Showing 15001 words to 18000 words out of 44681 words
Chapter 6 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
labarin mutuwar ne ya maido da ke”
“Kenan in haka ne sai dai mu bi jirgi ba ta madubi ba?” Zulyn ta faɗa sam babu wata damuwa a
tattare da ita.
Oga ya miƙe tsaye ya ce “eh hakan za a yi,na riga da na tsara komai” yana gama faɗa ya
murza zobensa nan take ya ɓace ɓat.
A ɗakin Zuly na kwana, washegari kuma tun da safe muka shirya tsaf zuwa aeroport,jirgi ne na
musamman wanda bai da buƙatar sai mun nuna wasu takardu.Tamkar zan fita daga wuta haka
nake ji,don na lashi takobin da zarar mun sauka Kamaru ko ƙasa da sama za su haɗe ba zan
ƙara shiga sabgar Zuly ba na fita daga family kenan.
Jirginmu na sauka ƴan sanda suka tarbe mu,nan na ga ikon Allah yadda Zuly ke kuka idonta
duk sun yi ja sai wani rangaji take kamar za ta faɗi sai na taro ta .Daga nan police station muka
wuce aka yi mata tambayoyi kafin ta nemi tana son ganin gawar mijinta.
Duk yadda ta so mu je tare zillewa na yi na tafi can asibiti,a zaune na tarar da Ummah tana
kuka.Tana ganina ta taso ta ce “ina kika shiga tun jiya muna nemanki a waya ba mu samu ba?
Auta kuma ta ce min kuna kwance tsakar dare kika fita kika bar gidan,ina ne kika je?”
“Wurin aiki mana Ummah,amma ai gani na zo.Ya jikin Abba?”
Hawaye ta goge da mayafinta kafin ta ce “ɗazun nan aka kawo masa kwara-kwara wacce zai
dinga yin tafiya kawai sai kwacaaa na ji ya faɗi.Likitoci sun ce aikin da aka yi masa a ƙafa ya
lalace sannan ya samu shanyewar ɓarin jikiii ” ta fashe da wani kuka mai tsuma rai ,nan take
jikina ya ɗau rawa.Ban ida rikicewa ba sai da na je na ga yadda Abba ya koma ,kukan ni ma na
dinga taya Ummah ga likitoci sai rubuta sabbin magani suke.
Cikin wuni guda suka rikita mana lissafi don kuwa an kai gaɓar da kuɗin hannun Ummah sun
ida dama oga ne ya bata su.
Wuraren sallar magarib kuma babban likitan ya fito da wani zance,“kuɗin gadonku sun ida ku je
ku zuba wasu kafin nan da ƙarfe goma na dare ”
Ummah ta dube ni ta ce “ Lubna ki je ki biya,ko har yanzu ba a baki ko dala ba sai aikin?” a
cikin kalamanta sai nake jin kamar har da ɓacin rai,wato gani take na ɓoye kuɗin ne musamman
suturar da ke jikina da ke tsadadiya babu wanda zai yarda kan cewa banda kuɗi.
“Bari na je na dawo” shi ne kawai abin da na faɗa kafin na fito,tafiyar ƙasa na soma yi ina tafe
ina tunani har na isa gidan Zuly .A falo na tarar da ita,muka gaisa sama-sama kafin na shiga
ɗaki na ɗauko wayata iphone wacce zuciyata da ruhina suka yarda da na sayar da ita na yi wa
Abbana magani.
Har na kai bakin ƙofar fita na ji muryar Zuly na cewa“kina tunanin kuɗin sayen magani su ne za
su warkar da mahaifinki? To in dai haka ne kin makaro ”
Da sauri na juya ina kallonta,ta sakar min wani murmushi tana mai kankare akaifarta.
“Me kike nufi a nan?” na samu dakyar na tambaye ta zuciyata na ɗan dokawa.
Ta miƙe tare da zuwa dab da ni sannan ta ce “ina nufin ko duniya za ku yawace babu asibitin da
za ta iya warkar da cutar mahaifinki,ke ce maganinsa in kina so ya warke dole ki bai wa Boss
haɗin kai” tana gama faɗa ta bar ni nan tsaye.Na jima cikin shock kafin na fice,wajen wani mai
sayar da wayoyi na je na karɓi kuɗi tare da bar masa wayata jingina. Ko da na isa asibiti na tarar ana yi wa Ummah tijara,haka dai na biya kuɗin gado da kuma na
sauran maganin da ba a siya ba.
Na yi tunanin na kawo ƙarshen matsalar duk da kuwa furucin Zuly bai bar kwanyata ba,ashe
nan duk shimfiɗa ce aka yi min mamakin na gaba.
Ƙanwata auta ita ce ta kawo mana abincin dare mun ɗan taɓa hira kafin ta koma gida ni kuma
na yanke shawara zan zauna tare da Ummah.
Dare ya tsala bayan duk kowa ya kwanta,na ji motsin buɗe ƙofa wanda yayi daidai da farkawata
daga bacci sai dai tamkar gawa haka na sandare na kasa motsi.A gabana oga da Zuly suka
shigo ɗakin suka yi tsaye kai ga Abba,can kuma Boss ya bayyana su biyu suka danne Abba
yayin da shi kuma yayi masa wata allura wacce ta sa shi soma yin ihu da kururuwa yana kiran
zai mutu su tausaya masa su bar cutar da shi,cikin ɗacin rai Boss ya ce “ƴarka ce duk ta ja
maka masifa ba za mu taɓa barinka ƙalau ba sai ranar da ta amince da ƙudirina”
Ina jin lokacin da Abba ya soma magana cikin azaba,“Lubnata ba za ta taɓa aikata abin da kuke
so ba,na gwammaci na dawwama cikin wannan masifar kan na ga ta gurɓata rayuwart...” Zuly
ce ta ɗauke Abbana da wani mari wanda hakan yasa sauran maganar ta maƙale masa,suna
gamawa suka fice sai kuma a lokacin kawai jijiyoyin jikina suka ci gaba da yin aiki.
Dakyar na iya tashi na je na yi tsaye gaban Abba ,idonsa ya zuba min yana kuka.Bakinsa ya
juye ba zai iya yin magana ba,amma a haka ina fahimtar abin da yake son sanar da ni.Na faɗa
jikinsa na saki wani irin kuka mai cin rai wanda yayi sanadiyar tashin Ummah ita ma sai ta soma
yin kukan don ta yi tunanin mutuwa yayi.
Sai da likitoci ne suka shigo suka tabbatar mata da ransa,allura bacci suka yi masa saboda
wani irin abu da ya soma yi kamar mai cutar hauka.
Jikin Ummah na je na ƙanƙame ta ina mai ci gaba da yin kuka yayin da ita kuma ta soma
rarrashina tare da kwantar min da hankali Abba zai samu lafiya.
Da gari yayi haske suka sake shigowa suka duba Abba,suka ce jikinsa ya ƙara mutuwa da
buƙatar a yi masa gashin ƙashi .Haka suka tura gadonsa aka shiga da shi wani ɗaki,ni da
Ummah iya bakin ƙofa kawai muka tsaya.Daga nan muna jin yadda Abba ke ƙwallowa yana ihu
da ransa.
Sosai kururuwarsa ke taɓa min zuciya ,sai nake ganin duk laifina ne.A haka dai na fita don
zuwa mu yi cinikin wayata da na baro jiya,nan ɗin ma wata masifar na tarar shagon wayoyi ya
ƙone ƙurmus sai gawawarkin wayoyin ga su nan jere ringis duk sun ƙone.Yana ganina ya ƙara
ƙaimin kuka,ni ce na basa haƙuri don da ace ya san ta dalilina ne yayi asarar nan ƙila kotu ce
za ta raba mu.
Idona sun rufe,babu komai cikinsu sai ɓacin rai.Gidan Zuly na nufa don so nake a yita ta
ƙare,ko da na isa na tarar da ita a zaune tana karɓar ta'aziyar mijinta ga mutane duk sun cika
falon.Ɗakin da aka ware domin ni na shiga bayan na yi mata alama da ido ina son ganinta,sai
dai ina shiga na tarar da Boss a hakimce kan gado yana murmushi...
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
[04/04 11:00] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
08
A lokacin da na ga Boss kwance kan bed sam babu sutura a jikinsa,wani irin bugawa zuciyata
ta yi sai dai na kasa ɗaga ƙafata ballantana na koma baya na fita daga ɗakin.
Cike da shaƙiyanci yake cewa “ki gama gujegujenki ni ɗin nan ne zan raba ki da budurcinki,in
kuma kin fi ƙaunarsa kan mahaifinki ai shi kenan” yana gama faɗar haka ya ɓata kamar
walƙiya.Na ja ajiyar zuciya,abin da na fahimta a family su komai nasu ba su yinsa dole sai ta
daɗin rai wannan dalilin yasa ko da wasa ba su saka ƙarfi ba wurin baiwa Boss ni ba.
Ina nan tsaye ina saka wasiƙar jaki Zuly ta turo ƙofa ta shigo,kallo ɗaya ta yi min ta ɗauke kai
tare da yin gaba.Ni kuma na take mata baya ina mai kiran sunanta,sai da ta cire zumbulen
hijabinta sannan ta juyo ta fuskance ni ta ce “Luby ban san wace irin zuciya ce da ke ba marar
tausayi,duk halin da Abbanki yake ciki kin kasa haƙura ki bada kai bori ya hau.Me za ki yi da shi
budurcin? Ina ce duk don da dai ki kai shi ne gidan mijinki,to ki sani a family ba a auren
bare.Duk wanda ko wacce ta shigo babu aure to dole ne ya zaɓi abokin rayuwa cikin ƴan
ƙungiya,kuma ina ce ai a gabansu za a yi komai ba za ki samu matsala da mijinki ba tun da ya
san komai”
Tamkar mai cutar dundumi haka na ji a lokacin,sai kuma na fahimci ba ƙaramar ƙungiyar asiri ce
wannan ba wacce ta ɓoye sirrika masu yawa sai a sannu ne za ka dinga ganinsu suna fitowa.
Ban kai ga cewa komai ba Zuly ta ƙara da “kawai ki amince ita ce shawara da zan baki”
Idona wani irin raɗaɗi na ji suna yi min kamar an watsa barkono ciki,maƙoshina ya bushe
ƙamas dakyar na iya tattaro yawu na haɗiye kafin na ce “ban gane ba zan iya auren wani ba?
Zulaihat wai wannan ɗin duk mene ne? Wane irin dokoki ne wannan? To ki tsaya ki ji in faɗa
miki daga yau a yanzu da nake faɗa miki na fita daga family har abada,ku je can ku yi tsafinku
kuɗi ne dai to ban so ku riƙe abinku.Kuma wallahi kika yi ƙoƙarin ɓullo min da wani sharri to sai
na je har ofishin ƴansanda na shaida musu ke ce kika kashe mijinki” ina gama faɗar haka ban
tsaya ɓata wani lokacina ba na fita na bar ta cike da shock.
Duk a tunanina shikenan na huta na jefar da ɗan mangoro na huta da ƙuda sai dai ina isa asibiti
na tarar da tashin hankalin da ban taɓa zato ba.
Jikin Abba ya rikice sai aman jini yake dunƙule-dunƙule,likitoci sun duƙufa wajen bincike amma
result bai nuna alamun wata cuta ba ga jinin Abba sai ƙasa yake yi ga shi banda kuɗi,jinin kuma
sai an saya.
Duk da yana cikin firgici da gushewar hankali bai hana shi isar min saƙon kar na saki na bayar
da mutumcina ba.Banda kuka babu abin da nake yi,ji nake kamar na je na cewa Zuly na amince
sai dai fa duk shaƙiyancina na tsani zina ban ƙaunarta ko kaɗan.Ko da ace saurayina ne wanda
nake so ban ji zan iya basa kaina ba ballantana sindiƙin ƙato mashuriki matsafi.
A lokacin da zuciyata ta yi rauni sosai,shine ganin yadda jini ya soma yi wa Abba zuba ta hanci
da kuma ido daga ƙarshe yayi shaƙuwa shikenan ashe ta fitar rai ce.Wuaren ƙarfe bakwai ne na
yamma likito suka tabbatar mana da hakan,tsabar tashin hankali yasa na suma aka bani
gado.Ban san abubuwan da suka faru ba sai a washegari na farka tuni kuma an kawar da
gawar Abba an kai shi mankwancinsa na gaskiya.Sai a lokacin na yi kukan mutuwarsa kamar
raina zai fita,kafin a sallame ni daga asibiti Allah ya ƙulla alaƙa tsakanina da wani Dr David
shine ma ya ɗauki nauyin biyan kuɗin maganina har na ji ɗan sauki.
Bayan na koma gida ma haka yake zuwa yana kula da ni,kusan ma in ce shi ya ɗauki nauyin
gidanmu tun da babu wanda ya tallafa mana daga dangi.
Cikin abin da bai wuce wata ɗaya ba wata irin shaƙuwa ta shiga tsakanina da Dr David ,sonsa
ya samu matsuguni a zuciyata duk da hankalina bai kwanta ba saboda shirun da Zuly ta yi sam
ban yarda da shi ba,don na sha jin yadda ƴan ƙungiyar asiri ke da mugun naci.Ashe kuwa ban
saɓa lamba ba,a wani yammacin Laraba mun ajiye magana Dr David zai zo ya ɗauke ni mu je
gaishe da mahaifiyarsa .Mun yi waya da shi kenan ya shaida min ya ga shi nan zuwa,bayan
kamar mitin goma aka kira ni aka shaida min yayi hatsari yana can asibiti .
Cike da tashin hankali na fita ko Ummah ban shaida ma ba,ina fitowa nan cikin layinmu wani
mai mashin ya kaɗe ni sai da na yi sama na faɗo duk kayan jikina suka ɓace da ruwan
dauɗa,dole na koma gida na yi wanka ina ƙoƙarin sake fita kuma ita ma Ummah ta soma nata
ciwon abu kamar wasa sai ga mu har da zuwa asibiti.
Bayan mun dawo gida na yi ta gwada kiran Dr David amma layin bai shiga,amma ban haƙura
ba a cikin haka na samu ya shiga sai dai ba shi ne ya ɗaga ba mahaifiyarsa ce wacce nan take
ta hau ni da masifa akan na rabu da ɗanta kar abin da nake ciki ya shafi ɗanta na je can na
ƙarata da matsalata.To a nan ne fa na gane zama bai same ni ba,sam kasa bacci na yi .Tsakar
dare kuma ciwon Ummah ya ƙara tashi ta soma numfashi kamar za ta mutu,a lokacin tuni na
soma yin kuka na ɗauki wayata tsabar ruɗewa wai da Dr David zan kira nan ne na ci karo da
saƙon Zuly tana yi min hannunka mai sanda tare da barazanar cewa in ban yarda na dawo
bakin aiki ba to zan rasa Ummah tamkar yadda Abba ya tafi.
Ina matuƙar son Ummana wannan yasa na aika mata saƙon zan koma a gobe,hum in faɗa
muku wani abin mamaki kamar cirar ƙaya haka Ummah ta warke ta samu bacci.Sai na ji na ɗan
samu nutsuwa,ni kam ban yi bacci ba har sai da na yi sallar asuba wacce zuwa yanzu ina yin
sallolina.
Sai wuraren ƙarfe tara na farka,na yi wanka na shirya sai kuma na shaidawa Ummah zan koma
a bakin aikina.
“Ni kam Lubna tun da Abbanku ya rasu ban ga wani daga cikin ƴan wurin aikinku ya zo ba,har
shi ogan naki” shine abin da Ummah ta ce.
Na ce “kin san na rasa wayata,kuma oga ba ya ƙasar ita kuma Zulaihat faɗa muka yi lokacin da
na ce ta ara min kuɗi ta ƙiya ƙila shi yasa ba ta zo ba ko kuma ba ta samu labari ba”
“To Allah kyauta,ki je Allah ya tsare ki ya kuma kare ki da sharrin dukkan mai sharri”
Cike da jin daɗin addu'arta na amsa da “amen” kafin na fita.Ina zuwa bakin titi motar Zuly ta
parker a gabana,zuciyata cike da ƙunci na je na zagaya na buɗe na zauna ta saki murmushi
mai sauti kafin ta ce “barka da safiya” ban amsa ma ta ba har muka isa gidanta na canza kaya
muka wuce.
Sosai na yi mamakin yadda aka shirya min tarba ta musamman,har da yi min wankan fure aka
yi min kafin kuma na yanka cake aka shiga taɓi.Bayan wannan sai muka wuce ofis ɗin oga ni da
Zuly,bayan mun zauna ne ya soma yin magana “Luby duk da dai ban so kika rasa damarki ta
farko ba,amma mun rarrashi Boss kan ya janye wannan dokar duba da yadda kike da ƙoƙarin
aiki dakyar ya yarda amma da sharaɗin za ki kawo sperm ɗin wani wanda kika sani mai ilimi”
Na ɗan yi saƙo kafin na ce “a ina kuma zan samu sperm oga?”
Zuly ta yi karaf ta ce “ saurayinki David mana ,ai kin ga yana da ilimi sosai kuma ma ai kin ga ba
musulmi ne ba ballantana ki sha wuya wurin shawo kansa”
Shiru kawai na yi,duk da na ga sharaɗin ba wani mai tsauri ne ba amma tabbas na san da
haɗari a ƙasa.
“Ko kuwa dai kin fi so a dinga yi wa ahalinki ɗauki ɗaiɗaya suna mutuwa ɗaya bayan ɗaya?”
Zuly ta jefo min tambayar da na ji tamkar na shaƙe mata wuya,kuma sai yanzu ma ne raɗaɗin
mutuwar Abba ya fi yi min ciwo fiye da can farko.
A hassale na ce “ kar ki yi kuskuren taɓa Ummana don wallahi zan shayar da ke mamaki,kun
faɗi sharaɗinku ai sai ku jira in ban yi ba sai ku bijiro min ta nan”
Oga ya ce “ Zuly ke ma ya kike yi mata magana haka? Ki yi haƙuri Luby ki je ki fara
shirye-shiryen taron da za ki gabatar yau da dare,Zuly ki bata sanadaran da kuka fitar na
taurari”cewar oga kafin ya miƙe ya shiga toilet,ita kuwa jakarta ta zuge ta miƙo min wasu
kwalabe biyu ɗaya mai baƙin murfi yayin da ɗayar kuma ke da farin murfi.Na karɓa ina juya su
yadda kowacce kwalba ke fitar da bata kalar hasken.
“Baƙin tauraro yana da matuƙar muhimmanci ga waɗanda suka san amfaninsa,shi kuma farin
yana ƙara ƙarfin power ne kawai” Zuly ta faɗa kafin ita ma ta tashi ta take wa oga baya.Ba a
ɗauki lokaci ba yanayin sautinsu ya fara farmakar kunnena babu shiri na fita na bar ofis ɗin
amma sam sautin ya ƙi fita da kwayanta hakan ya haifar min da zuwan wani hatsabibin feeling
wanda ya fi kama da na haddasawar sheɗanu.Ido kawai na lumshe tare da ƙanƙame jikina,a
inda nake zaune nake a cikin ofis ɗin Zuly nake jin wasu idon sharri na ankare da ni amma da
na duba ban ga kowa ba.
Ina zaune cikin wannan hali Zuly ta shigo,jan bakin da ta saka duk babu shi a leɓenta sannan
zaman rigarta ma haka.Ba tare da wata damuwa ba ta ce “kafin mu isa Japan ya kamata ki
aiwatar da aikinki na kawo sperm ɗin David,ki tabbatar komai ya tafi