Showing 21001 words to 24000 words out of 44681 words
Chapter 8 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki
an yi wa wurin mugun riƙo,ban tanka shi ba na fita.Ina
fara taka step na ga Lubna a tsaye tana kallon benen wanda yake ɓangaren Maheer ne,a cikin
idonta nake hango wasu abubuwa da suka haɗa da zargi da kuma mugun kishi amma ban kula
ta ba na wuce part ɗinmu.
Sai da zan shiga toilet ne na lura doguwar rigar baccinsa a jikina,na kwance ɗaurin na jefar da
rigar amma abin mamaki sai ta ƙi taɓo ƙasa.
Ban san lokacin da na furta “matsafi kawai” sai kuma na ɗauki rigar na ajiye ta cikin jakar
kayana.Bayan na shiga toilet na cire kayan jikina,ina wanka amma ƙamshinsa ne ke
tashi.Bayan na gama wanka na zo na gabatar da sallar asubah wacce ta wuce ni don tuni ƙarfe
bakwai ta buga.
A gaggauce na kimtsa cikin kaya masu kyau sannan na ɗauki rigar da nake ɗorawa a sama mai
sunan Hajiya da kuma restaurant ɗinta.
Ko da na fito tuni an jera komai a mota,cike da ladabi na gaishe da Hajiya .Yadda na ga Lubna
na kauce min yasa ban takura ta ba akan sai mun yi magana,a yau tare da Aliya za mu je a nisa
umarnin Hajiya hakan yasa muka shiga mota muka wuce can.
Bayan an gama jera komai a wurinsa sai kuma na fito nan inda ke teburan cin abinci na ƙara
gyarawa,babu jimawa kuwa mutane suka fara zuwa Aliya ta dinga taya ni aikin har muka samu
ƙafa ta ɗan tsana sai na zuba abincin da za mu ci,sai kuma a lokacin na dube ta da kyau na ce
“Aliya don Allah me ya faru a jiya a gidan Hajiya na kasa tuna komai,kawai dai na tashi na tsinci
kaina a ɗakin Alhaji ”
Dama tun tuni na lura ita ma da magana a bakinta,kawai dai ta yi shiru ne.
Aliya ta ce “to mu dai mun tashi ba mu gan ki ba,shine Anty Lubna ta je ta sanar da Hajiya ita
kuma tana shiga ɗakin Maheer don sanar da shi ta tarar da ke a gadonsa kina bacci sai ta yi
kururuwa duk muka haura sama kafin kuma mu iya cewa wani abu shi Alhajin ya fito daga
wanka dole muka fita waje saboda mugun kallon da watso mana.Amma ni ma ban san me ya
faru ba,na dai ji Anty Lubna na cewa kin ci amanarta kin je ɗakin Alhaji alhalin kin san tana
sonsa,kuma wai don kawai ta yarda da ke ne shi yasa jiya ta bamu labarin cewa sperm ɗinsa
ne ta kai a madadin na Dr David ”
Kaina ne na ji yayi wata irin sarawa,ɓacin rai ya ƙara dirar min.Tsakanin jin sperm ɗin Maheer
ne Lubna ta yi amfani da shi,da kuma jin zargin da take min sai na rasa wane ne ya fi yi min
ciwo.
Abincin na ji ya fita raina,na miƙe na wanke hannuna.Kuka nake son yi don samu salamar zuci
sai dai ina fitowa idona yayi tozali da wata mai ciki tana aman jini duk ya ɓata teburin da ke
gaban kujerar da take zaune,hankali tashe na nufe ta sai dai tana ɗago idonta na tsaya cak
sakamakon abin da ya gigita ji da ganina.....
My book is only 500 amma na yi discount daga yanzu zuwa kafin na saki page 10 ta ƙarshen
free.ki tura 300 ta wannan account 2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBABK sai ki turo min da shaida biya +22795045822
Wacce ba ta shirya ba don Allah kar ta yi min magana
[06/04 14:24] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*
```LoVe aNd HoRrOr story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.
*FCWA*☀️
________________________
Last free page 10
Fuskarta ta yi wani irin ja kamar za ta tsage jini ya zubo,ga idonta da suke baƙi ƙirin sam babu
hasken nan.Bakinta kuma jini ne shaɓe-shaɓe yana mai ci gaba da ɓulɓulo mata.A kallon
tsanaken da na yi mata duk ta yi gudu ba za ta haura shekara ashirin da biyar ba,sam kasa cira
ƙafata na yi daga inda nake sai ita ce ta yunƙura ta taso ta zo tare da zubewa gabana.Yatsun
hannunta na taɓa ƙafata na ji wani irin yanayi ya ratsa ni,yanayi ne wanda na taɓa shiga irinsa
lokacin baya shi ma ba zan taɓa mata wannan mummunar ranar ba.
Yawun bakina ne na ji sun fara taruwa da kansu kafin su soma ɗiga suna sauka kanta tamkar
ana zubar da ruwan pampo ko kuma ana yayyafi.Zafin hucinta da fitar numfashinta shi ya cika
wurin tamkar wacce ake zarar ranta,ƙila shi ya jawo hankalin Aliya ta fito daga can ɓangaren ta
zo nan.
“Ƙwayar cutar BAƘIN RUHI,Haule ki ja baya mana contact da ke yana iya haifar da tsayawar
numfashinta” Aliya ta faɗa tana mai jawo ni baya,sai a lokacin na ji wani irin raɗaɗi a ƙafata
daidai wurin da ta ɗora yatsun hannunta da na kai duba wurin sai na ga tamkar an zuba min
acid ne tuni ya wani kumburo ga wata uwar azaba da nake ji.
Na yi baya na samu kujera na zauna,yayin da Aliya kuma ta soma juya hannunta mai ɗauke da
ƙarfin iko na power nan take ya kawo haske tare da bayyanar da wani dunƙulalen haske sai ta
cillawa wannan mai cikin shi sai ya zagaye ta sai a lokacin ta nufo ni ta tsuguna ta kamo ƙafata.
Hankalinta na ga duk ya tashi,ni kuma na ce “kar ki damu zan warke hakan ya taɓa faruwa da ni
ai.Amma me yasa kika jefa mata wannan hasken?”
“Ɗaure ta ne na yi ta yadda ba za ta iya motsawa ba,haka shi ma dafin jikinta zai tsaya da aiki
don yana dab da raba ta da rayuwarta.Yanzu dai bari na naɗe miki ƙafarki,sai mu tattauna
yadda za a warkar da wannan baiwar Allah ”
Wani tissu ta samu ta ɗaure min ƙafa,na tashi tsaye kan ƙafafuna ina kallon mai cikin wacce ta
zama kamar gumki ta kasa motsi.
“Mene ne ke damunta Aliya?”
“Ya za a yi mu samo maganin cutarta ita ce tambayar da ya dace ki yi Haule,kar ki bari
kuskuren da kika yi baya ya sake maimatuwa ” ina jin furucin da Aliya ta yi sai na yi saurin
dubanta,ta jinjina kai kafin ta ce “na san antynki ai,kar kuma ki tambaye ni ta yaya yanzu mafita
za mu nemo kuma ke ce za ki jagoranci tafiyar”
Na ja wani gwabron numfashi kafin na ce,“dole sai na samu labarin mafarin abin da ya haifar
mata da wannan cutar”
Shiru Aliya ta yi kafin ta ce “in haka ne muna da buƙatar madubi ko da ɗan guntu ne”
Ban kai ga yin magana ba aka shigo,Lubna ce da sauri na nufe ta sanin kullum tana yawo da
madubi a jaka.
“Yawwa don Allah ki bamu aron madubinki” na faɗa .
Inda mai cikin take a durƙushe ta duba kafin ta zuge zip ɗin jakarta ta miƙo min,sai na je kusan
Aliya na tambaye ta “ya za a yi yanzu?”
“Ki je saitin idonta ki haska madubin za ta yi magana sai mu ji” cewar Aliya .
Dukka mu ukun muka yi tsaye,suka saka ni a tsakiya yayin da na daidaita madubin ita kuma
Aliya ta yi amfani do powerta ta ɗago kanta sai a lokacin na yi mata magana “Wace ce ke?
Mene ne dalilin shigarki wannan halin?”
“Sunana Meelat,ƴa ga masu matsakaicin hali,ba mu da kuɗi amma muna da rufin asiri.Na yi
karatuna a makarantun gwamnati har Allah yasa na kai matakin University,ina shekara ta biyu
yanzu haka.Tun zuwana can na ga yadda rayuwar jami'a take yadda ake challenge ɗin sutura
da kuma wayoyi.To dama tun can farko ina sha'awar rayuwar luxery,ina da babban burin shiga
mota ,zuwa gidajen cin abinci na manyan mutane da sauransu.Kwatsam wata rana na fito daga
jami'a zan je wurin gyaran gashi wata rantsatsar mota ta parker a gabana,a hankali ya sauke
madubin motarsa wanda yake baƙi ƙirin ɗin nan.Wani babban mutum ne na gani cikin shiga ta
alfarma,fari ne shi tasss mai kyau mai gayu wannan yasa ban wani ja aji ba da ya nemi ya rage
min hanya.Sam ban yi duba da ya haife ni ba ko kuma kusan yin jika da ni ba,abin da ke
gabana kawai kuɗi.Shi ya biya kuɗin da aka gyara min gashi da aka gama min kuma na kira shi
ya zo ya ɗauke ni kamar yadda ya buƙata ya bani lambar wayarsa.Kafin ya mayar da ni can
jami'a sai da yayi min shopping kuma ya faɗa min ƙudirinsa na sona yake,nan fa muka fara
soyayya ko sau ɗaya bai taɓa kai hannunsa jikina ba tsawon watanni uku muna tare kuma
komai nake so yana yi min.Ni da ƙawayena mun mayar da shi atm ɗinmu,a takaice dai sai da
muka kwashe wata biyar kafin ya gayyace ni gidansa ya ce yana yin birthday na zo mu yanka
cake sai na koma sannan kuma sai na duba gidan in yayi min nan zai ajiye ni in mun yi aure
.Haka na je can gidan nasa mai kamar aljannar duniya inda ake parker motoci ma kawai abin
kallo sannan akwai motoci iri-,kamar baƙauya haka na yi ta kallon har muka wuce can falonsa
ashe ban ga komai ba don cikin ya fi haɗuwa.Ya nuna min kujera ya ce na zauna zai yi sallah
ya dawo.Duk da a lokacin bai wuce ƙarfe biyar na yamma ba amma ban tambaye shi sallar
mece ce zai yi ba kawai abin da na ɗauka mutum ne mai addini.
Daga inda nake a zaune ina ɗan jin sautin muryarsa yana karatu,amma dai ba na Alkur'ani ba
ne cikin wani yare ne yake yinsa.Kamar minti goma haka sai ya fito jikinsa sharkaf da gumi har
goshinsa na ɗigar da zufa,hankali a ɗan tashe yake cewa “babyna zo! Taso zuwa gare ni,
please ina son ki yi min wani taimako ni kuma na yi miki alƙawari zan mallaka miki key ɗin mota
da gida da duk abin da kike so.Lokacin da yayi wannan furucin na yi tunanin sex ne zai nema
wurina sai duk ban damu ba don na taɓa yin aure ballantana na ji tsoron rasa budurci kuma a
shirye nake na biya masa buƙatarsa duba da hidimar da yake yi min,nan take na ce masa na
amince in dai gaske zai ban motar.Sai ya kama hannuna muka shiga ɗakin nan da ya fito,babu
komai a ciki sai wani ƙaton akwati a tsakiya yana buɗe shi na yi tsalle na ja da baya .
Ba komai ne cikin akwatin nan ba sai gawar wata mata har ta bushe da alamu ta jima da
mutuwa.Jikina ya ɗau kyarma,sai ya soma kwantar min da hankali yana cewa “kar ki wani damu
baby kawai ciki za ki shiga kwanta na tsawon minti ɗaya kacal sai ki fito.
Soyayyata da abun duniya yasa na yarda na kwanta a tsorace,kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa
babu jimawa na fito sai ya bani maƙudan kuɗi waɗanda ni kaina ban san yawansu ba kuma ya
mallaka min ɗaya daga cikin motocinsa da kuma gida.Tun bayan da na koma can in na kira shi
wayarsa ba ta shiga,da farko ban damu ba sai satin da ya wuce da na soma ganin cikina na
kumbura yana zama ƙato in kuma na yi tari sai jini yayi ta ɓulɓulowa na yi yawan asibiti har na
gaji amma likitoci ba su gano abin da ke damuna ba.Har gidansa na je amma yana rufe da ɗan
kwaɗo ,maƙwabtansa kuma sun ce yayi tafiya.Yanzu ma daga can nake saboda na ji labarin
yau zai dawo amma kuma bai zo ba,da zan wuce ne na tsaya don in ci abinci saboda yunwar
da nake ji sai kuma na soma yin tari haɗi da aman jini” tana kawowa nan na tashi daga
gabanta.
Ina mai kallonsu,Aliya ce ta soma magana “ina ga yayi amfani da jininta ne don bunƙasa
arzikinsa ”
Lubna ta karɓe da cewa “a'a bana tunanin domin kuɗi yayi hakan,don in don su ne to zai nemi
yayi sex da ita ne ko kuma ya nemi ta basa jinin period ɗinta tabbas sai dai don wata manufar”
Bayan duk na saurari jawabansu sai na ce “in dai ba don kuɗi ne ba to tabbas da buƙatar mu je
can gidan nasa”
“A'a zuwa gidansa ba shi ne mafita ba,neman taimakon ƴar aike dai ya kamata mu yi” cewar
Aliya tana dube-dube.
Na ce “wace ce kuma haka ?” ba ita ta bani amsa ba,Lubna ce ta ce “duk wata power ko
ƙungiya akwai shugabanta Haule ”
“Ina za mu samu tukunyar laka?” Aliya ta tambaya.
“Ko a kasuwa za a samu,me za a yi da ita?” na tambaya.
“Ku fito mu je kafin wasu costumer su zo .Haule rufe ko ina,mu tafi” Aliya ta faɗa ,duk yadda na
so yin tambaya kuma Lubna ta hana haka muka rufe restaurant muka nufi kasuwa tukunyar
lakar muka saya kafin kuma Aliya ta ja mu can wani guri mai ƙazanta.
“Ku rufe idonku ” ta bamu umarnin da na so yin gardama amma tuna halin matar da muka baro
yasa na yi yadda ta ce.
Wani irin hayaƙi na ji ya turnuƙe min hanci yayin da Aliya kuma ke karanto wasu abubuwa
maras kan gado.Yanayin yadda iskan shaƙata ya canza yasa na buɗe ido,cikin wani
ƙasurgumin daji ne muke duba da labarin da Lubna ta bamu sam ban yi mamakin hakan ba.
“Wannan shi ne ƙasurgumin dajin AOKIGAHARA,ana yi masa laƙabi da dajin fatale da
dodanni.Duk wani da ke son kafa ƙungiyar asiri to dole sai ya biyo ta nan domin samun albarka
aljanai da kuma tabarakin manya-manyan mashahuran matsafa waɗanda suka taka rawar gani
wurin zalunci.Kamar yadda kuke gani dajin ya rabu biyu, wannan shi ne tafarkin haske masu
kula da fararen ruhika kuma masu kyautar ƙarfin iko na power,to mu can ne za mu je” Aliya ce
ta yi jawabin tana mai nuna mana wata ƙofa wacce wani ƙaton icce mai kan mutum ya raba
tsakanin hanyoyin biyu ta sharri da kuma ta khairan.
“Kina nufin BAƘIN RUHI ya samo asali ne daga wannan hanyar kenan?” na tambaye ta ina mai
nuna ƙofar wacce ke cike da tarnaƙin hayaƙi da duhu.
“Wannan amsar ai ke za ki bamu ita Haule saboda maɗaukakiyar ceto da ke a jikinki” Aliyar ta
faɗa tare da yin gaba,muka take mata baya ina mai juya kalmar ni ce ke ɗauke da
maɗaukakiyar ceto a jikina.
Can cikin muka lula kafin mu samu wani keɓaɓen wuri mu zauna,ni ce a tsakiyarsu kamar
yadda Aliya ta ce na yi.Bayan duk mun zauna sai muka ajiye tukunyar lakar a tsakiyarmu,yawun
bakina na tofa a ciki sai wani irin haske ya soma bayyana daga can ƙasan tukunyar .Gaba na
ɗan yi da fuskata na leƙa ciki,da wani mugun sauri na dawo baya sakamakon fuskata da na ga
ta rabu biyu.Ɓangaren hagu fuskar Maheer ce yayin da bangaren dama kuma yake tawa,ban
san me hakan ke nufi ba sannan kuma ban tambayi Aliya ba wacce tuni ta soma kiran sunaye
barkatai sam ban aje hankalina sosai ba tunanin Maheer ne ke yi min yawo a zuciya.
“Ban san mene ne matsalar ba ƴar aike ta ƙi bayyana a gare mu,Haule ko da wani saƙo da aka
isar miki zuwanmu?” tambayar nan da Aliya ta yi min ya katse min tunanina,na girgiza mata kai
na ce “a'a babu wani saƙo da aka isar min”
Yanayin fuskar Aliya ya nuna rashin jin daɗi,sai ta miƙe ta ce “ku tashi mu tafi ba za ta zo
ba,ban san kuma me yasa ba” haka muka fito daga ɓangaren ba tare da na yi tunanin cewa
hoton da aka nuna min na fuskata ta tsage gida biyu sannan ta haɗe da ta Maheer shi ne
makullin nasarar da muke tunkara ba.
Da muka fito Lubna ta ce “ amma Aliya ita wannan hanyar fa? An hana a shiga ne ko da
haɗari?”
“A'a ko ɗaya,sai dai ita tana da sharuɗa ne masu tsauri shi yasa ba kowa ke son shiga ba.Kin
ga muddin mutum ya shiga to ko ya ga abin tsoro bai da ikon yin ihu ko ƙara,sannan duk abin
da za ka gani iya kallo ɗaya ne kacal za ka yi masa ka ɗauke idonka a kai,sannan ko ƙasar cikin
wurin ba a yarda ka ɗebo ba ballantana furanni ko wani abu da ke ciki” Aliya ta faɗa .
“Haule zo mu je mu shiga mu gani ko ba komai za mu ƙara ilimi”Lubna ta faɗa tana wani kamo
hannuna,haka kawai na ji gabana na dokawa amma na daure na yarda muka shiga .
Tun a bakin ƙofa wani irin iska mai zafi ya dake min,kuma tamkar an zuƙo mu ne ba tafiya muka
yi da ƙafafuwanmu ba haka na ga mun yi saurin shiga tsakiyar wurin.Wuri ne mai cike da
furanni masu tsantsar kyawu wanda ya ɓoye sharrinsu da kuma gubar da ke ɗauke da shi.Muna
tsaka da tafiya muka dinga jin kukan jarirai,Aliya ce ta yi mana bayanin dalilin kukan.
“Dayawan matan da suka rasa rayukansu suna ɗauke da ciki su ne in sun shigo nan suke haife
cikin,wani sa'in jariran na rasa madarar da za su sha ne to in sun ji ƙamshin bil'adama ne sai su
fara kuka.In da mace mai shayarwa to haka za ki ga madara na ta ɗiga daga mamanta tana
shigewa ƙarƙashin ƙasa” ina gama jin bayanin nan sai wani tsoro ya kama ni,duk gani nake ni
ma hakan na iya faruwa da ni duk da kuwa ni