
Furucin Aliya ya tuno min da gawar Haidar,murya na ɗan rawa na ce “Lubna bayan an yi wa
mahaifinki wanka shin jinin da ya fita ta idonsa ya wanku?”
Ta ce “wallahi ban sani ba saboda lokacin ai na faɗa muku ban cikin hayyacina kuma ko da na
farka tuni an kawar da shi”
Na ce “da buƙatar mu samo amsa,babu kuma wanda zai bamu tabbacin haka sai Ummah.In dai
hakan ta kasance to tabbas BAƘIN RUHI nada ƙarfi sosai ta yadda ya bazu a duniyar nan to
amma wane ne shi?” na yi tambayar da ni da su babu wanda ya san amsarta.....
My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Don Allah masu zuwa suce min complet suke so ku yi haƙuri Ni ma banda shi,yanzu nake
typing in kina so ki biya na saka ki group.
[05/04 12:15] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
BONUS na book ɗin *BAƘIN RUHI* mai so ya tura 300 kafin na saki last free page 10 gobe in
sha Allah ki tura kai tsaye ta wannan account ɗin 2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBABK sai ki turo min shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 .Da zarar na saki last free
page discount ɗin ya ƙare.
Masu sha'awar karanta tsofin Books ɗina ku zo na yi muku discount,ga wacce ta shirya ta
tuntuɓe Ni kai tsaye ta WhatsApp +22795045822
09
Dare yayi sosai wannan yasa muka jingine bayar da labarin,duk da na san akwai abubuwan da
Lubna ta ɓoye wanda ba ta faɗa ba amma haka na yi shiru na samu wuri na kwanta.Ido na
lumshe nan take Maheer ya bayyana cikin tunanina,zaune yake a ɗakinsa ya sha wata doguwar
rigar bacci ta maza fara sol da ita.Gabanta a buɗe yake,hakan ya bani damar ganin fafaɗen
ƙirjinsa mai ɗauke da suma baƙa silik ta kwanta sai sheƙi take.Duk da ban taɓa saurayi
ba,amma gargasar ƙirji na ɗaya da abin da nake fatan samu a wurin mijin aurena hakan yasa
na kafe gurin da ido ko ƙyaftawa ban yi.
Har sai da na ji muryarsa yana cewa ,“kin ga dama kin zo” da wani mugun sauri na buɗe idona
sai kuma na tashi zaune na dafe saitin zuciyata da take bugawa,sam na kasa gane shin
tunaninsa ne na yi? Ko kuwa dai ban sani ba bacci ne ya ɗauke ni sai na soma mafarkinsa?
Amma dai tabbas na gansa da idona sai dai irin wannan tunanin bai taɓa zuwar min ba.
Cike da tsoro na ƙara kwanciya na lumshe idona zuciyata na ci gaba da matsanancin
bugawa.Wannan karon jinsa na yi dab da ni har muna jin hucin juna kai kace hatta gangar
jikinmu na tare da juna ne,nan kuwa iya esprit ne.A hankali na ɗaga idona na kalle shi,yadda
yayi wani tsaye ƙiƙam a gabana duk ya kere ni kamar Giwa da ɗan tsako.
“Yanzu kuma wannan mene ne da ka jawo ni cikin tunaninka?” na tambaye shi.
Cike da shaƙiyanci yasa hannunsa mai sanyi ya wani matse haɓata tare da ɗago ta ya ce,“ni
kike yi wa magana haka? Sa'anki ne ni? Wato ni ne ma na shiga tunaninki? Kin zata ban gane
ba? Ke ce kika shigo tunanina,na lura tun da kika zo gidan nan idonki na kaina duk kin bi kin
takura ni kin hana ni saƙat,faɗa min wa ya aiko ki?”
Cike da jin haushi na sa dukkan hannuwana na tura ƙirjinsa sai dai ko gezau bai yi ba,shi ma
tuni ya hassala sai ya kama hannuna ya murɗe har sai da na saki ƴar ƙara na soma fizge-fizge
amma ya ƙi saki na.
“Duk shegen kinibibinki ne ya jawo miki halin da kike ciki amma ko kaɗan ba ki cancanci samu
wannan power ba,sam ban ga ma dalilin da yasa ƴar aike ta mallaka miki mahaɗin ƙarfin ikona
b...” ban bari ya kai ƙarshen aya ba na gantsara masa cizo a ƙirji da wani mugun sauri ya sake
ni tare da ja baya ,daidai nan ni kuma na tashi zaune tare da buɗe idona fayau.
Saitin hannuna na duba inda ya murɗe sai na ga yayi ja sosai tamkar a zahiri ne ya riƙe ni
ɗin,ƙin komawa na yi na kwanta sai na ci gaba da zama tsakiyar su Lubna da tuni sun yi bacci.
Ina nan zaune na ji handle na motsi ,kafin kuma ƙofar ta buɗe kanta ƙiiiii sai dai ban ga kowa
wanda ya shigo ba.Wani irin tsoro ne ya kama ni ,sai nake ganin kamar Maheer ɗin ne zai shigo
a zahiri.
“Haule!” na ji muryar da har na koma ga Allah ba zan taɓa mantawa da ita ba ta kira sunana
cikin wani irin yanayi.
Na soma waige-waige kafin na ce “Husseina? Husseina ke ce? ” ba ta bani amsa ba,sai jin wani
abu na yi cikin iska ya kama hannuna yana jana sai kawai na sauko daga shimfiɗar na soma
take mata baya duk da kuwa idona bai ganinta.
Da muka ratso falo haka ƙofarsa ita ma ta buɗe kanta,haka ma ta ƙofar gida.
Muna fitowa sai Husseina ta bayyana a gare ni,tana sanye cikin farin likafaninta har izuwa
yanzu kuma kukan jinin take.
Kan dakali ta ja ni muka zauna kafin ta ce “Haule sai yaushe za ki kuɓutar da mu daga cikin
ƙangin da muke ? Har yanzu ba ki samo mahaɗin sirrin tarwatsa BAƘIN RUHI ba?”
Jikina banda rawa babu abin da yake yi,na ce “ta ya aka yi kika zo nan? Kuma me yasa kika fito
da ni waje? Ai sai ki yi min magana a can ɗakinmu”
Ta ce “in muna cikin gidan nan idonki ba za su taɓa gani ba Haule,amma na tambaye ki wane
ne kike so har haka wanda ya mantar da ke dalilin zuwanki ƙasar nan?”
“So kuma? A'a ni ban son kowa” ban ida rufe bakina ba Husseina ta ɓace ɓat,cike da mamakin
ta ya za ta tafi ba ta yi min sallama ba na miƙe da niyyar shiga gida sai dai kuma na tsaya cak
sakamakon ganin mutum tsaye a gabana fuskar nan tamau fiye da kullum.Wani irin mugun
tsoronsa da shakkarsa ne suka yi min dirar mikiya musamman da na gansa da kayan jikin nan
irin na tunanina.
“Da wa kike magana?” ya jefo min tambayar cikin tsawa kamar wani ubana.
Mayafin jarumta na aro na yafawa kaina na ce “da kai mana”
Ya waro ido kafin ya ce “ke kar ki raina min hankali da ni kuma?”
“Eh to wa ka gani a nan bayan mu biyu?”
“Me kika fito yi to?”
“Abin da ka fito yi” na basa amsa kai tsaye tare da yin gaba sai dai ƙofar a rufe take ruf.Na juyo
na dube shi,sai na ga yana wani miskilin murmushi kafin ya ce “ina ce dai fatalwa ce ta fito da
ke waje? To ki ce ta mayar da ke in tana da izzar zama a inda nake” yana gama faɗar haka sai
ya zo yana tsayuwa ƙofar ta buɗe kanta na yi wuf zan shige amma tuni ta rufe shi kuma ya
shiga ciki.
Tsoro ne ya kama ni,cikin magiya na ce “don Allah Alhaji ka buɗe min ”
Banza yayi da ni duk da kuwa da ina jin alamun tsayuwarsa bai tafi ba.Hadari ne ya soma haɗa
kansa haɗi da tsawa da walƙiya,nan tsorona ya ninku don kuwa duk jarumtata ban son ruwan
sama su dake ni.
“Ki faɗa min da wa kike magana sai na buɗe miki ” na tsinkayo muryarsa.
Cikin kukan da ya fara zuwar min na ce “ka buɗe min na yi ma alƙawari zan sanar da kai” ai
kuwa ya buɗe ƙofar ina shiga na baza a guje na nufi can ƙofar da za ta sada ni da babban falo.
Cak na tsaya ina waro ido saboda wani jaririn maciji da ya sarkaye handle ɗin ƙofa,ina juyawa
kuma sai na hangi Maheer yana takowa izuwa inda nake.Timmm na ji ƙarar faɗowar macijin
kafin ya fara yin silululu yana tawowa,a mugun firgice na yi baya tare da rugawa na tarbo
Maheer ɗin na koma bayansa tare da ƙanƙanme shi ina kuka ashe gudun gara na yi na faɗa
gidan zanzaro shine mamallakin macijin.
“Sahut!” shine furucin da yayi kafin macijin yayi tsalle ya ɗale kafaɗarsa hakan ya baiwa
bindinsa bugun fuskata nan take na yi luuu zan faɗi da sauri ya juyo tare da taro ni sai dai muna
haɗa ido da macijin igiyar saita numfashina ta katse ban ƙara sanin abin da ke faruwa ba sai da
na ji muryar Hajiya a kaina tana cewa “ka ƙi faɗin abin da ya same ta,sannan ma wai me ya
kawo ta ɗakinka? Maheer me ka yi wa ƴar mutane?”
Wani irin sarawa kaina yayi jin wani batu wai ɗakin Maheer ,ban shirya ba na buɗe idona tarau
ai kuwa a ɗakin nasa nake kwance kan bed ɗinsa abin da ya fi ɗaga min hankali bai fi yadda na
ji duk ƙamshin jikinsa ya dabaibaye ni ba.
Muna haɗa ido da Hajiya ta yi saurin matsowa “Haule me kike yi ɗakin Alhaji?”
Shiru na yi don kuwa sam na kasa tuna komai da ya faru ciki kuwa har da zuwan Husseina,abin
da na sani dai shi ne ina kwance a ɗakinmu Lubna ta gama bamu labari.
Maheer ɗin na kalla wanda shi ma ni yake kallo da idonsa da suka kaɗa suka yi ja kamar
tsohon maye.
Hajiya ta mangare ni cike da masifa ta ce “don ubanki ba za ki faɗa min abin da kika zo yi
ɗakinsa ba?”
Shaaa hawaye suka fara yi min zuba,don sai yanzu ma ne nake ganin illar wanzuwata a nan
uwa uba kuma ni kaina ban san ta ya aka yi na tsinci kaina a nan ɗin ba.
A karo na biyu na juya na dubi Maheer,Hajiya ta buɗe baki da niyyar yin wata masifar iya
sunana kawai ta furta Maheer yayi wata irin busa mai ratsa dodon kunne sai ta yi shiru tana mai
cewa “In Haule ta gama gyara maka ɗakin ta je ta shirya don Allah kafin su Lubna su gama
saka kaya a mota” sai kuma ta fice.
Ya juyar da kai gefe ya ce “ki tashi ki koma ɓangarenku”
“Amma Alhaji me ya kawo ni nan?” na yi tambayar wasu sabbin hawaye na ƙara zubo min.
“Dalla Malama saukar min daga gado,ban sani ba ki je ki tambayi fatalwar da ta kawo miki
ziyara” ya faɗa a hassale.
“Fatalwa kuma?” na yi tambayar,ya zo da ƙarfi ya wani fizgo ni na faɗo daga gadon amma sai
na yi saurin miƙewa ina jin tsanarsa na ƙara ninkuwa a raina.Idona har wani rufewa suke na nufi
ƙofar fita,da na ratsa falonsa ne idona ya sauka da duwatsun awarwarona nan ma mamaki na
yi,na duƙa zan kwashe su amma tamkar yadda iska ke ɗaga leda haka duk suka tashi sama
suka yi bayana,sai na juya nan na ga ashe shi ne yayi amfani da siddabarunsa ya janye su.
Hannuna na duba na ga yayi ja alamun