Showing 1 words to 3000 words out of 86820 words

Chapter 1 - Aurenmu Book Compelet By Asma Baffa

19 Jun 2026

762

[4/1, 5:47 AM] Sis Asma: 🛢�AUREN MU🛢�

COPY BY ZAINAB BUTALAWA

1-5


Official

By
AsmaBaffa



Page naki ne
UMMU LATEEPHA






Biye yake da ita a baya tana gaba Yana fada itama tana Masifa tare da furta bar maka
gidanka zanyi,ya furta ki bar gidan Mana sai me nima haka nake so ki tafi dama kin isheni,ae
naji tafiya zanyi suka shiga bedroom suna masifa,cikin akwatinanta ta dakko daya ta bude
sannan ta bude ma'adanar kayanta ta Fara fito da kayanta,Hannu yasa tare da fisge wani leshi
yace wannan ai ba kayanki bane Rannan na siya Miki da kika zo gidan nan dama ba a kawoki
da kayan kirki ba,au haka kace yes wannan tsohuwar atamfar taki ce ya furta tare da fito Mata
da ita,ta sake dakko wata shadda yace ajiyeta maidata ai baki zo da ita ba idan kin tuna last
year na dinka Miki ita,ajiyewa tayi ta zabo Wanda tazo dasu kala biyu, fannin takalma tazo ta
dauki wani white flat yace maza ajiye shi ni na siya Miki,tace na manta au Kaine fa ka siya,na
tuna Miki yau to yace, amma Farooq baka da kirki amma ba komai,Farooq yace ae naji,cikin
fushi ta jawo akwatinta ta fito Yana cewa itama akwatin mutunci na miki amma wlh da sai dai ki
zuba kayanki a Leda,Aisha tace ni ka daina matsowa kusa dani bana bukatar taimakonka,yace
wayyo yarinya Allah ya kiyaye na taimakeki rakaki zanyi Sabo da na kulle gidana Kuma karki
sake kice Zaki dawo gidana daga yau,Aisha tace me Zan dawo nayi a wannan banzan gidan
naka.

A Palo ta tsaya tana karewa palon kallo tana son gidan bata son barin gidan yace malama ki
tafi ke nake jira tana kallon gidan tace karka taba min jaka karma kace zaka taimakeni kace
zaka daukar min jaka bana so karka soma bana so,cikin masifa shima yace Allah ya kiyaye na
daukar miki jaka ki daina kallar min gida ki Kara gaba,Ina kaga gidan wannan gidan nasan
komai yayanka ne ya siya maka Ina kaga kudin gina gida,ae naji jeki bana son ganinki,Aisha

sabo da maita sai kallon gidan takeyi karshe cikin fushi da azama ta fisgi akwatinta zata fita sai
suka ji ana Kwankwasa palonsu,juna suka kalla sai Suka ji muryar Babar Farooq tana cewa ko
ba kowa ne? Farooq da sauri yace gani nan Muna nan,da sauri ya dauki akwatin Aisha yace
maza koma ciki Umma ce,da gudu ta dauki akwatinta ta koma bedroom,Shi Kuma kofar ya
bude Mata cike da ladabi ya furta Sannu da zuwa Umma,da fara'a tace yawwa Farooq Ina
matar taka ne naji gidan shuru? Farooq yace tana nan aiki ma ta gama yanzu ai Yar Albarka ce
akwaita da kwazo,Umma tace Kai Kam kayi dace ba irin Dan uwanka ba gashi Kuna zamanku
lfy, Aisha ya kwalawa Kira ta fito harda saka katon Hijab har kasa ta gaida da Umma tace bari
na kawo Miki ruwa,a'a barshi ma tafiya zanyi dan Allah ku zauna lafiya duk da nasan Kuna
kokari ba a Jin kanku Kuna zamanku lafiya kowa ya sheda,Farooq yace to Mene amfanin mace
da miji su dinga fada ai babu amfani,Aisha ma tace shi yasa Muka fahimci juna mu ko fada
bama yi bama cacar baki,

Shima Farooq yace yanzu Umma ai ba a yayin fada mu bamu San ma ma'aurata suna fada
ba sai dai muji labari a makwafta,Umma tace ai ni haka nake so Allah ya Kara zaunar daku lfy
ta mike suna cewa ameen ta tafi,tana tafiya Suka gallawa juna harara,Farooq yace dalla daina
kallona mutuniyar banza marar tarbiyya,Aisha tace tafiya zanyi gidan Ubana dama,Farooq yace
ba inda Zaki je baki Isa ba na fasa barinki ki tafi kudi na biya na aureki,gidanku son abin
duniyarku ya baci,tunda na fara neman aurenki ake rokata kudi,sannan Sadakin da akace na
biya wajen aurenki iyayenki ai da tsada Suka sa min, ko ke lokacin da na fada Miki sai da kika
tsorata,sannan ai caka min akayi cewa Kika yi ke virgin ce da nazo na shige ki wuuufff na wuce
ciki ba abinda ya tareni sai kace rijiya haka na fada cikin ki,harda cewa virgin ce amma a haka
na hakura na zauna dake sabo da haka ba inda Zaki je kina nan gidan,Aisha kuka ta saki tace
wlh Farooq Allah sai ya saka min sharrin daka min ni zaka cewa ba virgin ba Allah Yana
ganinka ta fashe da kuka me tsuma zuciya,Tsaki yaja ya koma Palo yace ba inda Zaki je Ina
gidan Nan banza shashasha.

kwan....gwan...gwan taji ana uban buga Mata kofa,lemo ne a hannun na ina Sha uban kida
na tashi,kofa na bude kyakyawan Matashin ne ya dauki wanka cikin kana Nan kaya farin Jean
da riga sky cike da bala'i yace dalla malama kin cika Mana gida da kida ko ke kadai ce a gidan
nan, da masifa nima kyakyawar budurwa dani nace ai kudin haya na biya Kai fa nasan sirrin
komai baka biya kudin haya ba sai uban daukan wanka baka da sisi,Jin na fara tona Masa asiri
yasan bai biya sisi ba yayi mukus ya juya gwiwarsa tayi sanyi ihu na Masa wooo yaji kunya ba
uwar da ya sani Sai wanka shi a dole gaye na ja tsaki tare da komawa ciki,shi kuwa dakinsa ya
koma ya Fara shiri Yana kallon Kansa a mudubi yace gaskiya na hadu zanyi cizo,ya dauki
lokaci me tsawon gaske Yana kallon Kansa kafin ya fito Yana taku dai dai.

Lokacin nazo fita a motata ja me kyau ko kallona baiyi ba ya tako ya wuceni a bakin gate
Yana Shirin barin gidan,glass na sauke a hankali cikin nutsuwa na furta dan Allah Affan taimaka
ka bude min gate,kallona yayi shekeke da bala'i yace kin ga nifa ba sa'anki bane,Kawai Dan kin
mallaki wannan banzar motar kina tunanin ke wata ishashiya ce me kike da shi wannan har
mota ce Yana magana Yana dukan motar da hannunsa,stop insulting my car,mota hadaddiya
zaka dinga zagi,Tsaki yaja yace kinci sa'a Ina da appointment fita zanyi da kin gane kurenki ya

juya yaci gaba da tafiya da gadara,haka ka iya kullum kace kana da Appointment kuma har
Yanzu bama gani a kasa kullum jiya iyau na furta ina Jan tsaki na Bude motata na fito tare da
bude gate na fita Office

Affan gidan Abokinsa ya wuce Direct Mustapha Yana aiki a ministry of Environment,Shi kuwa
Affan baya aikin komai sai dai buga buga idan ya samu ya siyi kayan daukan wanka kudin gidan
haya ma a Estate din ya kasa biya duk lokaci in yazo sai anyi fada da shi,suna Palon Mustapha
me kyau a zaune Mustapha yace me ya kawoka gidana ne nasan sai da dalili,Yace zuwa nayi
ka ranta min dubu biyar bani da kudin abinci komai na kayan abinci na ya Kare, Mustapha yace
dama na sani to gaskiya bani da kudi, Affan yace please ka taimaka min Kai fa abokina ne na
gaske common 5k nasan baza ka rasa ba, Mustapha ba a son ransa ba yace ya zanyi da Kai
kazo a abokina bai kamata nayi baboki irinka ba amma ya zanyi Zan baka 3k Amma ka tattabar
ka biyani na gaji bashin da nake binka yayi yawa,Affan Yana murna yace karka damu muna tare
fa sai lokacin Mustapha ya saki ransa suka ci gaba da labarin duniya.

Affan gida yazo da Niyyar shiga sai ga wani Mallam yasha babbar riga da rawani ya tsaida
Affan yace Saurayi Innalillahi wa Innailayhirraju'un, masifa ta tunkaro ka,Mallam yaga Affan
Kalar Naira ya dau wanka Kalar me kudi yace kana da makiya Alhaji wasu suna nan zasu sace
maka mota,Affan ya bude baki yasan karya yake shi da baida mota,yace sannan makiyanka
Yan uwanka ne sun Kai sunanka za a maka asiri kwana nan zaka rasa milliyoyin kudi a cikin
dukiyarka,Affan ya sheke da dariya a ransa Shi da bai da ko sisi yanzu ma bashin dubu uku ya
samo da kyar,a fili gigicewa yayi yace yanzu Mallam ya zanyi kenan? Me ya kamata ayi?
Mallam farin ciki ya kamashi ya samu gara zai cuce shi,yace dubu dari zaka kawo ayi aiki me
zafi a kansu,Farooq yace an gama bani Address din gidan naka yanzu banda kudi a
hannuna,Nan take Mallam jiki na rawa yace ya bada address Affan ya wuce gida,Yana cikin
palonsa dake estate din kowa bangarensa Palo da 2 Bedroom ne a hadadden Estate a haka
ma Sai me kudi ko ma'aikata ke Kama gida a ciki da gate dinsu da komai kowa da part
dinsa,Yana ta kora lemo da bread babu kayan abinci.

Raudat ce tayi parking motarta ta iske Hajiya Mairo a compound kusa da part dinta turaruka
ta Bata kyauta masu kyau,Mairo tana ta murna mugun shiri sukeyi da Raudat har abinci ma
idan Mairo taga dama a part din Raudat take ci itama Raudat tana ci a wajen Mairo duk gidan
tasu tazo daya suna morar juna,Raudat tace landlady wancan Kuwa ya biya kudin haya? baki
Hajiya Mairo ta tabe tace yo mutumin banza Ina zai iya kullum sai wanka bako sisi na gaji da
halinsa a gidan nan nawa kwana nan Zan kore shi,Raudat kasa kasa tace mene amfaninsa face
kora ko dubu Hamsim bazai iya hadawa ba bare dubu dari biyu,Suna haka sai ga Affan ya fito
ya dau uban wanka cikin kana nan Kaya Yana taku dai dai Yana takama ko kallonsu baiyi ba ya
fice suka bishi da kallo cike da mamakin yanda yake da mugun gadara baida aiki sai wanka
kullum cikin kamshi amma babu ko kobo.

Wani kanti yaje inda suke siyayya kusa da gidansu Suka tafa da me kantin yace a wannan
wanka haka Affan Ina zaka je ne? Affan yace tafiya zanyi Ina so zanje Abuja ne akwai wani
business da nake ya zuba karya yace gashi ma kaga Atm dina yaki aiki,me kanti sabo da yasan

Affan Yana Masa ciniki Yana ganinsa cikin kyakyawar shiga ya zaci me kudi ne yace gaskiya
kana tafiye tafiye Oga ko yaushe a Hanya, Affan yace ya za ayi Harkar Business ai in kana
Business ba zama yanzu ma bank Zan koma Ina so zanyi siyayya kudi yaki fita dan Allah zan
karbi kaya idan na dawo daga tafiya sai na kawo ma kudin, nan take me shago yace ba
damuwa komai normal ebi abinda kake so,Affan ya kwashi manyan manyan madarar gari su
gwagwanin Milo kayan tea sosai ya hada sannan ya kwashi su tumatir din gongoni,shinkafa
yasa ya auna Masa kwano biyar,wake,taliya, macaroni komai ya har su Mai da kwai sai da ya
hada akayi Total aka rubuta a list din Yan bashi ya fita,Yana kaiwa gida ya zauna ya shirya girki
me rai da lafiya yaci ya koshi sannan ya fito sai gidan Mallam Wanda ya karbi Address.

Affan ba kudin mota a kafa ya dinga tafiya sai da yaci bakar wahala kafin ya Isa gidan
Mallam Yana zuwa yaga gidan Mallam hadden gaske sama da kasa,bai Sha wahala ba aka
kaishi har part din Mallam,Mallam Yana zaune shi da wani Yana fada Masa karya dan ya karbe
Masa kudi,Bayan ya sallameshi Suka gaisa da Affan, Affan yace Mallam ka firgita ni shi yasa
nazo da wuri kaganni sauri nakeyi zanyi tafiya yanzu ba kudi a hannuna Kuma tafiyar wani
kudade Zan karbo shi yasa nazo yanzu ka bani dubu Hamsim kafin na dawo sai na baka dubu
dari biyu ma kaci harda riba,Mallam Yana Jin Haka ya haukace zai samu kudi ba bata lokaci ya
irgo kudi dubu Hamsim ya bawa Affan ,yayi godiya tare da cewa sai ya dawo ya fice,Yana fita
yazo ya biya me shago kudin kayan abincinsa tas harda samun canji ya shiga harkarsa.

Mallam Shuru Shuru Babu Affan ba labarinsa bai San Kuma inda zai ganshi ba,Affan yaci
wanka cikin wani yadi me kyau Yana taku dai dai sai ga Raudat ta taso daga aiki ta tsaya kusa
da shi tare da sauke glass tace Affan shigo na rage ma hanya Naga Kamar gida zaka je,cike da
rashin mutunci yace ke kin Isa ki taimakeni,akan wannan banzar motar taki har kin Isa ki rage
min Hanya ya juya da Niyyar tafiya Katsam sai yaga Mallam shi da wani suna ta magana
juyawa yayi da sauri ya bude motar Raudat ya Shiga gaba taja mota suka tafi Babu Wanda ya
kula wani,sai da Suka Yi nisa tace da kace baza ka shiga ba me yasa ka canja? Cikin bala'i
yace to sabo da na Shiga motarki shine Zaki Raina min hankali motar ki din banza motarki din
wofi,Parking Raudat tayi tace amma baka San mutunci ba fitar min a mota,Tsaki yaja ya Bude
kofa ya fice tare da furta banzar mota bayan ma ba da kudin halak Kika siya ba maza ne Suka
siya Miki Karuwar banza da kudin karauwanci Kika mallaki mota tunaninki bamu sani ba Alhaji
Sanata ko dan majalisa ya siya Miki ya daki motar da kafa yaci gaba da tafiya cikin
gadara,Raudat ce ta leko ta window tace mutumin da ya kasa biyan kudin gida talaka da Kai
baza ka taba iya siyen mota irin tawa ba Never, wace zata kulaka a haka Kai a dole kyakyawa
kana daukan wanka ba abinka ka iya sai siyen Kaya kana nan kayan ma duk na gwanjo ne ta
fisgi mota taja gaba,yace stupid girl Wai ita me mota Allah ya kiyaye na shiga motar haram.

Raudat yau da takaicin Affan ta dawo tana zuwa bayan taci abinci ta fito ta faki Ido kowa ta
taka tsani tayi disconnecting wutar gidan Affan ta danna switch dinsa ta sakko ta koma
gidanta,Yana dawowa ya kunna ko Ina duf babu wuta ya rasa dalili gashi gudun Landlady yake
tana ganinsa zata ce ya biya ta kudin haya,shima Fitowa yayi Raudat tana ganinsa ta window
tana ta kyalkyala dariya Yana dubawa yasan itace sai ya kunna nasa ya kashe nata wutar itama
sai gata ta fito da masifa Affan kana neman masifa abinda kakeyi ka takura min a gidan nan

Zan dauki mataki a kanka, Affan yace amma ke banza ce wawiya Naga alama so kike nace Ina
sonki to wannan bazai Yi tasiri ba,nafi karfinki kije ki samu dai dai dake, me zanci da Kai me
zaka iya siyawa matarka kudin gida ma ka kasa biya me zaka iya,Hajiya Mairo me gidan itace ta
shigo da dalleliyar motarta ta fito tace Wai ku meke damunku ne baku da aiki sai fada a gidan
nan me ya hada ku? Affan ya bude baki zaiyi magana Hajiya Mairo tace rufe min baki Kai har
kana da yanci a gidan nan kudin haya ma ka kasa biya,kana da bakin magana rufe Mana
baki,ai Kuwa sai yayi mukus baida bakin magana,Raudat ta kyalkyale da dariya sanye take
cikin Arabian gown me kyau tana kamshi tace ka biya kudin gida? Ko kudin gida ka kasa biya ai
Kai ba Dan gida bane ihu ta Masa wooooo ko kudin gida ya kasa biya get out, Affan sadaf
Sadaf ya koma cikin part dinsa bai da sisi baida inda zai samu kuma.

Kuka tafashe da shi tace wlh Shehu Allah sai ya tambayeka yaranka shida amma ka kasa
ciyar damu kullum sai Yar sana'a ta nake cinyewa,Tsaki Shehu ya buga yace ai yaranki ne ke
Kika haife su yanzu Dan kin basu kudinki shine matsala,amma Shehu kasan ni ke daukan
nauyin kaina da yarana kana da kudin ba Babu ba baza ka iya ba,gasara nake siyarwa itace
sa'a ta amma Watarana har da rana Koko muke sha ga yarka Nusaiba har ta girma ta Zama
budurwa ko yaushe Yarinyar nan kamar almajira haka take yarinya kyakyawa amma kamar
almajira Shehu kaji tsoron Allah,Nusaiba ce ta shigo cikin jemammun Kaya da katon botikin
kosai a kanta tayi sallama tace Mama na manta da yajin kosan,Yajin Nusaiba ta dauka ta tafi
tallanta wurin tasha inda mutane ke taruwa,Nusaiba tana ta ciniki tana irga kosai a Leda ga duk
Wanda ya siya,ta mike tsaye tana mikawa wani drivern babbar mota,wani bugagge yazo ta
Bayan Nusaiba ya taba mata duwawu,Nusaiba tace Ina Wasa da Kai,Ni Yar iska ce? Ka taba
ganin Ina wasan banza? Ni ba irin yan Iskan Yan talla bace neman halak na fito,zaka taba min
duwuwu tayi fatali da ledar kosanta bundle sabo da masifar Nusaiba ta shatile Masa kafafu ya
zube a kasa ta dinga dukansa ta rufe shi da Naushi a Fuska sai da ta farfasa Masa baki mutane
ana ta bata hakuri,wani yace kiyi hakuri Nusaiba sabon zuwa ne bai sanki ba,Nusaiba cike da
masifa tace ba ruwana ni tunda kaga haka dama ba mutumin kirki bane yazo ya taba min
duwawu ta ja tsaki tare da tara Yara Almajirai ta raba musu kosan sadaka ranta ya baci haka ta
koma gida

Tunda Mamanta taga ta shigo ranta a bace tasan wani ya tsokaneta,Shehu Abbanta Yana
zaune Yana shan shayi a gaban yaransa kanana su Kuma yaran kokon da babarsu ta dama na
siyarwa shi suke Sha,Shehu ne ya kalleta yace to jarababbiya masifaffiya uban me aka miki
marar kunya kullum baki da aiki sai fada da mutane,kiyi fada da mace,kiyi da Namiji,kiyi da Yara
gaba Daya zubar min da mutunci kike yi a layin nan,Nusaiba tana kumbura da tashin hankali
tace Kai ka sani Abba, Mama kema kin sani bana fada sai da dalili Abba ai dole nayi fada kosan
ma na bada Sadaka,Abba yace uwarki Kika yiwa asara ba abinda ya dameni abinda nake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0