Showing 30001 words to 33000 words out of 55823 words

Chapter 11 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

50

marin da ya kifa mini shi ya hana ni ƙarasawa,ina jin lokacin da mai adaidaitar ke cewa “innalillahi Ubaidu? Wane ne shi?”

Mama Lantana ta basa amsa da “kwartonta ne”

Ganin mutane sun fara tsayawa kallo sai na nufi gida a guje ,Abba ya biyo ni ya ci gaba da dukana yana cewa “uban wane ne shi Ubaidun ? Aure aka ɗaura muku da shi? Karuwar gida kika zama ban sani ba?” yana yi mini tambayoyin ne yana dukana,Mama Lantana da mutumin da ban san ya suke da shi ba suna ƙara hura wutar rikicin.

Tun ina iya tsayuwa har na faɗi,irin dukan da Abba yayi mini ko kama ni yayi da namijin da idonsa to sai haka.

“Haba malam kana tsaye kana kallo ba za ka riƙe shi ba?” wani ladani ne na unguwarmu ya furta hakan yana mai riƙe Abba da yake ta yin huci.Ga gidanmu tuni mutane sun fara shigowa.

Mama Lantana na ganin haka don muzanta Suwaiba sai buɗe baki ta yi za ta maimaita abin da ta shirya na sharri na cewa ta kama ta da namiji.
“Malam Idi don ba ka san me ta yi ba wallahi....”


“In kika furta ko da kalmar A ce ban yafe miki ba,kuma wallahi akan aurenki” Abba ya furta yana jin ƙunci na luluɓe shi,tsit kake ji Mama Lantana an yi shiru sanin igiya ɗaya ta rage mata a cikin auren.

Malam idi ne duk ya fitar da kowa sannan ya turo ƙofa,sai kuma a lokacin Mamu ta fito tana tambayar abin da ke faruwa.
Cikin zafin rai Abba ya ce “ki tambayi ƴarki ga ta nan”

Mamu ta dube ni ta ce “Suwaiba lafiya?” ban bata amsa ba sai yunƙurawa da na yi dakyar na tashi zaune.Da rairafe na isa ɗakinmu,ina jin yadda Mama Lantana ke ta ƙoƙarin dole sai ta sanar da Mamu ɗin amma ta kasa ƙila tsoron furucin Abba ɗin.

Wuri guda na samu na cure,a haka Mamu ta shigo ta yi sallar magrib bayan ta gama ta tsura mini idanu.Wasu hawaye masu ɗumi suka sake keto idanuna suka zuba kan kumatuna,murya na ɗan rawa na ce “Mamu ban yi komai ba,Ubaidah ce ta zo ta sauke ni a mota amma dole Mama Lantana tana son juya maganar wai namiji ne”

“Shi kuma wanda kika kawo ɗazu har cikin ɗakin nan?” Abba ya jefo mini tambayar yana mai zuwa bakin ƙofa yayi tsaye.Cikin sauri na ce masa “wallahi Abba likita ne ya zo ne ya duba ƙafata da na ƙone”

“Likitan mata ko? Wanda bai duba mace sai kowa ya watse” wannan karon Mama Lantana ce ta faɗa daga nan kusan window.

Mamu ta dubi Abba ta ce “ni har yanzu ban fahimci meke faruwa ba”

“Za ki fahimta in na ɗaura mata aure aka kai ta can ƙauye” Abban ya faɗa cikin zafin rai yana ida shigowa.

“Aure kuma? Karatun nata fa?”

“Ai ta san da karatun ta soma kula Mazan banza,tun da auren take so ai gara na yi mata shi kafin ta jajiɓo mini abin kunya”

“A'a wallahi ba zan bari ka yi wa ƴata aure ba,sai ta gama karatunta tun da tana da ilimi” Mamu ta faɗa tana mai tashi tsaye,Mama Lantana ta yi wuf ta shigo tana cewa “kin ga ta'asar da ta yi mini ita da tantirin saurayinta tsinke suka tsira mini a hannu har sai da ya kusa katse mini jijiya ”

Mamu ta ce “duk ina a ina hakan ta faru?”

Wani kallo Mama Lantana ta yi mata kafin ta ce “wato Zainaba ƙaryata ni kike ƙoƙarin yin alhalin da idona na kama su suna masha'a? Yanzu ai kai gabanka shi Ubaidun da ta ce ya sauke ta a mota bayan sun dawo daga yawon ta zubar”


Wani irin kallo Mamu ta yi mini wanda ya saka zuciyata bugawa.Kai na shiga girgizawa,yayin da ita kuma Mama Lantana ke ta ƙarawa abin gishiri har da cewa ta ga lokacin da ya ɗora bakinsa kan nawa.Ido kawai Mamu ta rumtse yana saurare kafin can ta ce “ya isa haka Lantana,ya isa ban son jin komai”

Mama Lantana ta kalle ni tsakiyar ido kafin ta fice,Abba ya ce “yanzu ai kin ji abin da ta yi ko? To don haka ki fara shirin miƙa ta gidan miji“ yana gama faɗar haka ya fice.Mamu ma nan ta bar ni ta wuce can uwar ɗaka,duniyar ce na ji ta tsaya mini cak na rasa meke yi mini daɗi.


Har aka kira sallar isha'i ina nan zaune,har sai da dare yayi sosai sannan na je na cika bokiti da ruwa na yi wanka na zo na yi sallolina.Wayata kuwa kashe ta na yi,sai na haye kan kujera ina sauraren yadda cikina ke ƙugin yunwa amma ba shi ne damuwata ba .Mamu nake son gani a wane hali take? Wane hukunci ta yanke? Amma na kasa tafiya na gani,cikin wannan yanayi ne bacci ɓarawo ya ɗauke ni.Nan ne fa na soma yin mafarki marar daɗi,ga ni nan ina gudu shanu na bin bayana suna son cutar da ni.Duk gidan da na zo zan fake sai kuma na gansa a rufe,a ƙarshe dai kan bishiya na haye sai dai nan ma ban tsira ba baƙin kare ne ya zo yana haushi shi ma yana son ya cije ni sai girgizar bishiyar yake wacce a ƙarshe ta karye ina shirin faɗowa na tashi daga baccin ina buɗe idanu kuma Mamu na gani a tsaye ta saka ni a gaba tana kallo.

Na tashi na zauna ina mai kallonta,muna haɗa ido ta tafi ta shige ɗaki.Wani irin ciwo gaɓaina suke yi,ga kuma zazzaɓi wannan yasa na jawo ledar ɗazu na ɗauko jus da magani na sha.Ban ƙara komawa bacci ba sai bayan na yi sallar asuba ,muryar da na ji sama-sama ce yasa na yi saurin tashi.


Ammy ce ita da Ubaidah,gaishe ta na yi ta amsa cikin sakin fuska sai na dubi Udah ta ɗan sakar mini murmushi kafin ta ce “ya jikin?”

“Da sauƙi” na amsa,Mamu ta ce “tashi ki je ki yi wanka ga ruwa can na tafasa” cike da mamakin canzawar da ta yi na dube ta sai na ga kuwa fuskarta babu alamun damuwa.Haka na miƙe dakyar,Ubaidah ta take mini baya ita ce ta juye ruwan a bokiti ta ƙara mini da na pampo ta kai mini banɗaki.Soso da sabulu kawai na ɗauka na je na shiga,yayin da ita kuma ta tsaya bakin ƙofa har sai da na kammala na fito muka shiga tare nan muka tarar da Ammy na cewa “wallahi kamar yadda na faɗa miki wata mata ce bararoji da na yi wa aiki ta shaida mini haka,yanzu kuma kin ga maganin da ta bani ta ce a turara shi nan gidan da kuma can gidanmu”

“Suwaiba samo mana garwashi” cewar Mamu,haka na fita na ciko kasko da wuta.Ammy ta zuba maganin tana cewa mu fita da shi waje,haka kuwa aka yi Ubaidah na yin murmushi ta ce “in sha Allah komai ya zo ƙarshe,za su ji kuma za su gani ”

Daga can ɗaki muka soma jiyo tarin Mama Lantana,can kuma sai ga shi ta fito tana masifa.

“Tsafi kuma aka soma yi a cikin gidanmu?” ta faɗa tana taɓa hannuwa,ba mu kula ta ba haka muka ci gaba da yin hira hankali kwance.Sai muka ga ta koma ɗaki kafin kuma ta fito mayafi a kafaɗa ta fice.

“Ya Ubaid ya ce na gaishe ki da jiki” ta furta tana yi mini wani kallo sai na kasa cewa komai,ta ce “amma kin san kuna son junanku ko?”

“Me yasa yau ba ki je makaranta ba?” na tambaye ta don kawar da waccan maganar.Ta ɗan yamutsa fuska kafin ta ce “na san ba za ki je,to ni in na tafi me zan yi a can?”

Fitowar Ammy yasa duk muka yi shiru,sallama suka yi mana suka tafi .Duk a tunanina shikenan mun shirya ni da Mamu amma ko motarsu ba ta gusa daga ƙofar gidanmu ba Mamu ta canza fuska,duk sai na ji wani iri.Haka ta shige ɗaki ta bar ni nan tsaye,a sanyaye na je ni ma na shiga na zauna kan kujera ina kallon tarin magungunan da ke gabanta.


“Ki kira mini Sulaimanu” ta faɗa ba tare da ta dube ni ba,haka na ɗauko waya na kira shi.Amma har ta tsinke bai ɗaga ba, sai a kira na biyu ne ya ɗauka da sauri na miƙawa Mamu.

Ina gefe ina sauraren yadda take amsa gaisuwar da yake yi masa kafin ta ce “an tsayar da ranar ɗaurin aurenku nan da kwana uku,wato juma'ar nan.Zan aiko maka da maganin da za ka dinga yin wanka da kuma wanda za ka sha.Babu buƙatar sai ka zo don dai iya ɗaurin auren za a yi,bikin kuma sai nan da wata uku lokacin Daddynsu Ubaidar ya dawo daga Ingila ”

Wani irin sanyi ne ya ratsa mini zuciya,ga dai bikin zuwa amma babu zanen ɗaurawa.Ina son fitar da tsantsar murnata amma babu hali,ban ji shi me Sulaimanun ya ce ba amma sai na ji Mamu na cewa “kar ka faɗawa kowa wannan maganar ta zama sirri,saboda ka ga yadda lamarin auren ya kasance ”

Daga haka suka yi sallama ta kashe tana jan ajiyar zuciya,ta dube ni tana mai cewa “da zarar an gama zancen auren nan in sha Allah sai ki haɗa kayanki ki koma can ƙauye wurin Yadikko,in komai ya lafa sai ki dawo.Saboda muddin Abbanku na ganinki ba zai fasa aura miki duk wanda ya rakito ba,rayuwa dai taki ce kin kuma zaɓi wacce kike so”

“Mamu yanzu ke kin yarda zan iya yin abin da ba daidai ba?” na faɗa ina hawaye.
“Eh to ta ya ba zan yarda ba alhalin Lantana ta ce ta gani da idonta,inda ma a ce Abbanku ne da sai na ƙaryata na ce ko ƙiyayyar da yake yi mini ce ta shafe ki”

A abin da na fahimta duk duniyar nan babu wacce Mamu ta bai wa dukkan yardarta irin Mama Lantana, wannan yasa ban ma ba kaina wahala ba wurin son wanke kaina daga zargin da aka yi mini.

Daga can tsakar gida aka rangaɗa sallama,gabana ya faɗi don kuwa na gane wacce ke yin sallamar.Muryar Kaka ce mahaifiyar Mama Lantana,matar da tsabar mugunta inuwarta ma ba kowane lokaci take binta ba.
Jikin Mamu har wani rawa yake wurin amsa sallamar kafin ta miƙe ta fita,ta window na leƙa nan na hango Mamu ta zube gwiwa har ƙasa tana gaishe da Kaka,ga Hassana da Hussaina a tsaye gefenta su ko gaishe ta ba su yi ba.

Bayan sun gama gaisawar ne su suka wuce ɗakin Mama Lantana ita kuma ta dawo namu.Wayata na jawo na kunna tare da turawa Ubaidah saƙon congratulations,sai ta turo mini emoji na alamun jin kunya hakan ya wanzar mini da murmushi.

Mamu ta karɓe wayar daga hannuna tana mai cewa “mene ne ya faɗa miki kike murmushi? To ba zan sake baki wayar nan ba sai ranar da za ki je gun Yadikko” ƙuuu ta shige uwar ɗaka.Ni kam abin mamaki ma ya bani,fita na yi can ƙofar gida na yi zaune.
Babu jimawa kuwa sai ga Mama Lantana,mugun kallo ta yi mini tare da shigewa cikin gida.Ni kuwa sanyi itaciyar da ke kaɗawa shi yayi mini mugun daɗi,haka na yi zamana fiye da awa uku kafin na tashi na shiga gida.A zaune na tarar da su dukkansu har da Mamu suna cin abinci,ga uban nama cike da faranti.A gaban idona Mamu ta yi loma da ƙatuwar tsoka,buta na ɗauka na shiga banɗaki ina jin Mama Lantana na ce “ni kam Zainaba me surukarmu ta zo yi yau tun da safe? Allah yasa dai ba zancen Suwaiba na bin maza kika yi mata ba shi ne ta kasa haƙuri ta zo?”

Ido na rumtse,amma takaici bai ida rufe ni ba sai da na ji Mamu ta saki baki tana cewa “dama zancen auren Sulaimanu ne ta ce tun da ta ga abin ya ƙi ci ya ƙi cinye wa ...” da wani irin sauri na fito na ce “Mamuuu?” duk sai suka juyo suna kallona.

“Me ne?” Mamun ta tambaye ni,na ce “zo ki gani”

“Me zan gani gani a banɗakin kuma?” Mamu tambaya rai ɓace,inda na yi farin ciki shi ne zuwan Goggo Saude wato ƴar uwar Mamu ce nan garin take aure ita ma.Murnar ganinta ya saka Mamu farin ciki tana mai cire hannunta cikin abincin ta miƙe tana cewa "wuce mana”

Wata sanyayyar ajiyar zuciya na sauke,Mama Lantana ita da Kaka kamar za su cinye ni da ido,wani abin mamaki ma har da ƴaƴan.

Banza na yi da su na wuce can cikin shamaki na yi zaune tare da cin alwashin duk wuya ba zan bari Mamu ta fallasa zancen auren Yaya Sulaimanu ba ne gun maƙiyanta na ɓoye.Wannan yasa bayan fitowar Goggo Saude ma ban bari sun keɓe da ita ba,tamkar inuwa haka nake bin Mamu sam ban damu da mugun kallon da take yi mini ba.A haka har dare yayi,nan fa na ga jarabawa yadda ciwon ciki ya tisa Mamu a gaba.Allah ya ceto ni na yi saurin ɗauko haska, wannan yasa na ɗauko nonon raƙumin da Uncle Suhail ya bani na miƙa mata ina cewa “ga magani ki sha Mamu ” karɓa ta yi saboda uwar wuyar da take sha yasa ta mayar da gushinta gefe.Duk da ba ta wani sha dayawa ba amma ta samu sassauci kafin kuma wani lokaci ta fita a guje can tsakar gida ta soma kelaya amai .

Fita na yi da sauri na tsaya kusa da ita, Abba da shigowarsa kenan ya hasko fitilar hannunsa yana mai cewa “kin ɗauko mana abin kunya ko?” wato abin da na fahimta yayi dubin ni ce ke yin aman,ita kuwa kwalba uwar sharri har ta fito .


“Abbansu ƙara hasko mini nan na gani mene ne nake gani?” Mamu ta faɗa,Abba ya haska ƙasa sai ga shi gudan tulun tsutsotsi na ta yawo a ƙasa,wani irin tsoro na ji ya kama ni yayin da Abba ke cewa “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Zainaba aman tsutsotsi ne kike yi? Me kika ci haka?”

Mama Lantana na kalla wacce jikinta yayi sanyi,ni kuwa hamdala na yi kafin na ɗebo ruwa a buta na miƙa wa Mamu ta wanke bakinta da jikinta.Ƙasa na ɗebo na sa abin kwasar shara na kwashe aman na kai can waje na zubar.Ko da na dawo tuni kowa ya kama gabansa,da na shiga ɗaki ma tuni Mamu ta samu bacci.

Washegari ya kama ranar Laraba ,saura kwana biyu ɗaurin aurensu yaya Sulaimanu.Tun safe Mama Lantana ta zo duba Mamu tare da bugun cikinta sai so take yi ta tambaye ta amma na ƙi barin ta ji ba'asi don kuwa hatta banɗaki in Mamu za ta je haka nake bin bayanta.Hakan ya ci gaba da faruwa har daren juma'a wanda sam Mamu ta kasa yin bacci,cikin tsakiyar dare na ji ta buɗe ɗaki ta fita.Ta window na leƙa,sai na hango Mama Lantana zaune a kan turmi kamar mai jiran wani abu.Babu shiri na fito sai na laɓe ban ƙarasa wurinsu ba.

“Dama gobe ne ake son ɗaura auren Sulaimanu ina ta son faɗa miki ban samu hali ba” na ji Mamu ta faɗa tana daga tsaye a bayan Mama Lantana,tana faɗa kuma ta juyo ta koma ɗaki yayin da kuma na ga Mama Lantana ta kafe bayan Mamu da idanunta irin na mage can kuma ta tashi ta nufi ɓangarenta.Sam ban koma ɗaki ba sai da na ɗauro alwala na shiga na soma jera sallah ,yau a tsaye ma nake yi don addu'ar ta yi saurin shiga duk da kuwa ina jin zafi a ƙafata.

A can ɓangaren Mama Lantana kuwa kamar za ta ƙone haka take ji,dakyar ta iya barin gari ya waye sannan ta je wurin Malam Yawale.

Tana shaida masa zancen auren shi ma yayi matuƙar mamaki sai ya soma yin bincike,nan take zufa ta karyo masa ya dubi Mama Lantana ya ce “sai dai fa ki yi haƙuri,akwai wata addu'a da ta yi wa aljanun da ke kula da wannan lamarin auren ƙunar baƙin wake.Sam ban ma lura ba,don kusan kwana uku kenan da komai ya caɓe”

“Addu'a kuma malam? Dama akwai wata addu'a da ta fi ta ƙarfin ta malamai?” Mama Lantana ta faɗa cikin damuwa.

Malam Yawale ya ce “addu'ar da za a yi wa mutum ba tare da saninsa ba tana da matuƙar tasiri, musamman ma in ta fito daga zuciyar mai tsarki”

“Wato har yanzu Mamu na yi wa Sulaimanu addu'a ita ga uwa?”

“Wannan lamari ba daga ɓangaren Sulaimanu yake ba,addu'a ce daga Suwaiba in ba ki manta ba tun farkon zuwanki a nan na shaida miki tana da taurari masu kyau sannan imaninta a tsaye yake daram babu wata tangarɗa wannan dalilin ne ma yasa aiki a kanta yake da matuƙar wahala kina dai ganin hatta jinnun da aka tura mata na tsawon shekaru shidda har yanzu babu wani tasiri da suke yi a kanta.Yanzu ma a binciken da na yi kamar tana tsaye tsayin daka tana faɗa da duk mai son hana auren nan ta hanyar yin addu'a ”

Wani ɗan ƙaramin ihu Mama Lantana ta yi kafin ta ce “ina ga kashe Suwaiba kawai zan yi don na huta da baƙin cikinta,kana ji yanzu ka ƙara loda mata wani sharrin ina so a yawon bin mazan ta yi ciki ta yadda babu wanda zai ganinsa ballantana a zubar da shi sai dai kawai mu ji kukan jariri”

Malam Yawale ya dubi Mama Lantana da kyau kafin ya ce “wai ni kam wane laifi ne Suwaibar nan ta yi miki? Na ga yadda kika tsane ta ko ita Zainabar da kike kishi da ita albarka”

“Ina ruwanka ? Kai dai aiki na saka ka yi na biya ka,wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na tozarta Suwaiba a idon duniya”

Bai ƙara ce mata komai ba,sai nonon akuya da ya ɗauko yayi tsare-tsarensa ya ɗauko rariyar nan da yayi aiki da ita ranar nan ya tace nonon a wata kwalba kafin ya ce “wannan ki zubar da shi a watsar da shi a ƙofar gida,yadda ya zube haka duk wani mutumcinta zai zube,wannan kuma ki jefa a masai ” jikinta har rawa yake yi ta karɓa,da za ta fita ya ce “wannan aikin shi ne top wurin son lalatar da rayuwar ƴa mace,domin a gaban kowa ma za ta iya yin tarayya da namiji haka kuma za ta iya buɗa baki ma ta yi zantukan banza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login