Showing 42001 words to 44681 words out of 44681 words

Chapter 15 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki

sex da ƴarsa

sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“ Please Naf kar ki
kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?”

Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro amma na
kasa tuna abubuwan da suka faru.
“Faɗa min me kika gani?” ya sake faɗa .
Na ce “ni na manta komai”
“Kin sha maganinki kuwa kafin ki kwanta?” ya jefo min tambaya,ni sam na ma manta da ya bani
magani.Na ce “eh a'a...”
“Baby ina ga ke ma kina son na zo kusa da ke shi yasa kike wasa da shan magani,amma babu
damuwa duk weekend zan dinga zuwar miki” da sauri na ce “a'a ban so ka yi zamanka ”
“Saboda me? Naf me yasa kike son hana cikar burinmu ne ? Haƙurina ya ƙare fa ina buƙatar
kulawa kin san abin da nake ji duk dare? Da zazzafan feeling ɗinki nake bacci ina tuna surar
jikinki na matsu na ji komai na jikinki a hannuna yana sarrafa shi ...” kuka na saka masa ina
roƙonsa don Allah ya bari ban son irin wannan zancen daga ƙarshe na ƙara da cewa “uncle ka
je asibiti don Allah likita ya duba ka”
“Ke ce likitata domin ke kaɗai kike da maganin ciwona,kin ga yanzu ma duk kin tayar min da
hankali ji nake...” ban bari ya ida ba na kashe kiran ina mai ci gaba da yin kuka.


Inna A'i wacce ta fito daga toilet ta ce “in kin gama kukan sai ki tashi ki yi sallah”
Na ɗaga kai na dube ta ina mamakin yadda aka yi ta canza min,na turo baki gaba na ce
“Innarmu kin bar sona ” na faɗa ,ba ta kula ni ba ta haye dadduma.Ni ma tashi na yi na shiga
toilet na yi wanka sannan na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallah,ina Azkhar ina tuna
mafarkin da na yi da Uncle Salem nan take kuma na soma jin jikina na saki har wani sanyi-sanyi
nake ji yana rufe ni.Na je na ƙara haye katifa tare da jan bargo na rufa ina lumshe ido,karon
farko da na ji ina muradin yin saurayi mu yi soyayya sannan aure ya biyo baya sai yayi min duk
abin da Uncle ɗina yayi min cikin bacci.Da wannan tunanin bacci ya sake yin awon gaba da ni
sai kuma na ci gaba da mafarkina daga inda na tsaya wato cikin wani daji na tsinci kaina.A
gabana kuma wani ɗaki ne na kara,a bakin ƙofa wata tsohuwa ce zaune tana hura wuta amma
ban ganin fuskarta.


Na matsa kusa da ita na ce “Kaka jiya na yi ajiya a wannan ɗakin cikin dare” ko kafin ta ɗago
idona ya sauka kan ƙusumbinta.

Ta ɗago tana kallona,ganin mun san juna sai na sakar mata murmushi na ce “Kaka dama ke
ce? Nan ne gidanki?” na faɗa ina nuna ɗakin.
Ta jinjina kai kafin ta ce “ki shiga ciki yana nan yana bacci amma kar ki tashe ”

Na shiga ɗakin sai na tarar da ɗalibina kwance bisan kunnuwan ganye yana bacci,fuskarsa
kawai ake gani saboda yadda aka yi masa rufa da wata fatar dabba.

“Ya samu rauni sosai Allah yayi sa'a ma kin kawo shi nan kan lokaci da saura ƙiris ya rasa
ransa” Kaka ta faɗa wacce ta shigo hannunta riƙe da ƙwayar sai tururi ke tashi.


Zama ta yi kusa da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda ciwon nasa
yake buɗe har yanzu.
“Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa .
Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“
“Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar wuƙa da
kuma baƙin zare.
Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare kuma da
zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar wasu surkullen
da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida.


Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta ɗauko min
zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle Salem ya bani ita
tun ina ƴar yarinya.

Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat ba da ta
zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele ciwon idon
Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na ce “wai Granny
Mamar Daddyna?”
Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro kamar ke take,sai dai
ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana sane da komai ba kamar ke ba da
yake zuwar miki siffar mafarki”

“Yanzu mafarki ne nake yi kenan?”
“Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin bacci
yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ”

“Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin ta ce “in na
tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS SADAUKI ta fi kowa
iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo
min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya
ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da sauri na ware idona tare da yaye abin rufa.

“Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska.

Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton matattu har da
fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin Ayodele sai ya tuntuɓe
ni)”

“Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na daɗe da sanin
babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka duk kusancinta da
mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba.

Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga toilet,ruwa na sauka a
jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin
ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda
zan iya cewa wannan ne karon farko da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan.
A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi Inna A'i ta
saka min shi kafin na wuce can makaranta.
Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na fito na yi tsaye.

Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da Adama
wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani fuska ba sai
wani cijewa take.

A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar liste ɗin
ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji sunansa ba?”

“Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji sautin sai
idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi ne ba saboda
mafarkin da na yi na manta shi.

“Mene sunanka?” na tambaye shi.
“Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul wa me
sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste ɗin.

Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”
“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata
matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma
numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun
kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me
kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an
manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .
Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi
ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar
yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba
biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge

ba ka ma ganin abin da aka rubuta.

“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .

“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da
ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya
kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri
har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.
Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har
lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu
fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita
wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.
Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita
ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na
bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa
min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi.


Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda
duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan
Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake
wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma
kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse.
Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da
yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai
na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko
shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.
Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da
madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya
yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.

Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha hira da Inna
A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman dama tun da na
dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar ɗanɗanon magani amma ban yi
magana ba na ci na ƙoshi.

Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ”
Na ce “kin san kasuwar ne?”
“Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo”
“To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata sai dai sam
babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page ɗin farko na soma jin
kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya taɓa faruwa da ni,da na tsananta
tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe
saitin goshina da ya soma tsira min,ba tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi
niyya ba.

Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman wani
abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar halitta,har
tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci ba kuma na samo
amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban kuma ɗauki lokaci ba na
tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i tana ta sauri yayin da wata
matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a
tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan
rabin kurwar Inna A'i na hannunta.
Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi)

Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna ina kiran
sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu alamunta,daidai nan na
tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa da ni.


Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana kakarin mutuwa
jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki Innarmu?”

Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun kifi na ci
shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu”

Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai kifin.Tsam na miƙe
tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin rai,ni kaina ban san wa nuna
min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata hanya har na isa.Allon sanarwar na
duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar
shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada
hakan ya fi shuren masaki amma na kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye
numfashina na shirin tsinkewa.

Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA

Ecobank

Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni kaina
banda shi.
In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa.

30 Janairu 2025

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login