Showing 12001 words to 15000 words out of 44681 words
Chapter 5 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
ba,Zulahait abokiyar aikina ce” na bata amsa.
Umma ta ɗan yi murmushi kafin ta ce “ma sha Allah! Allah ya taimaka ya baku sa'a ya kuma
baku cimma nasarar aikinku,ki ƙara yi wa oganku godiya don Allah Lubna .Mutum mai kirki jiya
bai bar wurin nan ba har sai da ya ga an shiga an kuma fito da Abbanki”
Wani irin sanyi ya ratsa ni jin wani abin farin ciki,na so in zauna da iyayena amma Zuly ta ƙi bani
damar yin haka ta hanyar cewa “ki dai tashi mu je gida ki yi wanka ki canza kaya sai ki dawo
ko?”
Da wannan tasa ta ci galaba kaina muka fito,“Zuly mene ne haka? Na ga kamar ba ki son na
zauna tare da iyayena” na faɗa ina kafe ta da ido.
Ta ce “ke ba fa komai ne ba,ina so dai ki yi wanka ki canza kaya ko kin ji sanyi”
“Amma daga nan fa?”
“Za mu wuce kamfani” ta bani amsa.Kafin mu shiga mota mu koma can gidanta,da isarmu kuwa
wankan na shiga bayan na fito na shirya cikin ɗaya daga cikin abayar da muka siyo jiya.Ina
tsaka da fesa turare ta shigo sanye cikin kayan atamfa har da luluɓa uban mayafi kamar ta
ƙwarai,ina shirin yi mata tambayar ya na ga ta yi shiga ta kamala daga can falo na ji muryar
wani gardi yana kiran sunanta cikin tsawa “Zulaihat?” murya na rawa ta amsa kafin ta kama
hannuna ta ce “in ya tambaye ki wace ce ke sai ki ce ƴar uwata ce ke kun zo nan ne domin
jinyar mahaifinki” ba ta bani damar cewa komai ba kuma ta ja ni muka fita can falo.
Yadda duk ta nutsu cike da tsoro yasa ni ma na kama kaina tare da gaishe shi cike da
ladabi,dakyar ya amsa kafin ya ce “wace ce ke?”
Sai da na saci kallon Zuly kafin na ce “ƴar uwarta ce,jiya muka zo nan garin domin jinyar
mahaifina da ke asibiti”
“Ita kuma ta ce min yau ne kika zo”
“Eh nan gidan ba,amma ai tun jiya muka zo ni da iyayena suna can asibiti”
“Wace asibiti?”
“Private asibitin nan da ke kusa da babbar kasuwa” na basa amsa,bai ƙara cewa komai ba sai
ya je ya zauna kan kujera yayin da ita kuma Zuly ta je jikinta na ɗan rawa ta fara zuba masa
abinci tana gamawa ta zo ta kama hannuna tare da jana muka koma can ɗakina.Bayan ta rufe
ƙofa sai ta ja ajiyar zuciya,ni kuma na ce “wane ne kuma wannan?”
Cikin ƙasa da murya ta ce “mijina ne,ki bari daga baya zan yi miki bayani” tana gama faɗar haka
sai ta fice ta bar ni sake da baki ina mamakin kenan Zuly tana da aure amma ta rasa wanda za
ta aura sai babban mutum kuma irin mai zafin kai.
Bakin bed na zauna ina tunanin ni ma ai lokaci yayi da zan bai wa maza dama ,saboda can
baya gani nake in ba aiki na samu ba to fa ba zan taɓa kula namiji ba.
Tsawon lokaci ina wasiƙar jaki kafin Zuly ta shigo ,“ taso mu ci abinci” ta faɗa .Tashin na yi na
mara mata baya,ita ce ta zuba mana sai da muka fara ci sannan ta soma bani labarinta.
“Lubna kamar yadda kika sani ba duk abin da mutum yake so yake samu ba,to ni ma hakan ce
ta faru da ni.Bayan mun kammala karatu na fara neman aiki ,duk inda na je babu nasara sai na
samowa kaina mafita wato ita ce ta auren miji mai kuɗi shine fa na auri Alhaji ” tana kawowa
nan ta yi shuru ban matsa mata da sai ta ƙara cewa wani abu ba lura da yadda take bani labarin
a takure.Bayan mun gama cin abinci daga nan kuma kamfani muka wuce,kafin nan bisa hanya
sai da ta ƙara gutsura min labarin nata.
“Akwai wani group mai suna sugar Daddy ,a can muka haɗu da Alhaji ta hanyar wata ƙawata na
samun link ɗin.Tun da na tura hotona na gabatar da kaina ya biyo ni pc ya ce na yi masa ban
kuma ja aji ba muka fara soyayya kar ki so ki ga yadda yake yi min batal ɗin kuɗi.Ba a ɗauki
lokaci ba kuma ya zo gidanmu suka yi magana da iyayena waɗanda kafin auren sai da suka
tambaye ni ai dai ina sonsa ko ? Na kuwa ce eh.Amma a zahiri ba haka abin yake ba,kawai
saboda in samu gidan hutu ne yasa na amince da aurensa.Muna yin aure hannunsa ya koma
na jariri hahaha! Ya bar bani kuɗi sai dai fa duk abin buƙata yana zuba min su a store kuma bai
damu ba don na ɗiba na yi kyauta da su,ana haka sai na fara haɗuwa da manyan mata .In an
je biki su yi ta liƙen kuɗi,wata don ta ɓarar da 200k ba wani abu ba ne ,to abin sai ya fara
damuna har na soma tunanin ko rabuwa zan yi da Alhaji .Da na kai wa waccan ƙawata da ta
bani link kokena sai ta haɗa ni da oga” tana kawo wa nan da labarin ta yi parking duk muka
fito,duk da a lokacin na so jin yadda ta kaya amma na yi shiru muka shiga ciki.
Cike da girmamawa aka dinga gaishe ta,direct kuma ofis ɗin oga muka wuce.Yana ganinmu
yayi saurin tasowa ya shayar da ni giyar mamaki don kuwa rungume Zuly yayi ƙyam a ƙirjinsa
tare da feso wasu kalamai waɗanda suka sa na zauna ban shirya ba.
“Ya haka Baby? Na ji an ce mijinki yau yayi saukar asubah,shine ba ki faɗa min ba.Me ya kawo
haka ko yayi miki wani abu ne?”
Ita kuwa ƙoƙarin fizge wa take,tana satar kallona da sauri na kawar da kai.
Ina jin lokacin da oga ke ci gaba da cewa “faɗa min kun yi wani abu da shi ne?”
“A'a ! Please ka sake ni mana ” ta faɗa.
“Luby ki ɗan fita ina son yin magana da Oga” ko kallonsu ban ƙara yi ba na fita,direct kuma ofis
ɗinta na shiga wanda ke kusan na oga.Kaina na ji yana sara min a fili nake tambayar kaina “wai
da aurenta take kula wani? Da aurenta take zina? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Ya Rabb ka
tsare ni daga sharrin zina Allah kar ka jarabce ni da ita,kar ka kuma nuna min ranar da zan yi ta
Ya Rabb kafin ranar nan ta zo Allah ka aiko tirela ta markaɗe ni na huta” haka kawai na ji
hankalina ya ƙi kwanciya da wannan aikin,sai nake jin kamar na je na shaida musu ban so.
Bayan wajen minti talatin ina zaune sai ga Zuly ta shigo ,kallo ɗaya na yi mata na ɗauke kai.
Ta zauna tare da soma magana ba tare da na tambaye ta ba,“sai haƙuri Luby,ni ma na fara
gajiya sai dai ba a komawa baya.Kin ga a ranar da ƙawata ta haɗa ni da oga da farko iya aikin
yi masa lissafi kawai ne nawa,amma sannu-sannu sai ya fara bijiro min da ainahin zuwan
nawa.Cike da tako yayi nasarar kai ni kan shimfiɗarsa har sai bayan komai ya kammala ne na
fahimci kuskurena,don da soyayya ya ɓullo min .Amma yana bani kuɗaɗe masu mugun yawa
sai ya girgiza tunanina,sai kawai na biye masa kusan kullum in na zo aiki muna keɓewa yayin
da shi kuma yake cika min jakata da ƴaƴan banki”
“Ita kuma alaƙar tsafi?” na jefo mata tambayar.
“Shi ne ya bani power ya kuma nuna min yadda ake yin komai”
“To amma me yasa ba ki rabuwa da Alhaji ki auri oga ? Ai hakan ya fi nake gani tunda da
dukkan alamu shi oga kina sonsa”
Wani kallo ta yi min kafin ta ce “ki shirya za mu fita zuwa yawon ƙauyukan da za a soma aiki”
“Aikin me fa?”
“Na gina banɗakunan kan titi mana” ta bani amsa.
Ko da muka fito tuni motar da za ta yi yawo da mu ta zo,haka muka shiga mu da wasu sauran
ma'aikata.Yawo sosai muka yi muna duba wuraren da za a gina banɗakuna,wasu cikin kasuwa
wasu kuma kan titi.Sai bayan sallar azahar muka dawo,Zuly ce ta yi wa oga bayanin komai
kafin ta sauke ni asibiti. Ina shiga daidai nan Abba ya rufe idonsa ya soma bacci,bayan na gaishe da Ummah sai na
zauna na tambaye ta jikinsa ta amsa ana ta samun ci gaba.
Nan na wuni,har dare amma Abba bai tashi ba har likitocin sai da suka yi mamakin irin baccin
nan da yake alhalin ba a yi masa allura ko magani mai sa haka ba.Saƙon Zuly na samu kan ina
iya tafiya gidanmu ba sai na je can gidanta ba,da wannan na yi wa su Ummah sallama na je
can gidan.A daren ne kuma na yi wani mafarki mai matuƙar firgitarwa,ga Abba nan yana kuka
yana kiran sunana yayin da kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya sun ɗora shi kan
garwashin wuta suna gasa shi tamkar wani tsire.
A firgice na farka wanda yayi daidai da kiran Zuly,“ki fito ina ƙofar gidanku” shine abin da ta faɗa
min ta kashe wayar.
Cike da mamaki na duba lokaci,ƙarfe biyun dare ne.Amma haka na fita na same ta cikin
mota,ina shiga ta fizge ta kuwa ta soma yin gudu kamar za ta tashi sama tambayar duniya
kuma ta ƙi bani amsar abin da ke faruwa .
Gidanta muka wuce,tana yin parking duk muka fito hankali tashe take jan hannuna zuwa
ciki.Wannan dai ɗakin muka shiga wanda na yi laƙabi da ɗakin sirrinta,ko da muka shiga sai ta
buɗe madubinta ta tsaga yatsanta jini ya soma zuba ta kamo nawa da niyyar tsaga shi kenan
mijinta Alhaji ya shigo ɗakin yana salati tare da jefo mata tambaya “Zulaihat tsafi cikin gidana?
Dama ke MATSAFIYA (Mrs SADAUKI) ce ban sani ba? Ai kuwa yau...” bai ƙarasa kai ƙarshen
maganarsa ba Zuly ta jefa wuƙar hannunta tare da furta furucin tsafi nan take wuƙar ta sauka
daidai tsakiyar ƙirjin Alhaji a nan take ya faɗi jini na yi masa malala......
My book is only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[02/04 12:10] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
07
Ban taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba,kisan kai ne aka yi a gabana ga gawa kwance cikin
jini.Tsabar ruɗewa da na yi yasa na soma zagayen ɗakin ina ihu,yayin da ita kuma Zuly ta soma
tsafe gawar tana barbaɗa mata wata hodar tsafi kafin ƙyaftawar ido gawar ta ɓata ko kumfan jini
babu,a wannan lokacin ne na ƙara ganin bala'in da na tsoma kaina a cikinsa.Zuly ta nufo ni da
niyyar kama ni amma na yi tsalle na koma can gefe ,idonta ta juye tamkar wata zakanya kafin ta
soma yi min magana cikin wata irin murya “Luby ki zo mu wuce ba mu da sauran lokaci,in kuma
kika jinkirta duk abin da ya biyo baya babu ruwana”
Ina kuka ina ƙari na ce “amma Zuly kisan kai fa kika yi,mutum ne fa kika kashe kuma mijinki”
“Babu ruwanki da wannan matsalar ki zo mu wuce” ta yi furucin tare da yin tsalle ta zo ta cabko
ni muka tashi cikin iska kafin mu ratsa ƙofar da ke cikin mirror.
A wani ɗaki muka bayyana,da na duba da kyau sai na ga wancan dai ne na ƙasar waje.Duk
yadda na so na bijiro da zancen kisan kan da ta yi ta hana,a gaggauce ta tirsasa ni na shirya
cikin kayan arna kafin mu fito.Yanzu ma buɗe mana mota aka yi muka shiga ,muna tafe ina
duban hanya sai na ga wata ce aka ɗauka ba waccan ba.Mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu
isa, wannan karon a tare muka shiga ɗakin taron mai ɗauke da ɗumbin jama'a daga ƙasashe
daban-daban.Ciki kuwa har da oga shi ma ya haɗe cikin wasu baƙaƙen suit kamar sauran
mazan,wuri muka samu muka zauna oga ya dubo inda muke zaune fuskarsa ta nuna alamun
damuwa.
Can kamar minti biyu wani zabaya ya fito sanye cikin jajayen kaya kansa ya ɗora wata hulla
kamar ta sheɗan,gashin kansa da idonsa duk wasu iri ne kamar wani makaho haka ya
ƙanƙance su yana ƙarewa kowa kallo ,da ya zo kaina sai ya tsayar da dubansa gare ni.Gabana
ne yayi wani irin mugun faɗuwa ,so nake na kauce idona amma tamkar wacce aka yi wa
dabaibaye na kasa.
“Mansoor fatan ka yi wa ɗalibarka bayani?” shi ne abin da ya faɗa .
Muryar oga na ɗan rawa ya ce “a'a tukuna dai Boss ”
Bai ce komai ba sai ya zauna kan kujerar ya soma yin wasu maganganu da ban gane su ba
saboda kogin tunani da na abka,ban farga ba sai da na ji Zuly ta zungure ni sai na dawo
hayyacina nan kuma na ƙara jin wani zancen banza wanda kuwa hankalina ya kasa ɗauka.
Oga ne ke bayani kamar haka “Luby a family muna da wata ƙa'ida,babu virgine a tsarin
tafiyarmu in ma ta shigo to dole a yi amfani da ita don kawar da budurcinta.In irin wannan
damar ta samu to Boss ne yake yin wannan aiki ,kamar yadda tsarin yake zai yi amfani da ke a
gaban dukkan family bayan nan kuma sai ki karɓi zoben ƙarfin iko da kuma madubinki wanda
zai sauƙaƙa miki yin balaguro zuwa ƙasashen duniya da kuma in an tsara meeting”
Wata irin bazawarar dariya na yi,don abin jin shi na yi kamar wasar kwaikwayo sai na miƙe
tsaye kamar mahaukaciya ina mai ci gaba da yin dariya kafin na ce “wato na basa budurcina?
Akan wane dalili kenan? To ba zan yi ba,sai dai ku cire ni daga cikin family ɗin amma ba zan
taɓa aikata zina ba”
Da wani mugun sauri oga ya zagayo ya zo inda nake ya kama kafaɗuna ya ce “ Luby wannan
dolenki ne! Kin ga ki ajiye hankalinki babu fa wata matsala sau ɗaya tak ne zai yi shi kenan ”
Hawaye suka zubo min masu ɗumi,ji nake kamar na shaƙe wuyan oga har sai ya mutu na sake
shi .
“Na bata nan da sati ɗaya,ta je ta yi shawara don ina da ayyuka masu muhimmanci a gabana
kowa zai iya tafiya” Boss ya faɗa tare da miƙewa ya koma hanyar da ya fito.
Nan kowa duk ya watse,Zuly ta kama hannuna muka fito muka bar oga can.Har muka isa gida
tana yi min nasiha haɗi da shawarwarin banza wanda in sun shiga kunnena sai su fita ta ɗayan
kunnen,sam ban ji zan iya yin abin da suka ce ba.
Na yi tunanin da zarar mun je za mu koma can Kamaru ne,amma sai na ji wata sabuwa wai zan
sake yin wani zama da mutanen da na tallata musu hajarmu.
Cikin bahon wanka na shiga na lumshe ido,tunanin iyayena da kuma abubuwan da suka faru
suke ta min yawo a kwanya.Har sai da ruwan suka huce na zuba wasu sannan na yi wanka na
fito,cikin kayan bacci na shirya sannan na kwanta sai dai fa na kasa yin baccin haka na yi ta yin
juyi bisa gado.Can sai ga Zuly ta shigo hannunta riƙe da ƙaramin tray ,tashi na yi zaune ita ma
ta zauna bakin gado tare da miƙo min kofi ɗaya na madara ita ma ta fara shan guda.
“Wacce shawara kika yanke ?” ta jefo min tambayar.
“Game da me fa?” ni ma na tambaye ta.
Da ɗan mamaki ta dube ni kafin ta ce,“maganar Boss ɗin ce kika manta?”
“Shi wane ne?” ban ida rufe bakina ba kofin da ke riƙe da hannuna ya tarwatse har sai da
kwalba ta shige min hannu nan take jini ya soma zuba.
Jikin Zuly ya ɗauki rawa,sai ta dubi madubin da ke a ɗakin kafin kuma ta taimaka min ta tsayar
da jinin ta naɗe min shi da bandeji.
Sosai na tsorata ban taɓa tunanin Boss nada power har haka ba,don babu tantama shi ne ya
tarwatsa kofin.A tsorace nake kallon Zuly kafin na ce “don Allah ki mayar da ni gida”
Muryar Boss ta fito ɓaro-ɓaro ta cika ɗakin “duk inda za ki je ba za ki taɓa boyewa ganina ba,na
soma bibiyarki kenan”
Da sauri na rungume Zuly ,sai aka ƙwanƙwasa ƙofa ita ce ta bada damar shigowa.Ƴar aiki
ce,cikin Yaren turanci ta ce “oga na falo yana jiran ku ” tana gama faɗa ta fice.
After dress na ɗauko na ɗora a sama kafin mu fita falon,Oga na zaune ya hakimce fuskar nan
kicin-cikin kamar za ta tsage.
Na sunne kai tare da samun wuri na ja na tsaya ganin irin mugun kallon da yake jefo min.
“Zuly kin ga saboda ke ina shirin samun matsala da Boss ? Ta ya za ki kawo wacce kika san za
ta kawo mana cikas? Faɗa min wace shawara kuka yanke yanzu?”
“So take mu koma Kamaru,kuma ni ma na ga kamar hakan zai fi.In mun je can za ta fi samun
damar yin tunani in tana ganin Abbanta ” Zuly ta faɗa ,ban san dalilin da yasa ta kawo Abbana a
cikin wannan lamari ba.
Oga ya ce “babu matsala za ku iya komawa,amma ki bari har zuwa gobe don yanzu haka an
tsinci gawar mijinki ƴan sanda sun soma yin bincike.Kin ga in suka biyo ta kanki za su samu ba
ki ma ƙasar,kuma in kin je ki nuna cewa