Showing 15001 words to 18000 words out of 55823 words

Chapter 6 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

38

Allah a ci gaba da haƙuri kin ji ƴar nan ” babu wanda ya amsa mata duk shiru aka yi kafin Ammy ta miƙe duk sai muka mara mata baya,“Uwata ina kuma za ki je? ” Mama Lantana ta faɗa duk da na san da ni take amma ban juyowa ba,ta sake cewa “izala kika koma kuma wannan uban hijabi yana sharar ƙasa?” na ɗan juyo na dube ta kawai kafin na fice dama ni ce a baya.

A tsakar gida muka haɗe da Mamu tana ta shimfiɗa tabarma,ni da Ubaidah muka ƙarasa shimfiɗarwa yayin da ita kuma da Ammy suka koma gefe suna tattaunawa.
Ubaidah ni ma ta dube ni da kyau tana mai cewa “wai kin ga yadda Mama Lantana ke ɗingishi kuwa?”

Na ce “na gani ƙila faɗuwa ta yi ” ta girgiza kai ta ce “ina zargin wani abu,amma dai bari in an jima mu koma wurin Uncle Suhail mu ji me zai cewa”

Zuciyata na ji ta wani buga da sauri jin ta ambaci sunansa ,ta yi ƴar dariya ta ce “yi haƙuri my Suby zan tafi ni ɗaya”

Ina shirin yin magana Mama Lantana ta fito don masifa wurinmu ta nufo tana cewa “ba ki ji ina tambayarki ba? Ina ne za ki je?”

“Ko ina me aka yi?” na faɗa ,tsakiyar ido ta yi mini wani kallo kafin ta koma ɗaki tana ɗingishi.Unaidah ta furta “munafuka!”

“Don Allah ki rabu da ita ta yi tunanin har da ni za ku koma can gida”

“Kina nufin a nan za ki zauna?”

“Eh mana in na je gida me zan yi? Ƙila Mamu nan za ta zauna sai an yi sadakar uku”

“Ai gobe ne,sai mu je can gidanmu goben sai koma”

“Gobe fa Monday ne ko kin manta akwai makaranta?”

“Daga gidanmu ba a iya zuwa ko?”
“Ban ce ba” na faɗa kafin mu kamo wata hirar,da Ammy da Mamu suka matso inda muke kafin Ammyn ta ce “ku je mu tafi”

Na ce “zan tsaya nan kar a ce na ƙi zama gidan makokin”

“Ubaidah mu tafi to,Zainaba za mu wuce in sha Allah in komai ya daidaita zan kira ki ta waya na shaida miki yadda muka yi”

“To babu damuwa” daga haka suka fice Ubaidah na cika tana batsewa har Mamu sai da ta lura da hakan ta ce “Ke ba ki iya kawaici ba? Ko da ba za ki bi su ba ai bai kamata ki faɗa ba kai tsaye, maimakon ki yi musu rakiya kin yi tsaye da wani hijabi naki kamar matar liman.Dubi yadda Ubaidah ke fushi saboda furucinki”

Na ɗan turo baki gaba na ce “Mamu in don ta Udah ce to ba ta ƙi na koma gidansu da zama ba”

“Je ki cire hijabin dai ki zo ki taya ni zuba kunu a kofuka ”

Na amsa da “to” tare da komawa can ciki,uwar ɗaka na shiga na cire hijabin na ninke na ɗauko wani da ke kan gado na saka.Ina shirin fitowa na ji muryar Hassana tana cewa “Mama ashe yayan Ubaidah ne,inda kin gansa kyakkyawa kuwa da shi kuɗi sun kwanta ”

“Yi shiru bari za mu yi maganar daga baya” ita Mamar ta faɗa.
Fasa fitowa na yi daga ɗakin sai da aka ɗauki lokaci,a bakin ƙofar fita daga ƙurya ɗakin ne ashe suke a zaune.Ina fitowa Hassana ta ce “Suwaiba amma yau ba a gida kika kwana ba ko ?”

“Wa ya faɗa miki? Ina Hussaina? ” na faɗa.

“Tana gida sai ta gama aikace-aikace sannan za ta taho” ta bani amsa,na ce “bari na kira ta na ce ta taho wa da Mamu da wasu kayan ta sauya”


“Saboda kin fi ni sanin daidai ko? Su waɗanda na kawo mata fa?” Mama Lantana ta faɗa cikin masifa tana mai jefo mini wata leda a fuska ta bugi leɓena,tsabar yadda na ji zafi har sai da na rumtse ido.Ledar na ɗauka na fita ina hawaye,Mamu na miƙawa na ce “ki yi wanka ki canza kayan”

“Lafiya kukan me kike yi? Ai na yi wanka sai dai in wani zan sake” ta faɗa tare da karɓar ledar.
Na ce “ki je zan yi aikin” haka ta tafi ta bar ni da rabawa al'umma kunun.


Tsabar mugunta irin ta Mama Lantana da na kai mata kunun haka ta saki kofin ya wanke mini ƙafa tasss.Na fasa uban ihu don yana da zafi sosai ,kuma duk sai ta tada hankali tana yi mini masifa tana kamanta ni marar nutsuwa,mutane na ta jero mini sannu.Haka wata daga cikin matan da ke ɗakin ta jawo ni waje aka wanke ƙafar da ƙasari wai don kar wutar ta fito.
Ko da Mamu ta fito daga wanka tuni ma an gama wanke ƙafar,matar ce ta yi mata bayani kunu ne ya zube mini.Babu yadda na iya dole na je na zauna wuri guda,wuraren ƙarfe goma sha biyu na rana Mama Lantana ta ja Hassana a gaban idona suka fice.


★Sam Mama Lantana ba ta taɓa kawo wa a kanta tafiya da Hassana gidan malam hakan bai dace ba.Idonta sun rufe da yadda sam ba ta ganin tsoronta a idanun Suwaiba saɓanin Sulaimanu da shi ita kanta Mamu ɗin.Adaidaita suka shiga ya kai su,da suka je sun tarar da uban jira kowacce ta kama layi kan wasu kujeru da ya zuba a babban filin gidan.
Ita dai Hassana ta san shi amma iya ta waya ce sai kuma sunansa da take ji a bakin mahaifiyarta.

“Mama ni dai Yayan Ubaidah yayi mini ki sa a yi aiki a kansa ya aure ni ” Hassana ta faɗa ,Mama Lantana ta yi mata wani kallo kafin ta ce “ki ma cire wannan tunanin a ranki saboda ba zai taɓa yiyuwa ba,irin wannan aikin yana da matuƙar tsada ”

Hassana ta ɓata rai tana mai cewa “Mama ai sai a sayar da wani abu a haɗa kuɗin”

“Wa ya faɗa miki maganar kuɗi ce? Kin ga kar ki maido mini aiki baya ,yau Kaka ke dawowa zan karɓa muku ruwan wanka sai ki wuce can in Hussaina ta zo ita ma sai ta je can ɗin ku fara tare”

Ba don Hassana ta so ba haka ta ja baki ta yi shiru.Mutane na ta shiga layi na ragewa ,Mama Lantana ta miƙe don ta shiga bayi,wata da ke kusa da su ashe duk ta ji abin da suke tattaunawa ta ce “aikinsa na ci sosai muddin dai za ka bi sharaɗi,kin ga ni ma shi yayi mini aiki na auri baban yaron nan.Yanzu ma na zo ne a yi mini wani aikin mallaka mai ƙarfi”

Hassana na jin haka ta gyara zama,“bani lambarki ma ina so mu zama ƙawaye” ta faɗa ,Hassana kuwa ta bata nan ta yi ta tsara ta ita kuma tana ɗaukar darasi.
Ko da Mama Lantana ta dawo tuni Hassana ta iya allonta,a haka dai layi ya iso gare su.
Bayan sun shiga godiya ta soma yi masa na aikin da ya yi mata , sannan ta ɗora da cewa “a haɗa maganin ƴan biyu sai kuma wancan aikin na jikin Suwaiba ina ga duk ya lalace ta bar tsorona,sannan ina son ka ƙara loda wani a kai so nake ta lalace ta soma bin maza ta haka ne kawai zan ji sanyi a raina”

Malam Yawale da ya kasance matashin tuzuru ɗan shekara arba'in da biyu,baƙin buzu ne .Rawanin kansa ya gyara sannan ya soma yin rubuce-rubuce a jikin wani farin ƙyalle kafin ya ce “aikin ƴan biyu fa tuni na kammala,shi kuma wannan da kika ce ina buƙatar ɗan kamfai na Suwaibar da kuma hotonta”

“Ɗan kamfai? ”
“Eh wanda ta saka kuma ba a wanke shi ba,ma'ana ana cire shi daga jikinta ” malam Yawale ya faɗa cike da yaƙini.
“Babu damuwa yau ɗin nan zan nemo shi zan kwana a gidan makoki sai na cire na jikinta ”

“Yawwa hakan yayi” sai ya miƙo mata abubuwan da ya tanada na ƴan biyu tare da yi musu bayani.Kuɗi ta basa kafin su fito, Hassana ta ce “Mama yanzu ya za a yi ki samu wandon Suwaibar ?”
“Maganin bacci zan saka bata ta sha,yanzu zan sayensa shi da na ƙunar wuta sai in ba uwarta ta bata“ ta yi furucin tana wani murmushi.Tun a hanya suka rabu Mama ta bata makullin ɗakin Kaka da na gidan ta ce ta wuce can,ita kuma sai da ta sayi magunguna sannan ta koma can gidan makokin.


★A ɓangaren Ubaidullah kuwa sosai ya ji takaicin yadda bai ga Suwaiba tare da su Ammy ba.Iya fuskar Ubaidah da ya kalla ya fahimci abin da ke faruwa,don ya san yadda ƙanwar tasa ke mugun ƙaunar Subyn.Bai ce komai ba haka suka shiga suka ɗau hanyar gida,suna isa suka tarar da Hamida a zaune ta ci uban kuka har ta gaji.
Ammy ce ta tashi hankalinta ta soma tambayarta lafiya,ai kamar ma ƙara zugata ta yi haka ta tsiro da wani sabon kukan.Ubaidullah kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai tare da nufar step ɗin ɗakinsa,Ammy ta ce “ya za ka tafi kuma? Ko ba ka gane ta ba ne?”

Ubaidah ta ce “ai dama mun bar ta a nan ɗin”
Hamida ta tashi da sauri ta take masa baya,yana shiga ɗakinsa ita ma ta shiga ta ƙanƙame shi ta baya tana wani matsanancin kuka mai cin rai.Ido ya lumshe yana sauraren abin da take furtawa.

“Don me ? Don me ita? Ni ba ka taɓa nuna damuwarka a kaina ba,har suma na taɓa yi kowa ya bi ni asibiti amma kai ka ƙi tafiya.Shi ne..shi ne ita ɗan haɓo kawai jiki na rawa ka kai ta asibiti? ”

A ɗan dake ya ce “ita ɗin zaman ƙanwata take yi Hamida ”
“Ni ma ai wani ɓangare ƙanwarka ce”
Jawo ta yayi ya maido ta gabansa yana kallon yadda idanunta suka kumbura,“ ya isa haka ban so” ya furta a hankali.Jikinsa ta shige ta yi lamo tana jan numfashi,tsawon lokaci kafin ya ce “ki sauka ƙasa ina zuwa” a hankali ta zame tana kallonsa ta fita,shi kuwa bedroom ya wuce ya rage kayansa kafin ya shiga toilet ya sakarwa kansa shower.Kalaman Hamida sai gwaro da juna suke yi cikin ƙwaƙwalwarsa yana kuma tambayar kansa to don me yake jin ya damu da Suby?


Normal group 300,Vip 600 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[08/06 08:15] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*
Masu jiran book ɗin TIF DA TAYA ya kammala 1k ne kuɗinsa amma na yi discount duk mai so ya biya 800 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822

In kuma akwai wani book ɗina da mutum ke so yayi mini magana zan yi masa discount

06

Ko kaɗan bai danganta hakan wai da sunan so ba,abu guda ya sani Suby nada wani matsayi a zuciyarsa wanda ya alaƙanta hakan kuma da ƙaunar ƙanwarsa da take yi.
Towel ya jawo ya ɗaura a ƙugu kafin ya fito yana tsane kansa da ƙarami kuma.Bai wani ɗauki lokaci ba ya shirya cikin kakinsa na soja,ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito a hankali yana jin kansa wani iri tamkar bai ida cika ba.
Idanun Hamida ƙurrr a kansa ko ƙyaftawa ba ta yi,wani irin azababen so ne take yi wa Ubaid ɗin wanda ita da kanta take ƙarawa kanta shi ta hanyar wanka da maganin shirkar da malam Yawale ya bata.
Wata sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ƙamshin jikinsa da na turarensa suka turniƙe mata hanci,ta ɗan lumshe ido kafin kuma ta buɗe su a hankali ta ɗora su kan fuskarsa da sam babu walwala.


“Na zuba ma abincin?” ita ce tambayar da ta yi saboda takaicinta babba bai wuce yadda ciwon Suby ya tashi ba tare da Ubaid ɗin ya ci abincin da ta zuba masa magani ba.
Ɗan yamutsa fuska yayi kafin ya girgiza kai,ya dubi agogon hannunsa ya ce “zan wuce wurin aiki ne”

“Zan bi ka”
"A'a” ya furta tare da nufar ɗakin Ammy,da sallama ya shiga ta amsa cike da kulawa.Wuri ya samu ya zauna yana mai cewa “Ammy lafiya kika fita tun da safe?”

Sai da ta sauke numfashi kafin ta ce “wata patient ɗina ce na je dubawa,na yi tunanin ma ta farka sai ga shi har na baro asibitin tana bacci”

“Allah ya bata lafiya,ni zan wuce.Ina Ubaidah?”

“Tana ɗakinta“ ta basa amsa kafin kuma ɗora da addu'ar tsari a gare shi.
Ko da ya fito bai samu Hamida ba a falo,yana fita can harabar gida ya tsinkaye ta tana lalata tayar motarta, wato so take ala dole sai ya ɗauke ta a motarsa.Ya girgiza kai don shi a kullum mamakin Hamidar yake yi ,tana ganinsa ta yi saurin ɓoye ƙatuwar wuƙar hannunta.Kuɗi ya ciro a aljihunsa ya ce “in kin gama ɓata tayar motar sai ki kai a gyara miki ” kasa motsi ta yi sai shi ne ya jawo ɗaya hannun nata ya saka mata kuɗin kafin ya je ya shige motarsa.Tun kafin ya isa ga get yake horne tuni kuwa an buɗe masa shi ya fita a tsiyace yana jin ina mai yarda ya karɓi soyayyar Hamida ba,sam ba ta jin magana.Ya ja dogon tsuki a fili ya furta ita kuma “waccan ta je ta zauna gidan makoki sai ka ce wata uwar mata”

Wani sashen zuciyarsa ya tambaye shi ‘ to ina ruwanka? ’
Sai kuma ya furzar da huci yana jin cewa to ina ruwan nasa ɗin kuwa,bai wani ɗauki lokaci ba ya isa can wurin aikinsu.Tun a bakin ƙofa sojawa ke ƙamewa suna sara masa har ya isa inda yake ajiye mota,wani soja ya zo da gudu ya buɗe masa ya fito yana cewa “Abraham yau kai ne haka da safe?”

“Eh muna training ne,sabbin sojawan da za a ɗauka aiki yau aka kawo su” Abraham ɗin ya basa amsa.

Ya ce “yau bakwai ga wata ko? Shaf na manta”

Abraham ya dube shi da mamaki wai yau Captain Ubaidullah ne ke cewa yayi mantuwa game da abin da ya shafi aiki.

“Aboki ko dai- ko dai?” Abraham ɗin ya faɗa .

Ubaid na jin ya kira shi da Aboki ya fahimci yanzu kuma rigar abota Abraham ɗin ya ɗauko ya yaɓa ba ta aiki ba.Hararar wasa yayi masa kafin ya ce “ko dai me?”

Abraham ya biyo bayansa yana mai cewa “ka fara soyayya mana”

Ubaid ya ce “da dama ban soyayya ne?”

“A'a Hamida dai na sonka,faɗa mini wace mai sa'a ce ta sace zuciyar santalelen tuzurun abokina?”

Ubaid ya saki murmushi yana mai sa key ya buɗe ofishinsa,a tare suka shiga ciki ko ina a gyare fesss sai ƙamshi yake.Har sai da suka zauna bai basa amsa ba, Abraham ya ce “in fa aka kalle ka da kyau za a gane ka faɗa so”

Ubaid ya jingina ga kujera yana ɗan juyawa haɗi da lumshe ido ,a nan take fuskar Suby ta faɗo masa.Cikin cool voice ya ce “in dai wannan alamomin su ne so to kenan na kamu da son Suwaah kenan?”

Abraham ya saki baki da hanci yana kallonsa kafin ya ce “ kuma Kirista ka samu? Ko irinmu ce sababin tuba?”

Ya buɗe idanunsa yana cewa “ko ɗaya musulma ce,a gidanmu ta zo” sai kuma ya kwashe duk wani abu da ya faru a gidan tun zuwan Suby.

Abraham ya ce “aboki ko dai sha'awarta ce kawai kake yi?”

Ya girgiza kai ya ce “inda sha'awa ce da ganin da na yi mata da towel ɗin ya jefa ni cikin yanayin nan,amma ni ban damu da zuwa wancan matakin na mu'amulantar juna ba.Kawai ni abin da nake so na dinga ganinta kullum a gidanmu”

“Ta ya za ta zauna gidanku kuwa sai in aurenta za ka yi”

“Hamidar fa?”
“Dama ai ba sonta kake yi ba,ni tun farko ban so ka amince mata ba.Ƙila duk shiri ne babu wata guba da ta sha saboda sonka,ta yi hakan ne don ka yarda”

“Don guba ta sha,kuma na amince mata ne duba da cewa ita ɗin ƙanwata ce in na tsane ta sam Daddy ba zai ji daɗi ba”

“To yanzu da ka samu Suwaah duk aurensu za ka yi ko ya?”

“Kenan son Suwaah ne nake yi? A'a kawai ƙauna ce” Ubaid ya faɗa don ƙaryata abokinsa dama ita kanta zuciyar tasa.
Sun yi hira sosai kafin kuma su soma aiki,sallah kawai ke tsayar da su sai abinci da suka tsaya suka ci wuraren ƙarfe biyu da rabi.



★Hassana tana cikin adaidaita tana tunanin maganar da suka yi da wannan matar,gefe guda kuma tunani taf zuciyarta na dalilin da yasa Mama Lantana ke son sai Suwaiba ta yi yawon banza.A haka ta isa gidan Kakarsu,ta buɗe ƙofa ta shiga .Ɗakin yayi ƙura wannan yasa ta share shi tasss sai kuma a lokacin ne ta kira Hussaina ita ma babu wani jimawa ta zo.Bayani ta yi mata dangane da magungunan kafin su shiga yin aiki da su kamar yadda ya ce ɗin.Hira suka soma yi suna jin daɗi nan da ɗan ƙanƙanen lokaci duk za su yi aure saboda wankin ƙwaƙwalwar da uwarsu ta yi musu na cewa malam Yawale na iya yin komai sai in bai yi maka aiki ba .

Lokacin da Kaka ta shigo kuwa ita ma da nata kalar maganin shirkar da ta karɓo.Cike da murna suke nuna jin daɗin gatan da ake yi musu,Kaka ta ce “yanzun nan za mu aiwatar da ɗaya aikin,kowacce za ta rufe zakara ɗaya da ransa kuna mai ambaton sunan samarinku,nan da wani sati duk za a kawo muku sadaki”


Da sauri Hassana ta ce “to Kaka in wanda kake so fa kuma ba ka san sunansa ba?”

“Ka ji wani sakarci ta ya za a yi mutum ya ƙi sanin sunan saurayinsa? ” Kaka ta faɗa cikin masifa tana wani juya bakinta da goro ya ɓata .

Cike da damuwa Hassana ta ce “to ni dai Kaka yanzu wani ne na gani ina so kuma ban san sunansa ba”

“In ke ba ki sani ba ai su aljanun da za su je aiwatar da aikin sun sansa ” cewar Kaka.

Hussaina ta ce "aljanu kuma?”

“I ko kin zata ni ce zan je na shiga tunanin samarin naku a hana su sukuni har sai sun kawo kuɗin?”

Hassana ta tuntsire da dariya tana mai cewa “Kaka rabu da ita don Allah ”

“Ku tashi mu fita kun san an ce ba a bori da sanyin hali” Kaka ta faɗa tare da jawo wata ƙatuwar ɓota,a nan tsakar gida kowacce ta gina ramenta kafin Kaka ta kwance baƙaƙen zakarun da duk aka yi musu rubutu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login