Showing 3001 words to 6000 words out of 44681 words

Chapter 2 - Bakin Ruhi Book Compelet By Mrs Sadauki

yake ramewa ita ce duk ta cinye shi masifafe Allah ma ya raba ki da
aurensa,don wannan ina ga har dukan mace sai yayi”

Lubna ta ƙyalƙyace da dariya ta ce “mutumniyata inda fa kike burge ni ke ɗin kamar yayen
aljanu kike,to in faɗa miki jiya-jiyan nan ya ɗirka wa buduwarsa shegen duka saboda ya tarar da
ita tana hira da wani ɗan ajinsu.Ina jin Hajiya na bai wa uwar budurwa haƙuri wai shegiyar
zuciya ce da shi wannan yasa bai controling kansa”

Ban san me yasa na ji zuciyata ta yi min wani iri ba duk sai na ji babu daɗi,na ce “budurwa?
Dama yana da budurwa ne?”

“Kin ji ki da wani zancen kuma,kamar Maheee ɗin ne zai rasa budurwa? Hum! To in faɗa miki
shegen son mata ne da shi a yadda na ji Ummah na faɗa ƴan matan da yayi ba su da iyaka,in
kin gansa da wannan yau to da an kwana biyu ya canza wata”

Cike da ɗacin rai na ce “amma kuma bai yi kama da mai son mata ba,duba da ko kallon su bai
yi.In fa kin ga ya kalle ki to fitinarsa ce ta motsa kawai don ya tsorata ka da shegun idonsa
kamar na jinjirin jinnu”


Lubna ta ce “ki shirya wata rana mu je asibitin da yake aiki ki ga yadda mata ke ɗaukar wanka
saboda shi,kuma wallahi har da matan aure”

Ban ƙara ce mata komai ba na yi gaba don dama can tsaye muka yi muna ta zuba,sam ban ji
wuyar tafiyar ba saboda yadda zuciyata ke azalzala tana wani irin zafi .Ban taɓa jin haushinsa
sosai kamar irin na yau ba,kamar wasu kurame haka muka ci gaba da tafiya har muka isa
gidansu Lubna.
A tsakar gida muka tarar da Ummah tana gyara wake,bayan mun gaishe ta sai muka shiga
daga ciki.Kan katifar da ke shimfiɗe na yi wa kaina masauki na kwanta tare da yin
lamo,maganganu Lubna ta kai wa junansu karo a cikin kwanyata.

“Bari na yi wanka,kin ga kunun tsamiya nan ki zuba ki sha” ta faɗa kafin ta fice,sai dai a yadda
ta bar ni haka ta same ni.Cike da mamaki take cewa “wai ba ki sha kunun ba?”

Na ɗan yamutsa fuska na ce “ban ra'ayi ne”

Ta taɓe baki kafin ta ce “ke ma ai jujun ce kamar Maheer ba a gane kanki wani sa'in ni dai ci
gaba da bani labarin naki ”

Na ja ajiyar zuciya kafin na ce “zan baki har mu koma can gidan Hajiya ”

“Ni dai ki fara bani yanzu”


Na ce “a daren ranar muka faki idon Goggo Lami muka je ni da Hassana muka binciko kayan
Husseina waɗanda suke ajiye ko tsinke ba a taɓa ba.Kayan da ta mutu da su wata doguwar
rigar atamfa ce,tana mugun sonta wanda kusan tana yawan saka su wannan yasa har zuwa
lokacin ba mu manta ta ba.A nan cikin ɗakinsu Hassana na saka rigar sannan na hauda tawa a
sama,sai na mayar da hijabina.Waje muka fita kamar babu komai muka zauna cikin ƴan
uwanmu muka ci abinci kafin duk a watse saboda yau babu wata hira mai daɗi da za mu yi in
banda ta jajen mutuwar Haidar .
Ko da na je ɗakinmu sam ban cire hijabi ba da shi na kwanta,babu jimawa kuwa bacci ya ɗauke
ni.A cikin baccin na ji ana buga ƙofa tare da kiran sunana,na buɗe ido sai na yi tozali da
Husseina sanye cikin kayan matattu wato likafani.Idonta na zubar da hawayen jini take
kallona,kafin ta ɓace ba tare da ta ce min komai ba...” Lubna ta yi saurin katse ni “wai a zahiri
kika gan ta?”

Na ɗan harare ta na ce “ke fa ba ki iya cin ƙwan makauniya ba,ki bari na baki labarin mana”

“To na bari” ta faɗa tana gyara zama.

Ni kuma na ci gaba da cewa “daidai nan na farka daga bacci sai na fahimci mafarkinta ne na
yi,wanda kuma hakan ba ta taɓa faruwa da ni ba in ba yau da na saka kayanta ba.A lokacin
wani irin tsoro ne ya kama ni sai na kasa yin bacci,don da zarar na rufe ido Husseina nake gani
tsaye kusan ƙafafuna da fararen kayanta .Ƙwan lantarki na kunna saboda tsoro,ɗakin ya kawo
haske sai na ga Innarmu zaune a tsakiyar gado ta yi tagumi da dukkan hannuwanta yayin da
kuma hawaye ke yi mata shatata kamar an kunna pampo.Na matsa kusa da ita na ce “Innarmu
kuka kike? Ki yi haƙuri don Allah ki bar kuka in kina yi hankalina tashi yake” ban san me ya ja
ra'ayin Innarmu a wannan lokacin kawai dai na ji ta jawo ni tare da rungume ni tana mai cewa
“Haule ina son nesanta ki daga gidan nan amma banda ƙarfi ko izzar yin haka,na sani ke ce ta
gaba”

“Ta gaba kamar yaya? Innarmu wai mene ne kike son faɗa min?” na tambaye ta duk da a
lokacin ba zan wuce shekara goma sha biyu ba amma na fahimci kamar da akwai wani sirri da
Innarmu ke ɓoye min” ina kawowa nan sai na yi shuru ina goge ƙwallar da ke yi min zuba
saboda wata irin kewar mahaifiyata da ta tsirga min,na miƙe na ce “zan tafi sai kin iso”
“Jira na saka kaya mu koma tare” ta faɗa ita ma duk idonta sun yi ja,bayan ta kimtsa muka yi wa
Ummah sallama muka dawo gidan Hajiya sai kuma muka tarar da wani sabon tashin hankali
Maheer ne a kwance duk ya sandare kamar gawa ga kuma likita biyu kai gare shi.Ni da Lubna
muka kalli juna don kuwa tuni muka san mene ne matsalar,da kuma maganin da zai warkar da

shi.....
[07/03 17:32] MRS SADAUKI: *BAƘIN RUHI*


```LoVe aNd HoRrOr story```


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan iyayenmu MATA da suka tsaya tsayin daka don bamu kariya a
kan dukkan wani da ke son cutar da mu.


*FCWA*☀️

________________________

03


Daga inda nake tsaye muke ƴar kallon-kallon ni da Maheer,kallo ne yake yi min wanda ke nuni
da cewa eh ya san komai a kaina.A yadda yake juya idonsa tuni na fahimci abin da ke
zuciyarsa,magana yake yi min ta ido wacce kuma sarai nake jin abin da yake cewa tamkar da
bakinsa ne yake magana.

“Ki zo ki cire min ƙwayar kambun maitarki da kika jefa min ,in kuma mutuwata ce farin cikinki shi
kenan sai ki ci gaba da riƙon inuwata da kika damƙe”

Ido na lumshe bayan na gama sauraran abin da ke fito wa daga idonsa,maimakon na basa
amsa ko yi masa zancen abin da ya shafi maganin cutarsa sai tambaya da na jefo masa ni ma
ta ido kamar yadda yayi min ,“wane ne kai ? ” ƙin bani amsa yayi sai ya juyar da kansa gefe.


“Kar dai ki ce min zargina gaskiya ne ke ce kika jefa shi cikin wannan halin?” Lubna ta tambaye
ni tana mai matso bakinta kusan kunnena.“Ki ɗauko kofin ruwa ki same ni a ɗaki” shi ne abin da
na ce mata kafin na yi gaba abina,babu jimawa kuwa ta shigo kofin hannunta na karɓa na yi ta
kallon ruwan na ƴan sakanni kafin na tofa yawuna a ciki suka fara tafasa suna canza kala a
sannu-sannu,sai kuma na ƙara tofa wasu sannan na miƙa mata kofin ta fita.

Na ja wata ajiyar zuciya ina jin duk babu daɗi yadda ya wahala domin ni,duk da cewa ni kaina
ban son hakan nake yi ba na cutar da mutanen da suka ɓata min rai.
Na saki ɗan murmushi a fili na ce “ko wane ne shi? Ta ya aka yi yake magana da ido?” ban kai
ga samo amsa ba Lubna ta shigo tana yi min wani kallo kafin ta ce “sai ki je suna son yin
magana da ke”

Na ce “su wa?”
“Likitocin da suka kasa yi masa magani mana,a gabansu na basa ruwan ya sha ya kuma tashi
daram ya zauna kan ƙafafunsa shine suke son sanin sunan itaciyar maganin da kika yi amfani
da ita”

Banda kallonta babu abin da nake yi,kafin ma na ce wani abu Hajiya ta shigo ɗakin tana washe
baki tare da kamo hannuna ta ce “zo mu je yarinya kin zama cele ai ,manyan likitoci sun kasa
maganin cutar Maheer amma maganinki na gargajiya ya warkar da shi garas.Kar ki so ki ga
yadda na fita a guje neman taxi ni na manta ma da akwai mota a gidan,ina dawowa kuma aka
ce ke ce kika basa maganin” tana maganar ne tana jan hannuna har muka iso falon.


Wani irin faɗuwa gabana yake yi,ga manyan likitocin da duniya ta san da su don har a tv ana
nuno su.Duk sun gyara zama suna jiran amsa daga gare ni,shi kuma gogan ya wani haɗe rai
kamar ba shi ne ya gama shan yawuna ba yanzu.


“Ga ta nan ita ce mai maganin” Hajiya ta faɗa tana wani murmushi kafin ta ɗan bangaje ni ta ce
“ki gaishe su”

A ɗan rikice na ce “ina wuninku?” kusan duk a tare suka amsa kafin ɗayan ya ce “hajiya dama
wannan ce ai kamar na sha ganinta restaurant ” yayi furucin yana wani sanyayyen murmushi
yana ɗan ƙare min kallo.

“Eh ita ce, tana ɗaya daga cikin masu kula da restaurant ɗin ai” Hajiya ta faɗa .

“To likitar gargajiya muna son ganin maganin naki ” ya ƙara faɗa wannan karon cikin raha.
Da sauri na kalli Hajiya kafin kuma na maida dubana ga Maheer wanda nake jin idonsa a kaina
tun ɗazu.

“Eh muna son gani Please ” shi ma ɗayan likitan ya faɗa.

Hannuna na ji yana jimƙewa da kansa,yayin da kuma nake jin muryar Maheer tana furta wasu
harufa cikin Yaren da ba na Hausa ba,haka ma turanci.Kallonsa na tsaya yi yadda sam bai nuna
alamar yana yin wani abu ba,amma tabbas amon muryarsa na fita wanda ina da tabbacin iya ni
ɗaya ce kawai nake jinta. Ba a ɗauki lokaci ba na ji wani abu jimƙe cikin tafin hannuna,sai na ɗago hannun tare da buɗe

shi nan idona yayi tozali da wata koriyar flowers mai masifar haske.


“Waooo! ” likitan ya faɗa yana mai zuwa ya ɗauke flowers ɗin daga tafin hannuna kafin ya ce
“wannan ai furen floris,Dr Muhamud ka tuna Dr Maheer ya taɓa nuna mana ita?”


“Eh sosai ya ce tana maganin komai amma a lokacin ba mu yarda ba,amma Umar ba ka ganin
kamar abin nan camfi ne?”

“Ya isa haka don Allah,ku bata furenta ta tafi kun tsaya surutu sai ka ce yau ne kuka fara ganin
abin almara” Maheer ya faɗa cikin ɗaga murya,duk suka tuntsire da dariya kafin su fara
tsokanarsa can kuma shi Dr Muhamud ɗin ya zo ya miƙo min furen,sai da na saci kallon Maheer
kafin na karɓa.Har tuntuɓe nake wurin barin falon,ina shiga ɗaki na ja wata doguwar ajiyar
zuciya ban taɓa jin tsoron Maheer ba sai yanzu har wani ƙwarjini na ga ya ƙara min.


Ban tarar da Lubna ba, kitchen na wuce don na fi zaton tana can amma kafin nan sai da na
ɓoye furen floris ɗin cikin kayana.Ai kuwa can na same ta tana ta aikin tuwon gobe,wuƙa na
ɗauka na soma yanka mata albasa ba tare da na ce komai ba.Ita ma sai ta ƙi tanka ni sai ma
waƙe-waƙe da ta tsira wanda kusan duk na habaici ne.

Na yi ɗan murmushi na ce “ko ki tambaye ni yadda muka yi”

Ba tare da ta dube ni ba ta ce “ai na san ba za ki kasa nemowa kanki mafita ba tun da kamar
aljana haka kike ”

“A'a aljanar ce ba kama ba” na faɗa ina dariya .
Ta ce “to ƙila ɗin ma haka ne tun da babu wanda ya san abin da ke cikin duhu”

“Amma kin san da cewa na tsorata sosai?” na tambaye ta ina mai tsayawa da yankar albasar.
Ta ce “na san dai ba na Maheer ba sai dai ko abokansa”

“Wai ke duk komai kin sani game da shi? Ya aka yi kika san abokansa ne?” ba ta kai ga bani
amsa ba Hajiya ta shigo kitchen ɗin,wata ƴar matashiyar budurwa na take mata baya.


“Lubna ga sabuwar ƙanwa na samo miki,za ta dinga taya ki aiki ki dinga nuna mata komai
yadda ake yinsa,don ina sa ran ƙara sunayen jerin wasu sabbin abinci”


Cike da ladabi ta gaishe mu duk da dai ko na girme mata ba irin can ba,Lubna ta ce “me

sunanki?”

“Aliya” ta bata amsa sai muka ɗan kalli juna,Hajiya ta ce “mene ne kuma?”

“Babu komai” muka amsa mata.
Har ta kai bakin ƙofar fita ta ce “Haule ki haɗa wa Alhaji tea ki kai masa ɗakinsa ki saka citta
dayawa da lemun tsami”

“Wane alhajin ?” na tambaya da sauri har ina sakin wuƙar hannuna ban shirya ba,Hajiya ta juyo
fuskar nan kicin-cikin kafin ta ce “alhaji nawa ke da kwai gidan nan?”

Sai da na haɗiye wasu yawu kafin na ce “ɗaya” sai kuma ta juya ta yi tafiyarta.Jikina na ɗan ɓari
na ɗora tukunya kan gas na soma haɗa masa tea ɗin wanda dama can ni nake yi amma ban
taɓa kai masa shi ɗakinsa ba ina dai jera su kan dianing.


Tsit kitchen ɗin ta yi sai Lubna da ke magana jefi-jefi tana kwatanta ma Aliya yadda ayyukan ke
tafiya.Ni kuma ina gama dafuwar tea ɗin na juye shi cikin flask na ɗora kan tray da kuma
kofukansa,sai da na dubi Lubna kafin na fita na yi tunanin za ta cece ni ta ce na kawo ta kai.


Tun da na fara taka step ɗin da za ta kai ni ɗakinsa jikina ya soma rawa,hakan ya bai wa
kofukan yin ƙara suna fitar da wani sauti.
Bakin ƙofar na ja na tsaya,na fi minti biyu kafin na danna ƙarar rawar neman izinin shiga.Ƙofar
ce ta buɗe da kanta,wani sanyi ya ratsa ni haɗi da wani dadaɗan ƙamshi.Murya can ƙasan
maƙoshi na yi sallama,ba tare da kuma na ɗago kaina ba.


“In kika zuba min ruwan zafi mugun duka zan yi miki fiye da wanda aka baki labari” na tsinkayo
muryarsa.Da sauri na ɗaga kai sai na ga ashe ina kusa da shi,hannuna na rawa na ajiye trayn
kan table ɗin madubi da ke tsakiyar lafiyayyun kujerun ɗakin.Ina juyawa ƙofar ta rufe kanta,na
juyo da sauri ina kallonsa murya na ɗan rawa na ce “hajiya ta ce na kawo ma tea ga shi nan,ni
zan tafi”


Wani miskilin murmushi na ga yayi kafin ya ɗauki kofi ɗaya ya soma haɗa tea,bayan ya gama
ya ƙara ɗaukar wani kofin shi ma ya zuba a ciki duk ina tsaye ina kallonsa.


Ya ɗauki kofin ya soma kurɓa kafin ya ɗago ya dube ni ya ce “ki ɗauka ki sha” ko motsawa ban
yi ba,sai da ya ƙara cewa “in ba ki sha shayin nan to a nan za ki kwana” ko ida rufe bakinsa bai
yi ba na ɗauki kofin na soma sha da sauri duk da kuwa yana da zafi.Ina gama shanye wa kuwa
na ji ƙofar ta buɗe da kanta,da wani irin sauri na juya har da ɗan guduna don gani nake in na

tsaya wasa ƙofar za ta sake rufewa.


Da na fito ji na yi tamkar na baro wuta ne na shigo aljanna, kitchen na koma na taya su aikin sai
da aka kira sallah na fita.
Ko da na gama sallar ma ban koma ba,ɗaki na yi zamana don gobe ni ma a tsaye zan wuni
aikin kai wa mutane abinci.Har sai da aka yi sallar isha'i sannan na fita zuwa ɗayar kitchen
wacce ita kuma iya girkin gida kawai ake yi a cikinsa.Kuloilin da ta zuba abinci na soma ɗauka
ina kai wa can kan table ɗin cin abinci,bayan na gama sai na ɗauki kwanon abincinmu wanda
aka sauya mai girma ƙila saboda zuwan Aliya ne.Ko da na koma ɗaki sai na tarar da su duk sun
shigo,Lubna ta fara shiga wanka sannan ita ma ta yi daga nan sai na juye abincin cikin babban
faranti muka muka soma ci amma sai na lura Aliya babu abin da take sai satar kallona,tun ban
damu ba har na tsargu na ce “Lubna ƙanwarki sai kallona take ki tambaye ta halan na yi mata
kyau ne”

Lubna ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “to ke kin ji Aliya wai kina kallonta”

Maimakon ta kawar da dubanta a'a sai ma ta ƙara ƙure ni da ido kafin ta ce “na ga ba ta lafiya
ne”
Da mamaki na ce “wa ya faɗa miki banda lafiya?”

Sai da ta saki wani murmushin kafin ta ce “ga gubar maciji nan tana yawo a jikinki”
Kasa ci gaba na yi da cin abincin,ban ce komai ba sai Lubna ce ta yi magana “wace irin
magana ce wannan? Ya za ki ce guba na yi mata yawo a jiki? Ke ta ya aka yi kika sani? Ke ki
bar ma wannan maganar don in wani ya ji sai ya ce mayya ce ke,Ah to in ba maye ba wane ne
zai iya ganin abin da ke cikin ɓargon jikin mutum” Lubna ta ƙarashe cikin faɗa yayin da ita kuma
Aliya ta kai hannunta kan goshina ,nan take wani baƙin ruwa suka soma zubo min ta baki da
hanci.Kamar zan mutuwa haka na ji yayin fitar abin,can kuma ta janye hannunta wanda yake ta
kunno koren haske daga can tsakiya tamkar an kunna lantarki.
Lubna ta zabura ta tashi tsaye tare yin baya tana “Ya Rasulullahi! Manzon Allah!”

Ni kuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login