Showing 1 words to 3000 words out of 55823 words

Chapter 1 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

46

[02/06 16:26] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

01


Wuri guda na ƙara curewa ina kallon yadda magen ke wasar juya launin idanunta,tamkar fitilar hannu haka haskensu ke dalle nawa idon.Gumi ya jiƙa ni sharkaf kamar wacce ta yi wankan kwance,yayin da kuma fitar numfashina ya zama kamar na wacce aka maƙallawa oxygen.Bugun zuciyata ya tsaya cak da bugawa ne a daidai lokacin da na ga magen daf da ni kamar ƙyaftawar ido.


“Sannu Suwaiba ya jikin?” murya Mamu ta sauka a dodon kunnena a daidai lokacin da na buɗe idanuna na tsinci gangar jikina kwance a gadon asibiti.

“Zan yi fitsari” shi ne abin da na faɗa tare da yunƙurin tashi,ta zo da sauri ta taimaka mini na miƙe tsaye.Ina dafa bango a haka na shiga toilet ɗin wacce ke da ƙarancin haske,kan fo na hau tare da lumshe ido na soma yin fitsari .A daidai nan kuma na soma jin wata murya na yin suwa cikin kunnena,“mun san abin da ya ke damunki ki yarda mu taimaka miki ” da sauri na ware idanuwana zuciyata na matsanancin bugawa,sai dai na kasa gaskata ma abin da na ji ɗin.Ruwa na kama kafin na fito na samu Mamu na gyara shimfiɗar da na tashi a kai,tana ganina ta sake jefo mini tambayar ɗazu.

“Ya jikin naki?”

“Da sauƙi Mamu.Ƙarfe nawa yanzu?”

Sai da ta duba ƴar ƙaramar Nokia ɗinta kafin ta ce “ƙarfe uku ba kwata”

Ban ƙara cewa komai ba na je na sake kwanciya,duk yadda na so yin bacci kuma kasawa na yi.Sai Mamu ce dai ta rumtsa,a yadda take baccin kawai na fahimci na gajiya ne da dukkan alamu tun bayan da da suka fargar halin da nake ciki ba ta rumtsa ba.Wani tsoron ne ya sake rufe ni tuna abin da ya faru,addu'a na soma yi sai na dinga jin sassauci.Ina a haka har aka kira sallar asubah,a hankali na sauka na shiga toilet na sake yin ɗahara sannan na ɗaura alwala.Ina shirin fitowa ƙofar ta wani rufo kanta da ƙarfi,jiki na rawa na kama handle na soma kiciniyar buɗewa ta amma tamkar ma ina sake rufe ta haka take ƙara mannewa.Bakina na rawa na soma kiran sunan Mamu ina kuka kafin na waiwaiya bayana da nake jin kamar ana son damƙe ni,nan na yi tozali da fuskata a cikin madubi da kuma inuwar kaina wacce ta rabu biyu ina kallo a gaban idanuna kuma duka inuwoyin biyu suka haɗe wuri ɗaya.A daidai nan kuma na ji numfashina na barazanar sake ɗaukewa a karo na biyu,sai kuma ƙarar buɗe ƙofar ta ziyarci kunnena hakan shi ya ɗan farfaɗo da numfashin nawa.Wani tsalle na yi na fito waje ina haƙi,sai na ga Mamu na ta ci gaba da yin baccinta.Kusa da ita na je tare da ɗan jijigata,ta wani firgita tare da tashi tana zarar ido.

“Lokacin sallah yayi” na faɗa a sanyaye.Sai ta jawo wata leda daga ƙarƙashin gado ta miƙo mini hijabi tare kuma da wani zane,shi na shimfiɗa na gabatar da sallar.A sujudar ƙarshe sai da na yi dogayen addu'o'i sannan na ɗago,bayan na gama Mamu ita ma ta yi tata sallar.Babu wani jimawa kuwa likita ya shigo ya duba ni,sannan ya ce muna iya tafiya gida zuwa ƙarfe takwas na safe.


Lokaci na cika kuwa muka fito ni da Mamu muka tari adaidaita muka dawo gida.A bakin ƙofa muka haɗu da Abba yana kiciniyar fitar da babur ɗinsa,shi ne ya soma yin magana kafin mu.


“Har an sallamo ku?”

“Eh!” ta basa amsa a ɗan dake tare da jan hannuna muka shige ciki.A tsakar gida Lantana ce zaune da ƴaƴanta suna gyaran gyaɗa,Mamu ta yi sallama duk suka amsa cike da fara'a Lantana ta taso ta wani zo ta kama hannuna tana cewa “Uwata ya jikin naki? Sai yanzu kawai Abbanku ke sanar da ni wai jiya cikin dare suma kika yi Allah ya yi sa'a ma Mamunku ta zo tashe ki don ki bata ko kuɗin adashe sai ta ga ba ki numfashi”

Ɗan murmushi na saki kawai,sai Mamu ce ke bata ba'asi.
“Dare bai ma yi wani sosai ba,Sulaimanu ne ya dawo a jiyan shi ne fa nake tashe ta don bani makullin frigine na basa lemu mai ɗan sanyi” Mamu ke yin bayanin,ban sani ba ko ta lura da yanayin Lantana ya canza wacce muke kira da Mama.Ta haɗiye wasu yawu tana mai cewa “Sulaimanu ya dawo?”

Da ɗan mamaki ita ma Mamu ɗin ta dube ta tana mai cewa “kina nufin Surajo bai sanar da ke ba? Ai tare suka shigo shi ya ma kawo shi fa”

Idanun Mama Lantana suka yi wani irin ja tana mai cewa “amma shi ne ko ki kira ni Zainaba ? Fatan dai yana lafiya ko?”

Ɗan shiru Mamu ta yi kafin ta amsa a takaice “Alhamdullah”

Wani irin abu ne nake ji yana shigar hannuna da Mama Lantana ta riƙe,babu shiri na ƙwace abina ina mai yin gaba na wuce can ɓangarenmu.Da akwatin Yaya Sulaimanu kuwa na fara cin karo a nan falo,kan kujera na kwanta ina jan numfashi babu jimawa Mamu ta shigo.

Ledar hannunta ta ajiye tana masifa ƙasa-ƙasa,“ƴarka ba ta da lafiya amma ka kasa fitowa mu je asibiti don kawai kana ɗakin wata ,hum! Ai ciwo ne ya san ɗakin kowa”

“Mamu me yasa a kullum kike ganin laifin Abba amma kika yarda da Mama Lantana? Ai ko ma mene ne ita ce ta hana shi fitowa”


“Kwanta ki huta dai,kin fi sanin halin Abban naku ne ” daga haka sai ta fice,ni kuwa wayata na ɗauko na rubutawa ƙawata Ubaidah saƙo babu jimawa kuma ta kira ni.Hira muka soma sama-sama kafin na bata labarin abin da ya faru da ni ,ta ce “hum! Yanzu fa in na ce miki na yi mafarkin hakan sai ki ƙaryata ni ko? Wallahi Suby ba tun yau ba ake nuna mini a mafarki wata baƙar mata na binki da sharri,kuma kin san ni dai wacce nake zargi?”

Na ce “a'a”,ta bani amsa da “Mama Lantana,shi yasa ma ni sam na tsane ta saboda ita na rage zuwa gidanku don muddin na je can in dai har muka haɗu to ranar zan wuni da azababen ciwon kai ne”

Ina shirin magana Mamu ta shigo hannunta riƙe da leda,ni ta miƙowa tana cewa “ga shi ki ci in kin gama sai ki sha magani” karɓa na yi ina cewa “toh” sai kuma ta sake ficewa.

Na ja numfashi ina cewa “ƙawata don Allah in kin samu dama ki zo gidanmu ko da dadare ne gudun kar ki haɗu da ita wallahi akwai maganar da nake son sanar da ke mai muhimmanci ”

Ta ce “a'a ke ya kamata ki zo dai,ko ki bari SUL zai zo sai ki biyo shi ku taho”

Na yi ɗan murmushi mai sauti na ce “wai ya sanar da ke ya zo ne? Ni fa har yanzu ba mu haɗu ba”

Ta ce “ni ma sai yau da safe ya sanar da ni,ya ce mini ba zai jima ba zai koma”

“Kuma a hakan kike so na biyo shi? Ban takura muku?”
“Ke dalla ki zo, SUL ɗin ne ba ki sani ba da magana ma wuya take yi masa?”

“Ok to babu damuwa” daga haka sai muka ɗauko hirar makaranta kuma inda kusan nan dai katin wayarta ya ida kafin mu yi sallama.
Ledar da Mamu ta kawo mini na buɗe,waina ce da miya haka na juye a kwano na ci na ƙoshi sannan na sha magani sai kuma na ɗan kwanta don na huta.Sai dai hakan ba ta samu ba sakamakon shigowar Yaya Sulaimanu,da sauri na miƙe tare da zuwa na ƙanƙame shi cikin murna ina hawaye.
Yayi ɗan murmushi wanda ya bayyana tsantsar kamar mu da shi sai dai na fi shi kyawu,“Autar Mamu ?” ya furta yana goge mini hawayen fuskata da suka kasance na farin cikin ganinsa,shi kaɗai ne ƙwaya ɗaya tilo ɗan uwana da muka fito ciki guda shi ya raine ni,ya sangartar da ni.

Na amsa da “na'am” kafin kuma na yi shiru.Ya ja hannuna muka zauna kan kujera kafin ya riƙe dukkan tafukan hannuwana yana kallona,kallo ne wanda ta shi kaɗai ne yake iya karantar damuwata saboda girma da ya zo mini yasa na bar faɗa masa damuwata don na lura shi ma tasa damuwar wacce yake dako shi ɗaya.


“Me ya sumar da ke jiya?” ya jefo mini tambayar kamar daga sama.
Ni kuma don kawar da zancen na ce “me yasa ba ka je dubo ni ba asibiti?”

“Ni na kai ku fa,sai dai na baro can ne saboda kiran ujila da na samu” ya bani amsa.


“Mun yi waya da Ubaidah ta ce in za ka tafi mu je tare” na faɗa ina kallonsa ni ma,ya ce “ta faɗa mini amma sai dai gobe don yau akwai inda zan je”

Na ɗan ɓata rai kafin na ce “to ka kai ni sai ka yi tafiyarka in ka dawo sai ka biyo ka ɗauke ni ”

“Ya biyo ina?” Mamu wacce ta shigo yanzu ta tambaya.
“Gidansu Ubaidah kin san kamar wasu tagwaye haka suke”

Mamu ta washe baki tana mai cewa “jiya ma mun haɗe da Mamarsu ɗin tana yi mini zancen saka rana,na ce ai magana tana wurinsu tun da su suke da mace”

Sulaimanu ya ɗan sunne kai yana mai cewa “abin da ya kawo ni kenan Mamu sai dai kuma jiya ban samu mun yi maganar ba”

Mamu na jin haka ita ma ta samu wuri ta zauna,shi kuma Sulaimanu sai ya saki hannuwana da tun ɗazu suke cikin nasa ya fuskanci Mamu da kyau yana cewa “Mamu dama na zo ne a yi bikin in an gama komai ina so in tafi da Ubaidah can inda nake aiki”


“To ai hakan ba wani abu ba ne,zan kira Kawunku na sanar da shi sai ya je ya samu iyayen nata ya sanar”

“Yawwa hakan ma yayi” Sulaimanu ya faɗa yana jan numfashi,daga nan kuma sai Mamu ta soma tambayarsa wurin aikinsa tun ina saurarensu har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba .



★A can ɓangaren Mama Lantana kuwa ɗaki ta shige ta bar Hassana da Hussaina da kuma Ramatu ga aikin gyaran gyaɗar da take yin digadigi.Kamar ta yi hauka haka take ji,waya ta ɗauko ta shiga duba lambobi har ta kai ga wacce take so ta danna okay kiran ya tafi yayin da sunan malam Yawale ke yawo kan ɗan ƙaramin screen ɗin wayar .Bugu biyu ya ɗauka,ko gaishe shi ba ta yi ba cikin ƙasa da murya take cewa “malam da fa matsala ka ga Sulaimanu wai ya dawo jiya ”


“Ya fa dawo? Kin tabbata kuma kullum kina yin wuridin da na baki?”

“Ko yau na yi shi malam,ni dai yanzu abin da nake so a sake sabunta aikin nan shi ne kawai”

“Zan sabunta amma da buƙatar yanka wannan karon,jajayen zakaru guda uku sai kuma ki sayo jan muski guda ɗaya da fari guda biyu”

“Zan turo maka kuɗin sai ka sayi duk abin da kake buƙata” tana faɗar haka ta kashe kiran tare da dafe saitin zuciyarta da ke barazanar faɗowa ƙasa tun bayan lokacin da ta samu labarin zuwan Sulaimanu.


“Hassana?” ta ƙwala kiran sunanta,daga can waje Hassana ta tashi figai-figai ta zo domin amsa kiran mahaifiyarta.

“Ga ni Mama” ta faɗa ,Mama Lantana ta ɗauko wata robar mai wacce take ajiyar kuɗi a ciki ta ɗauko kuɗi ta ƙirga kafin ta ce “ungo je ki turawa malam Yawale kuɗin nan,ki yi sauri kuma ki dawo don za mu je markaɗe”

Ta karɓa tana mai cewa “har yanzu bai ƙara aiko mana da rubutun ba dai”

“Zai aiko ni na dakatar da shi” Mama Lantana ta faɗa.

Hassana ta ɗan ɓata rai kafin ta ce “amma Mama ...” kafin ma ta ida ta tari numfashinta tana mai cewa “don ubanki a wannan gidan a ina za ki yi wankan magani a tsakar gida? Na bari ne sai Kaka ta dawo sai ku je can gidanta hankali kwance ku yi komai ku dawo“ Hassana na jin haka sai ta washe baki,hijabi ta ɗauka da ɗan saurinta kuwa ta fita zuwa tura kuɗi.

Mama Lantana na ganin kiran malam Yawale ta san da tuni ya ga alert.Ta ɗaga tare da yin shiru,ya ce “in sha Allah ina mai tabbatar miki yau da zarar jinin zakarun nan ya zuba ga ƙasa Sulaimanu zai koma can ƙauye”
Mama Lantana ta washe baki tana cewa “na gode sosai Malam,goben ni ma zan zo saboda batun aikin ƴan biyun ”

“Babu damuwa hajiya” ya faɗa tare da kashewa.

Mama Lantana ta fito tsakar gida wanda yayi daidai da fitowar Sulaimanu shi ma daga can shamakinsu.Kamar kullum wani irin tsoronta ne ya ji ya ziyarce shi mai haɗe da faɗuwar gaba.Da wani irin sauri ya je gare ta yana gaishe ta,ya sunne kai sam ya kasa ɗago kai ya dube ta.
Mama Lantana ta saki wani makirin murmushi ganin har yanzu dai da sauran aikin da ta yi a jikinsa,“Lafiya lau Manu wannan bazata ,zuwa babu shawara?”

Zuciyarsa ce ta ƙara tsananta tsoron nata,yana jin in ta yi masa faɗa tamkar zai iya rasa ransa ne.Murya na ɗan rawa ya ce “yi haƙuri Mama na zo ban sanar da ke ba tukuna”

“Bai komai yarona Allah yi maka albarka ,sosai na yi farin cikin ganinka” Mama Lantana ta faɗa cikin ɗaga murya tana mai shafa kansa ganin Mamu ta fito.

Ita kuwa Mamu baiwar Allah murmushi ta saki duk da kuwa wannan ba baƙon abu ba ne duk mai shigowa gidan nan ya san yadda Mama Lantana ke nuna tsantsar soyayyarta ga Sulaimanu,da kuma shi kansa yadda ya ɗauke ta kamar uwa yake yi mata biyayya don in mutum baƙo ne zai iya dubin Mama Lantana ce ta haife shi ba Mamu ba.


Ba tare da tunanin komai ba Mamu ta ce “ashe ɗanki matarsa ya zo tafiya da ita ” ta yi furucin ne cikin raha.

Ita kuwa Mama Lantana zuciyarta ce ta ƙara rinewa da baƙin hassada amma kuma sam ba ta nuna hakan a fuskarta ba,wata uwar guɗa ta yi tana wani juyi .

Hassana da ta shigo ta ce “Mama lafiya kike rawa?”


“Auren Yayanku ya tashi” ta bata amsa,ƴan magana sun ce barewa ba ta yi gudu ɗanta yayi rairafe ba to haka ƴaƴan Mama Lantana suke duk ta koya musu makirci haka su ma suka hau murna wanda hakan ya sanyaya ran Sulaimanu yana kallon ƙannen nasa waɗanda suke uba ɗaya,har zai fita ya ji suna zancen fitar da anko.


Mamu kuwa haka ta zauna cikinsu suna ta zanen kalolin ankon biki da za a fitar kafin kuma ta ɗauki waya a gabansu ta kira Kawunsu wanda ya kasance ƙanen mahaifinsu ne ta sanar da shi.Tana ajiye wayar ita ma Mama Lantana ta tashi ta shiga ɗaki ta yi nata kiran,ta sanar da malam Yawale wanda duk unguwar da yake babu wanda bai tsoro da shakkarsa.


★Suwaiba

Ban san adadin lokacin da na ɗauka ba ina bacci.Ko da na farka fitowa na yi na ɗauki buta na shiga banɗaki,sai bayan na fito ne na samu Mamu a madafa ina tambayarta abin da aka dafa.


“Wake da shinkafa” ta bani amsa,gabana ne ya yanke ya faɗi har ban san lokacin da na furta “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!” wanda yayi daidai da shigowar Abbanmu a rikice yana kiran sunan Mama Lantana.

Mamu ce ta fito tana cewa “malam lafiya?”

“Ina fa lafiya wai Isiyaku ne mota ta kaɗe yanzun nan ko shurawa bai yi ba” ya bata amsa.

Mamu da ke riƙe da tasar da za ta soya mai sakinta ta yi tana cewa “kawun yaran ne ya rasu? Yanzun nan fa muka gama waya da shi”

Abba ya ce “ya kira ni,kuma ma sai da ya shaida mini kun yi waya da shi kan ya je ya tuntuɓi iyayen Ubaidah game da sa ranar biki shi ne ya ce bari ya kira ni kafin ya je ashe babu rabon zuwan”

Tamkar wacce ta hau tauri haka ƙafafuwana suka soma yin rawa,kafin kuma na soma yin kuka kamar raina zai fita.Duk a tunaninsu saboda mutuwar kawun ce nake yin kuka,ni kuwa a'a ba ita ba ce sai dai abin da zai faru a gaban ne nake yi wa kuka muddin dai mafarkin nawa ya ci gaba da zama gaskiya.Rarrashina suka haɗu suna yi tare da yin nasiha.

Mama Lantana ta fito wani kallo ne ta yi mini wanda yake mugun jefa ni cikin tsananin tashin hankali.
“Me yake faruwa?” ta tambaya,Abba ya bata amsa.

“Allah ya jiƙansa,Zainaba shirya mu tafi ki kwashe waken a kula mu tafi da shi” shi ne abin da Mama Lantana ta furta tare da juyawa tana yin wani murmushi wanda sarai da idona na ga haka.


Babu ɓata lokaci duk muka shirya, lokacin bai wuce ƙarfe ɗaya na rana da wasu mintina.Adaidai sahu muka shiga,Mamu da Mama Lantana da kuma ƴan biyu a can baya yayin da ni kuma da Ramatu muka shiga gaba.Ko da muka isa tuni an haƙa rumfa,dangi na kusa ma tuni sun zo.
Duk saukowa muka yi Mamu na miƙa kuɗin ɗan sahun Mama Lantana ta jefo tambayar “ni kam an sanar wa da Manu batun mutuwar?”

Mamu ta girgiza kai,kallonta na yi ni dai yadda ta ɗauki mutuwar kamar wani biki sai murna take.
“Hassana ungo kira Yayanku ki sanar da shi” ta faɗa tare da miƙa mata wayar,sai bayan mun shiga ciki har mun zauna sannan ta kira wayar ina jin yadda muryar Yaya Sulaimanu ta bayyanar da tsantsar tashin hankali.
Jingina na yi ga bango ina mai lumshe idanuna,wani irin ƙunci nake ji da ban taɓa ji ba a rayuwata.Tamkar ba gidan makoki ba haka mutane ke ta yin surutu,ga Mama Lantana sai maimaita kalmar ko yau an yi waya da shi game da auren ɗan wurin Mamu .Tun mutane ba su ɗauki abin wani kala ba har wata ta ce “ah wannan aure kuwa anya akwai alkhairi a ciki? Kila ma yana kan hanyar zuwa gidan ne aka kaɗe shi”

Da sauri na ware idanu sai na ga idanun Mamu sun nuna ƙin jin daɗin furucin,yayin da ita kuma Mama Lantana ke cewa “to wa ya sani abu kamar annoba sama da wata shidda kenan da kai dukiyar auren ”


Tsam na miƙe saboda ba zan juri ire-iren waɗannan maganganun ba.Idanuna har wani lumshewa suke tsabar yadda baƙin ciki ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login